Showing 90001 words to 93000 words out of 268365 words
Chapter 31 - Tana Tare da ni complete book document .txt
na Global investments. Tagama ta ajiye a gefe guda chan ta ciro wayarta tana game itade yau barata had’a ido da Mr. Fauzi ba sekace wanda tayi sata.
*****
Anas kuwa yakasa tsinana wa kansa komai banda tunanin Fannah wai anya yau inbe sata a ido ba ze iya kwanciya lafiya kuwa? “Oh No! No! No! Why am I acting in this way? Coffee nake missing ba Fannah ba, coffee ne” ya tunar wa kansa. Ai daga k’arshe kasa hak’ura yayi ya tashi ya nufi office na Fannah koda bare ganta ba yau yaga office nata he is okay with it. Fannah na cikin game taji an murd’a hannun k’ofar office nata ido tasa wa k’ofan jiran ganin ko waye dukda kuwa zuciyar ta na sak’a mata wai Yusuf ne.
Wayar ta tayi wulli dashi da suka had’a ido hud’u da Anas dama dalilin dayasa ta sako hijabi me hula kenan yau, da sauri sauri taja ta rufe fuskarta. Yin hakan seta tuna masa da incident na jiya seya gano dalilin dayasa take rufe fuskar kunyan sa takeji dan Afrah tace masa MP ke damunta, shi kansa kunyan ta yakeji bama batun MP’nta ba. In kuma tace meya kawo sa office nata fah? Karkuma tagane dan yana missing nata ne yashigo ta raina sa. Ganin batada niyyan magana yasa yayi giaran muryar. “So kinzo shine baki sanar dani ba? Nazo picking wani file ne dama” yayi k’arya yana wani basarwa.
Da k’yar ta iya bud’e baki ta gaishe sa. “Good morning, wani file ne?” ta tambaye sa cikin siririyar muryarta.
Rashin sanin wani k’aryan ze sake mata kawai yace, “to my office” chike da isa. Yana fita ta d’ago kai “to my office” ta kwaikwaye sa sannan tad’au jakarta da jotter’nta da pen da pencil tabi bayansa. Bayan like minti d’aya da shigan Anas office nasa Fannah tashigo itama kanta sunkuye a k’asa daidai gaban table nasa ta tsaya tare da mik’a masa jotter’n gabansa “here is your schedule for today, inda akoi abinda za’a giara let me know” D’agawa yayi ya dudduba yaga komai yayi, yaga ta ma fi Kacallah iya amfani da lokaci dan kuwa by 2:30PM ya gama komai nasa yau.
So yake ya tambayeta ya jiki amman kuma girman kai irin nasa bare barsa ba seya bud’a baki zeyi magana se wani abu ya katse sa. Itako tana nan tsaye kansa har yanzu tana jiran amsar sa in da akoi abinda be masa ba yafad’i seta giara. Can k’asa k’asa almost kamar da kansa ma yake magana yace, “ya jikin ki?”
Fannah kuwa taji sa amman dan yadda mamaki yaso kasheta se kawai tace hala kunnenta ke mata k’arya yaushe Mr. Fauzi ze tambayeta ya jiki? Karkuma tayi shiru yace ta rai na sa yasoma balbaleta yanzu a nan, dan haka tace, “eh? Excuse me” fuskar nan a rufe da hijabi har yanzu.
“Ya jikin ki nace” yasake nanatawa with thesame voice level dayayi d’azu. Se yanxu ta tabbata ba yaudarar ta kunnenta suke ba. “Da sauk’i” ta amsa a hankali duk seji take kamar ta nitse k’asa dan kunya. Da k’yar tayi managing tace, “thank you.”
“Bana buk’atar godiyar ki” ya fad’i mata gatsau sekace bashi yanzu yayi magana a hankali ba. Itafa har yau ta kasa gane hali irin na Mr. Fauzi yanzu yanzu seya mata mutunci take wajen kuma ya zagesa yadda yaga dama. Juyawa tayi ta nufa wajen coffee machine dan had’a masa ai bata soma ciro cup d’in ba ya jefa mata tambaya. “Me kuma zakiyi acan?”
“Had’a maka coffee sir.”
“Banaso, bana buk’ata just kitafi kije office naki if am in need of anything I will let you know.”
Wai yau Mr. Fauzi ne ke fad’in baya buk’atan coffee to kode wanda ta had’a masa jiya beyi dad’i bane kasancewar zogin da hannunta yake mata. Shi kansa be zata ze iya fad’in baya buk’atar coffeen ta ba se gashi ya fad’a confidently ma kuwa.
