Showing 111001 words to 114000 words out of 268365 words

Chapter 38 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54118

hankalinsa ba. Zakace baka son Fannah ko yaya?” Shiru Anas yamasa bece komai ba se nishin wahalan dayake yi abin tausayi.


“Farouq ga ‘yan patrol zuwa fa!” Baaba yayi exclaiming da ihun gaske ai kamar kyaftawan ido su Farouq suka lodu a mota suka bar wajen a 360. Anas na kwance helplessly a k’asa. Bayan motan patrol d’in ya k’ariso polisawan suka diddiro ganin mutum a k’asa, plate number’n motar Anas d’ayan ya karanta yaga “Mr. Fauzi.”
“Guys Mr. Fauzi ne!” da gudu sukayi kansa suka d’ago sa zuwa motar sa tare da miqar dashi a back seat. “Abba lets go, mu kaisa asibiti push the start button.” d’ayan officer’n ya fad’i. A wahalince Anas yace, “no karku kaini asibiti just drive me home, to my paint house.”
“Sir but you are badly injured.”
“I know, ku kaini paint house d’ina kawai.”
“Okay sir ina ne paint house d’in?” Nan Anas ya musu kwatance murya yana d’aukewa. “Sir su wa suka maka haka?” Har ya bud’e baki ze kira sunan Farouq seya tuna in ya fad’a musu definately zasu kama Farouq su rufe sa kuma, in hakan ya faru kuwa Fannah barata ji dad’i ba. “Nima bansan suba” yama officers d’in k’arya “ ‘yan iskan unguwa ne kawai.”


Daidai gaban paint house nasa suka iso. “You can go now zan k’arasa da kaina nagode.” Cewar Anas idanunsa suna kafewa.
“Sir amman kace barakaje asibiti ba? Wannan mutane sunji maka ciwo fah.”
“Don’t worry I can take care of myself.” Bottles na giyansa guda biyu yaciro da k’yar yake iya tafiya dan kalan dukan dayasha wajen Farouq da mutanensa, ahaka har ya samu ya isa ciki ko k’ofan ma yakasa locking. Bayi ya nufa da rarrafe da taimakon sink ya mik’e ya kalli fuskarsa a madubi. Sam beso sake kalla ba dan irin ciwon da suka ji masa. Ruwa ya gwada wanke fuskar nasa dashi. Aiko ruwan na tab’a fuskar ya saki k’ara dan azaba daga k’arshe hak’ura yayi yakoma d’aki tare da rage kayan jikinsa yabar short nicker kawai. Kwalba d’aya ya kwankwad’e tas dan samun bacci, yana shanye wa kuwa bugeggen bacci ya d’ibesa ko sallan maghrib beyi ba bale na isha. Wayoyinsa dake cikin mota kuwa se kiransa su Ummie suke ba iyaka amman bai d’aukawa hankalin kowa ya tashi, ko da sukaje office nasa suka tambaya kuwa, kowa ya shaida Mr. Fauzi yabar building d’in lafiya.


*****


_Washegari..._
8:10AM yama Fannah a office sede tata knocking a bakin k’ofar office nasa amman shiru chan ta gwada bud’ewa taji a rufe alaman Mr. Fauzi bezo bama kenan! To meya rik’esa? Shida ko lattin minti d’aya baya yi. Meya faru? Mesa bezo ba? Ko baida lafiya ne? Minti 15 ta k’ara tana jiransa amman ba alamansa. Gashi yanada board meeting by 10:30AM. Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta sauk’a k’asa ta samu Kacallah tare da tambayansa ko sunyi waya da Mr. Fauzi.
“A’a wallahi nima Fannah na kirasa ta duka layinsa baya d’agawa tun jiya na rasa dalili.” Kawai setaji gabanta na fad’i. “Toh nagode” tace masa.
Wayarta taciro ta kirasa har ya tsinke be d’aga ba. Tashin hankali. To ina yashiga? Amal ta kira ta tambayeta ko Anas na gida cike da tashin hankali Amal tace mata itama tun jiya suke neman Anas bedawo gida ba.


