Showing 147001 words to 150000 words out of 268365 words

Chapter 50 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54141

inda kan Anas yafi nauyi. “Anas” ta sake kiran sunansa.
“Uhmmm” yayi groaning cikin sautin bacci.
“Anas ka koma kan pillow naka kaji? Cinya na ya soma yin tsami.” Shiru yayi dan bema jita ba daidai kunnensa ta matso “Anas” ta kira sunansa.
“Fannah let me sleep mana kinji?”
“Toh Anas cinya na zafi.”
“Please...”
Badan tanaso ba ta amince. Gashin kansa take ta wasa dashi har gwada kitsawa take sede da ya kitsu se ya warware dan santsi ba kamar ta ta me uban tauri ba gara ma ace in tayi stretching. Chan cinyar hagunta ma yasoma ciwo. Hak’ura kawai tayi batasan seda ta fara gyangyad’i ba da taji zata fad’i seta farka ai haka bacci b’arawo yasata gaba batasan lokacinda ta fad’a kan Anas ba, kayinta kan nasa a yayinda nasa ke kan cinyarta. Bacci sosai duka sukeyi cikin kwanciyar hankali.


******


Se 2:30PM Anas ya tashi ko Sallah basuyi ba. Ji yayi nishin mutum a kansa gakuma alamun gashi kan fuskarsa wanda yanada tabbacin ba nasa bane. Hannu yasa yana tattab’ata har ya gano mace ce a kansa kuma Fannah ce. How comes? Ya tambayi kansa, nan ya tuna duk wani abinda ya faru. Gosh no! Why do I have to tell her? What if ta gane na tab’a raping wata a rayuwa na? God help me. Duk wannan magana da yake a zuci yayi su.
“Fannah” ya kira sunanta. Bacci take har yanzu bata ko motsa ba, “Fannah” yasake kira yana jijjiqa ta danko motsawa ya kasa duk nauyin ta na akansa. “Fannah wake up” nanne ta d’an bud’e ido. “Wake up kinji? Bamuyi Sallah ba.” Firgit ta tashi daga kansa tana sosa ido ita kanta batasan ya akayi ta fad’a jikinsa tana bacci ba.
“I’m sorry” tace masa.
“I too” ya miyar mata.
“You are sorry?” ta tambayesa cike da mamaki “for what?”
“For ealier, for making you cry.” Dad’i taji iya dad’i atleast koda be fito fili yayi spelling mata SORRY ba ya kwatanta.
“You are no more mad at me?”
“Yes I’m not, also nagode.”
“For...?” Ta tambayesa.
“For letting me sleep on your laps.”
“Ohh! bakomai you had a dream.” Shiru yayi kamar be jita ba dan bayyason ta tono da maganar. “Muyi Sallah first lokaci ya wuce.” Tsam ya mik’e ya nufa bayi ko motsawa Fannah batayi ba as se mik’a take. Bayan yafito yace, “you are next” tare da jawo wata bak’ar jallabiyansa yasa.


Ai tana gwada mik’ewa tasaki wani irin wahalallen k’ara cike da azaba da sauri ya nufo inda take. “Fannah whats wrong?” Take idanunta suka cike da hawaye. “Meneh?”
Cinyarta kawai take nuna masa se yanzu ya tuna time da take ce masa cinyarta yayi tsami yak’i tashi, seyaji guilty gabad’ai.
“Dan kwanciyan danayi akai ne koh?” Ya tambayeta cikin wani irin salo cike da tausayi. Hawayen nata yasa hannu ya share mata. “Don’t worry zafin ba sosai bane just help me in mik’e.” Da ya gwada mik’ar da ita seta saki k’ara, tausayinta sosai yaji ya kama sa musamman ma ya tuna shine sanadi, besan lokacinda bakinsa suka furta *“I AM SORRY”* ba. Words data juma tana jiran ranan da ze furta mata su se gashi yau yayi. “Anas karka damu I’ll be fine.”
“Taya barin damu ba bayan nine sanadi.” Da k’yar ya iya mik’ar da ita ya takata har zuwa bathroom d’in sannan yafito bayan data gama abinda zatayi ta kirasa yazo ya taimaka mata ya fito da ita tayi tayi ta fito da kanta amman takasa, ko yatsa ya tab’a cinyoyin nata zafi suke mata. Anas yayi tabari ya d’aga ta tak’i wai abin kunya ne taya da girman ta ze d’aga ta. Bayan ya tada Iqama ya juyo yana kallonta, yadda take ta yamutsa fuska cike da azaba. “Zaki iya yin Sallar a tsaye?”

