Showing 201001 words to 204000 words out of 268365 words

Chapter 68 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54108

saboda daman haka yake mata atimes sede kuma yawan kasalan datake ji yanzu tun shekaran jiya da ta zauna se bacci kullum bacci.
Da k’yar ta iya shirya Anas office yau se Allah Allah take ya tafi ta dawo ta kwanta haka kuwa bayan ta masa goodluck kiss ta rufo k’ofa ta dawo ciki ta baje se bacci ba ita ta tashi ba se kusan k’arfe d’aya nanma baccin be isheta ba dan de tasan zatayi girkin rana ne bayan tayi wanka tasa wani silky doguwar riga d’inkin booboo. Powder kad’ai ta shafa ta shiga kitchen sam batasan mezata girka masu bama parlour tafito se hamman yunwa da bacci take tayi.


Fridge ta dosa ta bud’e taciro ragowar kazan da Anas yaci ya bari jiya, shi ta k’arasa sannan ta kora da ruwa amman sam seji take kamar bataci komai ba tana kurb’an fanta akai kawai seta jiyo amai guest toilet ta nufa a gurguje tariga kwararo amai wane zata harar da kayan cikinta bayan ta gama ta wanke bakinta abin tausayi tayi alwala sannan tayi Sallah, rashin sanin mezata dafa musu har yanzu yasa ta kira Anas.
“Halo Baby” tayi maganan cikin wani erin kasalaccaccen murya.
“Flower are you okay?” Ya tambayaeta cike da damuwa.
“Eh meh ka gaka?”
“Your voice sounds not okay.”
“Babu karka damu nace me zakaci yau I can’t think of anything.”
“Flower cook anything kinji? Karki damu I’ve got to go inada meeting I love you.”
“I love you too” ta katse. Duban agogo tayi taga 10 minutes to 2 “barin d’an mik’e zuwa 3 haka se in dafa masa ko spaghetti.” tace da kanta. Throw pillow taja ta miqe kan 3 seater anan tasamu ta kwanta ba ita ta tashi ba 3:10PM brushing kad’ai tayi ta fad’a kitchen da wurwuri ta had’a markad’an ta aza kan gas nanma tana girkin tana kwanciya ahaka har tasamu tagama had’a komi sauran jiran nunansa kad’ai ta juye a flask ganin tagaji da tsayuwan ta dawo dining taja kujera ta zauna chan ta aza kanta kan table d’in aiko daga nan bata sake sanin ina take ba ruwan abinci kam har ya shanye Fannah batazo ta sauk’e ba da kad’an kad’an girki ya fara k’onewa duk anan bataji ba.


4:10PM Anas ya dawo gida tunda ya bud’e k’ofar yafara jin warin k’onuwan abu ko jakansa be ajiye ba ya nufa kitchen yayi turning off gas d’in se anan ya ga Fannah dake kwance a dining area tana sharb’an bacci. “Flower” yayi tapping nata anan ma bata tashi ba seda ya matso kusa da ita yakira sunanta cikin kunnenta sannan firgit ta tashi. “Ya Salam! Abincin ya k’one Baby sannu da zuwa” takama hanyan kitchen kenan ya rik’o hannunta tare da dawo da ita baya.
“Baby ka sakemin hannu please abincin is burning.”
“Na riga na kashe gas d’in Flower.”
“Huh! Ya k’one koh?” Kai ya gyad’a mata. “Ya Salam! Habeebi I’m so sorry bansan meke damuna ba tun shekaran jiya banida aikin dayafi bacci yanzu me zakachi? Kuma kanajin yunwa koh? Tsaya ko indomie ne in dafa maka I’m sorry kaji Habeebi.”


“Calm down Flower karki damu banajin yunwa naci abinci a meeting d’in da mukayi.”
“Habeebi are you sure?”
“Yes Flower, kinsan bakida lafiya kuwa?”
“Mesa kace haka?” Ta tambayesa
“You are weak Flower meke damunki?”
“Baby babu bacci kawai nakeji.”
“Akoi tell me.”
“Seriously babu kawai amai kad’an nayi d’azu shid’inma nakega saboda gas dake cikin fantan dana shan ne, muje ka huta kaji?” Nan ta ja hannunsa sukayi d’aki bayan ta tayasa ya rage kayan jikinsa ta mik’e gado ta kwanta se bacci, bece da ita komai ba se 4:30PM ya matso kusa da kunneta yayi whispering. “Flower kinyi Sallan La’asar?” Cikin baccin ta amsa sa “banyi ba amman zanyi.”
“Se yaushe?”
“Yanzu” ta amsa sa.
“Then tashi” haka da k’yar ya tada ta tayi alwala tayi Sallah kasancewar shi ya idar tun a office nanma tana idarwa ta koma baccin jikin Anas se basa yake Fannah ba lafiya ba tun shekaranjiya yake monitoring moves nata ba aikinta se bacci ga wani kasalan da take yawan ji. Toh meneh? Kode sleeping sickness ke damunta?
Nide Miemie nace ciki ne ya kukace masu karatu...???




