Showing 144001 words to 147000 words out of 268365 words

Chapter 49 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54131

samu wannan k’aton wayar? Waya baki?”
“Wanne wai?” ta tambaya cike da tsiya. “Awww Iphone d’ina? Hot baby ya siya min wallahi, yayi kyau ko?”
“Hot baby wa kenan?” ta kuma tambaya cike da rashin fahimta.
“Wa kuwa inba Shettima darling ba, business nasa se bunk’asa yake wallahi.”
Dariya sosai Fannah ta sheqe da dan tasan ina yake samun kud’in daya ke kashe mata. “Shi business d’in kenan?”
“Eh mana abin hassada ne kuma?”
“A’a babyn Shettima Allah barku tare ni taho ki tayani in shirya atamfofina gu d’aya dasu zan koma.” Afrah ta bud’e baki zata kuma wani zancen Fannah ta katse ta “a’a banason bayani muje.” Suna hira suna shirya kayakin har suka gama.


_11:30AM_


Daidai nan Anas ya dawo d’aukanta beso sake shiga ba se kawai ya kira ta ta waya alokacin wayar tata na d’akinsu itako tana d’akin Baba se hira suke bazawa kamar ance ta mik’e tace bari taje d’aki. Tana shiga taji rurin wayarta nan ta d’aga tare da duban waye. ‘Anas’ taga tubuce kai. K’in picking tayi dan battason sake komawa hotel nasun nan its so boring. Se a karo na biyu ta d’aga nanma seda ya kusa tsinkewa.
“Kifito I’m waiting for you.”
“Anas mana please, bamu had’u da Aiman bafa, tana school se 1:00AM zata dawo kaji? In jira?”
“Banji ba kuma baraki jira ba, Fannah kifito don’t let me repeat myself.” Karap ya katse wayar, tsuka taja. Aiko ya fad’a kunnen Mami. “Keda waye ne?”
“Erm.. Ermm...” kafin ta had’o k’arya Mami tace, “keda Anas ko? Fannah tun ba’ayi nisa ba kin soma masa rashin kunya, iyyeh? Me dalili?”
“Mami waifa har ya dawo infito mu tafi.” ta fad’a tana turo baki.
“Toh se meh? Out!” ta nuna mata k’ofa. Dake kafad’a tayi. “Fannah zan sab’a miki fa!” Haka kamar wacce zatayi kuka taja akwatinta ta fice ko sauraron Afrah batai ba. Bayan fitarta ta bud’e gidan baya tasa akwatin yana kallonta bece komai ba. Tana shiga ya kunna motar ba wanda yace ma wani ko uffan. Bayan isarsu gida suka gaggaisa, Ummie kamar ta cinye Fannah. Besamu ya had’u da Amal ba dake tana school haka Shettima ma.


“Kuyi sauri ku gama gaisawan ku zan d’au abu cikin d’akina ne yanzu mukoma.”
“Kai Babana daman ba yini kuka zo mana ba?”
“Yini? A’a fa Ummie gaisuwan minti biyar ne kacal.” Yana kaiwa nan yashige d’akinsa. “Oh! Fannah kinga halin mijin naki ko? Yafiye rowa dayawa.” Murmushi cike da kunya ta saki tana kare fuskarta.


Bayan shigan Anas d’akinsa ya nufa wajen safe dan ciro kud’ad’ensa wanda ze buk’ata to his suprise yaga an kwashe kusan rabin kud’ad’en. Dubawa dakyau ya kuma yi yaga eh fa kud’in nasa ne babu to waye ya masa wannan d’anyen aiki? Rufewa yayi tare da dawo wa cikin parlon “Ummie” ya kira sunanta.
“Kin d’au abu cikin d’akina?”
“Kamar ya abu kuma Anas?”
“I mean my money morethan half of it are gone.”
“Wai! Wai! Ka duba dakyau kuwa?”
“Eh jeki duba kiga” nan ta mik’e ta nufa d’akin nasa. Ganin haka Fannah ta b’arke da dariya har rufe bakinta take, ashe nan ne business na Shettima yake bunk’asa tunda Anas bai gida. Kallon ta Anas yake ya rasa dalilin dariyar tata. Ummie tagama dube dubenta ba kud’ad’en, ko kad’an Anas be kawo aransa Shettima neba.


