Showing 57001 words to 60000 words out of 268365 words
Chapter 20 - Tana Tare da ni complete book document .txt
sa!” Afrah tace.
“Me kike nufi?” Fannah ta tambayeta a takaice.
Wayar ta ta mik’a mata “duba nan kiga.”
“Innalillahi! Na mutu!” Fannah tayi exclaiming. “4 missed calls?? Yau Mr. Fauzi zeyi ferfesu na.”
“Akan wannan pointless suratan da kike ba gomma kin kirasa ba.”
“Afrah wallahi baran iya ba balbale ni zeyi da masifa.”
“Oh!” Afrah ta saki numfashi
“Ya Fannah yanzu kuka kike? Ai yaci ace kin saba da masifa tun gun Baffa Khaleel. Ki kirasa.” Kai Fannah ta kad’a, fisgan wayan Afrah tayi aiko ta soma dialing number’n Mr. Fauzi. “Afrah in kinayi wa Allah ki kashe tun kafin ya shiga dan Allah, wallahi zan kirasa ki kashe dan Allah.” Ai wayar na nuna an d’aga Afrah ta wurga wa Fannah wayar tayi bakin k’ofa jiran kallon drama tana dariya.
B’ari Fannah take ta kai wayar kunne nan ma takasa fad’in komi, kamar yadda shima Anas d’in yayi shiru ransa b’ace se tafasa yake. “Hello Mr. Fauzi.” Tayi managing ta fad’a cikin murya me rawa.
Cike da tsiwa yake maganar. “Se yanzu kika ga damar magana? Eh?? Me kika maidani? Toy abin wasa? Wayyo!” Ya saki k’ara tare da rik’e cikinsa dan yunwa.
“Mr. Fauzi I’m sorry dan Allah kayi hak’uri.” Ta fad'a idanta na cikowa da hawaye.
“Meya hanaki zuwa office yau?” Ya daka mata tsawa. Kuka take kam yanzu.
“Si..sir naga jiya danaje baka kirani ba kace na dena ma shisshigi sesa banzo ba ya-” bata k’are maganar ba ya katse ta.
“Nonsense na baki nan da 20minutes be at my office” karap ya katse wayar. Hannu Fannah tasa tana share hawayerta a yayinda Afrah ta k’ariso ta zauna kusa da ita. “Haba mana Ya Fannah wallahi kidena masa kuka ze raina ki.”
“Da Allah rufa min baki ba duk ke kika jawo ba, ba abin na ja miki Allah ya isa ba.”
“Yi hak’uri Anty babba, meya ce miki?”
Harara Fannah ta galla mata “bansani ba muguwa kawai.” Nan ta mik’e ta canza kaya ta sako red hijabi tare da jan jakarta ta fice. Afrah na mata Allah kare ma ko kulata batai ba. Bata sha wahala ba tasamu keke napep sede hold ups daya rik’a rik’e su a hanya. A takaice de lattin minti 5 tayi. Duk yadda tayi tabar b’ari takasa. Se addu’o’i take ta suburbud’owa Allah kare ta daga sharrin masifan Boss nata.
Knocking tayi bisa k’ofar “come in” yace. Bayan data shigo tagansa yana attending wasu mutane kanta ta sunkuyar tajira har se sanda ya sallamesu. Kallonta yake bema san me ze mata ba chan yace. “In nache you are fired zaki ga laifi na?” Kai ta kad’a a hankali fuskarta na kallon k’asa se b’ari take.
Table d’in ya buga da k’arfi a tsorace ta d’ago kanta tana hawaye.
“Ban kuma hanaki min magana da body language ba?”
“Ka hana” ta fad’i tana share hawayenta. “Na farko yau dagangan kik’a k’i zuwa office kika bar ni da yunwa, na biyu dana kiraki har 4 missed calls baki d’aga ba saboda kin mayar da Boss naki sa’an wasanki.”
“Kayi hak’uri dan Al-”
Katse ta yayi a tsawace “ban baki izinin magana ba so shut up!” Hawaye se gangara suke kan kumatun ta tana sharesu “na uku da kika kirani back kika k’i magana se sanda kika ga dama. Na hud’u kikayi latti akan latti. Zakiga laifi na in nace na koreki daga nan? Am talking to you!” Ya k’ara mata wata tsawan.
Hak’urin ma takasa basa se kuka takeyi shark’af shark’af. “Baraki amsa ba kenan?”
“A’a I’m sorry” ta fad’a da k’yar muryarta na rawa.
“Kuma kinsan me? Wannan kukan da kikeyin ba damuna yake ba, koda zaki tsiyaye hawayen ki tas barin damu ba, gara kiyi saving nasu kuma har yanzu tsaye kike?”
