Showing 120001 words to 123000 words out of 268365 words
Chapter 41 - Tana Tare da ni complete book document .txt
ba tunda ba ganinka take ba. Nan ya bud’e ya sake kai baki nan ma yakasa sha. “Oh God! NO!!!” Toilet ya nufa ya juye a bathroom yayi flushing haka yayi da d’ayan ma, sannan ya koma ya kwanta. Ina fa, bacci ya gagara, mafarkin Ummimi se hunting nasa yake.
Wayarsa ya d’ago daga kan side drawer yaga k’arfe 1:20AM. Miyarwa yayi ya sake kwanciya daga ya rufe ido se mafarkin Ummimi ya dawo daga inda ya tsaya. Yayi hakan sau uku kawai ya hak’ura da baccin inda giyansa na nan da yana sha nan da ‘yan mintuna zeyi everlasting bacci, duk laifin Fannah ne ita tasa sa yayi making promise kan bare sake shaye shaye ba, yanzu haka ita tana bacci shi yana nan yana wahala sede ayi 2-0. Wayarsa ya sake d’agowa yaga 1:40AM kan lambarta yakai ya danna mata kira.
****
Fannah na cikin baccinta me dad’in bala’i tajiyo ringing na wayarta ita tama rasa meya hanata sawa a silent har yagama ringing bata d’aga ba se a karo na biyu. Cikin bacci ta d’aga “hello” dan ko duba wake kira batai ba.
“Miss Aleeyu” ya kira sunanta ai take ta nemi baccin nata ta rasa.
“Mr. Fauzi”,takira sunan sa cike da mamaki. “Me ya faru da daren nan?” Torchi ta haska taga k’arfe d’aya ne.
“I can’t sleep” yace da ita sincerely.
“Toh Mr. Fauzi nikuma me zan maka?”
“Nima bansani ba all I know is that is your fault.” Hamma ta saki tare da zaro idanu “nikuma Sir? Mena maka?”
“You made me promised to you that barin sake shan wani abu ba, I’m badly in need of that now kuma na kasa sha, because I can’t break my promise to you!” ya fad’a ad’an tsawace.
“Is okay calm down Mr. Fauzi, calm down okay? Karka sha please, zaka iya tashi zuwa kitchen?” ta tambayesa a hankali cikin murya me sanyi.
“Yes” yace mata.
“Good you are going to make your coffee, trust me in kasha you’ll go back to sleep peacefully but please kar ka sha wancan abun you promised, kaji Mr. Fauzi?”
“Naji” yace tare da mik’ewa zuwa kitchen d’in. Haka tana fad’a masa directions d’in yana bi har ya had’a sede koda ya tab’a be kai nata dad’i ba.
“It didn’t work Miss Aleeyu, ni barinsha ba.”
“Yi hak’uri kasha, first thing gobe I’ll come to your office in had’a maka kaji? Yi hak’uri kasha wannan d’in please will you do that for me?” Shiru yayi bece komai ba “please” ta rok’esa.
“Okay” ya fad’a can k’asa k’asa.
“Sleep good okay? Gobe da safe zan zo in had’a maka coffeen kaji?”
“Naji” yace karap ta katse wayar. Da k’yar ya iya shanye rabin coffeen. Kasancewar ba Fannah ce ta had’a masa ba, sam ya kasa bacci amman dan yadda muryarta ke yawo masa a kai besan lokacin daya koma bacci ba.
*© miemiebee*
beeenovels.mywapblog.com
[12:53, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
5⃣1⃣
Nishi take sosai tana hak’i a yayinda zuciyarta ke bugawa d’ari bisa d’ari, ko damuwa ta kewayo dan ganin ya cikin gidansu Anas yake bataiba, abinda tasani kawai gidan nada kyau, bayan ta tabbata dawakan sun wuce tagwada bud’e k’ofar daidai lokacin Shettima ke dawowa daga yawonsa shima a tare suka tura k’ofar sede ya rigata. Suna had’a ido ya sakar mata da murmushi, murmushin ta mayar masa sede daga yadda take abu yagano tana cikin hanzari.
“Fannah!”
“Na’am Shettima.” Ta amsa.
“Yau kece a gidan namu?” Ya tambaya yana mata murmushi.
“A’a dawakai suka biyo ni, ina jiran Anas ne barin wuce please.” Ta fad’a cikin hanzari duk hankalinta ba’a kwance ba.
“Fannah lafiya?” ya tambaya tare da sake blocking nata.
“Shettima please ka matsa min in fice, kar Anas yaganni anan.”
“Ya Anas? Shi yace karki shigo ne?” Shiru ta masa bata amsa ba hakan ya tabbatar masa da ‘eh’ ne amsar. “Karki kula sa haka yake shigo please kinji? Amal tayi missing naki.”
