Showing 102001 words to 105000 words out of 268365 words
Chapter 35 - Tana Tare da ni complete book document .txt
hankali.
“Yes Sir” ta amsa ba tare da ta d’ago kai ba. “Make me coffee” ya fad’i. A sanyaye ta juya ta nufa wajen machine d’in sede hankalinta ko kad’an baya jikinta tayi nisa tunanin abubuwan da suka faru jiya she actually can’t believe Baffah Khaleel da d’ansa Ya Farouq sun dawo suna san maida ita Bama da bata sake tsammani zata koma wataran ba.
Bayan ta gama had’a jagual-gualenta ta juyo dan ba coffee ba sunan abinda ta had’a. D’an k’usa ne ya kama mata hijabi agarin cirewa tayi b’arin coffeen duka ya zube a k’asa cup d’in kuma ya fashe. Kid’imewa tayi a lokaci guda batasan lokacin da ta tsuguna ba dan tattarawa. “Don’t Miss Aleeyu karki ki tab’a” Anas yayi warning nata da ihu chak ta maida hannunta. “I’m sorry” ta fad’i hawaye na cikowa a idanta. “I’m sorry please” ta sake basa hak’uri.
Toh kuma kukan meh? Ai be tab’a taba, bekuma mata masifa ba kodan d’an ihun dayayi dan kar ta tab’a glass d’inne ya sata kuka? Tasowa yayi daga mazauninsa ya nufo gabanta har yanzu tana tsugune “get up” yace mata. A hankali ta mik’e kanta sunkuye se hawaye takeyi side bag nata ya mik'a hannu yaja a hankali, batace masa komai ba, bud’ewa yayi ya ciro handkerchief daya batan “wipe off your tears” amsa tayi ta na gogewa sede the more tana gogewa the more kukan yake k’aruwa harda me sauti da k’yar ya zaunar da ita.
Besan me ba se kawai yaji ya damu da ita bayasan ganin ta tana kuka. “Miss Aleeyu mesa kike kuka na miki wani abu neh?” ya tambayeta a hankali. Kai ta kad’a masa da nufin a’a tana me cigaba da kukan.
“Toh mesa kike kuka? Sabida glass cup da kika fasa min ne? Don’t worry I have lots more.”
Kukan take har yanzu ba makawa hasali se k’ara volume na kukan nata ma take. “Miss Aleeyu what is it?” Kai kawai take kad’a masa chan ma ta tashi ta ruga office nata a aguje kan table nata ta baje sekuka take shark’af shark’af abin tausayi. Anas nason bin bayanta amman girman kai irin nasa bare barsa ba. “For goodness sake what is wrong with me? Mesa nake damuwa da Fannah? She is not my responsibilily so let her be, duk abinda ke damun ta ita taji wajen.” Mik'ewa yayi tare da zama kan kujerar sa yana me cigaba da abinda yakeyi. Sede inaa mind nasa gabad’aya yana wajen Fannah. What if har yanzu kuka take? Me aka mata ko daga gida ne aka b’ata mata rai? Wayarsa ya d’ago dan kiran Mami se in ya soma shiga se ya katse haka ya kasa kirarta dan tambayen meke damun Fannah. Meeting dayake dashi ma yau shi kad’an sa yaje saboda yasan there will be no point yaje da Fannah tunda haka ta taho yau tana kuka. Shi kad’ansa yaje though shima duk hankalin sa na kan Fannah bayan da meeting d’in ya k’are as usual driver ya wuce dashi hotel dan cin abinci.
Ga abincinsa a gabansa amman yakasa chi, dududu sau nawa suka chi abinci da Fannah amman yaji yau inba ita bare iya chi ba kuma bawai fa baya jin yunwa bane kawai seda ita ze iya chin abincin. Kacallah ya kira kan ya sanar da Fannah driver ze zo d’aukanta yanzu dan bayasan ya kirata da kansa ta raina sa, hakan kuwa akayi bayan 20minutes aka kawo Fannah hotel d’in tana shiga tagansa zaune dan bata masan nan za’a kawo ta ba ce mata kawai akayi Boss na nemanta. Idanunta sun kumbura sunyi ja dan kukan datasha a hankali ta k’arisa gaban table nasa ta tsaya ba tare da tace uffan ba.
“Sit” yace mata hakan ko tayi bada jimawa yasa aka kawo mata abinci sak irin na jiya. Nan ma “eat” yace mata.
“I’m not hungry” ta masa k’arya dan kuwa ko breakfast batayi ba yunwa takeji amman batada appetite na cin abincin saboda damuwar dake kanta kad’ai ya isheta. Spoon biyar yakai yaga ko yunk’urin tab’a abincin ta batayi ba.