Kai ta d’ago a hankali “a’a” nan ta wuce ta had’a masa coffeen bayan ta ajiye masa coffeen ta juya zata fice kenan ya finciko ta da hijabin ta da mugunta wanda sanadiyar haka ya shak’e mata wuya k’ara sosai ta saki take ta soma kuka.
“Nan gaba zaki sake nanata abinda kikayi yau. Mschwww!” Bata ce masa komi ba jakarta kawai ta d’auka ta fice sam yi yayi kamar be ganta ba. Data sauk’o ma tana jin Yusuf na kiran sunanta ta sharesa k’ofa na bud’uwa ta fice bayan ta yabi da gudu Allah ya so ba keke napep a lokacin tsaye take tana hawaye tana kuka me d’an k’ara isowan Yusuf wajen yace, “Haba Fannah mene yafaru ina ta kirarki kika yi kamar bakiji niba. Wani abu ne?” Batace dashi komi ba se kukan da takeyi.
“Fannah meya faru kike kuka haka?” Ya tambayeta cike da tausayi. Kukan take har yanzu kamar ‘yar yarinya tayi covering fuskarta da hannu. Hijabinta yaja a hankali ya zaunar da ita kan wata bench. Be sake ce mata komi ba har se sanda ta gama shan kukanta. “Fannah zaki iya fad’amin meya faru?”
“Ni nabar aiki a nan.” tace tana share hawayenta.
Cike da mamaki yace, “ban gane kinbar aiki ba Fannah kinsamu wani aikin ne?”
“Ban samu ba amman zan shiga nema.”
“Mesa Fannah, na miki wani abu ne?”
“Baka min komi ba amman Boss naka yamin. Yusuf niba mutun ce me neman magana ba, nayi hak’uri da erin abinda Mr. Fauzi yakemin, I can’t take it anymore wallahi ko kashi bara’a masa abinda Mr. Fauzi kemin ba neman kud’in ba hauka bane. Ni kawai ya biyani kud’in ‘yan kwanakin dana masa aiki zanje in nemi wani.”
“Fannah kibar magana, nasan you don’t mean what you are saying. Kinsan yadda neman aiki keda wuya ki hak’ura, sekace ban fad’a miki matsalan Boss ba? Haka yake inya k’untata wa mutum ne yakejin dad’i kiyi hak’uri. Yanzu har kika bar aikin nan baki sami wani bafah? Dame zaki biya kud’in magamunan Baba. Kiyi hak’uri.”
“Kana nufin in cigaba da aiki k’ark’ashin Mr. Fauzi kullum yata cin mutunci na yana masifeni?”
“Ba abinda nake nufi ba kenan. Abinda nake nufi shine ki k’ara hak’uri, ki cigaba da wannan d’in kina neman aiki nima in shaa Allah zan tayaki. Kinga in muka samo miki seki bar nan d’in amman karki bar nan bakida wani aikin please.”
Shiru tayi na d’an lokaci “you are right Yusuf nagode sosai.”
“Always... Mushiga daga ciki kinji?”
Kai ta giad’a masa suka dawo ciki tare. Duk inda zasa tana biye dashi. Seda azahar yayi ta koma office na Anas knocking tayi yace, “come in.” Bayan ta shiga ko kallonsa batayi ba ta zarce ta had’a masa coffee.
“Na d’au kinbar aikin ne ai.” Yace da ita yana daddana laptop. Nanma shiru ta masa ta fice ba ita ta sake dawowa ba se to 4 ta had’a masa coffeensa cikin flask ta d’auka takai masa mota. Shiko Anas ko a kwalar rigarsa daman haka yake so, tana aikinta me kyau ba shisshigi.
Washegari ya kasance Asabar ba aiki Anas kuwa through the week yasaba da karyawa da coffeen Fannah sam yak’i cin breakfast seya sha coffeen ta tukunah. Wayarsa ya d’au ya kirata da misalin k’arfe 10:30AM alokacin se shiri suke ita da Afrah zasu gidan wata k’awar Afrah data haihu tun bata gama secondary school ba aka mata aure, zasu yin barka. Fannah tayi bala’in kyau tunda nake ban tab’a ganin Fannah tayi kyau kamar na yau ba dake Afrah ce ‘yar gayu ta mata kwalya. Brick red jan baki tasa mata da kwalli da lining sannan ta taje mata dogayen gashin idanunta da mascara ta mata brushing gira tare da shafa mata powder had’adden daya mugun amsar skin nata.
