Showing 180001 words to 183000 words out of 268365 words
Chapter 61 - Tana Tare da ni complete book document .txt
tayi zuwa fridge na d’akin hamdala ta saki ganin da akoi cookies da drinks uku ciki. Ledar cookies d’in ta ciro ba makawa ta soma kaiwa cikinta seda taci fiye da rabi sannan ta kora da fanta nan ne tad’anji dama-dama. K’aran shigowar sak’o taji a wayarta kamar wacce barata duba ba sekuma ta miqe ta bud’e taga saqo ne daga Anas ta karanta kamar haka;
_Fannah please in wani abun na miki ki sanar dani stop punishing me like this zuciyana bare iya d’auka ba please Flower I’m missing your smile, body, and fragrance already open the door for me please. I love you #crying_
Wani sabon kukan ta fashe da har k’asa ta sauk’a tana birgima a kan rug na d’akin. Anas dake bakin k’ofar ji yake kamar ya b’alla k’ofar yashiga if only he could. “Fannah please stop crying kinji dan Allah kibari... Kidena please stop it” yayi stating cikin sautin kuka. Zama yayi bakin k’ofar yana hawaye tana kuka.
Isha nayi ya rok’eta da ta tashi tayi Sallah ba gardama ta d’au hijabin ta tayi Sallan kamar yadda shima yayi a parlour bayan yagama shafa’i da wutr nasa ya dawo. “Fannah kifito kichi abinci kinji? I get it bakison sake sani a ido, zan koma d’aki sekin gama infito kinji? I love you.” Yana kaiwa nan ya juya a sanyaye kamar wanda k’wai ya fashe mai a ciki ya nufa d’akinsa bayan minti ishirin ta bud’o d’akinta a hankali, parlour ta nufa dan tattara wajen da plate ya fashe mata d’azu to her suprise taga wajen tsaf ko alaman miya babu tsaf Anas ya share yayi mopping. Dining area ta nufa ta d’iba abincin kad’an se sauri take kar ya fito su had’u gefen flask d’in taga wani paper hannunta na b’ari ta d’aga ta karanta.
_Flower please wear the plaster and cover your wound please kinji? I’m sorry._
Wani sabon kukan taji yana k’ok’arin rufeta ga plaster’n tana gani amman batajin zata iya d’agawa, miyar da paper’n tayi ta ruga d’akinta a guje ta baje kan gado, ta cigaba da kukan daga inda ta tsaya. Bayan shiganta da kamar minti uku Anas yafito daga d’akinsa wajen daya ajiye mata paper’n ya nufa disappointedly yaga bata d’aga plaster’n ba to ko bata fito bane? Flask d’in ya bud’e yaga da alaman ta d’iba abincin mesa bata d’au plaster’n toh?
“Fannah haka kika tsaneni yanzu? Bakiya son koda help d’ina?” Ya k’are maganar da hawaye na gangarowa daga kumatunsa guda. Hannu yasa ya share ya koma bakin k’ofar d’akin ta ya zauna yana sauraron sautin kukanta yana hawaye shima har bakin sa yayi dogo da ce mata tayi shiru amman tak’i.
K’arfe 9:00PM na bugawa ya mik’e “Fannah anan zaki kwana?” Ya tambayeta tana jinsa amman tak’i amsawa dan batada burin sake masa magana a rayuwarta again. “Fannah kifito muje mu kwanta kinji? I can’t sleep without you by myside please kifito.” Sautin kukanta yaji ya k’aru. “Flower kibar kukan nan please...” ba irin rok’ar duniyan da be mata ba amman tak’i bud’e k’ofar ta kuma k’i barin kukan, ga wani uban ciwon kan da ke cinta.
D’akinsa ya koma ya d’ago pillonsa da bargo ya dawo bakin k’ofar d’akinta ya shimfid’a ya kwanta kai be damu da uban sauron Maiduguri ba all he knows is that he don’t want to leave his flower alone. “Fannah goodnight, I love you so much.”
Alokacin da yayi maganan tana kwance kan gado ta d’au tafiya yayi wani irin tsoro taji ya ratsa ta ko kashe wutan d’akin ta kasa, duk’unk’une kanta tayi cikin bargo se b’ari take cike da tsoro. Tafi awa d’ai tana neman bacci sannan a wahale yazo mata. Anas kam sam ya kasa bacci he is missing her in his hands se juyi yake amman ya kasa bacci bare iya kwatanta how he is missing her legs wrapped around his body ba.