Napep ta tsara bata tsaya ko inaba se paint house na Anas motarsa tagani fake gaban gidan wani hamdala tasaki har ta ciro wayarta zata kira Amal ta sanar da ita se kuma ta fasa, bari de ta tabbata ko yana ciki tukuna. Door bell ta danna sau uku amman ba response. Tana gwada murd’a hannun taga k’ofar abud’e ba sak’e sak’en da bezo mata ba toh kode barayi ne suka shigo masa? Subhanallah amman ai kuma ga motarsa. Ciki tashiga ta lek’a kitchen ba alaman ko motsin mutum “Mr. Fauzi!” ta kira sunansa shiru d’ayan d’akin ta bud’e taga nan ma bayanan toilet dinma haka, guest toilet ma ta duba bata gansa ba. Daga k’arshe d’ayan d’akin ta bud’e a hankali kwalban giya ta soma cin karo dashi, se fad’i gabanta yake ta d’aga tare da k’arisawa cikin d’akin tana taku a hankali cike da tsoro. “Mr. Fauzi!” Ta kira sunan sa alokacin data gansa kwance kan gado yayi ruf da ciki se bacci yake yi ba ko riga jikinsa se bedsheet daya ja zuwa tsakiyar cikinsa.


A nitse ta k’arisa gefen gadon tare da ajiye kwalban kan side drawer. “Mr. Fauzi!” Ta sake kiran sunansa shiru be amsa ba. Toh kode mutuwa yayi ne? Sede kuma tajisa yana numfashi. Jijjik’asa ta hau yi har se lokacin daya soma motsawa. “Waye ne?” Ya tambaya cikin bacci.
“Sir Fannah ce, Fannah Aleeyu.”
“Fannah? Me kikeyi anan? Ban rufe k’ofan bane?”
“Eh sir baka rufe ba, you need to get up kanada board meeting by 10:30AM.”
Cikin bacci yace, “barinje ba kiyi cancelling, tell them barin samu zuwa ba.”
“Sir but why? Kayi hak’uri ka tashi please.” Bece da ita komai ba ya cigaba da baccinsa. Pillow’n daya rufe fuskar sa dashi ta d’aga. Ido ta zaro tana salati alokacin da taga irin ta’addancin da aka ma Anas a fuska. Meya samesa? Waya masa duka haka?


“Subhanallahi Mr. Fauzi meya sameka? Omg!” ta tambaya a kid’ime a lokacin da ta tsuguna gabansa.
Da k’yar ya iya bud’a baki yace, “ki rufe min fuska banasan hasken nan.”
Ignoring nasa tayi “Mr. Fauzi waya maka haka da fuska? Fad’a kayi da wani neh? Meya sameka?”
“Bansani ba nima just leave me get out.” Haka kawai yaji baya san Fannah tagansa a bad condition irin na yau, bayasan yasa ta cikin damuwa bayasan taji tausayinsa.

“No Mr. Fauzi I’m not leaving you like this.” Hannu tasa ta dafe goshinta bata ma san ta ina zata fara ba. Hawaye kawai taji yana gangaro mata kan kumatu dan uban tausayi irin nata. Hannu ta aza ta tab’a gefen idansa daya kumburo dan bugun daya sha. K’ara ya saki wanda yasa ta mayar da hannunta baya da wuri. “Sorry” tace cikin kuka. Idanunsa na sauk’a kanta yaga tana hawaye abinda baya so kenan.
“Miss Aleeyu leave please, goo.”
“I can’t leave you like this, Mr. Fauzi asibiti yakamata muje su duba ka.”



“Barinje ba” yabata takaicaccen amsa idanunsa a rufe.
“Please” ta rok’esa tana hawaye ganin yadda aka masa destroying kyakkyawar fuskarsa da a yanzu mutum bare so ya kalla sau biyu ba.



*© miemiebee*


b[truncated by WhatsApp]
[12:53, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
4⃣5⃣










*THANK YOU SO MUCH DA ADDU’O’INKU MASU SO DA K’AUNA TA, ALHAMDULILLAH NAJI SAUK’I SOSAI*



Shiru tayi bata ce komi ba as tana nazarin abu a ranta.
“Say it out” yace yana kallonta. Mamaki ne yacika ta how comes ya gane ta nada magana a ranta.
“Errm babu” tayi k’arya.
“Akwai say it.”
“I was thinking ko za’a zubar da abubuwan da suke cikin fridge d’in kar in-” katse ta yayi “jeki d’iba ki zubar, kiyi flushing duka.” Dad’i sosai taji nan take ta mik’e. “After kin gama cin abincin ki amma.”
“Sir na k’oshi thank you” bata tsaya jiran me zece ba ta nufa fridge d’in tafito da duka kwalabe guda 15 d’in. “Sir akwai wani bayan wad’annan?” kai ya gyad’a mata.
“Are you sure Sir?”
Kai ya girgiza “akwai kwali d’aya k’ark’ashin gado na a d’aki.”
“Thank you Sir.” Uku-uku ta riga d’iba tana kaiwa toilet tana zubarwa har tagama duka kwalaben kuwa tayi disposing nasu. Bayan ta gama ta d’au first aid box daga toilet tafito dashi zuwa dining space inda ta tsinci Anas zaune yayi zurfi cikin tunani. “Sir?” Ta kirawosa tare da dawo dashi daga duniyar tunanin daya wula. Kallonta kawai yayi ba tare da yace komi ba.