“A’a Shettima, wataran zan dawo amman yanzu ka matsa min in fice please.” ta fad’a tana duba bayanta gudun kar Mr. Fauzi yaganta.
“Haba mana Fannah yanzu baraki shigo ba? Yi hak’uri, Ummie naciki kinga seku gaisa kinji ko bahaka ba?” Kai ta girgiza masa tana tuna irin warning da Mr. Fauzi ya mata. “A’a I promise next time amman yanzu wallahi nashiga Anas ze sab’a min.”
“Trust me ba abinda ze miki shi Ya Anas haka yake, sharesa please kishigo.” Nan ma kai ta kad’a “please mana Fannah sena had’aki da Allah ne? Kishigo please.”
“Shettima wallahi Anas yace kar in shiga, kabari next time.” Kafad’a ya buga “ai wallahi sekin shiga Fannah, mubar musu kawai kinji? Bismillah.”
“Shettima please...” Kai ya girgiza mata ganin ba mahalicci se Allah tace, “Shettima inyamin masifa fah? Seda yace min kar inshiga fa.”
“Ai sharesa zakiyi, haka yake mushiga please.” A sanyaye tabi bayansa duk tsoro yabi ya ratsa ta tunanin wani erin masifa zata sha wurin Mr. Fauzi kawai take, sun kusa da bakin k’ofar ganin Shettima bai ganinta taja da baya zata gudu aiko tuni yaganta ta jikin mirron window karap ya cafko abayanta. “Fannah aini ba’a min wayo, mushiga kawai.”
“Shettima kayi hak’uri please kabarni in tafi.”
“Mushiga kawai Fannarmu.” Haka suka shiga cikin katafaren parlour’n su, dake d’auke da kayan tafiyar da imanin mutum a kowani second. Zaune ta iske Anas da Ummie kan kujera. Bayansa ta hango saboda kallon direction na Ummie dayake. A lokacin da idanunsu ya had’u da Ummie kuwa tayi saurin sunkuyar da kanta.
“Shettima!” Ummie ta kira sunansa cike da mamaki ganinsa da budurwa. “Yau kuma budurwarka ka kataho mana da ita gida?” Jin an ambaci budurwa Anas ya juyo dan ganin wannan budurwar Shettiman yayi dariya.
Ai zubewa ne kawai idanunsa basuyi ba a k’asa dan yadda ya warwarosu ganin FANNAH a parlour’nsu. Inba wai ya manta bane he made it clear to her karta kuskura tashigo. K’in d’ago kanta tayi su had’a ido tinda taji alamun blue eyes nasa a kanta. Yafi minti d’aya yana kallonta totally speechless bema san me zece mata ba dan yadda tabasa mamaki.
“A’a Ummie ai wannan tafi k’arfina zubin billonaires ne da ita” cewar Shettima har yanzu Anas bebar kallon Fannah ba launin fuskarsa take ya koma ja dan b’acin rai ko sauraron Shettima ma beyi ba. “Dade Ya Anas kika tambaya bare rasa amsar da kike nema ba.” Se yanzu hankalinsa yadawo, kallon Shettima yake tare da watsa masa wani irin wawan kallo.
“Kai Shettima deh!” Cewar Ummie cike da zumud’i. “Fannah ga Ummie, Ummie ga Fannah.” Shettima yayi introducing nasu wa juna. Har k’asa Fannah ta tsuguna ta gaishe da Ummie cike da girmamawa, itama Ummien cike da fara’a ta amsa ta. “Taso ‘yata taso dan Allah” kafin ace meh Ummie taje ta r’iko Fannah tare da k’ariso da ita kan kujeran da suke zaune da Anas, a yayinda ta zauna kan hannun kujerar irakuma se kallon Fannah take kamar ta cinye ta, Fannah kuwa fitsari ne ya matse lokaci d’aya dan har yanzu Anas bebar kallonta ba.
“Shettima kace wannan kyakkyawar ba budurwarka bace?”
“A’a Ummie, Ya Anas kama Ummie explaining mana.”
Kallonsa yadawo gare da Shettima, “wallahi inbaka min shiru anan ba zan maka duka.”
“Kai Ya Anas a gabantan ma bara muyi koda shirin k’arya ba? Ai ganga ake bugi ba mutum ba. Zaka fad’awa Ummie wace ita ne ko in fad’a mata.” Takalmin k’afarsa yayi yunk’urin cirewa, Shettima na ganin haka ya lab’e bayan labule. “Fannah koh?” Ummie ta tambaya a nitse.
“Eh Ummie” ta amsa ta cikin siriryar muryarta.
“Toh Masha Allah ke da wa kuka shigo?” A hankali ta d’aga kai ta kalli Anas da ba abinda yake in banda hararan dayake watsa mata, miyau ta had’iye takasa amsa tambayar Ummie duk tsoro ya cika ta.
