Showing 24001 words to 27000 words out of 268365 words
Chapter 9 - Tana Tare da ni complete book document .txt
zakizo in baki details d’in plus don’t be late bana jiran mutum sede a jirani.” Shiru tayi tana mamakin wannan bawan Allah. “Are you there? Cause bana repaeating kaina twice”
“Yes I’ll be on my way.” Nan ya katse wayar. Tsuka takuma ja “lallai akoi arrogant people dayawa a duniya what is he feeling like? D’an Adam de ba wanda yafi wani we are all equal.” Asma’u dake kallonta tace, “ji yadda kike magana sekace bakisan Anas ba.”
Fannah tace, “Anas? Waye shi?”
Asma’u tace, “no wonder sesa kike tada jijiyoyin wuyanki haka, ni rananda ya kira na d’aga bakiga zagin duniyan daya min ba aike yamiki mutunci ma.”
“Toh waye shi? Whats he feeling like?”
“Shine PA’n Mr. Muh’d na Flames Enterprises kuma ance Mr. Muh’d nasan sa tamkar d’an cikin daya haifa, cewa ma yake Anas d’in d’ansa ne.”
“Ikon Allah! Lallai kam.” cewar Fannah cike da mamaki.
“You better go kafin yasake kira ya balbale ki.” A sanyaye Fannah ta fice bata tsaya ko inaba se Flames Enterprises can akayi directing nata zuwa office na Anas tsaye take a bakin k’ofar office nasan takasa shiga zuciyarta se bugawa take musamman ma data d’aga kai taga ansa *Mr. Fauzy* asaman. Tafi minti biyu tsaye a wajen sannan jiki na k’yarma hannu na b’ari tayi knocking k’walli d’aya tal jin ba’a amsa ba yasa ta k’ara d’aya “come in” taji muryan na miji ya fad’i authoritatively. Tabbas tasan wannan murya shine wanda yace mata thank you rananda Mr. Muh’d ya bata bandir na N500 kawai haka taji zuciyarta na bugawa tarasa dalili.
Numafashi taja sosai sannan ta bud’e tashiga. Wannan office shi ake kira da Aljannan duniya tana shiga k’amshin turare ya buga mata hanci ga wani uban sanyin da office d’in ya d’auka ko ina tsatsaf yake files, papers da books duk anyi arranging nasu. Hijabinta iya guiwa takuma daidaita sa sannan tayi sallama.
“Salamu alaikum” mutum ta hango kan kujera da P cap (facing cap) akansa wanda ya b’oye kamanninsa. Sanye yake da black long sleeve shirt wanda ya mugun amshe farar fatarsa me kyawun gaske. Yanada fad’i dadai, na matashi ne me jini a jik’a. Laptop ne a gabansa se faman danne danne yake akai he is si focused akai, can yad’an tsaya ya sha wani abu cikin cup wanda Fannah batasan ko ruwa ne ko juice ba can ne tagane ashe soda ne.
“Zaki iya dena kallo na haka dan ba TV bane ni, and you don’t knock and say Salamu alaikum all at thesame time you choose either one.” Ya fad’i batare da ya d’aga ido yaga kowaye bane. Kunya taji kamar ta nitse k’asa dan kunya “taya yasan ina kallonsa toh?” Ta tanbayi kanta a zuci. “I'm sorry” ta fad’i cikin muryar ta dake b’ari.
*I'm sorry nasan chapter’n nan yayi gajere sosai compared to other chapters d’in bayan nawa ne har yanzu na ciwo. In shaa Allah zan yi k’ok’ari inyi dayawa gobe. Thank you for the lovely prayers and warm concern. I love you all*
*© miemiebee*
beeenovels.mywaoblog.com
[16:09, 12/19/2016] Swtbaby: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
1⃣1⃣
Bayan tafiyan Ya Khaleel bada jimawa ba su Mami suka dawo gida, Fannah na d’aki tana kukan cire rai bata ma ji shigowansu ba kawai ganin Mami tayi tsaye a kanta take ta soma share hawayenta “sannu da zuwa Mami, yaushe kuka dawo?”
“Habibti kukan me kuma kike? D’an mayen can yazo ne?”
“A’a ba kuka nake ba Mami, inasu Afrah?”
“Fannah ga idanunki sunyi ja sun kunbura, fad’a min meneh? Keda waye?”
“Ya Khaleel ne yazo...” Nan ta irga mata duk abinda yafaru tana kuka.