“I think ciwon fuskan kan zefi healing da wuri in aka rufe” ta fad’i tana ciro wasu transparent bandages guda biyu. B’antare d’aya tayi. “May I?” Ta tambayesa kai ya giad’a mata nan ta manna masa na gefen bakin nasa a hankali sannan na kusa da idansan shima a hankali. “Get well soon” tace dashi a lokacin data rufe first aid box d’in ta mayar toilet, fitowarta ta nufi bakin k’ofa.
“Miss Aleeyu” ya kira sunanta chak ta tsaya tare da kewayo wa. “Yes Sir.”
“Ina zakije?”
“I’m going home, jikin naka da sauk’i ba?”
Alokaci d’aya kuma se yaji bayasan ta tafi, shi yake korarta d’azu amman yanzu kuma so yake ya cigaba da kasancewa *_TARE DA_* ita, bayasan ta tafi wanda shi kansa besan dalili ba.


“Must you go?” Ya tambayeta.
A hankali tace, “Sir I have to, bareyi in cigaba da zama anan ba.”
“Okay” yace blankly. Bata ce dashi komai ba ta fice. So yake ya tsayar da ita yace mata ta zauna dashi baya san ta tafi amman bayasan ta raina sa bayasan ta d’auka da wata manufa, ta zata ko santa yake.


Isar Fannah gida ke da wuya ta tarar da Farouq tsaye bakin k’ofa da alama ita yake jira. Bugun zuciyarta taji ya k’aru in akwai d’an Adam data tsana a doron k’asa toh Ya Farouq ne. Bayan ta sallami meh napep d’in ta sunkuyar da kanta tayi kamar bata gansa ba se tafiyarta take a yayinda idanunsa suke biye da ita. Takai da shiga cikin gidansu kenan kawai Farouq ya jawo ta da k’arfin gaske, kafin tayi yunk’urin yin wani abu ya matseta jikinsa gagam shi a dole yana hugging nata. “Ya Farouq me haka? Ka sakeni” se k’ok’arin k’watan kanta take amman ta kasa. Batasan lokacin data fara kuka ba. Se bugin k’irjinsa take amman kamar super glue yak’i sakinta. “Fannah mesa bara ki soni ba? Mesa Fannah? Ke bakisan ina sonki bane? Akan ki kowa ze iya mutuwa, mesa se wancan me idan turawan zaki so? Me yake dashi da banida? Tell me mesa bakiya sona?” ya k’are maganar yana wani erin zakin nishi kamar ze cinye ta tare da shunshuna hijabinta sekace ze cire.


“Ya Farouq ka sake ni dan Allah zan fad’a maka dalili.” Chak ya sake ta, “fad’a min my Fannah.”
“Ya Farouq bana sanka yaci ace ka hak’ura inhar kanaso na kamar yadda kake fad’i abinda nakeso ya kamata kamin, ka hak’ura you and I are not meant to be please ka fita daga hark-” bata k’are maganar ba ya tsinke ta da wani erin wawan marin da take ga ba’a tab’a mata ba erin sa ba, gefen bakinta ne ya fashe take yana zubda jini, harwani kurma-kurma tazama for the mean time.


Kukanta ne ya tsananta a yayinda taga jini na fita daga gefen bakinta. “Bakiya so na? Bakiya sona se wancan d’an iskan?” Hannunta ya rik’o cike da mugunta. Cikin kuka da azaba tace, “Ya Farouq dan Allah ka sake min hannu da zafi...”
“Toh wallahi baki isa ba, inada tabbacin kinga halin da Mr. Fauzi yake ciki wallahi in be fita ya bar harkarki ba kinji na rantse har kashe sa senayi kamar yadda nasa aka masa duka.”
Ita bata damu ma da kanta ba yanzu, Mr. Fauzi ne damuwanta. “Ya Farouq yanzu kai kama Mr. Fauzi duka haka sekace kashe sa zakayi, me ya maka?” Ta tambayesa tana hawaye.
“Yace min yana sanki abinda yamin kenan, nikuma muddin ina raye ba mahaluk’in daya isa yace yana sanki, ke tawa ce Fannah, you are mine! Inhar kinasan Mr. Fauzi ya rayu toh wallahi kifita daga harkansa kije kiyi ending up duk wani abinda ke tsakanin ku ni na fad’a miki if not next time gawansa zaki tsinta.”