“Eh don’t worry, lets pray.” Har hawaye seda ta zubar acikin sallar musamman suka zoyin sujjada da zaman tahiya. Bayan da suka idar ya juyo yana kallonta nan ya karanchi tayi kuka. Cikin akwatinsa ya nufa ya zaro wani man muscle pain killer ya nufo inda take. Kallonsa take cike da rashin fahimta. K’afanta d’aya yaja a hankali a yayinda ta sakar dawani irin k’ara dan azaba.
“Sorry” yace da ita. Ganin yana k’ok’arin kwaye mata abaya tasa hannu ta rik’e nasa.
“Anas lafiya me haka?”
“Fannah magani zan shafa miki.”
“A cinyan?” ta tambayesa tana zaro ido waje cike da mamaki.
“Eh” ya bata takaicaccen amsa.
“A’a’ahhh!” ta sake baki tana kallonsa. Taya ze gane mata cinya ana zaman lafiya ai ta gwammaci tacigaba da zama da cinyar haka har seda ze sab’e da kansa. Kayan nata ta matse gam a jikinta.
“Fannah me haka?”
“Banaso, kabari ze warke da kansa.”
“Kinga banson sututan banza yaushe nene ze warken? Harfa kuka kikayi da muke Sallah, bari na shafa miki.”
“Anas banaso please ka bari.”
“Dalili?”
“Dalili kuwa itace taya zan kwaye maka cinya na a waje? Gaskia ba kyau kabari kawai.”
“Toh ba mijin ki ne niba? Naga dama ko ba kaya ajikinki zan kalleki amman I’m not interested, cinyarkin ma dan yazamo dole ne. Bring it.” Kafad’a ta buga “o’o gaskia ni banaso.”
“Fannah kinason in miki na k’arfi koh? Ki kawo k’afar, mema zan gani ajikinki wanda bangani ba a waje.”
“Eh ni koma me banaso, kaje kata ganin na karuwai a waje amman banda nawa.”
“Haka kikace?”
“Eh mana taya ana zaman lafiya zan hau kwaye maka cinya na.”
“Okay you want it in a trouble way, you are gonna get it.” Ajiye maganin yayi gefe guda ya rik’o siraran hannayenta biyu cikin nasa guda d’aya...




*© miemiebee*


[12:56, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
6⃣ 0⃣










“Anas wai me haka? Kasake min hannu.” Se k’ok’arin k’watan hannun nata take amman takasa.
“Barin sake ba, is better kibar wannan fad’an da kikeyi ‘cause sena shafa miki zan bar nan.”
“Anas dan Allah kayi hak’uri zan shafa da kaina, kaji?”
“Banji ba” kayan nata yasoma yunk’urin kwayewa, wani ihu ta sakar seda ya tsaya yana toshe kunne. “Me haka? Fyad’e zan miki? Ko yanka ki zanyi?”
Kai take girgiza masa, “a’a Anas dan Allah ka sakemin hannu banaso please dan Allah.”
“Amiki a sanyi kink’i ba, barin sake miki hannun ba.” k’afafun nata ta gwada shurewa aiko cinyar tata suka soma zafi.
“Wayyo Allah! Cinya na!”
“Ai kad’an kika gani, I told you to stop fighting it kink’i.” Kayan nata ya kwaye zuwa guiwarta. “Anas dan Allah kabari ba kyau wallahi haramun ne karka kwaye min kaya please.” bata bar k’ok’arin k’watan hannun nata ba har yanzu sede sam ta kasa dan ko rawa hannun Anas baiyi. Beko saurareta ba ya d’aga kayan nata sama, harta panties nata seda ya bayyana, santala santalan fararen cinyoyinta masu gashi dogaye kwance akai suma suka bayyano. Ganin haka ta fashe masa da kuka “Anas dan Allah kabari ka rufe min cinya bakyau wallahi.”
“Gomma ma kiyi shiru dan ba sauraranki zanba.” Maganin ya bud’e da d’ayan hannunsa ya matse kan cinyartan duk da hannu d’aya. Yana gwada murzawa ta saki wani irin k’aran da sekace ana cire mata rai, da ace akwai mutane kusa dasu da se sun fiffito.
“Wayyo Anas dan Allah kayi hak’uri in kanayi wa Allah karka sake tab’amin cinya wallahi da zafi, kayi hak’uri dan Allah” ta kuma fashewa da kuka.