Rungumota Mami tayi “Shikenan yi shiru in shaa Allahu Kawu da d’ansa barasu k’arisa da duniya lafiya ba, mugayen mutane kawai bar kuka kinji? Akoi Allah Fannah always have this at the back of your mind, in shaa Allah baraki auri Farouq ba.”
Hannu tasa ta share hawayenta, “Mami ni nasan zan auri Farouq ba abinda zamu iya Ya Khaleel yariga ya gama komi.”
“Fannah kin cire rai daga Allah kenan?” Kad’a kai Fannah tayi “toh ki bar fad’in haka, Allah ba azzalimin bawansa bane. Allah da kansa yace a Qur’ani auren mazinaci se mazinaci aikinsani koh?” Kai Fannah ta giad’a “toh kibar kukan ya iso mik’o mai in taje miki gashinki.” A sanyaye ta mik’e ta d’auko mai da comb mama ta taje mata gashinta takama mata gu d’aya sannan ta bata waje tasa kaya. Itakuwa ta fice zuwa d’akin Baba.
Kwance ta samesa, “Malam ya jikin?”
Baki na k’yarma yace, “da sauk’i.”
“Sannu, Malam ko kanada labari d’azu Kawu yazo ya cicci mutuncin Fannah? Duk nazo na sameta se kuka take.”
“Eh..Mam.. Maman Aiman saisa yazama dole in siyar da gwalagwalen da Umma (mahaifiyarsa) ta tab’a bani dana ajiye kan duk sanda Fannah tazo aure se in sayar mu mata kayan d’aki amman tunda ga yadda abu ya kasance dole mu siyar yanzu...” Tari ya tsaya yayi sannan ya cigaba.
“K’ark’ashin wancan akwatin akoi d’an kunne da sarqa da zobe dakuma warwaro guda hud’u na gwal, da ace ina da lafiya da a gobe zan jeni Maiduguri in siyar amman gajan haka yasa dole seke zaki Maman Aiman.”
“Ina jinka Malam, in mun siyar me zamu da kud’in?”
“Gidan nan zamu bari, garin nan zamu bari gaba d’aya mukoma Maiduguri inason bayan kinje kin siyar da gwala gwalen ki kama mana gida me arha koda 2 bedroom ne kawai wanda zamu iya affording, sekuma da essential abubuwan da zamu iya bu-” tari ne ya tsaida sa sosai.
“Malam shikenan ya isa nagane kar jikin ka ya tsananta. Amman Malam bara mu tafi da kayakin mu ba? Inaga zefi mana sauk’i inda hali ma gidan nan se mu siyar.”
Gyaran murya yayi sosai “inaaa... hakan bame yuwu wa bane Maman Aiman mukayi haka ai kamar mun fad’awa duniya zamu bar garin Bama ne kisani no one must know about this. Fannah kawai na yarda ki fad’a mata itanma dan mu cireta daga damuwa ne kuma ki gargad’e ta karta kuskura ta fad’awa Afrah kar da baki taje cikin jama’a ta tona mana asiri. Dan maganan nan na fitowa fili shikenan namu ya k’are dole Fannah zata auri Farouq, ni na fad’a miki.”
“In shaa Allah Malam, Allah kaimu goben zan wuce Maiduguri dan kasan matsalar samun gida, in bamu soma nema a kan lokaci ba zamu makara har lokaci ya k’ure we have just a month.”
****
“Fannah habibti. Fannah!” Kirar Mami dake tsaye daga bakin k’ofa.
Sanda Fannah takai k’arshen ayan datake karantawa sannan ta amsa “na’am Mami am sorry bansan yanke ayan ne.”
“Bakomai karatu kike ne?”
“Eh Mami wani abu ne?”
“Ina Afrah da Aiman?”
“Suna can parlour suna assignment.” Fannah ta amsa a takaice.
“Oh toh magana daman nazo miki.”
“Toh bismillah Mami” nan Mami ta k’ariso ciki tare da rufo k’ofar tayi joining Fannah kan katifar sanan a hankali ta sanarda Fannah abinda ita da Baba ke da shirin yi. Sosai Fannah taji dad’i harda hawayen nin dad’i.
“Mami dagaske kike? Zamu koma Maiduguri barin auri Ya Farouq ba?”
“Sosai Habibti ai dama na fad’a miki koda bamuda komai munada Allah, kuma Allah ba azzalimin bawa bane kamar yadda na fad’a miki gobe zani Maiduguri.”
