Showing 132001 words to 135000 words out of 268365 words

Chapter 45 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

44730

“Anas wani side kafiso? Zan kwanta.” Banza yayi da ita. “Kaji Anas?”
“I prefer the rightside.” yace cike da nuna rashin damuwa. Tokari taji a zuciyarta wanda harta fuskarta seda ta nuna. Ko a gida a gefen dama take kwanciya, shi Anas kuwa da gangan ya ce gefen daman yafiso dan yasan sarai itama daman zatace tafiso tunda take tsaye ta wajen. Ba dan tanaso ba ta koma leftside d’in tare da tattaro duka pillows d’in shide Anas kallonta yake. One by one tasoma jera pillows d’in ta hanyan yin katanga tsakaninta dashi.
Lallai ma Anas yace a zuciyarsa. Me take nufi? Tunani take waiko insun kwanta ze mata wani abu? Toh she is decieving herself. Bece da ita komai ba seda ta gama raba tsakaninsu sannan yace, “ni barin had’a kwanciya dake ba, zan kwanta kan kujerar nan so ki kwantar da hankalinki” ya nuna dogon 3 seater dayake zaune akai. Bata ko kallesa ba sede ta kasa b’oye dad’in da taji.


Da hijabinta ta kwanta, bayan tagama tofe addu’o’inta ta rufe ido. Nanne Anas ya tashi ya fad’a bathroom ya watsa ruwa shima. Sabuwar nicker yaciro yasa. D’aya daga cikin blankets dake kan gadon ya zaro da pillow d’aya ya koma kan kushion d’in. Alokacin Fannah tayi nisa da yin bacci, wuta ya kashe ya koma ya kwanta.
Da misalin k’arfe 3:23AM na dare Fannah ta farka tare da tsala wani irin ihun daya firgita Anas lokaci guda a sanadin mafarkin data sabayi datayi.

“Wayyoo Allah! Dan Allah kayi hak’uri karka tab’ani dan Allah bawan Allah dan Allah.” Hawaye take sosai tana b’ari gawani gumin dake k’eto mata duk da AC’n dake huruwa. “Mami! Mami! Mutumin.” Anas besan lokacin daya taso ya nufo inda take ba. “Fannah wani mutumi kuma?”
wani ihun ta sake tsalawa ganin Anas.
“Mami wallahi gashi nan ze k’ara, dan Allah kayi hak’uri.”
Hankalin Anas ya mugun tashi ganin yadda take kuka fiye da na d’azu duk ta tsorata se b’ari take, murya cike da damuwa yace, “Fannah is me, Anas your husband bawani mutumi.” Ganin yadda take zufa yagano mafarki tayi dan shima anytime yayi mafarki haka yakeyi.
“Bar kuka kinji?” Hannunta ya gwada rik’ewa wani irin rikicaccen ihun ta sake saki tare da matsawa baya. Hab’arta ta had’a da guiwa se kuka take tana b’ari...



*© miemiebee*


beeenovels.mywapblog.com


*Kuyi hak’uri da rashin posting da nike two days, wallahi harkoki suka mani yawa, I love you all*
[12:54, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
5⃣6⃣









Wani irin tausayin daya jima be mata irinsa ba ya soma jimata yau, azabarcaccen kuka take na hak’ik’a daga ya gwada tab’a koda hannunta ne sekuma ta tsala ihu tana had’asa da Allah. Toh wannan wace erin mafarki ne? Ya tambayi kansa. Kasancewar akoi d’an haske d’akin be damu ya kunna wuta ba, wajen dispenser ya nufa ya tsiyayo mata ruwa a cup cike da tashin hankali. “Fannah gashi sha kinji?” Ko kallonsa batai ba se b’ari da take tana hawaye, “Fannah mafarki ne bawani mutumi anan kinji? Sha ruwan ki koma bacci.” Hannunsa daya aza kan bayan ta taja jikin nata baya da wuri. “Dan Allah kayi hak’uri Mami please kizo wallahi gashi nan.” Cup d’in ya ajiye bisa side drawer tare da finciko ta da hannu seda ta fad’a a jikinsa, gagam ya matse ta a jikinsa me k’amshin bala’i dakuma d’umi, ta hanyan hugging nata. Ihu ta saki sosai tana b’ari a yayinda kukanta ya tsananta sekuma had’a sa da Allah da take tana k’ok’arin k’watan kanta amman sam ta kasa. “Dan Allah kayi hak’uri ka sakeni, kar ka k’ara dan Allah...”


