Showing 195001 words to 198000 words out of 268365 words

Chapter 66 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54115

Hira suka sha sosai da Fannah tama Ummie tayin d’umamen kuwa tace akawo mata haka suka zauna ita da Shettima suka narki tuwon banda Amal dake nan kamar Anas itama wai batachin miyan kuka se bayan Azahar suka tafi.


****
“Kai aman gaskia Habeebi ka iya had’a k’arya sosai fah” ta kwashe da dariya. Banza da ita yayi.
“Habeebi is a liar.” Wani kallo ya watsa mata “ki ka sake kirana liar sena miki abinda baki tsammani Flower.”
“Do your worse” tamasa gwalo “My Baby is a liar” da gudu ta wuce kitchen tasa lock a duka k’ofofin se dariya take masa. “Ai ba kwana zakiyi ciki ba, zaki fito ki sameni.” Ya fad’a mata.
“Zakachi miyan kub’ewan?”
“Bansani ba kikayi abinki ke kad’an ki zakichi.”
“Nida Baby na zamuchi.”
“Babyn da one day zaki haifa ba amman bani ba.”


****
A d’aki ta samesa da laptop gabansa yana d’an aiki. “Baby fito lunch is ready.”
“Banajin yunwa.”
“Tun safe banda chips da kachi me ka sake kachi?”
“Toh laifin wa? Ba kece kike ajeni da yunwa ba.” K’arisowa d’akin tayi ta zauna kan cinyansa tare da zagaye hannayenta a wuyansa. “Kamar ya Baby? Ni ke ajiye ka da yunwa?”
“Eh manah tun jiya kike dafa kalan abincin da bana chi kuma kin sani.”
“Baby ai so nake ka saba bahaushe yace ba kullum ake kwana kan gado ba yanzu for instance in one day kaje Bama ina zaka samu irin abincin nan daka saba chi? ”
“Even still je kichi abincinki ni baran chiba.” Gajeren hot kiss tamasa sannan tayi pecking nasa a kumatu “tashi muje kaji Habeebi na?” Besan a lokacin da yatashi ya bita ba ita da kanta take basa, ba kamar jiyan ba yau yaci kub’ewan sosai sabida yamasa d’and’ano bayan sun k’are chi suka koma d’aki tayi assisting nasa aikin dayake kai.

_10:20PM_
Daidai nan Fannah tagama canzawa cikin wani had’ad’d’en rigan baccinta Anas kuwa akan nickers nasa da vest as always seda ya bari ta kwanta sannan ya hauro gadon ya had’e hannayenta gu d’aya “wa kike kira da liar d’zu?”
“A’a ba kai ba.”
“Nide nine liar ba?”
“A’a Baby ba kai ba dan Allah kar ka min cakulkuli wallahi ba kaiba please karka-” bebari ta k’arisa maganan ba ya fara mata cakulkuli dariya take tana hawaye sosai tana had’asa da Allah sam yak’i bari. Seda ya tabbata ta galabaita sannan ya sake mata hannu ya share mata hawayen. “Next time zaki sake kira na liar.” Se “wayyo cikina” take tayi har a yanzu. D’agota yayi ya kwantar da ita jikinsa seda tagama dawowa hayyacinta ta d’ago kanta “Liar nasake fad’a” bata bari ya soma mata cakulkulin ba ta rufe sa da kiss sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya har wani su juya nan su juya chan suke alokaci d’aya Anas yasoma fita hayyacinsa dan wani irin kisses da Fannah ke masa kamar yadda shima yake mata all over her face and neck, duk sun zurfafa suna romancing junansu. Yasani in beyi stopping kansa ba yanzu he can’t later in kuma hakan ya faru zeyi breaking mata promise daya d’aukar mata before nacewa seda yardan ta abu ze gudana tsakaninsu.


Da k’yar ya iya ya tashi daga kanta yaja baya ya zauna. “Baby meya faru?” ta tambayesa cike da damuwa tana k’ok’arin miyar da hannun rigarta daya fad’i sannan ta matso kusa dashi ta zagaye hannayeta daga bayansa. “What is it Habeebi?”
“Babu” ya amsata blankly.
“Da akoi Baby tell me.”
A hankali ya cire hannayen nata ya juya yana fuskantar ta. “Flower I can’t go further... I..” Sekuma yayi shiru.
“Why can’t you Habeebi?”
“Flower kin manta promise dana miki seda concent naki zan tab’a ki?” Kai ta kad’a nufin ta tuni. “Kinga in ban tsayar da kaina yanzu ba I can’t later lets just sleep.”
“No Baby I’m ready for it.” Ido ya zaro cike da mamaki yana kallonta “Flower me kikace?” kad’ai abinda bakinsa ya iya furtawa dan yadda mamaki ya rufesa.