“Toh Mami in bi ki mana muje tare.” Cewar Fannah tana share hawayen jin dad’i.
“A’a Fannah kinsan Kawunki wane bodyguard haka yake kusan kullum seya zo gidan nan inkuma yazo bani ba ke kinsan dole yayi bincike the moment asirin mu ya tonu kuwa kinga dole sekin auri Farouq. Saboda haka ni kad’ai zanje addu’a kawai zakimin Allah sa inje a sa’a in dawo lafiya.”
“In shaa Allah Mami Allah baki sa’a. Nagode sosai, keda Baba kun gama min komai aduniya Allah biyaku da gidan aljannah.”
“Ameen Habibti barin koma in had’a akwati na.”
“Toh muje in tayaki shiryawa.”
“A’a Habibti zanyi dakaina, go on da karatunki.”
“Toh Mami.” Har Mami takai bakin k’ofa Fannah ta danna mata kira da
“Mami!”
“Na’am Fannah.” Ajiye Qur’anin dake hannunta tayi ta ruga gun Mami da gudu tayi hugging nata “Jazakumullahu bikhairan keda Baba nagode sosai, Allah sak’a muku da gidan Al-Jannah.”
“Ameen Habibti Allah miki albarka kema.” “Ameen” ta ce sannan ta sako Mami tana kallonta har sanda ta shige d’akinsu da Baba. Sujjada tayi tana gode wa Allah sannan tashiga bayi tayi alwala tayi nafila raka’a biyu tare da sake gode wa Allah ji tayi kap matsalolinta sun gushe. Kan katifar su ta fad’a se murmushi take.
****
_4 days later..._
“Oyoyo Mami! Oyoyo Mami!” cewar Aiman tana daka tsale. “Oyoyo auta ta” Mami ta d’aga ta sama. Nan su Fannah suma sukazo suka mata oyoyo. Kwanan Mami uku a Maiduguri tadawo, tafiyar ta kuwa was a success kap addu’o’insu Allah ya amsa musu. Kud’in data samu bayan ta sayar da gwala gwalen ta kama musu gidan haya 2 bedroom dashi a unguwar jiddari polo, na shekara, seda katifu guda biyu da d’an kayan abinci da kayan kitchen. Alhamdulillah!
_2 weeks later..._
Farouq ne tsaye bakin gidansu Fannah shi a dole yazo ganin matarsa nan da sati d’aya da ‘yan kwanaki zata zama mallakinsa tsabagen iskanci ba abinda yake imagining illa first night nasa da Fannah. Wani almajiri ne yazo wucewa take ya tsaida sa “kai shiga nan kace wai inji Farouq matarsa ta fito.” Da “toh” yaron yashiga gidansu Fannah suna zaune tsakar gida suna tsintar shinkafa ita da Afrah.
Ita kanta Afrah mamakin yadda Ya Fannah ke walwala kwana biyu ke bata kukan data sobayi safe rana dare yamma duk tadena yanzu, dukda batasan reason nayin hakan ba itade tana ma yarta murnan dawowar farin cikinta.
“Assalamu Alaikum” cewar almajirin. “Wai inji Farouq wai matarsa tafito” dadai lokacin Mami tafito daga kitchen. “Me kace?”
“Farouq ne ya aiko ni wae matarsa ta fito.”
“Dan ubansa kace barata fito ba yaushe tazama matartsa? Fice kabani waje.”
“Almajiri tsaya” cewar Fannah “kace masa ina fitowa.” Kallo Mami ta watsa mata “Fannah baraki fita ba kinsan wannan d’an mayen yanzu seya saki kuka ki zauna.”
“A’a Mami kibari inje ai ba abinda ya isa yamin a waje a idan mutane, kiyi hak’uri.” Mami zata sake magana Fannah tace, “please Mami.” Da d’aga kan da Mami tamata Fannah ta shiga ciki ta d’au hijabinta sannan ta fice a zaune ta samesa kan benchi da alama yau ba a buge yake ba.
“Ke zo nan kizauna yaci ace kin saba dani yanzu, nan da ‘yan kwanaki zaki zama tawa.” A zuci Fannah tace, _taka? never! Allah ya riga ya kare ni daga auren mazinaci kamar ka._ Kawai jin hannun sa tayi kan kumatunta firgit ta matsa baya. Yasake matsowa kusa da ita “wai tunanin me kike haka? Kode tunanin first night namu?” Ya d’an murmusa “karki damu I'll take it easy on you” batace dashi komai ba illa kallonsa da take.