“Shhh! Fannah is okay, stop crying kinji? Bawani mutum anan Anas ne kawai, stop fighting it keep calm, I’m here for you bar kuka kinji?” Anas ya sanar da ita cikin wani irin salon da be tab’a using ba, hab’ansa na akan kanta. A hankali ta dena fad’an da takeyi na k’watan kantan sede kukan da take har yanzu bata bari ba.
“Is okay kinji? Mafarki ne, I’m here, bar kukan.” Hijabin ta daya jik’e jak’af da gumi yayi yunk’urin cire mata wata ihun tasake tsalawa.


“Fannah ba abinda zan miki you are sweating, duk kin jik’e tsaya in cire miki hijabin kinji?”
“No banaso dan Allah kayi hak’uri, karka k’ara.”
“Ba abinda zan k’ara kawai cire miki zanyi, you’re sweating.” Sam tak’i yarda yacire mata shiko ya dage seya cire saboda irin zufan datake ta had’awa duk wuyan hijabin nata ya jik’e. Da k’ak’ani k’ak’a yasamu ya cire mata hijabin tana manne a jikinsa har yanzu. Sunyi kusan minti goma a haka se daddad’un kalamu yake fad’a mata yana shafa bayanta a hankali, hankalinta yana kwanciya, nan ne tasamu tabar kukan sede numfashinta be dawo saiti ba har yanzu. Bacci sosai Anas yakeji, “Fannah” ya kira sunanta a nitse. Cike da tsoro ta amsa kanta manne a k’irjinsa. “Uhmm” tace.
“Ba wani mutumi mafarki ne ba?” Ya tambayeta.
Kai ta giad’a a hankali.
“Good toh lets go back to sleep, nasan kema kinajin bacci.” Hannunsa daya zagaya a bayanta ya zaro wani tsoro taji ya sake ratsa ta atake batasan lokacin da ta zagaya hannayenta bibbiyu a jikinsa ba gagam ta matsesa not letting go. Wani erin sparks Anas yajiyo within him.


“Dan Allah kar ka tafi wallahi mutumin ze dawo.”
“Fannah I’m here bare dawo ba, ba tafiya zan ba kinga ina chan, ba mutumin da zezo kinji?”
Kai ta girgiza “please kar ka tafi wallahi zezo.”
“Fannah we need to sleep, bacci nakeji.”
“Anas please...” Ta rok’esa cikin sautin kuka.
“Okay okay naji barin tafi ba amman lets sleep kinji? Barin d’auko pillow na se mu kwanta.” Nanma kai ta girgiza da k’yar ta sakesa ya d’auko pillow ahakan ma binsa take hannunta nannad’e cikin nasa. Bayan ya ajiye pillow’nsa kan gadon yace, “oya hau ki kwanta.”
“Ina jin tsoro.”
“Fannah I’m here.” Ture pillows datayi katanga dasu a jiya yayi a k’asa sannan ya kwanta tana tsaye a kansa se b’ari take. Hannunsa ya bud’e mata “come here.” Ba musu bale gardama ta haura kan gadon itama, hannunta yaja a hankali ta fad’a kan k’irjinsa, kanta ta daidata ta kwanta comfortably a jikinsa, da rabin jikinta akan nasa se b’arin take har yanzu. A nitse ya zagaya hannunsa a bayanta yana shafawa a hankali.