*****
“Bari in yaran suka dawo zan tambayesu halan sunkai wani wajen daban.” Cewar Ummie dake tsaye bakin k’ofa ayayinda Anas ke k’ok’arin kunna mota. “Okay in Abuu ya dawo ki gaishe min shi.”
“Toh, amaryar mu semun shigo ko? Mungode.”
“Yawwa Ummie se anjima” Fannah ta amsata. Acikin motan ne Anas ya juyo yana kallon Fannah. “Dariyan me kuke d’azu?”
“Da yaushe?” Ta tambaya pretending as if bata gano inda ya dosa ba.
“Fannah banaso answer me.”
“Babu kawai daga yin dariya yazama matsala.”
“Bari zakiyi mafarki ma ai yau zamuga waze zauna dake, infact seperate d’aki ma zan kama.” Jin haka tace, “a’a zan fad’a maka.”
“Good ina jinki.”
“All I know is business na Shettima ya bunk’asa.”
“Kamar ya kenan?” ya katse ta.
“Oho nifa kar azo ace ina had’a munafirci.”
“Just tell me.”
“Promise barakayi reacting akai ba?”
“I promise.”
“Nide naga Afrah da 6s plus kuma tace Shettima ya siya mata.”
“6s plus?” Ya tambaya tare da juyowa yana kallon ta cike da mamaki.
“Anas kalli gabanka please kar ka bugamu ko mu fad’a rami.”
“Wato da kud'i na aka sai wa Afrah 6s plus d’in koh? Da kud’in mijinki shine kike dariya. Da kyau zamu had’u dashi.”
“Toh me zanyi? Shida kud’in yayansa. Plus a’a Mr. Fauzi kaga you promised you won’t react.”
“So kike inyi shiru in zuba masa ido? Ya kwashe morethan half of kud’in dake cikin safe d’ina fa.”
“Hak’uri zakayi he is in love kuma dan baida aikinyi ne, let them be please, kaji Mr. Fauzi.”
“You really wants to annoy me ko Miss Aleeyu?”
“A’a Anas toh, nide kar ka masa magana.” Chan k’asa k’asa yace, “barin masa magana ba kamar yadda barin canza masa motar sa ba kuwa”
“Yafi amman dekam karka masa magana.” tache.




*© miemiebee*
[12:56, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
5⃣9⃣








Chicken chop ya wuce dasu dan siyo musu roasted chicken. Bayan yayi parking yafito ya bud’e mata k’ofarta, kamar d’azu haka ya matso ta jikinsa. “Anas yanzu kama hannun ma kadena? Se haka?” Ta tambaya a nitse.
“Eh na dena nan gaba ma I think d’aukan ki zan soma.” Bata sake che dashi k’ala ba suka shiga ciki d’aya daga cikin kujerun ya ja mata bayan ta zauna ya nufa wajen siyan. Shiru Fannah ta zauna tana ‘yan kalle-kalle kafin ta hankara ta jiyo sallamar sabon murya akanta. Data d’ago kai taga matashi ne jik’a a jini ko suyi shekaru d’aya da Anas koya girmi Anas da kad’an.


“Wa’alaikumus-salam” ta amsa sa d’auke da murmushi a fuskarta. “May I sit?” ya buk’ata in a calm way.
“Yes sure.” Nan yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna. “Koban tambaya bama nasan bakida aure ko?”
Murmushi ta saki tare da girgiza kai ta bud’e baki zatayi magana kawai taga Anas from nowhere ya cukumo kolar rigar bawan Allah yakai masa punch a fuska take gefen bakinsa ya fashe. A firgice ta mik’e “Ya Salam! Anas meh hakan please? Taya zaka hau dukansa be maka komai ba, ka sake shi.”
“Bemin komai ba? Are you kidding me Fannah?” hannun mutumin ya murd’a ta bayansa cike da mugunta wanda har yasa mutumin sakar da k’ara.
Cike da azaba yace, “hey who are you? And meh na maka? Let me go will you? Taya zakazo ka kamani in public kana murd’a min hannu.”
“Awww tambaya ma kake meka min?”
“Anas everybody is starring at us dan Allah ka sake shi, its embarrassing” Fannah ta katsesa cikin salon da bareji haushi ba.

Juyawa yayi ya kalli jami’un wajen. “Mind your own god damn businesses! Now!” yace dasu a tsawace nan kowa yacigba da harkan gabansa.
“Barin maka warning, ko a lahira kaga Fannah karkayi yunk’urin mata magana ‘cause it might be the end of you, ba’a mutuwa a lahira but when it comes to toasting my wife I could kill you. Do you get me?” Ya sake murd’a wa mutumin hannu. Cike da azaba da mamaki mutumin ya d’ago kai yana kallon Fannah data tsure itama.
“Why didn’t you tell me you were married?” Abinda yace kenan. Wani irin gulity concious ne ya kama Fannah.