*© MIEMIEBEE*


beeenovels.blogspot.co.ke
[12:58, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

7⃣8⃣


I dedicate this chapter to *FATY MALUMFASHI* for the love, I love you Habibty😘😘











Had’ad’d’un blue eyes nasa yazaro cike da rashin yarda dan jin dad’i, farin cikin da baya iya misaltuwa ne kwance karara a fuskarsa “Flower its positive! you are pregnant!” ya fad’a cike da jin dad’i. Jakansa da ledan abincin ya ajiye kan kujera tare da d’aga Fannah sama dan jin dad’i “Flower we did it!” Murmushi sosai take wanda ya sake qayata ta. Bayan da ya sauk’o da ita yayi pressing mata hot kiss sannan ya rik’o ‘yar fuskarta duk suna murmusawa, rungumota kawai yayi “thank you Flower thank you so much I love you and our little one.”


“I love you too Hyena.” Bayan ya sakota ya had’e gira “bance miki banason sunan nan ba.”
“LOL to ai Hyenan ne kai Father to our child.”
“Lets eat Mammy to be.” Ledan abincin ta miqa hannu zata d’aga yayi sauri ya rigata “uh-uh” ya kad’a mata kai “banason kina aikin komai yanzu zan k’aro masu aiki harda chefs ko girki ma banason ki sake kinji Mammy to be?”
“Baby ai gatan yayi yawa kod’an girki ne seka barni inayi.”
“Banaso kinsan abinda nakeso dake?” Kai ta kad’a mai.
“Abu d’aya nakeso dake just take care of yourself and our baby shikenan, zakimin?”
“Ofcourse Habeebi.”


Shi da kansa yayi serving nasu abincin suna ci suna hira gwanin sha’awa har suka gama d’aki ya shiga ya canza suit nasa yasa sweaty pants da longsleeve shirt sannan ya d’auko mata hijabin ta itama. “Baby zamu fita ne?” Ta tambayesa alokacin daya k’ariso cikin parlour’n. Be amsata ba seda ya sa mata hijabin tukuna. “Asibiti zamuje.”
“Muje muyi me kuma? Ba gashi munyi test d’inba and its positive meh amfanin zuwa?”
“Trust me Flower lets go no arguement” badan tanaso ba tayi shiru hannunta cikin nasa suka fice, isarsu asibitin keda wuya Fannah ta soma rigima ita barata fito ba da k’yar da lalashi yasamu ya fito da ita daman already ansan da zuwansu basuyi wani zaman jiran doctor ba aka kaisu d’akin sede Anas be d’au na miji neba doctorn acewarsa mace ce. Bayan sun gaisa yayi ma Dr bayanin komai sabida yasan bayi Fannah zatayi ba. D’an k’aramin k’ofan dake cikin office d’in Dr’n ya buk’aci Fannah data shiga bayanta Anas yabi suka shiga tare haka shima Dr’n, kan wani k’aramin gado dake a gefe guda a d’akin likitan ya buk’aci Fannah ta hau kafin ta miqe akai Anas ya dakatar da ita ta hanyan rik’e hannunta “Dr I don’t get it kana nufin kaine zakayi mata scanning d’in?” yayi magnar cike da rashin yarda.
“Yes Mr. Fauzi this is something I do everyday karka damu.”
“Inaaaa!!” ya fad’a yana girgiza kai. “A nemo female Dr kawai ba yadda za’ayi matata ta kwaye maka cikinta banaso.” (kishi ya k’osa) Dariya sosai yabawa Dr’n.
“Toh nid’in acewarka banida mata ne? Ko bakasan har karb’an haihuwa inayi ba. This is my job.”
“Oho bansani ba nide a nemo female Dr.” Fannah dake tsaye a gefensa ne tasoma jin kunyan abinda yakeyi shegen kishi sekace d’an k’aramin yaro. “Baby kabari please its embarrassing.”
“No Flower its not nide barin bari ya gane miki ciki ba.” Dawo da kallonta kan Dr’n tayi. “Dr please I’m sorry, haka yakeda wawan kishi in akwai female Dr a nemo mana ita please I’m sorry.” Kai kawai ya kad’a sannan ya fice ya kira wata female Dr in less than 10 minutes ta iso se mita take jin an ambaci Mr. Fauzi tayi shiru ta fara fara’a. Shi da kansa Anas ya kwantar da Fannah ya kwaye mata kayan daidai cikinta sannan ya riqo hannunta cikin nasa yana kissing.