“Fannah inba’a murza ba bare wassake ba k’afan naki tsami zeyi.”
“Na yarda wallahi amman dan Allah karka sake tab’awa da zafi sosai.” Kuka take harda majina. “Fannah I’m sorry bareyi inbar ki haka ba, just close your eyes kinji?”
“Anas dan Allah karka sa-” ihu ta sakar sanadin murza maganin kan cinyarta dayayi da k’arfi. “Arghhhh! Wayyo Allah na mutu.” Murza man yake sosai kan cinyarta da k’arfi in bahaka ba tsami zeyi. Sosai Fannah take kuka fuskar nan duk hawaye da majina seda ya tabbata yashafa mata man zafin kota ina a cinyan ya sake mata hannu ta huta kafin ya shafa a d’ayan. Bata bar kukan ba har yanzu, hannunta har yayi shati dan yadda Anas ya rik’eta, kayan nata ta mayar a wahalance ta rufe jikinta dashi. Ruwa ya tsiyayo mata daga dispenser tare da d’ibo tissue.
Nishinta har wani sama sama yake dan kuka. “Fannah ya isa mana” fuskarta ya rik’o ta fisge da wuri. Murmushi kad’an ya saki “yi hak’uri toh. Kawo face naki na miki clearing.”
“Banaso zanyi da kaina.”
“A’a ni zan miki.”
“Nikuma banaso haka kawai dan kaga kafi k’arfina seka na min mugunta.” Fuskar nata ya sake rik’owa “don’t fight it Fannah ki tsaya.” Badan tanaso ba tasaida fuskar natan hancinta ya goge mata sannan ya share mata hawayen. “Ga ruwa sha kinji?”
“Banaso.”
“Yi hak’uri kisha kinji?” ya d’ago cup d’in tare da kai mata baki. K’in bud’e bakin tayi. “Fannah kisha or else in sake matsa miki k’afan” jin haka ta bud’e bakin nata tasha kusan rabi.
“Good sauran d’ayan koh?”
“A’a wallahi d’ayan baya ciwo.” Tsbagen yadda ta tsure bata ma san seda ta rantse akan k’arya ba.
“Naji baya yi tsaya mu shafa miki shima.” Sabon kuka ta soma “Anas kayi hak’uri dan Allah” jikinsa take turewa daga gareta.


“Fannah kinga ki tsaya mushafa miki a hankali ko kalan na d’azu kikeso?”
“A’a banason ko d’aya.” Kayan nata ya soma kwayewa a yayinda take taresa, “dan Allah karka min haka please.” Be saurara mata ba ya had’a hannayenta biyu gu d’aya cikin nasa. “Anas wallahi zan cije ka in baka sakeni ba.”
“Don’t worry ko kin cijen barin bari ba” nan ya sake kwaye mata kayan, ganin yasa man zafin kan cinyarta ta tsala ihu, ignoring nata yayi ya soma murzawa da zafi zafi se ihu se kuka take, daga k’arshe ma seizing muryar tata tayi se hawaye kawai take zubarwa. Bayan daya gama ya share mata hanci da fuska sekuka take har a yanzu. D’agota yayi chak kamar ‘yar baby ya aza ta kan gado ganin batada niyan barin kukan yayi joining nata akan gadon shima tare da kwantar da kanta akan k’irjinsa yana bubbuga bayanta a hankali. “Shhh! ya isa kinji? Bar kuka.”

“Allah ze sak’amin” tace cikin sautin kuka.
“Eh ze sak’a miki bar kukan amma.” Se chan datayi shiru ya tambayeta, “are you hungry?” Kai ta gyad’a masa nan ya miyar da kanta kan pillow yayi musu ordering abinci. Bayan abincin ya iso ya buk’ace ta da ta sauk’o da k’yar take taka k’afar bayan sun gama chi ta mik’e da tafiyar tata d’ai d’ai, towel nata ta ja da hijabi ta shiga bayi ruwa ta watsa sannan ta fito, kamar yadda ta saba cikin hijabi take sa kaya, wata red simple doguwar riga tasa ta haye gado ta kwanta.


****
_9:30PM_
Yanzu suke gama cin dinner, inbanda bin Fannah da kallo ba abinda Anas yake, bayan tagama duk wani abinda zatayi ta haura gado ta kwanta se anan ya d’auko maganin zafin tare da hayewa gadon shima. “Oya mik’o k’afan ashafa miki.”
“Wallahi barin yarda ba, ai yazama mugunta kenan, ka shafa min d’azu ai ya isa.”
“In miki kalan na d’azu kenan.”
“Ai wando ne a jikina ba yadda zaka ciremin kuma.” Murmushi ya saki ta gefen da dimple nasa yake. “Haka kikace?” Kai ta gyad’a masa. “Okay” kawai yace mata tare da jawo ta da hannu d’aya seda ta fad’a jikinsa. “Anas me haka? Ka sakeni bacci nakeji.” D’ayan hannun nata ya sake ja tare da had’asu waje d’aya da d’ayan hannunsa ya soma sauk’e mata wandon baccin nata.