*© MIEMIEBEE*


beeenovels.blogspot.co.ke
[12:58, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
7⃣7⃣










Wajenta ya nufa ya tab’a body tempreture nata nan yaji ya d’anyi rising. “Flower bakida lafiya” yayi concluding.
“Habeebi kawai stress ne bawani abu ba.”
“Wani aikin kikeyi in natafi? Ba girki bane kawai? Toh wani stress kike nufi Flower? Tashi muje asibiti sekace me sleeping sickess ko da yaushe bacci.” Juyowa tayi tana kallonsa “Baby wai me haka? Yanzu bacci ma barin iya yiba sekace seka kaini asibiti? Lallai fah Allah kacika bin diddigin abu, nikam ma inda zani” tana kaiwa nan ta juya tacigaba da baccinta kallonta ya tsaya yayi sannan ya zagaya ya sameta suka kwantan tare.
“Flower I’m sorry didn’t mean to upset you.”
“You didn’t my Lion nima I’m sorry.”
“Your Lion is hungry.”
“Baby kaifa kace kachi abinci a meeting yanzu kuma kana jin yunwa?”
“Flower bana son tsiya fa sarai kinsan kalan yunwan da nake nufi feed me.”
“Ni gaskia bansani ba” tana kaiwa nan ta juya masa baya chan k’asa-k’asa tace “mutum sekace sex machine ni barin iya ba.” Murmushi sosai ya saki lallai kuwa rabuwansa da ita 2 days now shine take wannan magana?
“Nafa jiki Flower najiki da kyau kuma fushi zanyi.” Take ta juyo “a’a karkayi dan Allah yanzu bacci nakeji kabari ko anjima yi hak’uri lets sleep yanzu koh?” Shiru... “Koh Habeebi? Wallahi ji na nake ba k’arfi” Kai ya gyad’a mata ta matso kusa dashi ta kwanta.


****
Bayan sun idar da Maghrib Fannah ta wuce kitchen dan soya musu scrambled egg a yayin da Anass ke parlour as ysual da laptpp nasa, tana cikin fasa k’wan d’aya ya fad’i ya fashe a k’asa aiko take kitchen d’in ya soma k’arni kafin ta hankara taji bakinta ya cike da amai. Guest toilet ta ruga a guje nan Anas dake parlour shima yabi bayanta. “Anas please karka shigo ka tsaya daga chan” ai kaman shigo tace masa ya k’ariso ciki yana shafa mata baya a hankali se aman take tayi se datayi sosai sannan ya taimaka mata ta wanke bakinta suka fito idanunta se wani kafewa suke a kan 2 seater suka zauna.
“Flower whats wrong? Nafa fad’a miki bakida lafiya.”
“Baby k’wai ne ya fashe so se k’arnin ya fitine ni dalilin aman kenan if not ba abi-” bata k’are maganar ba ta fad’a jikinsa dan wani jiri datake ji yana d’ibanta ko a zaunen ma. “Baby hold me kaji?” ta buk’ace sa. Hannayensa ya zagaye a bayanta “I’m here karki damu” bayanta ya riga shafawa up-to-down na zuwa wani lokaci. “Flower” ya kira sunanta shiru yana leqa fuskarta yaga tayi bacci mamaki ne sosai ya rufesa Ipad nasa ya jawo ya sake daidaita kanta a k’irjinsa sannan shikuma ya kishingid’a jikin kujerar.


Nan ya shiga google yasoma browsing abubuwan dake jawo yawan bacci dakuma amai abubuwa da dama ne suka fiffito masa wanda one by one yake bi yana karantawa dayazo kan wani point seya tsaya yana nazari sekuma ya dawo da kallonsa kan Fannah “it might be true ban tab’a neman Flower tak’i ba se d’azu itan da sometimes ma take nema da kanta, ga wani kasalan da takeji dashi 2 days, ga baccin asara dakuma amai. Flower are you pregnant?” Ya tambayeta chan ciki-ciki.