Cikin scanning machine d’in aka nuna musu d’an d’ayansu wanda yake nan d’an k’ararrami kasancewar Fannah is only 5 weeks pregnant dan marmari har printing photo scan d’in seda sukayi har copies uku. Shawarwari da dama female Dr d’in ta basu takuma buk’acesu da suna zuwa on regular basis bayan ta rubuta musu ‘yan maguna. Godiya sosai sukayi mata sannan suka fice chemist siyan maganin tun achan nurse d’in tasoma yima Anas wani gane gane taga mutum da blue eyes aiko Fannah na noticing haka ta tura Anas ta amshe maganin da kanta shiko basarwa yayi, yi yayi kamar besan meya faru ba.


Suna zaune cikin mota Fannah taciro photos d’in ta mik’awa Anas d’aya duk sun zurfafa suna kallon photo d’in daga bisani suka ce da juna “what do you think is our baby’s gender?” a tare. Murmushi duka sukayi “you go first” Anas ya buk’ace ta.
“No you” ta amsa sa.
“Okay nikam ban damu ba muddin mutum ne like us and zan iya kiransa ko ita Mini Fauzi alhamdulillah.” Dad’i sosai taji dayace haka ba kaman wasu jahilan maza masu cewa se na miji suke so ba basu san ‘ya mace. “Kefa Flower?” ya tsamota daga duniyar tunanin data wula.
“Me too Baby I love our baby look at it.” Ta matso masa da picture’n se admiring babyn da basu san hannayensa ba bale k’afafunsa suke. A hanya Anas ya riga tsayawa yana siyawa Fannah kayan k’walama kasancewar female Dr tace masa mata masu ciki akoi su da kwad’ayi kuma ana iya k’ok’ari ana biya masu buk’ata.
“Baby wai ina za’a kai wannan abubuwa ne?”
“Nakine dana babyn mu in ke bakiso shi ko ita suna so.” Bayan sun iso gida ya cicciro komai da kansa be barta ta ta cire koda tsinke ba suna zaune a parlour suna shan ice cream Anas ya d’ago wayarsa dake kan centre table.
“Me zakayi Habeebi?”
“Zan kira Ummie in sanar da ita ne.” Take ta taso daga jikinsa tana zaro idanunta.
“Ka sanar da ita meh?” Ta tambaya cike da rashin fahimta.
“That you are pregnant.” Hannu tasa ta wabje wayan. “A’a wallahi bara’ayi kayan kunyan nan dani ba.”
“Flower wai wani kayan kunya?”
“Ai kafini sani dawani idan kakeson Ummie ta fara kallo na? Ni gaskia kabari in cikin ya girma da kanta zata gani amman haka kurum ka hau kiranta kana fad’a mata inada ciki banaso”
“Toh naji sarkin kunya Mami fa? Kawo in sanar da ita.”
“Danqaree! ashe bakason na sake sa k’afa a gidanmu kenan ai in Afrah taji inada ciki I don’t think zata barni in sake shan iska.”
“Kefa kike damuwa, kowa ta yadda muka bi aka haifesa kuma shima haka yabi ya haifi wasu, I see nothing wrong.”
“Eh koma meh ni kar a kirasu.”
“Toh Mrs. Fauzi naji yaushe zamu fita first shopping wa baby?” Ya k’are maganar tare da dafe hannunsa kan cikinsu (injisa da fad’i) yana shafawa a hankali.
“Kai Habeebi yanzu cikin wata biyar za’a ma siyayya?” ta k’are maganan tare da kai spoon na ice cream bakinta.
“Eh mana koda cikin kwana d’aya nema you just don’t know how excited I am nima nakusan zama Daddy.” Gira ta had’e wanda a dalilin haka Anas ya tambayeta ko lafiya.
“Wani irin lafiya Habeebi? Bayan tun ban haifo baby’n ba ka fara nunawa kafi son sa fiye dani.” Kwashewa yayi da dariya “aww dariya ma nake baka koh?”
“No Flower I’m sorry, I love you guys all kinji? You guys are my family ai kema kinsani duka inasonku kuma ma nafison ki tunda kece source d’in happiness d’ina.” Ya k’are maganan tare da placing mata peck a kumatu anan ne ta d’anji dama-dama.