“Yi bacci kinji ba mutumin daze zo.” Kai ta gyad’a a hankali tare da yab’a hannunta kan cikinsa ta zagayesa gagam. Ganin bata bar had’a gumi ba har yanzu ya d’an k’ara k’arfin AC’n. A hankali bacci me uban nauyi yayi gaba da Fannah, jin nauyinta a jikinsa ya k’aru ya tabbata tayi bacci. Cike da dabara ya gwada mai da ita wajen kwanciyarta sede anytime ya gwada motsi seta sake matsesa a jikinta. Sau biyu ya gwada janta daga jikinsa amman tak’i sakesa agarin haka ya since mata ribbon. Uban gashinta ya bayyano kamar wadda zeyi kuka ya gwada packing mata gashin amman ya kasa gashi anytime ya gwada janta daga jikinsa seta sake matsesa.


Ahaka shima wahalellen bacci yayi gaba dashi da gashin Fannah duk yabi ya cika masa fuska.
Asuban fari Fannah ta tashi a hankali ta soma bud’e idanunta har ta bud’e duka ganinta tayi kwance jikin na miji da hannunta zagaye kan cikinsa ihu tayi niyan sakarwa sewani abu ya dakatar da ita. Hannun nata taja daga kan cikinsa da wuri tana d’ago kanta taga Anas ne, meh hakan? Meya kawosa kan gadon? Me takeyi a jikinsa? Bata gama nemo amsoshin tambayoyin nan ba ta tab’a jikinta taji ba hijabinta me zata gani? Gashinta baje a fuskarta da jikinta gabad’aya. Ihun da tayi niyan yi d’azu ta bud’e baki zatayi yanzu, chak tunanin mafarkin da tayi ya fad’o mata akai ya dakatar da ita.

Se a yanzu take tuna duk wani abinda ya faru a daren. Kunya taji sosai inta tuna Anas ya ganta da ‘yar kayan dake jikinta dakuma yadda ta riga matsesa a jikinta jiya. Ribbon nata ta lalimo a garin haka ta farkar da Anas tun idanun nasa suna kafewa har ya bud’e su gabad’aya. Idanunsu na had’uwa tayi saurin kawar da kanta bedsheet ta soma ja tana kare k’irjinta. K’aramar tsuka yaja tare da juya mata baya dan cigaba da baccinsa. Ribbon natan take k’ok’arin miyarwa amman takasa batada ma k’arfin kamawa batasan lokacin da tasaki wani wahalallen k’ara ba take Anas ya juyo yakusan minti yana kallonta tayi nan tayi chan amman takasa kama gashin ya tashi ya zauna. Hannu ya mik’a mata da nufin bani. Itako sam bata gane meyake nufi ba. Hannu kawai yasa ya amshi ribbon d’in daga hannunta cike da tsoro ta gwada matsawa baya ayayinda yajawota ta fad’a jikinsa. Uban gashin nata ya soma packing nasu gu d’aya a yayinda take k’ok’arin fisgo jikinta. “Stop it Fannah” yayi warning nata. Ba tare da b’ata lokaci ba ya kama mata gashin a daidai tsakiyar kanta yabar jelan na yawo. Bayan ta d’ago daga jikinsa ta tuttusa jelar ta nannad’e waje d’aya. “Thank you” ta fad’a masa kanta sunkuye.


Bece mata komai ba illa observing nata da yake, nan ya gane hijabinta take nema hannu ya mik’a ya d’ago a k’asa tare da mik’a mata. Hannu tasa ta amsa da wuri ta miyar jikinta sannan ta mik’e tashiga bayi, bayan tafito tayi kan Anas taga har ya koma bacci.
“Anas” takira sunansa a hankali. Idanunsa kawai ya bud’e be amsa taba.
“Asuba tayi ka tashi kayi muyi Sallah.” Bayan daya gama sauraronta seya sake rufe idanun nasa ba tare da ya amsata ba. “Anas kaji?” Ta fad’i.
“Naaji!” Ya fad’a a d’an fusace. Mik’ewa yayi daga kan gadon daga shi se nickers nasa, k’are wa jikinsa kallo tayi nan ‘yan seconds sannan tayi saurin kawar da kanta. Ko ta kanta beyi ba ya nufa bathroom kafin yafito ta shimfid’a musu dadduma tana zaman jirar fitowarsa.

