Showing 150001 words to 153000 words out of 268365 words

Chapter 51 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

44733

mana.”
“Kinga fa banason fitina ko ki zauna ko in fasa, kinma samu zan kitsa miki kai kina min tsiya.”
“Toh yi hak’uri amman kad’an rage zafin hannun please.”


Sun d’au kusan minti biyar be gama kitsa ko d’aya ba, har Fannah tagaji da zama. “Anas har yanzu bamu gama ko d’aya ba?”
“Acewarki kitsa wannan uban gashinkin is easy neh? Ni barin na k’arasawa har bakin ba yayi tsawo dayawa.”
“Amman Anas ai ze warware, yi hak’uri ka k’arasa.” Cikin awa d’aya guda biyar kacal sukayi.
“Nagaji se anjima.”
“Anas biyar kacal fa mukayi.”
“Ina sane ai, in kinaso mu gama a yau muyi trimming bakin gashin seya dawo d’aya dana Amal kinga then zan iya kitsa miki.”
“Toh ai ba kyau Anas.”
“Naji Malama ke dama komai ba kyau” ribbon nata ya nema ya kama mata gashin. “In na huta zamu cigaba.” Hannunsa ta rik’o “Anas please kowani biyar d’in ka k’ara seka huta gaji? Yi hak’uri.”
“Fannah kalli nan” ya ciro hannunsa dake nan sekace bana miji ba dan laushi. “Kiga yadda gashin ki ya yanke min hannu.”
“Yi hak’uri kaji zan maka tausa, please ko biyar ka k’ara.” Biyar d’in kuwa ya k’ara yace ze huta.
Haka har dare yayi basu gama ba rabi sukayi sauran rabi.


Se a washegari suka gama kitson, sosai kuwa k’ananun calaban daya matan yayi kyau sosai sekace wani k’wararre. “Wow! thank you yayi kyau.” ta fad’a a lokacin datake kallon kitson nata a madubi.
“I know ba sekin fad’a ba.”
“Kai Mr. Fauzi kullum cikun girman kai, in aka yaba abin da mutum yayi cewa yake thanks.”
“Aww in miki kitso kuma in sake miki godiya? Lallai fah, kema girman kan Mr. Fauzi ya soma tab’aki Mrs. Fauzi.”


★‡★‡★‡

Da bikin Mr. Fauzi and Mrs Fauzi sati biyu kenan yau, sosai sun sake sabawa da juna sede kunsan halin Mr. Fauzi in abin nasa ya bugesa suburbud’awa Fannah rashin mutunci yake iya san ransa baiwar Allah kam sede ta zauna tayi kuka, inya tashi nuna mata care kuwa kamar ba gobe. Sauran sati uku agama masa gininsa su tare. Tun a daren jiya Sunday Fannah takejin alaman zuwan period nata ta duba kayakinta tasa ba pad ko d’aya ciki ta rasa wani irin shirya kaya Afrah ta mata dayasa ta mance da important abu haka ba. Gashi sunyi fad’a da Anas basu magana bale ta tambayesa kud’i taje ta siya.
Kasancewar yau Monday, leave da Anas ya karb’a ya k’are yau zeyi resuming office. Kwance suke kan gado Fannah nachan nata b’angaren shima haka, Allah ma ya sota batai mafarki ba yau data shiga uku.


Tun kafin Asubah ta tashi tana rik’e da k’asar mararta dan azaba, batasan lokacinda ta soma kuka ba. Sautin kukanta ya tada Anas dukda fad’a sukayi amman ganin ta tana kuka yaji tausayinta ya ratsa sa, duk yadda yayi dan ignoring nata ya kasa. Wutan d’akin ya kunna, tare da dafe bayanta “Fannah what is it? Mesa kike kuka?” Shiru ta masa har yanzu haushinsa takeji inta tuna yadda yata mata masifa jiya dan kawai ta gyara masa wardrobe nasa ko me yake b’oyewa ciki se Allah. Shiru ta masa bata amsa ba se k’ananun kukanta take.
“Okay Fannah I’m sorry about yestarday kinji? Barin k’ara ba. Meke damunki?”
Kamar wacce baratayi magana ba tace “Anas marata ciwo.”
“Sorry ina zuwa” cikin kayansa ya shiga ya ciro pain killer da ruwa ya mik’a mata “gashi sha kinji? Sannu.” Amsa tayi ta had’iye har yanzu ciwon be dena ba. “Kwanta” ya buk’ace ta.
“Barin iya ba Anas barni ahakan kawai.”
“Fannah ki mik’e nace.” Nan ta kwanta juyo da ita yayi ta yadda tana kallon ceiling. Hannunsa ya aza kan cikinta daidai gun marar tata yana massaging. Hannunsa ta d’aga daga kan cikinta, “Anas meh haka? Ni banaso.”