“Kai anya? Na kusan zama DADDY kenan?! Flower!” yayi whispering a kunnenta “na’am” ta amsa. “Please Baby barin d’an kwanta kad’an wallahi I’m weak.”
“Kiji nace when last kika ga period naki?”
“Baby meya kawo maganan period d’ina kuma anan? Dan Allah barni in kwanta” matso rigarsa tasakeyi a hannunta tare da sake daidaita kanta kan k’irjinsa ta cigaba da baccinta. Duk wannan magana da take kuma idanunta a rufe suke. Jijjik’ata yayi seda ta mik’e ta zauna.
“Ohhh! Habeebi meneh?” Ta k’arisa maganan tana k’ok’arin zama, idanunta da take ta k’ok’arin bud’esu kuwa se kafuwa suke. “Good kinga period naki watan nan?”
“Mesa kakeson sani?”
“Flower mesa kike rashin ji ne waikam? Two days se misbehaving kike kode shima yana cikin symptoms d’inne?” Ya tambayi kansa kasancewar tana kusa dashi yasa tajisa. “Symptoms name Habeebi?”
“Bansani ba ki amsani first.”
“Babu bezo ba amman nasan sooner or later zezo saboda atimes haka yake min, se yayi skipping 4-5 days.”
“Kin tabbata?”
“Eh mana shikenan? Zan iya komawa baccin?”
“A’a kitchen d’infa? Wa zeyi mopping wajen da egg d’in ya fashe?” Fuska ta maraice “Baby wallahi k’arnin amai yake sani kuma ma banjin inada k’arfin mopping inaji na ba k’arfi ko kad’an ji nake kamar nayi aikin d’aga block please kabari gobe in masu aiki suka zo senayi kaji Baby?”
“Another symptom” yace da kanshi nanma ta jisa. “Wai wani symptom Baby?”
“Flower look at me” nan ta maido da kallonta a agaresa.
“Don’t you think you are pregnant? Mun kusan zamowa Daddy and Mammy?”
Cike da rashi yarda tayi maganan, “Kana nufin wai ciki ne dani?” Ta k’are maganar hannunta kan flat cikinta, hannun sa shima yabi ya aza akan nata dake cikinta “sosai ma kuwa Flower karanta nan kiga” nan ya miqa mata Ipad d’in data gama karantawa kuma setaga almost all yadda take feeling haka aka yita bayani ciki toh ko dagaske ne tana da ciki? Ta kusa zama Uwa kenan itama?
“Flower what do you think?” maganarsa neya tsamota daga tunanin da takeyi.
“I think yes!” Ta fad’a delighted cike da jin dad’i. “I think so too Habeebi I might be pregnant!”
“Yes Flower” hannunta yacire daga cikin nata ya sa nasa kai “we have a baby in here.” Hannunsa ta cire ta aza nata kan cikin “tsaya let me feel it.”
“No!” ya zare hannunta ya d’aura nasa kai “ki tsaya inyi feeling first bani ne babba ba?” Nan ta sake cire hannunsa “sekaci girma ai kabarni inyi feeling nasa first, nida ciki na abeg d’aga min hannunka.”
“Cikinki ko cikinmu?” Haka suka tayi Anas yak’i cin girma yabar Fannah ta fara feeling Babyn nasu kamar yadda itama tak’i cin k’ank’anta. Seda tagaji ganin Anas baida niyan barinta kawai ta barsa yafara feeling hannunsa yafi minti biyu kan cikinta yak’i d’agawa.


“Toh ai haka yayi nima let me feel my Baby.”
“Flower Allah kika sake cewa Babynki zamu b’ata. Its our Baby.”
“Toh our Baby, kasan meh?” Kai ya kad’a mata. Matso da kansa tayi ta rad’a masa wani abu a kunne.
“LOL yes I am Flower, so gobe zamuje asibiti?”
“Muje muyi meh kuma Habeebi?”
“Muje mu tabbatar da cikin naki mana ayi scanning.”
“Shine se munje asibiti?
“Yes Flower.”
“A’a nikam barinje ba zan saya pregnancy test strip in gwada da kaina a gida ba se munje asibiti ba.”
“I know Flower but still yakamata muje kinga zamu san how many weeks ne pregancy nakin and za’a bamu shawarwari dayawa kinga this our first time.”
“Nikam gaskia Baby kayan kunyan nan badani ba.”
“Wai wani kayan kunya Flower? Ciki abin farin cikin ne kuma abin kunya yanzu?”
“Eh mana Baby kowa de yasan ta yadda ake samun cikin nan ni kawai mu rufa wa kanmu asiri kar muje.” Dariya sosai ya tsaya yanayi “Flower you are too much to meh? Suma haka akayi aka haifesu kowa ma haka akayi aka haifesa I see nothing wrong with that.”
“Nide ba ‘yar iska bace barin jeba” tana kaiwa nan ta mik’e aiko seconds talatin batayi ba ta fad’a kujeran ta dan jiri da sauri ya taro ta. “Flower fa dole muje asibiti final decision.” Chak ya d’agata yakaita d’aki black tea ya had’o mata bayan tasha yajasu Sallah wanda rabinsa ma a zaune Fannah tayi dan jiri.