Bayan ya fito ya zaro wata milk jallabiyansa sabo pil ya zira sannan ya nufa inda tayi musu shimfid’an, ganin ze fara sallan ba ita takira sunansa. “Anas.”
“Meh?” Ya amsata a fusace.
“Ba tare zamuyi sallan ba?”
“Kowa yayi nasa” ya amsa ta a takaice.
“Anas but Sallar jam’i yafi lada.”
“Da a gida keda su wa kikeyi?”
“Dasu Afrah.”
“Naji lets pray then.”
“Uhm amman se munyi Rakatainul~fajir ba?” Ta sanar dashi kanta a sunkuye.
Raka... Rakatainul~fajir? ya nanata a zuciyarsa. “Me kuma rakatainul~fajir?” Ya tambayeta a fili.
“Raka’a biyun da akeyi gabanin k’etowar al~fijr.”
“Ohhh! Fannah!” Ya fad’a rai ad’an bace tare da sa hannu cikin gashinsa yana hargitsawa. “Ke komai ne sekin had’a masa concussion? Sallan Asuba ma se anyi rakatainul~fajir ne ko meh?”
“Anas hadisi ne fa ingancecce, yin nafilar yafi duniya da kanta dakuma duk wani abinda ke cikinta”
“Toh naji raka’a nawa ne?”
“Biyu ne kacal, a first raka’ah suratul~kafirun na biyu kuma ikhlas.” Kai kawai ya giad’a mata yajasu. Ita Fannah bata zata ma Anas ya iya Sallah kamar yadda yajasu ba, ta d’au ko sallan ma seta koya masa. Bayan sun sallamesa yajasu Sallar Asuban, duk wani k’aidojin karatu taji yana karewa, duk wani hukunce hukunce yana biya, a takaice sautin k’ira’ar sa ya burgeta ba kad’an ba saboda yadda yake da zak’in murya, sosai yayi impressing nata ashede ba jahili ta aura ba.


Bayan sun sallame ya mik’e ze koma ya kwanta.
“Anas” ta dakatar dashi da wuri.
“What now Fannah? I want to sleep please.”
“Babu kawai so nake na fad’a maka qira’arka tamin dad’i.”
“Naji” yace sama sama yana k’ok’arin cire jallabiyar. Chan k’asa k’asa tace, “aini ban zata ka iya karatu bama.” Sekuwa yaji ta.
“Kafiri ne ni ai dole kice baki zata na iya karatu ba. Toh in baki sani ba barin sanar dake yau cikin izu sittin na Qur’ani nayi talatin da biyu, kin gane? Ba jahili ne niba.”
Mamaki sosai tajiyo, 32? Ta nanata a ranta. Amman shine bai aiki da ilimin Qur’anin nasa? Kuma besan hukunce hukunce ba a addinin muslinci.
“Anas amman shine baka aiki da ilimin naka?”
“Me ruwanki? My life is not your business, kuma ai ba ce miki nayi islamiyya nayi attending ba hadda ne, zallan Qur’ani da tajweed kawai akeyi sesa kiga ga bansan sauran religious stuffs d’innan ba time daya kamata nashiga islamiya nak’i ban shiga ba.” Sekuma yayi shiru “why am I even explaining these to you? Kin ga dama kice ban san komai ba game da addini keda kika sani sekita bragging dashi be damen ba kuma bare damen ba, allow me to sleep now, will you?”