“Sir indan na jiya beyi dad’i bane I apologise hannu na ke ciwo, will make it better yanzu.”
“Banaso nace just get out kuma na hanaki ja min wannan hijabin kina rufe fuskarki dashi, me kike dashi da banida? Ja hijabin baya.” Dakewa tayi tak’i ja seda ya daka mata tsawa “ja nace!” Tana b’ari ta giara “now leave” a sanyaye ta juya ta fice tana isa office nata ta zauna kan cushion.
“Mschww wallahi Mr. Fauzin nan kanada mental illness, yanzu kama mutum mutunci da ‘yan mintuna kuma ka koresa kaman kashi thank god kai kazo har nan ka kirani bani na kai kaina office nakan ba. Wallahi kawai dan na danne zuciyata ne da nayi kuka, sede kata wa mutane masifa kai aikin ka kenan, Allah shirya wallahi ina tausaya wa matar da zata aure ka” (ni miemie nace kina tausaya wa kanki kenan) “ace kullum masifa, masifa. Ni barin cigaba da yin game d’ina ma.” Wayarta ta ciro tacigaba da buga candy crush.
Kusan to 12:30PM Anas ya danna mata kira ta telephone kan ta shirya zasu meeting. Yau akeyinta ita gaskia bata shirya zuwa meeting ba amman ya ta iya? Bayi ta nufa tayi changing sannan tafito tak’i shiga office nasan ma bale ya mata korin kare kona akuyan daya saba mata. Bayan like 5 minutes Anas ya fito taga ya canza shirinsa yasa navy blue suit, white shirt da ocean blue tie sosai kam yayi kyau ga yadda gashinsa yasha giara kafin ya kamata tana kallonsa tayi saurin kau da kai, bece mata komi ba koda yaganta tsaye bakin office nasan juyawa yayi ya soma tafiya a yayinda take binsa a baya. Driver ne ya tuk’asu har hall da za’ayi meeting d’in sun iso da shiga ya juya ya kalleta “sauran yau ma kiyi tsaki kokuma ki baje kina bacci kinji ba Miss Aleeyu?”
“Naji” tace ba tare da ta kallesa ba. Kamar ranan yana shiga mutanen suka tashi masa bayan sun gama gaggaisa wa ya zauna a kujerar tsakiyan nufin shine babba ma a meeting na yau kenan.
Duk abinda ke gudana Fannah ta kasa kunne tana sauraro tare da jotting down major points kuma, gajiya tayi da tsayuwan ta zauna still hankalinta na kan meeting d’in. Time to time Anas yake d’ago kai yana kallonta sam idanunsu basu had’u ba.
Se 2:30PM suka k’are boring meeting d’in, indagin Fannah yayi tsami dan zama bayan sun shiga mota ya tambayeta, “ina abubuwan da kikayi jotting?” Cikin jakarta tasa hannu ta ciro jotter’ta tare da mik’a masa. Se kuwa yaga duk important abubuwan da sukayi discussing akai na had’a kan Flames Enterprises da C&C Enterprises duk tayi jotting down da kuma abubuwan da zasu amfanar da juna dashi, sosai kuma yaji dad’i. Amman meya kamata yayi wa Fannah? Godiya koba haka ba? But saboda dan girman kai irin nasa ya kasa, “nan gaba in ana meeting seki dena frwoning fuskarki ai kowa yasan meeting d’in ba dad’i gashi ki ajiye zan buk’ata anjima.” abin da yace da ita kenan.
Sanyi taji sosai a ranta da beyi complaining akai ba amman kuma yak’i mata godiya dan uban girman kai. Sede abin da ta lura yau shine besa an k’ure AC kamar na ranan ba, kad’an kawai yasa driver ya kunna. Shikuwa Anas yayi hakan ne saboda batada lafiya, bayasan ya k’ara mata wani rashin lafiyar akan wanda take fama dashi, tunda ya karanci bame san sanyi che itaba. Yauma daidai gaban wata makekiyar hotel driver ya tsaya tare da bud’e masu k’ofa. Bayan sa tabi a hankali har suka shiga ciki, ba kowa daga su se masu aiki. A ranta tace wato kai baka iya cin abinci se kayi reserving, lallai kud’i ya maka yawa. A table daya zauna ta zauna itama, ko da waiter yazo d’aukan order’nsu Anas ne yamasa bayanin komi ita batace ko uffan ba ,wasa da siraran yatsunata kawai take tana kallon yankan da tayi shekaran jiya a yayinda Anas ke latse laste kan wayar sa. Bayan 3 minutes abincin su ya iso sede taga combination na yau yafi na ranan yawa, ba abinda babu kan plate nata k’wai ne kaza ne, kayan ciki na, pepper soup ne bade abinda babu shiko Anas kalan abincin ranan ya sake ordering.