“Kuma Baby please kad’au min alk’awari baraka na biyewa ‘yan matan wajen nan ba kaga ko nurse na d’azun nan se kallonka take.”
“Toh Flower taga Mr. Handsome ba dole ba.” yayi maganar cike da gatsine dakuma gira d’aya d’age.
“Naji kuma nasani you are handsome and thats why am jealous of you banason ana gani mun kai haka.”
“LOL Flower is jeolous.”
“Habeebi I’m serious wallahi banaso” ta k’are maganan kamar wacce zatayi kuka.
“Shhh! Baby Mamah karkiyi kuka hakan bare k’ara faruwa ba, I promise.” murmushi kad’ai ta saki masa.

*****
Tun daga ranan Anas ya maida Fannah tamkar gold da ba’asan yasha wahala, ko aikin d’aga tsinke ya hanata yi ba aikinta se kula da kanta dakuma little one nasu. Wani soyayyan ma se a yanzu yasoma nuna mata kamar hauka fiye dana da bayasan komi ya tab’ata kullum hannunsa na akan cikinta yana feeling baby’nsu, Anas ya d’au son duniya ya d’aura wa cikin Fannah, ko kwanciya anyhow ya hanata wai shi kar ajima baby’nsa ciwo wani sa’in har haushi yake bawa Fannah dan abinda yakeyi itan da abu ke jikinta amma batada iko akai.

A dalilin condition nata da rashin samun cin abincin da takeyi atimes yasa ya samo mata nutritionist me kula da cin abincin mara lafiya. Morning sickness kuwa bata dena ba har a yanzu dakuma kasala kamar yadda female Dr ta fad’a musu se ta wuce first trimester’n ta zata dawo old self nata. Sosai Anas yake kula da ita kusan a kullum sesun ma baby nasu shopping duk abinda Anas yagani ina a store kokuma online seya siya wa baby’n, bayi barin komai ya wucesa. Duk yadda Fannah zata iya bi dan hana Anas sanar dasu Mami da Ummie tana da ciki tabi amman haka seda ya kirasu ya fad’a musu tsantsan murna, duk suka tayasu murna babu kamar Afrah dake ma Fannah wak’a wai taci wake.
Anas fa ba wasa tuni ya bada d’aki d’ayan dake tsakanin d’akinsa dana Fannah aka soma renovating dam aka cikasa da kayakin wasa da had’ad’d’un gadajen baby har guda biyu wanda yayi placing order daga Italy koda Fannah ta tambayesa dalilin dayasa akayi painting d’akin baby pink ce mata yayi wai ji yake ajikinsa mace kyakkyawa zata haifa masu me blue eyes kamar nasa danko har mafarki yayi, dad’i sosai taji, Anas is her everything bata tab’a neman abu k’ark’ashinsa ta rasa ba sesa a kullum take masa addu’a Allah ya cigaba da kare mata shi. A kullum kafin yadawo daga aiki suna kan video call inkuwa ya dawo suna a d’akin babynsu suna admiring d’akin, ga story books dam cike a cikin shelve d’akin baby on board na Mr. And Mrs. Fauzi kam se wanda yagani!


2 weeks after first visit nasu suka sake komawa asibiti akayi scanning cikin, baby’n na nan cikin k’oshin lafiya kuma sosai ya k’ara girma compared to zuwansu na farko, cikin nata nada 7 weeks yanzu sam kamar bame ciki ba, cikin nata na nan flat shide Anas ya k’osa yaga lokacin da cikin Fannah ze fito kodan yasamu abin neman tsokanarta.


★★★★★
_3 Weeks Later..._

Cikin Fannah nada 10 weeks cus! 2 months two weeks kenan dake takusan fita a first trimester nata yasa yanzu morning sickness d’in ya ragu compared to da a hankali take gaining back k’arfin jikinta unlike before da kullum take cikin bacci cikin nata wani haske da fresh ya k’ara mata sosai ga wani cikowan datake tayi daga sama har dan haka tasoma zama da hijabi agida wai kunyar Anas takeji se in an


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login