Sanye take da blue and red atamfa amman red d’in yafi yawa dan dolenta tasa gyale sabida Afrah ta tak’ura mata. Tana zaune tana game tana jiran Afrah wayarta ya soma ringing ganin Mr. Fauzi ke kira ya mugun bata mamaki yaude Asabar ce bakuma ranar aiki ba toh me zekira yace min? Ta tambayi kanta a zuci. “Afrah kiga Mr. Fauzi ke kira meze cemin?”
“Taya zamu sani in bawai d’aga wa kikayi ba Ya Fannah.” A hankali ta d’aga tasa a kunne.
*© miemiebee*
beeenovels.mywapblog.com
[12:48, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
2⃣5⃣
“Hello” tace a hankali.
“coffee nakeso.” Ya fad’a authoritatively.
“Sir amman ai yau saturday ne ba’a aiki a weekends.”
“In Boss naki yace se kinyi kuma fah? Can you say no.”
Can k’asa k’asa tace, “a’a.”
“Good, meet me at my paint house...” Nan yamata kwatance kafin tace, “okay” ya katse wayar.
“Meh yace wai?” cewar Afrah dake d’aura kai.
“Wai coffee yakeson sha inje in samesa a paint house nasa.”
“Ranan Asabar d’inma?”
“Humm! sekace bakisan Mr. Fauzi ba? Haka yake d’an ra’ayi ne.”
“Kina nufin yanzu bara muje gidan Haleeman ba kenan?”
“Zamuje mana ai had’a coffee kawai zan masa within 2-3 minutes nagama semu tafi yanzu kiyi ki gama shirinki muje tare.” Da “toh” Afrah ta juya ta gama d’aurin ta sannan sukayi sallama da Mami daidai gaban paint house na Anas kamar yadda ya mata kwatance suka tsaya bayan ta sallame me napep d’in suka tsaya admiring gidan dududu barefi 2 bedroom flat bane ciki fari ne tas gidan ya k’ure kalman kyau.
“Ya Fannah wannan ne motarsa?” Tana nuni da yatsa.
“Wai ba” cewar Fannah.
“Wow! Wow!”
“Ke kin fara ko? Nikam kizo mushiga”
“Wa? ni? In shiga? Saboda ya koreni kimin dariya? Kefa kikace baida mutunci a dalilin me zan biki ciki? Nide kiyi sauri ina jiranki nan.”
“Amman Afrah bakiyi ba wallahi ai da sekice min baraki shiga ba, da bamu sallami me napep d’inba.”
“Oho sorry zamu samu karki damu, kiyi sauri kar muyi latti.”
“Afrah da Allah mu shiga wallahi bansan shiga ni kad’ai.”
“Ya Fannah dan Allah kibar had’a ni da Allah dan wallahi barin shiga ba. Off you go” ta mata gwalo. Baki Fannah ta murgud’a mata sannan tayi hanyanta ciki.
Door bell data gani bakin k’ofar ta danna zuciyarta se bugawa yake tana jiransa. Bayan kamar minti d’aya k’ofar ya bud’u. Anas tagani tsaye jikin k’ofar ko singlet babu jikinsa bale kaya ¾ wando ne na soja jikinsa, da alama yanzu yafito daga wanka danko gashin kansa a jik’e yake kad’an kad’an ruwa na d’iga a k’asa, ga wani kyan da skin nasa yayi a jik’e har shining shining yake. Blue eyes nasa kuwa sun sake shiga ba k’arya yayi kyau sosai ga body kam masha Allah very muscular ta kasa dena kallonsa kamar yadda shima yake kallonta and for the first time bada wata manufa ba. Be tab’a ganinta da shiri irin na yau ba, kullum cikin hijabi take banda gyalen data yafa yau ga d’an kwaliyan datayi wanda be tab’a gani tayi ba. Sosai ta canza kamanni, ga yadda Afrah ta yafa mata gyalen, ta d’an bar kad’an daga cikin k’irjinta dake a cike dadai ‘yar budurwa a waje. Za’a iya ce miki kinyi kyau ya fad’a a zuciyarsa.