Toh mesa? Mesa za’a bani wannan babban plate cike da abincin kusan dubu biyar? Na Mr. Fauzi kuma na N1,500? Kode waiter’n yayi b’atan kai ne? “Uhm Sir are you sure wannan shine abincin nawa?” Ta tambayi waiter’n a yayinda yake zuba mata drink.
“Yes Miss your Boss asked me to bring it for you.”
“Boss?” Ta nanata a ranta tare da juyawa ta kalli Anas. Sam yi yayi kamar bema san maganar da sukeyi ba yakai spoon bakinsa a hankali. Bayan waiter’n ya tafi still Fannah ta kasa tab’a abincin ta dan bata yarda ba har yanzu.
Anas kuwa dalilin dayasa ya sai mata abincin dubu biyar yau shine akoi time da ya tab’a kai Amal asibiti da menstral cramp ya tab’a rik’eta bayan da likita ya dubata ya bata maguna seyake cewa Anas a tabbata tana cin abinci me kyau saboda asaran jinin jikinta da take in tana period same goes to Fannah, sesu samu suyi restoring energy’n jikinsu. Itama saboda bleeding da takeyi yazamo dole taci abinci me kyau dan lafiyarta sesa ya siyo mata wannan abinci me kyau kuma me tsada.
Ganin batada niyyan chi yasa ya dakata tare da kallonta, “well? Bara ki chi bane? Kinsan ba jiranki zanyi in na gama bako?”
Baki na rawa tace, “S... Sir yayi yawa. In kace ni zan biya bansan ya zan biya ba.”
Kallo ya watsa mata “last time da mukazo ke kika biya? Kin cika surutu, mschw. In zakici fine in bara ki chi bama fine” ya cigaba da chin abincinsa. K’in ci tayi wane ita abincin dubu biyar. Miss Aleeyu eat! Ko sena sab’a miki zakici? Ko kici kokuma in muka koma office inciro miki 500 papers kiyi zaman giaransu”
Ai a hankali ta d’aga spoon nata ta soma ci a hankali, ta tab’a nan ta tab’a can sosai abincin ya mata dad’i. Bata san lokacin data baje ta fara ci kamar ba gobe ba Anas dake satan kallonta se mamaki yake mutum gata ba k’iba amman se aukin chi. Duk uban girman plate nata sanda taci morethan half, data jita dam tukuna ta goge bakinta ta kora da juice. Kallonta yake cike da mamaki har yasa ta jin kunya.
“Kin k’oshi ko a k’ara?” Kai ta kad’a masa cike da kunya da nufin a’a. Waiter yakira ya biya kud’in plates nasu sannan suka kama hanyan dawowa office.
*© miemiebee*
beeenovels.mywapblog.com
[12:51, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
3⃣9⃣
Zaman makoki sukayi cikin motar har sanda suka iso building d’in. Office nata ta wuce a sanyaye shima Anas d’in office nasa ya nufa bayan ya zauna kan kujerar sa ya soma tunanin abubuwan dasuke faruwa dashi lately. “Me had’i na da lafiyan Fannah da har zan tambayeta ya jiki? Me sa zan saya mata meal me kyau? What is wrong with me?” Duk yadda yayi ya kawar da tunanin Fannah ya gagara ga wani san shan coffeen ta daya keson yi, no matter how yau seya sha coffeen nan. Surrender kawai yayi daga k’arshe ya kirata kan tazo bayan minti d’aya ta shigo. “Yes Sir” ta fad’i kanta a sunkuye.
“Make me coffee.” Kai ta d’ago tana kallon sa cike da mamaki ba shi yace baya buk’ata ba d’azu? Meya canza masa mind toh?
“Bakiji meh nace bane?”
“Naji” ta amsa sa a takaice nan ta nufa wajen coffee machine d’in ta fara had’awa. Daidai lokacin wayar Anas ya soma ruri, yana dubawa yaga Shettima ba tare da b’ata lokaci ba ya d’ag “hello maza?”
“Ya Anas gani da Amal fa muna cikin elevator ma yanzu ta matsu wai seta ganka harda lunch ta kawo maka.”
“Iyeh!” yayi exclaiming tare da zaro blue eyes nasa “Kana nufin kuna building d’in yanzu?”