“Why do you always think negative? Niba abinda zan miki am just helping you.”
“Toh shine seka tab’a min ciki?”
“Fannah stop it” hannun nasa ya cire daga nata yacigaba da mata tausar. Sanyi taji sosai, har taji ciwon na raguwa haka yayi ta mata. Asuba nayi Anas ya shiga bathroom yayi alwala nanne Fannah taji sauk’an period nata. Anzo wajen tace a ranta. Batasan ta ya zata fara sanar da Anas batada pad ba duk yadda tayi barata iya ba kunya bare barta ba.


“Anas I need money please kabani d’ari biyar.”
“Me zakiyi dashi?”
“Abu zan saya.”
“Wani abu ne haka zaki siya da Asubah? Ko Sallah fa bamuyi ba.” Kawar da kanta tayi daga garesa, “banayi.” Tace chan k’asa k’asa. Sam be jitaba “tashi kiyi alwala muyi Sallah.”
Kai ta girgiza masa. “Dan ciwon cikin ne barakiyi Sallah ba?”
“A’a... Kawai kayi zanyi anjima.”
“Kefa kikace Sallan jam’i yafi lada.”
“Nasani kawai kayi naka yau d’in.”
“Nak’i tashi kiyi alwala muyi Sallah kinsan inada office yau.”


“Banayi” tace chan k’asa k’asa tare da kare fuskarta.
“Shine baki fad’amin ba tun d’azu kika tasani surutu. Mschw!” Yaja k’aramin tsuka “kinada case wallahi.” Bayan ya idda Sallan ya hauro gadon ya kwanta. “Anas kaji kabani koda N500”
“Wai kiyi me dashi?”
“Abu zan saya”
“Abu like?”
“Anas ermm. Ermm” kasa fad’a masa tayi. Wayarta tajawo daga kan side drawer tayi typing abu a text bar ta mik’a masa wayar seda ya gama ja mata aji ya amsa karantawa yayi kamar haka;
“Anas I need N500 please, I want to buy p...a...d.”
“Ke wace erin mace ce? Ko Amal ma ta rik’e date nata kece baki rik’e ba? Ina zakije ki saya yanzu?”
“Ba ruwanka bane, ni kawai kabani kud’in.” Tsuka yaja ya mik’e tare da zira jallabiyansa ya fice.


Kuma ina zeje ta tambayi kanta.


_25 minutes later..._


Dawowar Anas kenan, shinfid’e a k’asa ya tarar da Fannah se juyi take. Da wuri ya nufe ta tare da d’ago ta “cikin ne?” Kai ta gyad’a masa.
“Sannu kinji? Ko zamuje asibiti?”
“A’a zuwa anjima ze dena, please kabani kud’in inje in siya kaji?”
“Gashi” ya mik’a mata ledar hannunsa. Tana dubawa taga pad d’inne har guda biyu. Dad’i taji sosai “thank you.” Tayi tayi ta mik’e amman ta kasa daga k’arshe shi yayi assisting nata yakaita bathroom d’in sannan ya bata space bayan minti biyar tafito se wani rik’e cikin ta take. Coffee ya had’a mata dukda be k’ware ba, sosai tayi appreciating ta shanye duka tare da masa godiya.

Ajikinsa ta kwanta har tayi bacci. Se k’arfe 9:30AM Fannah ta tashi sema yanzu ta tuna Anas nada office. “Ya Salam!” ta fad’a a fili. “Anas! Anas ka tashi.” A hankali ya bud’e idanunsa. “Ciwon be dena bane har yanzu!”
“A’a da sauk’i, Anas barakaje office bane?”
“Yes se gobe.”
“Why?”
“You are sick I need to take care of you.”
“But An-”
“Shhh! lets go back to sleep.” Hannunta yaja ta fad’a jikinsa ya matseta gam tare da cigaba da baccinsa.




*© miemiebee*
[12:56, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
6⃣1⃣










★‡★‡★‡
PRISON HOUSE MAIDUGURI, BORNO STATE.

K’aramin gate ne ya bud’u Ya Khaleel ya sa kai ciki, be tsaya ko ina ba se wajen da aka tanada dan masu visiting prisoners. Da zamansa befi minti biyu ba aka bud’o wa Farouq k’ofa sanye yake da orange T-shirt na ‘yan prison meh ‘32’ rubuce a ta bayan. Sosai ya rame yayi bak’i, ta gefen bakinsa yanka ne alaman fad’a dawani yayi har yasamu injurin. K’arisowa yayi a kasalance ya zauna a kujera opposite Ya Khaleel.