Kusan a tare suka kawar da ido daga kan junansu gyalen dake wuyanta ta d’aga ta yafa kai tare da rufe k’irjinta dashi. Kad’an ya matsa gefe “come in” yace da ita a hankali ta shiga ta tsaya ba daga nesa ba “ga chan kitchen d’in” ya nuna mata da yatsa k’ok’ari tayi kar ta sake kallonsa kafin ya silleta. Kai ta giad’a nan take ta tuna dokokinsa tace, “okay.” A sanyaye tabi direction daya nuna mata ta shiga kitchen d’in komai tsatsaf ba datti ba wari. A gefe guda ta hango coffee machine gefe guda kuwa fridge. Wajen fridge d’in ta nufa ta bud’e as expected taga bottles na giya jere daban daban kai kawai ta kad’a taciro abinda zata buk’ata ta nufa wajen coffee machine d’in ta ajiye cupboards d’in tabi tana bud’ewa har tasamu na cups and spoons. Sosai ta mayar da hankalinta gu d’aya gudun kar ta fasa masa d’aya daga cikin fancy cups nasa yasata biya. Bayan ta gama had’a masa ta d’auka da hannu bibbiyu shes very careful ta bud’e k’ofar a hankali ta rufe tana juyawa kawai taga mutum tsaye gabanta gashi har yanzu besa kaya ba ¾ wandon ne. Tsorata tayi sosai iya tsoro dayasa tayi b’arin coffeen saura suka zube a jikin Anas dako singlet baida saura kuma jikinta saura a k’asa. Da cup da plate data d’aura kai dakuma spoon d’in duka suka fashe a k’asa.
K’ara sosai Anas yasaki dan zafin coffeen ita bata ma damu da kanta ba, batasan ma yatayi taciro gyalenta ta soma goge masa jikinsa ta cikinsa dashi ba “sorry sir, I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri” duk ta rikice. Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki tab’a masa jiki ma take, lallai kuwa. Alokaci d’aya kuma ta tsaya cak! A kunyace ta d’aga hannunta daga jikinsa ta d’aga kai suna had’a ido tayi sauri ta kawar da kanta. “I’m sorry” tace kallonta ya tsaya yi, besan meke damunsa ba, shi d’inda ko matan turawa kan bikini (pant and bra) ma basu masa ba mesa yake kallon Fannah toh? Me take dashi? Jik’ak’en mayafinta ta bud’e zata yafa ya kama karap! A razane ta d’ago kanta tana kallonsa alokaci d’aya tana k’ok’arin fisgan gyalen sede k’arfinsu ba d’aya bane.
Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta d’aura hannayenta biyu tana tare k’irjinta da kanta k’asa har yanzu Anas be motsa ba kallonta yake sosai sosai da ta d’aga kai seta ga ita yake kallo. Da k’yar tayi gathering courage ta bud’e baki zatace masa “kabani mayafina” kawai ya juya ya fice da gyalen zuwa wata d’aki. B’ari sosai Fannah take, shikenan tabar Anas yaga jikinta duk laifin Afrah ne da hijabinta ne da asirin ta a rufe. Ido ta d’aga sama “Ya Allah ka yafemin astaghfirullah astaghfirullah.”
Daidai lokacin Anas ya fito daga d’akin da wani leather a hannunsa baya ta juya take tana kare k’irjinta seda yagama matsowa kusa da ita ta tuna kayan tan ma show me your back ne sanda tace wa d’an iskan tellan su kar ya mata yak’i ji.
Kallon spotless bayan ta yake da gashi kad’an kad’an kwance luf akai uban gashinta kuwa an kama sa a tsakiyar kanta wanda dan uban yawansa still sanda yafito daga d’an kwalinta. Sanda ya k’are mata kallo tukuna ya bud’o leather’n har yanzu Fannah bata juya ta kallesa ba ita alhamdulillah tunda be tab’a ta ba. Ta gommaci ya kalli bayanta dayaga k’irjinta.
Zuciyar ta kuwa se bugun d’ari d’ari yake. K’aran leather tajiyo a lokacin dayake ciro gyalen daga cikin leather’nsa wani tsoro tasakeji ya ratsa ta se addu’o’i take ta suburbud’owa idanta gagam ta rufe. A hankali taji sauk’an gyale ajikinta a razane ta juya tagansa tsaye a bayanta kwata kwata distance dake tsakaninsu befi inchi uku ko hud’u bane. Da sauri ta rufe jikinta dashi dukda kuwa gyalen shara shara ne amman yafi babu, gashi kuwa yayi kalan me tsada sosai gashi kuma sabo gal. Stepping back tayi “nagode” tace tanasan tambayansa ina gyalenta sekuma ta fasa.
Tsugunawa tayi zata tattara broken glasses d’in ya cafko ta da hannu “so kike ki sake yankewa kimin kuka anan? Ko an fad’a miki inasan tab’a jikin ki ne?” Wai ace mutum yanzu ya gama showing kindness wa mutum kuma yana zaginsa, wani hali sena Anas. Fannah tayi tunani a ranta.
Hannunta take k’ok’arin fisga dan zafin rik’onsa amman ta kasa, yana noticing haka ya sake ta. “Wuce ki sake had’a min wani coffeen akoi flask akan counter d’in ki cika min shi in kin gama ga kud’inki” ya nuna mata bundle ma N100 kan dining table. Fat