“Ita da Ya Anas ne” cewar Shettima dake lab’e bayan labule. “Wai Ummie ke baki gane bane? Budurwar Ya Anas ce fah.” Ido gam Fannah ta matse tana niran sauk’an duka.
“Budurwarsa fa kace Shettima? Alhamdulillah!” Rungumo Fannah tayi, se mammatse ta take a jikinta. Anas ji yake kamar ya k’urma ihu dan takaici da bak’in ciki.
“Ashe Allah ze nuna min ranan da Babana ze kawo min mace gida, kai alhamdulillah. Fannah tunba yau ba nake jirar wannan rana, ranarvda zamu had’u. Allah miki albarka, kai nagode. Kinga sekina hak’uri da Baban nawa sabo-” bata k’are maganar ba Anas ya katse ta.
“Wai me haka Ummie? Nifa ba budurwa ta bace, tsiyar Shettima ne kawai, ke tashi mu tafi.” Yace da Fannah alokacin daya dawo da kallonsa gareta yana galla mata wani erin harara.
“Baba na meyayi zafi? Ai wannan ba abar b’oyewa bace iyyeh? Ko rowarta kake mana ne?” Shafo fuskar Fannah tayi “ ‘yata karki jisa kinji? Yi zaman ki.”
Cike da kunya da tsoro tace, “uhm Ummie ba buduwarsa ce ni ba, wasa Shettima ke miki.”
Da murmushi sosai a fuakarta tace “ni nagane ‘yata, Allah barmin ku tare. Barin kawo miki koda ruwa kinji?”
“Wai Ummie meh haka ne? Kekuma tashi mutafi.” Anas ya fad’i a fusace.
“Ba inda zataje, Shettima duba ko Abuu na gida ka masa magana.”
“A’a Ummie karki damu please-” Fannah bata k’are maganar ba Ummie ta katse ta “ ‘yata karkiji komai kinji? Feel free, feel at home. Jeka duba Abuu Shettima.” Nan ta fice kitchen a yayinda Shettima yaje duban ko Abuu na gida shima, yarage daga Fannah se Anas. Hannunta ya kama tare da murd’awa cike da mugunta. K’ara ta saki “arghh! Mr. Fauzi please ka sake min hannu da zafi.” take hawaye ya soma cikowa a idanta.
“Da zafi? Me nace miki amma, didn’t I tell you kar ki shigo? Mesa bakiya jin magana ne?” Azaban ne yamata k’ak’a har hawayen suka soma tsiyaya dan yadda ya murd’a hannun nata. Daidai nan Ummie tafito da tray cike da snacks da drinks akai. “Ya meke faruwa?” ta tambaya alokacin datake k’arisowa cikin parlour’n. Hannun Fannah ya sake da wuri gudun kar Ummie tayi suspecting wani abu amman ina ta riga ta hango hawayen dake mak’ale cikin idanun Fannah.
“Ya Salam Mama na meya sameki?”
“Bakomai Ummie abu ne yashiga mata ido.” Anas ya amsa tun kafin Fannah da aka tambaya tayi magana. “Sorry dear ya fita? Muga.” Kamar dagaske yawani sa hannu yana duban idanta harda hura mata iska.
Hawayen ta had’iye “shikenan yafita” tare da kawar da kanta ba tare da ta kallesa ba. Serving nasu drinks d’in tayi. “Bismillah uwata” Ummie tace da Fannah. “Babana fad’amin mana toh ina kuka had’u da Fannah?”
“Ummie please me haka ne? Fannah tashi mutafi.”
“Yanzu Anas itanma se an mana rowanta?”
K’arya ya mata, “Ummie we need to go ne, zan kawo ta some other day.”
Dad’i sosai taji “ka yarda budurwarka ce kenan.” Ta fad’i dawani shu’umin murmushi tattare a fuskarta.
Shiru yayi kamar be jitaba. “Anas fad’a min mana.”
“Eh Ummie shikenan kinji? She is my girlfriend. Tashi mutafi Fannah.” Daidai lokacin Shettima ya dawo “Ummie Abuu fa bai gida kuma ga motarsa a pake.” Wani sanyi Anas yaji a ransa bashi kad’ai ba hatta Fannah dagajin Abuu bai gidah. Mik’ewa yayi itama haka, ko jiran tama Ummie se anjima beyi ba yasoma janta, itade Ummie cike da mamaki take kallon Anas budurwarsan ma bare saurara mata ba.
Bayan sun shiga mota ya soma suburbud’a mata masifa wane an turoshi. “Wai ke mesa bakiya jin magana ne iyyeh? Didn’t I tell you karki kuskura ki shiga? You are not my girlfriend you are just a fake one banasan family na su ganki, kin huta ai yanzu da Ummie taganki mschww! Mutum ace mishi don’t amman seyayi.”