“Subhanallahi Farouq meya sameka anan?” Ya Khaleel ya tambaya cike da damuwa yana tab’a gefen bakin Farouq. Hannu yasa ya kawar da hannun mahaifin nasa “ba komai.”
“Kamar ya ba komai Farouq da wanne kakeson inji ne? Da rashin ka kokuwa da rashin jinka? Cikin nan d’in ma baraka bar fad’a ba?”
“Baba niba fad’a nayi ba” ya fad’i cikin murya cike da takaici.
“Allah shirya min kai Farouq” hannu yasa ya d’ago wata leda tare da azawa kan table d’in yana bud’ewa. Abinci ne mai rai da lafiya, ga kaji kota ina. Ba makawa Farouq yasoma chi dan ko rabuwansa da abinci me kyau about a week now tun komawar Babansa Bama. Seda yayi dam ya kora da cool malt drink sannan yajisa d’an dadai.


“Baba ya batun kud’in bailing nawan? Nagaji da zama anan.”
“Farouq kasan kud’in bailing nakan ba abu neba na wasa, gun aikinka nayi masu bayani ko zasu d’an ji k’anka, albashin ka suka yanke sunce ba ruwansu dakai. Banki kuma sunk’i bani loan saboda ba aiki nakeyi ba, bakuma wani abu nayi possessing ba.”
“Baba amman wannan abu is not fair, menayi da wannan Fauzin zesa a rufe ni?”
“Saboda kai talaka ne Farouq shikuma yanada kud’i. Kai baka gani bane? Ba lawyer’n dayakeson tsaya mana kan case d’innan da zaran sunji Mr. Fauzi ne opponent d’in se su soma mana wasa da hankali.”


“Bawani Mr. Fauzi dan ubansa, Fauzi kawai in bare amsa bakuma chan masa, uwarsa da Mr d’in. Wallahi na fito he must rule the day he was born.”
“Ai fitowanka ba nan kusa ba Farouq.” Cike da rashin fahimta Farouq yace, “what do you mean Baba? Ina dubu d’ari biyar da muke dashi a k’asa?” Kai kawai Ya Khaleel ke girgizawa. “Baba talk mana, ina yake?”
“Farouq a hanya na, na komawa Bama b’arayi suka tsare mana mota suka k’wace duka d’ari biyun danayi aiki na samu da k’yar sesa kajini shiru through out last week.”
“What?!” Ya fad’a a tsawace tare da zabura. “Farouq yi hak’uri ka zauna.”
“No! No! Baba this is unacceptable wallahi nagaji da zama anan. Nagaji, I can’t take it anymore. Yaushe ne zaka samu miliyan d’ayan da suke buk’ata ka cireni anan? Mschww!”
“Calm down Farouq-” katse Baban nasa yayi.
“No! I can’t calm down.” Mik’ewan shima Ya Khaleel yayi yace, “in har dan wannan baraka iya calming kanka ba then inaga there is no point ma in sanar dakai main abinda ya kawoni, ai wannan jaririn tashin hankali ne aganga da wancan.” Cike da rashin fahimta yace. “wanne kenan Baba?”
“A’a barin fad’a maka ba tunda wannan ma yayi freaking naka out there’s no need in sanar dakai wanchan.” Hannun Baban nasa ya rik’e suka zauna atare. “Mene Baba please tell me. Ba abinda ze tada min hankali se lafiyar Fannah. Baba ina ba wani abun bane ya sameta?” Shiru Ya Khaleel yayi hakan ya bawa Farouq daman sake magana, “Baba talk mana please.”

“Farouq inason ka kwantar da hankalinka ka sauraren da kyau.” Kai kawai ya gyad’a duk yakasa samun sukuni. “Jiya na je gidansu Fannah nake tambayan ‘yan gidansu ina take sabida ban ganta ba duk sukamin shiru ba wanda ya amsani I had to ask their neighbours nan ne suke sanar dani cewa Fannah tayi... Tayi...”
“Tayi meh Baba?? Tell me!” yayi demanding
“Farouq, Fannah tayi aure.”
“Tayi meh?” Ya tambaya disbelievingly.
“Tayi aure Farouq.”
“No... No” kai yake girgizawa ba makawa. “Baba halan baka gane bane, Fannah is mine, she belongs to me no one can take her away. Whats mine is MINE, FANNAH TAWA CE Baba.” T shirt nasa ya yaga daga gefe d’aya tattoo ne d’an babba ya bayyana a saman hannunsa anyi zanen heart ciki kuma an rubuta ‘F&F’ ma’ana ‘Farouq and Fannah.’ Cike da mamaki Ya Khaleel ke kallon hannun d’ansa totally speechless.