*****
2:34AM Firgit Fannah ta farka dan wani erin masifaffen mafarkin datayi. “Anas!” ta kira sunansa da ihu take ya jiyota dake daman baccin nasa beyi nisa ba. “Fannah” ya kira sunanta tare da mik’ewa. “Fannah I’m here kinji?” Kuka take sosai cike da tsoro duk ta duk’unk’une kanta da bargonta ta cusa kanta cikin cinyoyinta se kuka me sauti take. “Anas” ta sake kiran sunansa.
“Yes Fannah I’m here please stop crying bud’e min kinji please I beg you...” Har a yanzu bata bar kukan ba. Zaman gadon ne ya gagareta ta tako zuwa bakin k’ofar ta tsaya adaidai lokacin yake kiran sunanta again “Fannah.” Kuka ta fashe da, yana jin muryarta kusa dashi hankalinsa ya sake tashi. “Fannah, Fannah ki bud’e min kinji? Let me in please.” Kuka take sosai ta inda yakejin sautin kukan nata ya matso tare da had’a kansa da wajen “Fannah I’m here please kibar kukan.”
K’asa ta sulale kamar yana ganinta shima ya sauk’a. Hannunta ta aza jikin k’ofar tare da dafe kanta jikin k’ofar tana me cigaba da kukan. Daidai inda hannunta yake ya aza nasa shima “Flower I’m here you are not alone I’m here with you kibar kukan kinji?” A hankali taji tsoronta na gushewa da dad’ad’d’un kalamun Anas awajen bacci ya d’auketa tun Anas najin k’arfin nishinta har yazo yaji shiru hakan ya tabbatar masa tayi bacci anan ne shima yasamu ya d’an kwanta although sauro sunk’i barinsa saura na masa waqa a kunne saura suna cizon sa farin fatarsa duk yayi pink amman haka ya hak’ura dan baison barin Fannah ita kad’ai ahaka har Asuba tayi bayan ya idar da nasa ya gama addu’o’insa ya dawo ya soma kirar sunanta a hankali cikin baccin tasoma jin sunanta.
“Fannah ki tashi kiyi Sallah kinji? Asuba yayi. Fannah tashi kinji?” A kasalance ta mik’e ta nufa bayi ta d’auro alwala tayi Sallah sannan ta koma kan gado ta kwanta har a yanzu Anas ya kasa bacci. Ko kad’an baijin ma ze iya zuwa office yau, bare iya barin Fannarsa awannan hali ba. Se anan ne yasamu yayi bacci shima 9:45AM ya tashi har anan Fannah na bacci tattara bargon nasa yayi ya wuce d’akinsa yayi wanka sannan yayi shirinsa na kullum fridge ya dosa ya ciro irin sliced potatoes d’innan da ake packaging ya musu frying da omalet ya had’a musu breakfast. Cikin awa d’aya dining table is set agogon hannunsa ya duba yaga 11:02AM knocking yaje yayi a k’ofar d’akinta alokacin da take fitowa daga wanka kenan.
“Fannah kin tashi? If yes good morning kifito ki karya kinji? I love you” yana kaiwa nan ya koma dining ya soma zaman jirarta. Kukan dake son k’eto mata ta shanye simple doguwar riga tasa bak’i me silky jiki. Babban akwatinta ta ciro ta soma tattara kayakinta wanda zatayi amfani dasu ciki. Dam ta cika da essential stuffs nata ba mantuwan da tayi tana gama had’a akwatin ta ja ta rufe sannan ta zira hijabinta dogo har k’asa ta d’au wayarta sannan ta soma ja, a hankali ta bud’e k’ofar ta fito tafiya take kanta a sunkuye da jakarta tana ja daidai ta iso parlour ta bayyana a idon Anas.
Kasa believing abinda idanunsa suke gane masa yayi. What is he seeing? Ina Fannah zataje da wannan babban akwati? Ganin se dosan bakin k’ofa take ya k’urma mata kira “FANNAH PLEASE STOP!” A guje ya nufa inda take, k’ara saurin tafiyar ta take gabanta yasha da wuri idanunsa take suka kad’a sukayi ja. B’ari bakinsa yake kalamunsa suna stammering “Fa.. Fan.. Fannah meh wannan? Ina za kije? Meke faruwa Fannah? Tafiya zakiyi ki barni? Mena miki Fannah? Dan Allah karki tafi in wani abin na miki tell me I’m sorry for everything that I’ve done I’m sorry please karki tafi.” Ya k’are maganar cikin sautin kuka.