“Ke wai yau azumin magana kike ne?” Juyawa tayi zata tafi ya danna mata kira cak ta tsaya bata tanka sa ba. “Kiyi sha’aninki iya san ranki kimin rashin mutunci iya san ranki amman kisani nan da sati d’aya da ‘yan kwanaki ni zanna ja miki aji. You can go daman nazo inga kyakkywar fuskarki ne kafin na wuce bayan gari.” Kai kawai takad’a tashige ciki.
Tsaye ta tarar da Afrah da Mami da damuwa karara a fuskarsu. “Ya haka Mami wani abu ne?” Ta tambayesu
“Farouq fa inade be miki komai ba?” Cewar Mami.
“Kai Mami da Allah ki kwantar da hankalinki Mami, kema haka Afrah ba abinda Ya Farouq yamin banda suratan banzan daya saba wai yanzu haka ma bayan gari zasa.”
“Shege mazinaci” cewar Mami. “In shaa Allahu baraki auresa ba.”
“Amman Mami yau fa sauran sati d’aya da kwana uku ne bikin anya akoi abinda ze hana aukuwan wannan aure?” Afrah ta fad’i cike da damuwa.
“Akoi Allah Afrah, always have this at the back of your mind. Jeki huta Fannah nida Afrah zamu gama girkin.”
“Toh Mami, ina Aiman tazo mu mata tsifa.”
_3 days later..._
Ana saura sati bikin Fannah da Farouq. Ya Khaleel ne tsaye cikin tsakar gidansu Fannah. Mami, Fannah da Afrah suna tsaye kansa. “Toh nide nafad’i nawa tun ana wata bikin nan na fad'awa Fannah ta sanar dake batun gadon nan gashi har yau baku sai ba wallahi zakusha mamaki dan kuwa amaryarku kan tabarma zata kwana. Wasu erin matsiyata ne ku? Ace ‘yarku zatayi aure ko gado kun kasa yi mata? Wai ahaka ma dan na d’auke maku nauyin kayan kitchen. Allah wadar in erinku wallahi.”
“Kawu kayi hak’uri nan da ‘yan kwanaki zan kwashe adashe na se in sai wa Fannah gadon dan Allah ka k’ara hak’uri.” Cewar Mami.
“Wannan kuma ku ya dama, ko ku sai gado ko amaryarku tayi kwanan tabarma. Ni na tafi.”
Yana ficewa Mami taja hannun Fannah sukayi d’aki gudun kar Afrah ta fahimce wani abun. Itade Afrah tasoma zargin abu da a da ne Kawu yayi wannan magana definately Fannah zatayi kuka sega yau ko nuna damuwa batai ba.
Da daren ranan Fannah da Afrah suna zaune d’akinsu Aiman tayi nisa a bacci. Afrah tafi minti biyu tana kallon Fannah har sanda tasa ta tsarguwa. “Afrah wannan kalo haka?” Cewar Fannah tana duba pages nawani Government text book.
“Ya Fannah kallen.” D’ago fararen idanunta tayi wanda suka sha bak’in kwalli ta azasu kan Afrah. “Na kallekin” tace. “Kina b’oye min wani abu kinsan na sanki fiye da yadda nasan kaina I can tell in kina b’oye min bu.” Cewar Afrah
“Me zan b’oye miki Afrah? Kawai de inajin dad’i ne.”
“Dad’in me fah? Dad’in zaki aura Ya Farouq??” Ta tambaya tare da d’age gira.
Dariya kad’an Fannah ta saki “ko kad’an Afrah ina murna ne saboda inaji ajikina barin auri Ya Farouq ba.”
“Toh Ya Fannah Allah sa, kinsan happiness naki ya fiye min komai a duniya.” Hugging junansu sukayi cike da so da k’aunar juna.
****
_Ana saura kwana biyu biki..._
Da misalin k’arfe 8:00AM
“Farouq! Farouq!” Kiran Ya Khaleel yana zaune kan tabarma. “Na’am Baba” Farouq ya amsa yana isowa sannan yasamu waje ya zauna.
“Ni ya jiya ka had’u da Fannah kuwa? Mahaifiyarta tace mun cikin satin nan zasu kawo gadon gashi saura kwana biyu bikin naku basu aiko ba. Anya mutanen nan lafiya kuwa?”