_Washegari..._

Asuban fari Anas ya tashi bayan yayi alwala ya taimakawa Fannah ma tayi suna idar da Sallah suka koma suka kwanta sede unlike jiya yau jikin nata da zafi amman ba chan chan ba gudun karwani abu yasamu lafiyan babynsu yasa Anas yabata paracetamol kad’ai tasha cikin ikon Allah yamata aiki kuwa, k’arfe shida ta tashi as always taje ta had’a musu breakfast hancinta toshe da hanky dan gudun k’arnin fashasshen k’wan bayan tagama ta jera dining sannan taje ta tada Anas.
“Baby katashi kayi wanka kaji?” Bayan ya bud’e idanunsa ya k’are mata kallo bakomai ne d’auke a idanunta ba banda kasala.
“Flower kinyi wani aiki neh?”
“Breakfast kawai na shirya mana se ruwan wankan ka tashi kashiga.”
“Flower why? Daga yau banason ki sake yin wani aiki kinji? Its not fit for your condition.”
“Baby bamu ma tabbata ko cikin ne dani bafa tashi kayi wanka” towel nasa ta mik’a masa nan danan yayi wanka yashirya sannan yafito suka fara breakfast kad’an daga cikin fried egg d’in Fannah taci ya sata amai aguje ta ruga bathroom shima Anas yabi bayanta yana shafa mata baya, amai ta rigayi abin tausayi, data gama ya tayata kimtsa kanta suka fito tana manne a jikinsa dan jiri.
“Flower bara muje asibiti ba?” Kai kawai ta iya ta gyad‘a mai. “Sorry kinji? I can’t leave you alone like this.”
“Me kake nufi Baby?”
“Nafasa zuwa office I will take care of you.”
“Common Habeebi karka damu I will be fine je ka gama breakfast naka kaji? I love you” peck ta manna masa a kumatu da k’yar tare da komawa ta lume cikin kujeran.
“Flower in kaiki d’aki?”
“Nanma yayi kayi sauri.” Mik’ewa yayi yaje d’aki yafito da blanket bayan ya kunna AC ya lullub’eta dashi sannan yayi pecking nata a goshi. Dining ya koma yayi rushing ya gama breakfast nasa, wayarsa ya d’aga dan kiran Kacallah ya fad’a mai bazasa office ba yau yaga Kachallan na kiransa. Bayan yayi picking Kacallah ya gaishesa “Sir na kira ne dama in tuna maka meeting da zakuyi da board of directors na F&C Enterprises regarding 2% shares nasu da zasu siyar mana dakuma investing da zamuyi.” Kallon sa ya miyar kan Fannah ji yayi bare iya barin ta haka ba dan kuwa batada lafiya. “Hello Sir?” Cewar Kacallah dan jin shiru.

“Kacallah baraka iya presenting d’ina ba? My wife is sick I’m afraid barin iya barinta ita kad’ai ba.”
“Ayya my regards please kuma Allah ya sawaqa unfortunately I can’t Sir dole se kai in ba haka ba barasu siyar mana ba kuma kasan we can’t lose this oppurtunity please Sir.”
“I will see to it” nan yayi hanging. Wajen Fannah ya nufa ya zauna a gefenta. “Flower” ya kira sunanta.
“Na’am” ta amsa a kasalance.
“How are you feeling? Ki fad’a min tsakanin ki da Allah karkimin k’arya.”
“Baby kasala ne kawai sekuma zuciya na dake yawan tashi thats all.”
“Bakiya feeling feverish? (zazzab’i)”
“Kad’an ba.” Ta amsa shi.
“I can’t leave you like this zanyi canceling meeting d’in.”
“Wani meeting Baby? Bade na F&C Enterprises ba!”
“Shi Flower barin iya barin ki haka ba.”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login