“Anas I’m sorry ba abinda nake nufi ba kenan also in aka idar da Sallan Asuba dama kowani Sallan ba direct akeson mutum ya tashi ba. Akwai morning azkar da akeyi wanda yake da falala sosai shima.”
“Ohhhh!” Ya sa hannu cikin gashinsa a fusace yana hargitsawa. “Fannah please, please nace nan ba islamiyya bane kince inyi rakatainul~fajr nayi be isheki ba yanzu kuma azkhar kikeson sani yi? for goodness sake jiya bansamu nayi bacci ba, wannan mafarkin da kikayi duk ya bi ya tadda min hankali, haka kika hana ni bacci yanzu kuma dayakamata in kwanta shina kice barin yi ba?” Ya tambayeta a tsawace. Bata san lokacinda ta soma hawaye ba.

“I’m sorry, Allah baka hak’uri.” Ta fad’a tana tare hawayenta. Kallonta yayi na ‘yan seconds tare da kawar dakansa, nan yacire jallabiyan ya haura kan gado. Sautin kukan tane ya hanasa sukuni, ya d’au pillow ya rufe kunnuwasa amman still yakasa bacci gashi kuma ita tak’i yin shiru besan ina ze kaita ba. Mutum da an masa magana se kuka sekace ‘yar yarinya. Ganin ba ubangiji se Allah ya taso daga kan gadon tare da zura jallabiyar sa, gabanta ya tako ahankali ya zauna tana azhkar nata da hisnul muslim nata ahannu tana kuka a hankali ko d’aga kai ta kallesa batai ba. Zama yayi a gefenta yana fuskantar ta.

Littafin ya k’wace nan ne ta d’ago idanunta da suka soma canza launi. ‘I’m sorry’ yakeson fad’a mata but he can’t saboda girman kai instead yace, “they came out wrong, I don’t mean any of those words, kinji? Stop crying.” Yi tayi kamar bata ji sa ba “kabani littafi na” tace ba tare da ta d’aga ido ta kallesa ba. Shi mesa baya cewa sorry? Ita abu kad’an tayi masa zata ce sorry amman shi sede yace they came out wrong.
“I said they came out wrong, ba haka naso su fito ba ko bakiji ba?”
“Naji kabani littafi na toh.”
“No zanyi Azkhar d’in.” Batasan lokacin da fuskarta ta sake ba, “zakayi?” ta tambayesa cike da jin dad’i.
“Yes zanyi, show me the page.” Nan ya mi’ka mata bayan ta bud’e masa daga farin ta nunnuna masa. Kai ya gyad’a tare da amsa ya somayi. Kallonsa ta tsaya yi, ba k’aramin dad’i taji ba, a rayuwa batada burin da yafi ta shiryar da Anas, kuma alhamdulillah a hankali yana shiryuwan. Ya d’anyi nisa seya dakata tare da d’ago kansa nanne ya kama Fannah na kallonsa. ‘yar murmushi ya saki. “Kefa bara kiyi ba? Gashi gama seki bani, I’ll wait for you.”
“No karka damu na iya a ka zanyi just use it.” Kai ya giad’a mata tare da mayar da hankalinsa kan littafin. Koda ta gama nata bata tashi ba seda ta jira ya gama shima sannan suka tashi atare. Jallabiyar yakuma cirewa ya haura kan gadon. So take tace masa ya koma wajen sa na jiya sede kuma ta tuna batada iko. D’ayan b’angaren ta nufa ta d’an ajiye pillows uku a tsakaninsu sa’annan ta kwanta itama daga chan nesa nesa.


A hankali ya juyo yaga tana fuskantar d’ayan gefen ga kuma jera pillows d’in data sake a tsakaninsu. Kai kawai ya kad’a. “Da hijabin zaki kwanta?” Ya tambayeta.
“Eh” ta basa amsa.
“Yayi kyau.” Ahaka duk suka koma bacci ba su suka tashi ba se chan k’arfe 11:30AM nanma Anas ne ya tashi, idanunsa basu sauk’a a ko ina ba se akan kyakkyawar fuskar Fannah, tad’an gangaro kad’an zuwa wajen data yi katanga tsakaninsun. Wayarsa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login