“Miss Aleeyu bakiya so ne akawo miki wani daban?”
Kai ta kad’a masa. “Then why are you not eating?”
“Sir I’m sorry bana jin yun-” bata k’are maganar ba cikinta yayi wani irin kuka.
“Yes kinajin yunwa eat.” Nanma kai ta kad’a masa. “Kichi kokuma in baki 500 papers kiyi correcting nasu” ya gwada taorata ko dan haka zata chi. “Okay I’ll do it in muka isa office d’in.” Mamaki sosai amsarta ya basa itan da kullum take had’asa da Allah in ya bata aikin yau ita ke fad’in zatayi kai tsaye? Toh meke damun ta?
“Miss Aleeyu meke faruwa? Meke damunki? Tell me.” Ya tambayeta cikin sanyin murya dan duk yashiga cikin damuwa ganin Fannah a damuwa.”
“Babu Sir thanks for your concern, zan jiraka a waje in ka gama se mutafi in fara correcting papers d’in da wuri saboda in gama on time.”
“Barakiyi correcting komi ba, I don’t mean it kawai kichi abincinki kinji? You are sick har yanzu zama da yunwa won’t help, eat.” A hankali ta d’aga spoon nata ta soma ci sede ba hab-hab kamar yadda ta saba ba. Anas ko da jimawa yagama cin nasa yayi zaman jiranta saba’anin yadda ya saba. Dududu quarter kawai taci tace ta k’oshi. “Are you sure?” Ya tambayeta kai ta gaid’a masa. Bayan ya biya kud’in suka fice.
Shigarsu mota Anas yace da driver “ba office zamu wuce ba gidansu Miss Aleeyu zaka kaimu.” Cike da mamaki ta d’ago kai se yanzu suka had’a ido dashi tun had’uwansu yau. “Gidan mu kuma Sir? Mesa?”
“Saboda inji meke damunki.” Yabata takaicaccen amsa.
“No Sir please don’t ba abinda ke damuna kawai fad’a mukayi da Afrah” tanasa k’arya
“Ban yarda ba” ya bata amsa yana duban agogon sa.
“Sir I’m serious.” Ita tsoronta kar in sunje su had’u da Baffah Khaleel kamar yadda ya saba kiranta da karuwa ko karya ya kirata gaban Anas. “Sir please mu juya na bar wayana a office I need to get it.” ta masa k’arya ko ze canza mind nasa.
Resting kansa yayi jikin kujerar “karki damu zansa Ahmad ya kawo miki.”
“Sir-” hannu ya aza kan lips nasa “shhh! Banasan surutu dayawa.” Ahaka har suka iso gaban gidansu Fannah zuciyarta se bugun d’ari d’ari yake. Driver na parking Fannah ta fito da sauri dan duba ko su Baffah Khaleel suna gida takai da shiga k’ofar gidansu kenan kawai suka ci karo da Ya Farouq kafin tayi wani k’wak’waran motsi ya cafko ta da hannu daidai lokacin Anas yake fitowa daga motan shima, idanunsa basu tsaya ko ina ba se kan hannun Farouq rik’e dana Fannah se k’ok’arin k’wata take amman ta kasa. Wani erin mahaukacin kishi yaji ya bugesa inba wai kashe koma waye mutumin yayi ba yana ganin bare samu sukuni ba.
A fusace ya k’ariso wajen. “Matata me haka dan na kama miki hannu? Ke wai bakiyi missing d’ina bane? Ko d’an shafaki bara ki bari inyi ba?” Cewar Farouq dawani shu’umin murmushi fal a fuskarsa.
“Ya Farouq ka sake min hannu niba matar ka bace let me go” ta fad’i tana hawaye tare da k’ok’arin k’wace hannunta.
“Ka sake mata hannu!” Anas ya fad’a cike da isa. Fannah da Farouq tare suka juya suna kallon Anas. “Waye kuma wannan baturen?” Farouq ya tambaya.
“Mr. Fauzi please ka tafi, don’t involve yourself in here.”
“Kinsan sa kenan” Farouq ya sake tambaya. “Bade shima saurayin ki bane kina kwana dashi, kinsan sana'a sa’a.” Anas be san lokacin daya kai wa Farouq naushi a fuska ba da zobobin azurfa a hannunsa. Take hancin Farouq ya fashe gefen bakinsa yasoma na d’igan jini.