Zuciyarta taji ya karye, batasan seda hawaye suka soma ambaliya a fuskarta ba sam ta kasa dena kukan musamman ma dataga alaman cizon sauro all over his face and hands nufin a waje ya kwana yana gadinta jiya. “ Fannah please karki tafi mena miki da zaki tafi? Kiyi hak’uri dan Allah.” Hannunta yayi yunk’urin rik’ewa baya taja da wuri taja akwatin nata tabi ta gefensa da wuri ya rik’o hijabinta. Abin da be tab’a faruwa ba ya faru yau.
Mr. Fauzi ya sauk’e girman kai da duk wani feeling daya keyi ya sauk’a har k’asa akan knees nasa duka biyu. Hawaye yake sosai “Fannah please don’t go dan Allah karki tafi. In wani abun na miki please let me know.” A nitse ta juyo ganinsa akan guiwowinsa ba k’aramin mamaki ya bata ba. Idanunsa a raunane ya d’agosu yana kallonta duk setaji wani iri tasa mijinta kneeling tace masa ya tashi kuma batason sake masa magana ganin yadda yake kuka itama ta k’ara k’arfin nata kukan. Juya masa baya kawai tayi batason ganin hawayensa kamar yadda shima baison ganin nata.
“Fannah turn and look at me please mesa zaki tafi? Mena miki? Kinsan barin iya rayuwa ba ke ba please karki tafi Fannah in wani laifin na miki ki sanar dani dan Allah.” Juyowa tayi cikin sautin kuka ta soma magana har wani sama sama nishinta yake. “Anas are you serious? Bakasan me kamin ba? Kana nufin har a yau baka gane ni ba? Kana nufin baka san yarinyan dake *_TARE DA KAI_* ba har a yau?” Cike da rashin fahimta ya taso “Fannah what are you talking about? Wace yarinya kike nufi?” Hannu tasa ta share hawayenta kamar yadda yayi shima.
“Anas kaine mutumin, kai nake mafarki kullum zaka dawo ka sake azabartar dani kamar yadda kayi 5 years back. Anas don’t you get it? I’m the girl, nice yarinyan... Ni kayi raping 5 years bacm. Nice yarinya from the incident a Bama na yammacin Asabar 23rd of March...” Sekuma ta fashe da wani irin masifaffen kuka.
K’wak’walwarsa kasa d’aukan abinda ke faruwa yayi. Se kai yake kad’awa yana salati a ransa da k’yar bakinsa ya bud’u cike da tashin hankali da rashin yarda yace “no you are not Fannah, you are not the girl inda kece da nayi noticing naki bake bace Fannah baki gane bane taya ma kika sani? I never told you.”
“It doesn’t matter ‘cause I read your diary Anas ni kayi raping. Anas nice yarinyan da ka raba ta da budurcinta, ka cuceni Anas saboda kai nida family na muka bar Bama muka bar ‘yan uwanmu, saboda karya me bin maza da ‘yan unguwa ke kirana dashi muka bar Bama a sanadin abinda kamin, saboda abinda kamin Anas ka rabani da first love d’ina AHMAD wanda yasoni tsakani da Allah, saboda kai na rasa gatana, sabida kai Ya Farouq da Baffah Khaleel suka samu baki suke zagina suna kirana karuwa saboda abinda kamin kasa Baba ya kamu da ciwon zuciya Anas you are the source of my sorrow and fear. Mena maka Anas? Mena tab’a maka daka gommaci ka k’untata min? A rayuwa ba abinda naso kamar in gyara maka rayuwarka and I did mesa ni baka min haka ba? Mesa ka shafawa rayuwata bak’in fenti Anas? Barin iya zama dakai ba, barin iya cigaba da zama da mutumin daya cuceni kamar yadda kayi ba. Ka sallameni in tafi gida ka sallameni inkoma gun Mami na dan Allah karka hanani takarda na. Anas I’ve loved you but not anymore, I thought I could trust you why is the handsome Anas I know turning into a monster? Ka sallameni dan Allah...”
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[12:57, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
7⃣1⃣
Kai yake kad’awa cike da tashin hankali a yayinda zuciyarsa tak’i amince masa da abubuwan da Fannah ta fad’i masa, hawaye yake sosai abin tausayi sam yakasa koda bud’e baki yayi magana because of how shocked he is. Ina ma ace ba’a tab’a qaddara masa wannan rana ba, mesa se Flowersa? Nufi kenan itace yarinyar data ta had’asa da Allah karya mata abin amman ya mata? Just how much pain have he made her gone through? Itace yarinyan datake fito masa kullum a mafarki tana ce masa *_TANA TARE DA SHI_* there’s nomore denying Fannah ce yarinyar mesa betab’a noticing nata ba? Why? Sede a sosai yanajin yatab’a saninta wani wajen amman baya iya tunawa.