“You mean you didn’t know?” Anas ya tambaya cike da mamaki shima.
“Bawan Allah a tunaninka haka kawai zan hau toasting mace me aure ne? Seda na tambayeta ko matar aure ce ita sekuma ta min shiru. Da shigowa na garin nan sati kenan I know barely no one.” Take Anas ya sake sa “I’m so sorry please kaji? Accept my apologies.”
Seda mutumin ya k’are masa kallo sannan yace, “accepted amman nan gaba don’t just jump into conclussion” yana kaiwa nan ya waiwayo ya kalli Fannah tare da kad’a kai sannan ya fice. Hannunta Anas ya finciko cike da azaba ita kanta tasan she is in trouble ko d’ago kai taga ya yanayin fuskarsa take ma batai ba a iya sanin ta fuskarsa da idanunsa zasu iya fin jan kala yin ja saboda daga yadda yake nishi za’a iya kwatanta b’acin ransa.


K’ara ta saki tana k’ok’ari k’watan hannun nata. Bakin k’ofa yajata. “Sir your order is ready” ko jin mutumin beyi ba yajata suka fice daidai motarsa yayi wulli da ita kad’an ya rage bata fad’i ba. “Get in” yace cike da b’acin rai hawaye tasoma wanda batasan lokacin ba, a hankali ta bud’e k’ofar ta shiga ya kunna mota. Koda suka isa hotel d’in fitowa yayi tsaye yana jirarta bayan tafito yakuma kama hannunta irin na d’azu.


“Anas dan Allah ka saken da zafi.” Ko sauraronta beyi ba ahaka har suka haura d’akinsu. Banging k’ofar yayi da k’arfi tare da bugata jikin k’ofar. Ba abinda take banda kuka ba sauti dakuma b’ari. Dududu ratan dake tsakanin fuskarsa da nata befi inchi biyu zuwa uku ba. Wani irin kallo yake mata tsabagen yadda ransa ya b’aci yama rasa me ze mata. Cikin wani irin tsawacaccen murya yace, “bakida hankali neh?! Kina matar aure zaki zauna kusa da wani? For crying out loud harda k’in cemasa you are a married woman? Huh?!” Kai kawai take girgiza masa hawaye nabin k’uncinta.

“I’m talking you!” ya fad’a a tsawace tare da sake buga jikin k’ofar. B’ari take harwani sama sama nishinta yake, “Anas dan Allah kayi hak’uri, I’m sorry please.”
“You still haven’t answered my question. Why Fannah? Answer me!” Cikin sautin kuka tace, “Anas kaifa da bakinka ka fad’amin koda anyi bikin you can see any girl you want tunda contract marriage ne shine nima naga ai bawani abu ciki dan mutumin d’azu yamin magana.”
“Damn it!” Ya sake buga k’ofar. “Damn everything Fannah! What if na fad’a miki I don’t mean it, tunda akayi bikin kinga naje gun wata ko wata tazo min ne? I don’t mean any of those words kawai na fad’a ne.” Ya k’are maganar yana kallon k’asa.
“Anas I’m sorry dan Allah kayi hak’uri.”
“No Fannah ke kanki kinsan what you did was wrong, how could you not respect our marriage?” Yana kaiwa nan ya juya binsa tayi, tayi hugging nasa ta baya tana meh hanasa koda motsi. “Anas I’m sorry dan Allah kayi hak’uri I thought you meant what you said shiyasa, am sorry please.” Har a yanzu baijin he can forgive her. Hannunsa yasa ya raba jikinsa da nata. “Anas please...” Ta rok’esa se ambaliya hawaye ke a fuskarta.


Kayan jikinsa ya rage yabar shorts da vest zalla tare da hayewa kan couch ya kwanta. Kuka take har yanzu ba sauti ganin ba mahalicci se Allah ta mik’e ta nufa bayi, fuskarta ta wanke sannan tafito ta juye masa coffeen sa cikin cup tare da kai masa. Ganin haka ya juya mata baya. “Anas kayi hak’uri kasha please.” Banza da ita yayi. “Anas please, I said I’m sorry be isa ba?” Nanma banza da itan yayi.
“Anas koda contract marriage ne tsakanin mu you are still my husband kadena fushi dani banasan tsinuwan mala’ikun rahma please talk to me.” Nanne yayi magana.
“Ince miki meh?”
“Anas me zan maka ka yafemin please, stop being mad.” Juyowa yayi yana kallon yadda take ta zubda hawaye sekuma ta basa tausayi. Coffeen ya amsa ya kurb’e tare da miyar mata da cup d’in. “Nasha shikenan?”
“Anas bakace ka hak’ura ba.” Shiru yayi tamkar bejita ba. “Anas mana...”
“Naji, bacci nakeji yanzu allow me, will you?”
“To katashi ka haura gadon ka kwanta, kaji?” Shiru bece komai ba. Hannu tasa ta jijjik’a sa bece da ita komai ya mik’e ya nufa gadon ya kwanta. Mayafinta ta d’auka tayi bakin k’ofa. “Ina zakije?” Ya tambayeta.
“Akwatina zan d’auko.”
“Wait.” Nan ya d’au wayarsa yakira wani in less than 2 minutes aka kawo mata jakar tata. Amsa tayi ta bud’e ta soma jera wanda takeso da wanda battaso tun Anas yana kallonta har yayi bacci. Bayan ta gama taga still da saura Azahar. Kan couch d’in ta nufa ta mik’e nan itama tayi baccin.