“Subhanallahi Farouq dan girman Allah me wannan? Tattoo ka zana a hannunka? Kana muslimi?”
“Eh Baba” ya amsa sa confidently “and I mean it I will never rest se ranan da Fannah tazamo TAWA sabida TAWA CE dama. Koma waye ya aureta seya sake ta inkuma hakan be yuwu ba, I don’t care koda zanyi spilting blood. Fannah tawa ce, ba mahaluk’in daya isa ya k’wace ta.”

Kai Ya Khaleel ya kad’a “koda kuwa mutumin Mr. Fauzi ne? Koda Mr. Fauzi ne mijin nata?”
“Mr. Fauzi? Kana nufin shine ya auri Fannah matata???”
“Shi ya aureta Farouq, Mr. Fauzi shine mijin Fannah, hak’uri ya zama 2 Farouq you can’t fight with Mr. Fauzi he is too powerful.”
“Baba abu d’aya nakeson kamin, kawai kasan ya za’ayi in fita daga god forsaken place d’innan. Wallahi kaji na rantse sena koya wa Mr. Fauzi whats mine is mine and mine alone!” ya buga kan table d’in.


★★★★★
MAIDUGURI INTERNATIONAL HOTEL LTD.

Kwance Fannah take bisa gado se kuka take duk tabi ta tadawa Anas hankali yarasa meke masa dad’i. “Fannah to muje asibiti mana” yace da ita cike da tausayi yana a zaune kan bediside drawer’n kanta.
Kai kawai ta girgiza masa “zuwa gobe ze dena we don’t have to.”
“Har se gobe? Tun safe ba abinda kikeyi banda kuka ko breakfast kink’i chi haka lunch ma. Ni ban zama care giver ba na gaji da kula dake, kimutu kika ga dama.”
“Ai banche ka kula dani ba nima, tun farko ma banche ka zauna nan ba, kaje office abinka.” Ta juya masa baya.
“Ai da kin fad’a hakan tun d’azu seda aka tashi a office d’in zaki wani cemin da ban zauna dake ba? Mschw!” Banza tayi dashi ta cigaba da kukan ta tana juye-juye. Ignoring nata yayi ya koma kan couch ya zauna tare da ciro wayarsa yana latsawa.


Chan da kwanciyan kan gadon ya gagareta ta sauk’o k’asa se juyi take tana kuka, sekuma ta basa tausayi shi aduk lokacin da baida lafiya zata bar duk wani abinda takeyi takula dashi, why can’t he do thesame? Ajiye wayar nasan yayi ya taso zuwa inda take a kwance ya tsuguna. “Fannah” ya kira sunanta. Baya ta juya masa. “Fannah okay I’m I’m...” sekuma yayi shiru bayajin ze iya ce mata sorry.
“Tashi kinji?” Nanma banza dashi tayi. “In had’a miki coffee?”
“Don’t bother, banaso.”
“Fannah bakici komai bafa since in the morning.” Shiru tayi bata ce komai ba. “Okay Fannah I’m sor-” be k’arasa fad’a ba yayi shiru. “Kinji?”
“Banji ba.”
“I just apologised to you, you have to accept it.”
“Ni haka nake baka hak’uri ne? ka rik’e hak’urinka banaso.”
“Okay I’m sorry kinji? Tashi ki koma kan gado.” Ba gardama ta mik’e ta koma gadon. Nan ya had’a mata yakai mata seda ya tabbata ta shanye yabarta ta koma ta kwanta.


****
Washegari Fannah ta tashi garau masha Allah taji sauk’i sosai. A farko ma cewa Anas yayi bare je office ba, Fannah ce tasa sa a gaba saboda tasan halinsa duk wani alkhairin daya ma mutum seya k’arisa da tsiya, dan haka kawai tasa sa a gaba seyaje, shikuma dan nuna mata be damu da ita ba ya shirya yayi tafiyarsa ko breakfast yak’iyi. Yana ji tana kirar sunansa ya dawo su karya yayi banza da ita.
Isarsa office ya baje kan kujera nan Kacallah yashigo masa da files ba adadi yasoma bi one-by-one yana signing, by 10:00AM yafita meeting sede tunda aka soma yakasa gane me akeyi kwata kwata hankalinsa bayya jikinsa yana chan yana tunanin Fannah for sure yasan ta samu sauk’i but he can’t stop himself from being worried, ana fitowa daga meeting d’in ya kirata a waya a lokacin tana bayi tana wanka seda tafito taga missed call nasa k’waya d’ya. “Shegen girman kai, ko kiran mutum sau biyu ma be iya ba” nan ta kirasa back bada dad’ewa ba ya d’aga. Shiru tayi bata ce komai ba shima haka sun kusan minti biyu shiru sannan yakira sunanta “Fannah.”
“Na’am” ta amsa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login