Hawaye take sosai “Sir kad’au wai dagangan na shiga gidanku ne? Doki ne ya biyoni ta fad’i” cikin kuka tana share hawayenta.
“I still don’t care!” Ya fad’a a tsawace. “Acikin motan me ze miki? Msschw! Kin d’au wasa nake ba, you’ll be suprised 1000 paper zan baki kiyi correcting.” Kukanta ne ya tsananta kamar ‘yar yarinya ta tsaya tana kuka harda me sauti tsuka yaja ya soma driving ganin kukan nata bana tsayawa bane ga kuma kukan ya soma damunsa ya tsaya gefe guda akan titi. Ko d’ago kai ma batai ba se kukanta da takeyi kanta cuse cikin cinyarta.
“Toh kukan ya isa” ya fad’i a hankali. Banza tayi dashi ta cigaba.
‘Sorry’ yakeson fad’a mata amman bare iya ba, “ya isa I shouldn’t have shout at you kinji? Stop crying” namma bata bar kukan ba. “Okay barakiyi correcting 1000 papers d’inba, I take that back, bar kukan.” Bata d’ago kai ba har a yanzun sede ta d’an rage kukan nata. “Bafa dan wai inaso bane na shiga gidan naku, doki har biyu ne suka biyoni ni nikuma inajin tsoro, dana shiga na had’u da Shettima, shine yayi insisting sena shiga.” Ta sanar dashi cikin sautin kuka.
Sekuma yaji wani iri amman ai still da ta shiga koda gidan neighbours ne. “Toh d’ago fuskarki, kukan ya isa na fad’a miki banasan jin kukanki.” Tana d’ago kai ya mik’a mata hand kerchief nasa, amsa tayi ta share hawayenta a yayinda yayi zaman kallonta, kukanta na d’aya daga cikin abubuwan da yake burgesa a gareta, abu kad’an setayi kuka. Ice cream shop ya wuce da ita bata ce dashi komai ba. Bayan yayi parking yafito ya bud’e mata nata tare da rik’o mata hannu mutane kad’an suka samu ciki.
Kap flavours dayasani na ice cream seda ya siye mata amman kuma bece mata nata bane haka suka dawo cikin motar, zaman makoki suka tayi har seda ya kawo ta gaban gidansu, a nitse ta bud’e k’ofar ko se anjiman ma batayi niyyan fad’a masa ba “girlfriend” ya kirata, banza tayi dashi da sauri ya cafko abayanta kafin ta rufo k’ofar. “Your ice cream take it.”
“Banaso” tace tana turo bakinta, har yanzu haushi yake bata jibi yadda ya riga mata masifa.
“Girlfriend take it kinji?” Hak’urin nan de dayakeson bata ne ya kasa. Ganin battada niyan d’aukawa yace, “okay barin sake miki masifa ba, kema obey all my rules yanzu d’auka kinji?”
Wato shi be iya bama mutum hak’uri bako? Tace a ranta. “Ni ka sakemin abaya in tafi.”
“Fannah” yakira sunanta yadda takeso “take it kinji? Barin k’ara ba.” Kallonsa tayi na ‘yan seconds sannan ta ciro ledan tayi tafiyarta ko godiya babu.
★★★★★
“Ummie dan Allah Ya Fannah tazo?” Amal ta tambaya.
“Eh kai!” Ummie ta amsata se dad’i takeji Anas yakawo budurwarsa gida. “Yace ze sake kawo mana ita karki damu.”
“O’o ni barin yarda ba. Ni zanyi inviting nata birthday party na.” Daidai lokacin Anas yake sa kai cikin parlour’n da alama yajiyo abinda Amal tace just now.
“Wa zakiyi inviting a birthday nakin?”
“Ya Fannah mana Ya Anas shine ko ka fad’a min zaka kawota, amman ka iya cemin kar in fad’awa kowa picture’nta dake wayarka.”
“Rangem! Ya zama fashashhen k’wai” cewar Shettima yana daka tsalle. “Ashe abin kenan, wayyo! Ya Anas ka nunwa Ummie mana taga hoton surikar tata.” Dafe baki Amal tayi batasan lokacin data fad’a ba. “Ya Anas I’m sorry wallahi bansan ya akayi na fad’a ba.”
Wani irin kunya ne ya ratse Anas dayakeji kamar ya tone k’asa ya shiga ai yanzu shikenan sekowa ya zata eh son Fannah yake, bece da Amal komai ba illa k’arisowa cikin parlour’n da yayi a gaban Ummie ya tsuguna.
“Ummie please kar kowa ya fad’awa Abuu yau wata ta shigo gidan nan.” Cike da mamaki Ummie ke kallonsa “toh Babana ai abu ne me kyau kuma shima dad’i zeji.”
“A’a Ummie ni kawai kar kowa ya fad’a masa kaji Shettima?”
“Senayi tunani