*****


Sakamakon ihun da Anas ya tsala ne ya farkar da ita daga bacci a firgice. Ganinsa tayi zaune kan gadon ya had’a wani irin gumi da sauri ta nufesa. “Anas” ta kira sunansa, beko amsata ba se girgiza kai dayake. Remote na AC ta d’aga ta k’ara k’arfin. “Anas are you okay?” Ta tambaya a nitse. Nan ma be amsata ba. Tissue ta zaro tana goge masa gumin nasa bayan data gama ta yasar sannan ta dawo ta zauna kusa dashi. Hannunsa ta d’aga tayi interwining yatunsu su a hankali.
“Anas mafarki kayi?” Kai ya gyad’a mata.
“Want to talk about it?” Kai ya girgiza.
“Okay toh keep calm kaji, I’m here if you need someone.” Chan k’asa k’asa yache, “yarinyan ta dawo.”
“Yarinya kuma?” Ta tambaya cike da rashin fahimta. “Wace yarinya kenan Anas?”
“Yarinya from the incident. *_TANA TARE DA NI..._* haka tacemin kuma nima I can feel it. *_TANA TARE DA NI..._* Ina take?” Ya d’ago idanunsa da basu gama dawowa asalin colournsu ba yana kallonta.

“Anas bansan wace yarinya kake magana ba, its just a dream kaji? Inma wata yarinyar kake nema sooner or later zata bayyana maka, kaji?” Kai ya gyad’a tare da mik’ewa kan gadon, kansa ya aza akan cinyoyinta masu uban laushi da tsoka daidai ya kwanta. Bata ce masa komai ba ya daidaita position na kansa akanta yana kallon d’ayan direction d’in. Fannah kad’ai tasan irin electric sparks da suke going mata ajiki. Wannan ne karo na farko dawani d’a na miji ke kwanciya mata a cinya.
“Fannah kina ganin zata yafemin abinda na mata?” Yace da ita cikin wani irin salo. Shiru tayi danko batasan ina ya dosa ba.
“Wa ce kenan?” Ta tambaya.
“Yarinyar, kina ganin she can forgive me despite abinda na mata?”
“Me kama ta Anas?” ta tambaya cike da neman k’arin bayani.
“Its horrible I can’t say it, na cuce ta nasani shiyasa koda in mun had’u tace sena aureta zata yafemin zan aureta, I will do it” Bugun zuciyarta taji ya k’aru, meh Anas yana wannan yarinyar dayake fad’in ze aure ta na hak’ik’a? Shida bayason aure koda wasa yake cewa zeyi toh mesa? Kamarya ya cuce ta kuma? Toh kode ciki ya mata ya gudu? kai a’a Anas beyi kalan me bin mata ba har ace yama wata ciki, toh me ya mata? Shi ya tsamota daga duniyar tunanin data wula.


“Fannah kinaga zata yafemin in na bata labari na?” Hannu tasa cikin silky gashin kansa me uban tsayi da cika daidai ba kamar nata ba. Shafa gashin nasa take a hankali tana curling wasu a yatsunta. “I’m sure zata yafe maka Anas muddin kayi nadaman koma mene ka mata, dakuma in ta sake jin labarinka. Zata yafe maka kaji?” Kai ya gyad’a a hankali. Daga nan be sake cewa komai ba.


Bayan like 10 minutes takira sunansa shiru taji be amsa ba. Data lek’a fuskarsa setaga har yayi bacci no wonder taji ya k’ara nauyi. Dukda cewar idanun sa a rufe suke se ji take a jikinta ta tab’a sanin Anas a wani gun to a ina ne? Hannu tasa ta rufe fuskarsa tabar daidai wajen idanun nasa, nan kamannin nasa ya sake fito mata sede ta rasa gane a ina ta sansa. Maybe me kama dashi na sani ai wannan girman London yayi nikuma ban tab’a zuwa chan ba, theres no way zamu tab’a had’uwa. Ta tunatar da kanta a zuci.
D’an k’ara ta sakar sakamakon zogin da cinyarta na dama ke mata ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login