“Anas dan Allah kayi hak’uri wallahi ba kyau kadena dan Allah. Wallahi iskanci ba kyau.”
“Ba cewa kikayi barin iyaba? we shall see.”
“A’a zaka iya, wallahi zaka iya kayi hak’uri dan Allah karka ciremin dan Allah.” Ko saurara mata beyi ba seda ya sauk’o da wandon nata har guiwa light pink pant nata ya bayyana. Haka yabi duka cinyoyin nata yashafa mata man zafin. Ba irin had’asa da Allan da batayi ba. Bayan daya gama ya sake mayar mata da wandonta sannan ya sake mata hannu. “Wallahi Allah ze sak’a min.”
“Toh me zan kalla a jikinki Fannah? Light pink panties naki ko meh?” Pillow taja ta rufe fuskarta dan kunya she still can’t believe Anas yagane mata pant.


Bada dad’ewa ba shima ya haye gadon ya kwanta. “Fannah” ya kira sunata. Batayi bacci ba amman tak’i amsa sa. Pillonsa ya matso kusa da nata nan tayi baya da nata haka suka tayi seda ta isa k’arshen gadon rukuna. “Wai Anas me haka?”
Shiru ya mata bece komai ba. Chan itama tayi baccin bata jima da farawa ba ta fara mafarke mafarkenta sede na yau beyi nisa ba ta tashi da wuri. Tsoro ta soma ji hannunta ta had’a da nasa ta matse gagam, ganin bata dena jin tsoron ba tabar kan pillonta ta kwanta akan k’irjinsa tare da zagaye hannunta kan cikinsa nanne tasamu tayi baccin itama.


Sab’anin kullum Anas ne ya fara tashi yau, ganin Fannah yayi kwance a jikinsa se baccinta take sha koda ya gwada d’age hannunta daga kan cikinsa gangamesa ta sake, da k’yar yasamu ya raba jikin sa da nata.
Suna zaune bayan sun idar da Sallan Asuba sungama Azkhar kenan Anas yace, “ya k’afan naki?”
“Da sauki ya warke.”
“Aikoda ya warke se na sake shafa miki anjima.”
“Wallahi Anas ya warke kayi hak’uri.”
“Yau bakiyi mafarki ba.”
“Eh...” Ta amsa shiru.
“Kodan saboda kwanciya da kikayi ajikina?”
Bata masa k’arya ba tace “eh, kaima ai da kayi mafarkin yarinyar chan seda ka kwanta kan cinya na.” Shiru yayi kamar be jita ba dan bayason maganan yarinyar.
“Anas wace yarinyar?”
“Kinga irin suratan ki d’inba? Ke waye mutumin? I'm going back to sleep.” A rarrabe suka kwanta.


_10:40AM_
“Anas kayi hak’uri ka kaini Saloon d’in mana.”
“Barin kai ba ina ni kike cema mugu.”
“Nikuma da yaushe?”
“D’azu da nake shafa miki muscle pain reliever.”
“I’m sorry zafi ne yamin yawa.”
“Shine zakije saloon da k’afar nakin?”
“Toh Anas nagaji da zama dakan a tsefe haka, ko calaba ne zasumin it won’t take long.”
“In calaba ne ai nima na iya.”
“Ka iya kitso?” Ta tambaya tana zaro ido.
“Ba kitso nace miki na iya ba, calaba na iya, inayi wa Amal.”
“Toh ai ni ba Amal ceba ka kaini saloon d’in please.”
“No Fannah barakije ba, naga har maza ake ajiye wa a saloon na mata yanzu barakije wani gardi yaga gashin kiba.”


“Toh Anas sekace nikad’ai ce mace a wajen? Ai hak’uri zakayi.”
“Barin iya ba nemo comb na miki calaban.” A zuciyarta tace ai kuma wallahi seka kitsa. Nan ta d’au comb cikin jakarta ta kawo masa yana zaune kan gado. “Gashi” ta mik’a masa, amsa yayi tare da mik’ewa. Gaban dressing mirror ya jata ya zaunar da ita kan kujerar. Ribbon nata ya warware seda yaji tsoro dan yadda gashin yayi wani buf!
“Ke wani irin gashi ne haka? Dama haka gashin naki yake? Barin iya ba miyar da ribbon nakin.”
“Haba mana Anas sekace yau ka fara gani, to ka kaini saloon d’in tunda baraka iya ba.”
“Nifa na fad’a miki bara kije ba.” Gashin nata ya taje sama sama sannan ya tsaga ya soma kitsa mata calabar daga ta k’eya.
“Awcchh! Anas da zafi kad’an rage zafin hannun naka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login