“Eh Ya Anas gamu nan.” Ding! Ya katse wayar. “Ya Shettima me na fad’awa Ya Anas toh?, suprise nefa.” Amal ta fad’i tana turo masa baki harda harara.
“Allah sa supbeans ne ba suprice ba, kuma the next time kika sake harara na wallahi kwad’e ki zanyi da mari.”
Can k’asa k’asa tace, “mugu kawai.”
Seko ya jita, “me kika ce?” Ya tambayarta tare da matse hannunta cike da mugunta.
K’ara ta saki “awchh! Nace kayi hak’uri.” Kallon ya mayar mata shima tare da sake mata hannun.
Anas kuwa lokaci d’aya hankalinsa ya tashi, kawai yaji bayasan Shettima ya had’u da Fannah, tun kafin ya ganta ma yana masa tsiya bale ace yazo ya gansu su bibbiyu. Take ya mik’e ya nufa wajen Fannah tare da fincikota da hannu kad’an ya rage ruwan zafin be zube k’asa ba. k’ara ta saki. “Argh! Mr. Fauzi me haka? Kasake min hannu.” Hannu ya aza kan lips nasa “shush!” D’akinsa ya jata wanda tuni zuciyar ta ya soma bugu “ki zauna anan, don’t move or talk and karki fito kin jini ba?”
“Mesa?” ta tambayesa.
“Because I’m your Boss Miss Aleeyu, I’m telling you kika fito daga d’akin nan 500 pieces zakiyi correcting.” Jin 500 papers ta giad’a kai cikin tashin hankali. “Good” yace tare da rufo k’ofar, kamar su Shettima suna jiransa daidai lokacin shida Amal suka shigo gudu tayi, tayi hugging nasa. “My Angel yau kuma visit aka kawo min?”
“Eh Ya Anas ranan kace yunwa na damunka a office shine na kawo maka lunch cikin lunch box.”
“Awwn! My Angel thank you” peck ya manna mata a forehead. “Zanci zuwa anjima” ya fad’a mata tare da ajiye flask d’in kan table nasa. K’aramin tsuka Shettima yaja erin kallesu d’innan mana. Ignoring nasa Anas yayi ya tambayesa, “Shettima yau ba lectures ne?”
“Eh babu ina cikin bacci na wannan fitinanniyar ‘yar taka ta tadani wai setazo.”
“Ba ruwanka, be tab’a kiba aiko Angel?”
“Wallahi Ya Anas ya zungure min kai da muka shiga mota a elevator kuma ya kama min hannu da zafi.”
“Haka ya miki? Bari muje gida mu rama miki.”
“Ya Anas zanyi fitsari” kafin Anas yayi magana takama hanyan d’akinsa inda ya rufe Fannah gashi besa lock ba k’ofar kawai ya ja, kaman aljani ya b’ullo gabanta. “A’a Angel bareyi ki shiga nan ba.”
“Ya Anas ya matseni” ta fad’i tana mammatse k’afa tana bugawa.
“Bari Shettima ya raka ki toilet a k’asa.” Shettima uban san jiki wai, “mesa Ya Anas? Bayan ga toilet anan yaushe zan kaita har k’asa? Barta ta shiga mana.”
“Shettima! Ka kaita toilet a k’asa.”
“Ai seka fad’amin me kake b’oye wa cikin d’akin.” Fannah dake zaune kan gado duk tana jinsu, se mamakin yadda Anas yake walwala cikin ‘yan uwansa take, ashe de yana wasa da dariya ko dashike ai da yazo gidansu ma yata murmumushin munafirci but wannan kuma na gaskiya ne.
“Me zan b’oye ciki? Abeg ka akita k’asa hurry.”
“Ya Anas kode mace kake b’oyewa cikin d’akin?”
“Shettima zan b’ata maka rai wallahi, giara akeyi ciki saisa bareyi Amal ta shiga ba.” Ya fad’a confidently sekace ba k’arya yake ba. Fannah harda rufe baki tana dariya, wato ma giara akeyi gaskia Mr. Fauzi ya iya k’arya.
“Muga giaran toh” Shettima yafad’i yana wani shu’umin murmushi.
“Shettima k’aniyanka, kaji ba.” Amal da tun d’azu ta kalli Anas ta kalli Shettima tace da ihu;
“Ya Anas let me in fitsari please.”
“Yi hak’uri Angel, Shettima setayi a jikinta zaka kaita ne?”
Kallon tsiya Shettima ya ma Anas ina irin