Mr. Fauzi yace yana sona? Abinda ta nanata kenan a ranta. Ya fad’i hakan ne dan kareni daga Ya Farouq badan yana sona tsakani da Allah, banida standards da Mr. Fauzi ze gani har yace yana so na.
“Ya Farouq dan Allah badan ni ba, whatever that is going on between us karka sa Mr. Fauzi aciki ba abinda ya maka dan Allah.”
“Rai da lafiyan Mr. Fauzi lies in your hands, kifita daga harkansa tell me you love me zaki aureni as soon as possible and ba abinda ze sake samin Mr. Fauzi kinji my wifey?”
“In nayi haka zaka fita daga harkansa baraka sake tab’a lafiyar sa ba?” Ta tambayesa tana hawaye ba makawa.
“Eh my wifey kika min haka ba abinda ze sake tab’a lafiyar Mr. Fauzi.”
“Okay Ya Farouq I will do it, na yarda zan aure ka amman karka sake tab’a Mr. Fauzi dan Allah.”

“Bar kuka tawan, tell me you love me” ya fad’i yana k’ok’arin rik’e hannunta. Hannun nata ta rik’e gam a jikinta hanasa yin bainda yayi niyyan yi. Cikin kuka cike da tashin hankali tace, “Ya Farouq I love you zan aure ka, please kar ka sake tab’a Mr. Fauzi.”
“Good girl, sesa nake sonki akwai sanin yakamata. Bar kuka toh kinji banasan ganin wannan hawayen” jinin dake mak’ale a kusa da bakinta yasa hannu ze goge a yayinda ta ja da baya cike da tsoro. “Jeki huta sena dawo gobe se ayi maganan auren namu ko?”
Shiru tayi bata amsa saba. “Koh?” Ya sake tambaya. “Eh” tace masa.
“Toh ni zan wuce, I love you” jira yake ta amsa masa da ‘I love you too’ yaji tayi shiru. “Wifey baraki cemin I love you too bane ko bakijini bane?”
Kamar wacce baratayi magana ba can tace, “ban jika ba.”
“Yanzu kin jini ai ko? So answer me.” Shiru tayi bata ce komi ba.
Hannunta ya cafko cike da mugunta. “Tell me abinda nakeson ji.”
A wahalince tace, “Ya Farouq I love you dan Allah ka sake min hannu da zafi.”
“Say it again.” Yayi demanding.
Tana hawaye tace, “I love you ka sakeni please.” Wulli da ita yayi sannan ya fice. Har k’asa ta sauk’a tana kukan takaici na kusan minti ishirin, sanda tayi me isarta sannan ta mik’e tashiga ciki bakowa tsakar gidan daga d’akin Baba ta jiyo sautin hirar su. D’akinsu dasu Afrah ta nufa ta baje kan gado “mesa Mr. Fauzi? Mesa baka fad’a min Ya Farouq bane ya sa aka maka duka? Mesa kak’i fad’amin?” Wayarta ta zaro daga jakarta ta kira layinsa sede har ta tsinke be d’aga ba.




*****


Da tunanin Fannah arai Anas yayi bacci yak’i komawa gida saboda bayasan acika sa da surutu. Su Ummie de da tashin hankali na kisa da yayi musu, dan ko damuwa Anas ya ciro wayoyinsa daga mota beyi ba yini yayi yana tunanin Fannah.


_Washegary..._
K’arfe 8:00AM on the dot yama Anas a office, sosai kowa yaji dad’in dawowarsa. Fannah kuwa 8:03AM ta hallaro. Yasan fuskan nan, yasan mood da Fannah ke ciki yau dole abu na damunta. “Good morning Sir, how are you feeling?” ta gaishesa a hankali kanta a sunkuye.
Beko damu da gaisuwar nata ba damuwansa ya ji abinda ke damunta. “Miss Aleeyu” ya kira sunan ta a hankali. “What’s wrong?” Ya tambayeta cike da damuwa.
Kanta still a sunkuye tace, “babu” a hankali.
“Look at me Miss Aleeyu.” bata ko motsa ba. “Look at me, will you?” ya sake fad’a. Idanunta dasuka cike da hawaye ta d’ago tana kallonsa, sun kumbura iya kumbura dan yadda ta kwana tana kuka, ba kalan hak’urin da su Mani basu bata ba ammsn tak’i dena kukan. “Mr. Fauzi I’m so sorry, I’m terribly sorry mesa baka fad’a min ba? Mesa ka b’oye min abinda Ya Farouq ya maka? Mes-” kukan ne yafi k’arfin ta takasa k’arisa maganan. Baro kujeransa yayi cike da tashin hankali da tausayi ya matso ya tsaya kusa da ita tare da ciro hanky daga aljihunsa yana share mata hawaye,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login