*© miemiebee*
beeenovels.mywapblog com
[12:52, 12/18/2016] +234 903 612 6826:
•° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
4⃣2⃣
Baki Fannah ta bud’e tare da aza hannunta bibbiyu kai cike da mamaki da tsoro duka. Hannu Farouq yasa tare da tab’a inda yaji moisture a fuskarsa yana dubawa yaga jini ta hanci da bakin sa, “Kai! Ni ka fasawa baki? Dama nasha jin cewa ku turawa bakuda tarbiyya yau zan koya maka.” Hannu ya d’aga da k’arfin da Allah ya bashi shima ze kai wa Mr. Fauzi punch ai karap Anas ya kama hannun nasa tare da murd’awa cike mugunta ta bayansa. K’ara sosai Farouq ya saki dan azaba.
Fannah duk ta rikice “Mr. Fauzi please ka sake sa ya isa please” ko saurarenta Anas beyi ba k’ara murd’a hannun nasa yayi a bayansa k’ara sosai Farouq ya sake saki dan azaba. “Repeat what you just said.” Anas yace dashi, daga yadda yake magana ma kad’ai za’a san ransa a b’ace yake, na bala’i ma kuwa. Duk zafin da Farouq ya keji be hanasa misbehaving ba. “K’arya nayi dan nace kuna kwana tare karuwarka ce”
“You really want to die” Anas ya sake shi, kafin Farouq ya sake wani k’wararren motsi Anas ya sake kai masa punch a fuska fiye da yadda yayi d’azu sosai jini yake fita daga baki dakuma hancin Farouq.
“Mr. Fauzi please ya isa dan Allah” Fannah ta fad’i duk a kid’ime idanta tuni suka cike da hawaye.
“Kai ko kasan waye ni? Mijinta ne fa ni, aurenta zanyi banza da kai zakazo kana intruding. In ita karuwan kan bata fad’a maka yanzu ai kaji I’m her husband. Ke Fannah dan iskanci ya miki yawa kin kusa aure ma baraki fad’awa ‘yan iskan samarukan kin su hak’ura bako?” Hannu ya mik’a ze jata dan wanke ta da mari. Kamar a kyaftawan ido Anas yajata bayansa kamar ‘yar baby tare da rik’e hannun Farouq, rik’o kawai ya masa amman idan Farouq sanda ya cike da hawaye. D’ayan hannunsa ya d’aga ze sake kaiwa Farouq mumunar punch Fannah ta rik’e hannunsa da nata bibbiyu. Hawaye take sosai “Mr. Fauzi please ya isa kayi hak’uri ya isa please.”
Hawayen da takeyi ne kawai ya hana Anas kaiwa Farouq punch da ze iya kwantar dashi a asibiti. Kwalan rigar Farouq ya chukumo. “In bakada manners na magana wa kamilallaiyar mace I will teach you some, the next time ka sake kwatanta Fannah da wad’annan munanan suna I assure you zakayi kwanan cell, pathetic fool kawai, idiotic bastard.” Sannan yayi wulli dashi har k’asa Farouq yayi landing, daidai lokacin Ya Khaleel ya yanko kwanan gidansu Fannah shi a dole yazo cin abincin ranan da surikarsa ta dafa masa kamar yadda yace jiya.
Ai ganin his only son a k’asa ga kuma jini ko ta ina fuskarsa ya falfala da gudu yayi kan Farouq. “Farouq meya same ka? Wani d’an shegiyan ya maka wannan tsiyan, waye shi?”
“Baba kafin ka kira wani da d’an shegiya make sure ka cire sunan d’anka daga number a list d’in. Nayi warning nasa but I think I have to warn you too, the next time ya sake shiga harkan Fannah bare kwana a garin Maiduguri qalau ba.”
“Tohh sannu fa, sannu shugaban k’asan Nigeria. Toh kaine d’an shegiyan ba d’ana ba, kai har kanada da right da zaka hana Farouq shiga harkan Fannah ne? Ka tab’a jin inda aka shiga tsakanin mace da miji?”
Fannah dake tsaye bayan Anas tace, “Baffah Khaleel Ya Farouq ba miji na bane.”
“Ke karuwa rufa min baki.”
Ran Anas in yayi dubu be b’aci ba, taku yayi yunk’urin yi zuwa gaban Ya Khaleel dan kai masa had’add’en punch shima, “how dare you call Fannah karuwa!” yace a yayinda Fannah ta rik’e rigansa dan hanasa aiwatar da abinda yayi niyyar yi. “Mr. Fauzi let them be please, ya isa ka tafi wannan problem d’ina na ne bansan na jaka ciki, please go.” Wayarsa ya ciro a fusace bayan an d’aga yace, “Hello send me 10 men, I mean 10 a unguwar Polo...” Nan ya masa kwatance. Baki na b’ari police d’in yace, “yy.yyyes Sir right away!”