Da k’yar bakinsa ya iya bud’uwa cikin wani irin murya cike da nadama yace _“Fannah... Fannah I... I’m so so sorry dan Allah kiyi hak’uri Fannah kece yarinyan kece ita, kece yarinyan danayi taking advantage naki Fannah bansan ta ina zan soma baki hak’uri ba, raping naki danayi shine BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA (littafin rash kardam) if only I can tell you how sorry I am danayi. I’m sorry for everything that I’ve done, I’m sorry for breaking you precious heart. Fannah barin iya baki hak’uri ba tun rananda abin ya faru nasoma living a life full of guilt tun daga ranan nakasa samun sukuni kullum cikin tunani da mafarkin ki nake. Fannah please karki tafi ba’a cikin hankali na na aikata abinda na miki ba I was drunk that evening takaicin abinda Ummimi ne duk ya sani I needed someone to blame it on sekuma Allah ya kawoki path d’ina. Fannah wannan k’addaran ba naki kad’ai bane I know you’ve suffered morethan alot amman kisani nima I did wallahi I will do everything I mean everything inga kin yafemin. Fannah I was just 18 nayi wrecking naki I was young and stupid kema kinsani barin tab’a aikata abin danayi da a baya ba yanzu, kisani ba’a son raina na rabaki da martabarki ba, Fannah ba’a son raina na rabaki da Ahmad, kamar yadda ba’a son raina nasa Baba yakamu da ciwon dayake fama dashi ba dakuma saku barin ‘yan uwanku a Bama. Fannah kece yarinyan danayi spending shekara da shekaru ina nema saboda in nemi gafararta...”_
Matsowa kusa da ita yayi ganin zatayi baya ya dakatar da ita sake sauk’a yayi kan guiwoyinsa ya ajiye duk wani girman kai da feeling nasa a gefe. A raunane ya d’ago idanunsa ya azasu kan kumburarren fuskarta da hawaye ke ambaliya kai. _“Fannah please forgive me dan Allah ki yafemin I’m so so sorry for breaking you heart for making you go all through those meseries, dan Allah kiyi hak’uri nasan banida right na neman gafararki but nasan kinada pure and good heart ki tausayamin kiyafemin please I’m sorry for everything that I’ve done to you, Fannah inda zan iya reversing time in miyar da komai normal da nayi, abinda ya faru ya riga ya faru mu d’ausa as k’addarar a rayuwanmu Fannah I don’t want you to leave please stay with me kamar yadda kikecemin a kullum_ *_KINA TARE DA NI_* _prove it to me. I will never hurt you Fannah this I promise. Wallahi ban tab’a son wata macbayan keba Fannah bame matsayinki a zuciyana koda kuwa Amal ce banida kamarki ki tausaya min karki tafi dan Allah..._ ya k’are maganar cikin hawaye.
Sosai ta tausayawa Anas kalamunsa ba wanda be kwanta mata a rai ba, tana son Anas tana sonsa sosai amman batajin zata iya yafe masa abinda ya mata... Aduk lokacin data tuna da irin azaban datasha alokacin dayayi forcing kansa cikinta cike da azaba da rashin imani ko tausayi setaji barata iya yafe masa ba dukda kuwa a bige yake a lokacin amman still hakan be basa daman yayi raping duk wanda yagani kan hanya ba. Hannu tasa ta share hawayenta har a yanzu idanun Anas basu bar kanta ba ya zura mata jajayen idanunsa yana jiran amsarta yana nan a kneeling position d’in har yanzu.
“Anas dan Allah ka tashi stop kneeling infront of me, katashi please”
“Fannah har senaji kin yafemin baraki tafi ba zantashi kiyu hak’uri please.”
Muryarta daya dishe dan kuka tayi clearing sannan tasoma kamar haka; “zama na dakai ya k’are Anas. Batun yafiya kuwa zan yafe maka Anas saboda d’an Adam ajizi ne musamman ma danasan labarinka nasan duk wani abinda ka aikata na haramun Ummimi ce sanadi ga kuma yadda ka tuba, na gamsu da tubar dakayi. Zan yafe maka duk wani abinda kamin Anas amman hakan bawai yana nufin zan cigaba da zama dakai bane tafiya yazamo min