Aiko cikakken minti biyar da gama wayan Anas beyi ba sega motan polisawa guda biyu. Farouq harda rud’ewan ciki Ya Khaleel kuwa sanda ya saki fitsari a wando shi be d’au dagaske baturen yake ze kira polisawa ba, toh waye shi.
“Take them both, kuje ku rufesu right away” ya fad’a a fusace.
Farouq da baki ke jini yace, “wallahi kayi k’arya me mukayi da zakace aje a rufe mu?” Can k’asa k’asa Ya Khaleel yace, “kai kayi shiru se yanzu nagane waye wannan mutumin, ba bature bane shine wanda aka nunasa da Fannah ranan a BRTV wallahi babban mutum ne mu basa hak’uri in bahaka ba in aka rufemu me bailing namu se Allah.”
“Mr. Fauzi ko? Dan Allah kayi hak’uri, wallahi misunderstanding aka samu anan my apologies please karka sa a rufe mu dan Allah. Farouq baraka basa hak’uri bane?”
“Officer take them away banasan jin komai.”
Nanne bakin Fannah ya bud’u. “Mr Fauzi please kayi hak’uri karka rufesu dukda cewar basuda kirki ‘yan uwana na ne, Ya Khaleel Baffah na ne Ya Farouq kuma cousin d’ina kayi hak’uri and set them free please.”
“Miss Aleeyu why? Bakiji munanan sunan da suke kiranki dashi bane?”
“Naji Sir just please set them free, please.” Ta fad’a idanta na cikowa da hawaye.
“Officer let them be zaku iya tafiya sorry for the disturbance.”
“Ba komai Mr. Fauzi muna da godiya”
“Zuwa anjima zakuji alert thanks.”
“Mungode sir, mungode sir” a haka suka ja motocinsu suka fice.
“Miss Aleeyu kinasan in samusu retricting order from the law yadda barasu sake zuwa kusa dake ba? So they won’t disturb you in na bar nan?”
“Sir thank you but karka damu in shaa Allah ba abinda zasu iya min you can go kadena b’ata lokacinka akaina please, thank you”
“Call me in wad’annan foolish mutanen suka sake miki wani abu” ya k’are maganan yana ma Ya Khaleel da Farouq kallon banzaye cikin banzaye. Farouq zeyi magana Ya Khaleel ya taka masa k’afa dan haka yayi shiru.
“Ki shiga ciki.”,Ba musu bale gardama ta shige ciki sanda ya tabbata ta shiga ya dawo da kallonsa kan like father like son yana nuna su da yatsa “kun ji na rantse in kukayi ma Fannah wani abu zaku k’are rayuwanku a jail, assholes.” Yana kaiwa nan yashige motarsa driver ya rufe yajasa suka fice.
Se yanzu bakin Farouq ya bud’u. “Shege se meh? Wallahi kasani ka tab’o tsuliyar dodo, zancen kakeso.”
“Kai Farouq ya isa saurayin nan babban mutum ne a garin nan ka rufa mana asiri muyi abinda ya kawo mu mukoma da Fannah Bama cikin kwanciyan hankali.” cewar Ya Khaleel.
“Wallahi Baba be isa ba ya zubar min da jini ya kwana lafiya Allah kaimu gobe. A ina yake aiki kace?”
“Wai meka isa kayi masa ne dawani fashasshen bakin ka da hancin ka, se uban kurin baki wai kana zuwa gym ji yadda kabari wancan Fauziya ne ko Fauzi ya maka tatas. Kona fad’a maka inda yake aiki me ka isa ka masa?†
“Niko nasan me zan masa just tell me ina yake aiki?”
“A Flames Enterprises shine CEO’n wajen naga sun sa a TV”
“Good” Farouq yace tare da ficewa. Babansa na kiransa ko a kwalan rigarsa, Ya Khaleel kuwa shegen tsoro ne dashi sekace farar kura. So yake ya shiga cikin gidansu Fannah amman kuma yana tsoron abinda Mr. Fauzi ya fad’a masa. Dan haka ya nufa masauk’insu kawai.
Anas kuwa isar sa gida ya wuce d’akinsa tare da sa lock ba tare da yace da kowa komi ba. Wani irin tausayin Fannah yaji ya kama sa, ba abinda yakeso yanzu kamar yayi protecting Fannah daga wannan shegun Baffan nata da d’ansa. Mesa zasu na kiranta da karuwa? Mesa zasu na kiran yarinya me tarbiyya kamar Fannah da karuwa? To kode ta tab’a yin hakan ne da a baya se Allah yamata shiriya? “No!” ya fad’a a fili no matter