Showing 204001 words to 207000 words out of 268365 words
Chapter 69 - Tana Tare da ni complete book document .txt
lura yanzu za’a iya ganewa tanada ciki danko ya b’ullo kai kad’an wanda in tasa tight kaya yana d’an nunawa.
Yau ranar ta kasance Tuesday kamar yadda tasaba ada ta cigaba dayi yanzu dukda Anas ya hanata amman sam tak’i jinsa. 6:00AM ta tashi ta had’a musu breakfast sannan ta tada Anas yayi wanka seda ya gaishe da babynsu sannan ya gaishe da Fannah bayan sun k’are breakfast ta tayasa gama shiri tana cikin gyara masa necktie tayi noticing kallon ta da Anas yake danko ‘yar vest ce kad’ai jikinta.
“Habeebi wai me haka? Kadena kallo na haka.” Tayi maganan a lokacinda ta sauk’e hannunta daga wuyansa bayan ta gama d’aure masa neck tie d’in ta juya masa baya nan tashiga nemo hijabinta daman tasan this is coming. Juyo da ita yayi tare da sauk’e hannayenta data azasu kan k’irjinta tana karewa.
“Flower kin gani kuwa?”
“Ga meh?” Ta tambayesa fuskarta ad’an tamk’e. “Kasakemin hannu.”
“Bakiga...” Yakasa k’arisa maganan dan yadda k’irjin Fannah daya cike dam ke d’aukar masa hankali.
Hannu tasa ta mari kansa a hankali “Habeebi kabar kallo na haka banaso.” D’an k’ara yasaki “awch! Flower tsaya kiga” hannunta yaja ya kaita gaban dressing mirror “kiga fa” yace da ita yi tayi kamar bata gane me yake nufi ba.
“Mezan gani?”
“Flower wai so kike kice bakiyi noticing ba?”
“Noticing meneh? Nikam bye ga jakanka d’auka ka fice.” Murmushi sosai ya saki “kema kinyi noticing kenan.”
“Eh mana nida jikina taya barinyi ba, Habeebi yayi muni ne?” Ta tambaya fuskarta kan wanda zeyi kuka.
“Oh common Flower ko kad’an it actually fits you kin ma fi kyau haka.”
“Habeebi are you sure?” Ta juyo gaban mirror tana kallon kanta.
“Yes Flower I love you.”
“I love you too Baby nace ko driver ka turomun se ya kaini asibitin kasan tace yau mukoma kuma kanada meeting.”
“Flower kibari mana muje gobe.”
“Habeebi yau fa tace karka damu I will be fine.”
“I will cancel the meeting.”
“Habeebi no need off you go.”
“Flower are you sure?”
“Eh mana zuwa asibiti ne kuma sabon abu? Zanje indawo fine and good in shaa Allah.”
“Okay in driver yazo ki kirani ki sanardani in kuka isa asibitin nanma ki kirani sannan inya dawo dake nanma ki kirani ki fad’amin I can’t afford it in wani abu ya sameki ko baby’n mu Flower.”
“Yes Sir zanyi as you say in shaa Allah ba abinda ze faru.”
Kallon d’an k’aramin cikinta ya tsaya yi ganin tasa hannunta cikin rigar ya sasa murmusawa “kinga cikinki ya fara fitowa very soon ze zama k’ato irin na Nigerian police.” Bugi cike da shakwab’a ta kai masa a hannu “haba! Habeebi banaso in shaa Allah ciki na bareyi k’ato ba.”
“Se yayi kijira nan da months kawai kiga wonders”
“Habeebi manaaa!!!” ta hau bubbuga k’afa.
“LOL Flower” ya matso da ita jikinsa “karki damu ko ya kike koya girman cikinki yake you are still the slim, elegant Fannah Aleeyu Fauzi that I know nothing will ever change kinji?” Kai ta gyad’a masa tana murmushi sanan tayi hugging nasa.
Har bakin k’ofa ta rakasa as always ta miqa masa jakansa sannan tamasa goodluck kisses shikuma yayi kissing cikinta tare da cemasa ko ita “I love you” ganin Fannah ta had’a rai ya matso kunnenta itama yayi whispering “I love you also Baby Mamah” se anan ta murmusa “I love you too Habeebi, take care of yourself for me and our baby”
“I will Flower and you too in na dawo se muyi maganan wani country kikeson muyi proceeding ante natal namu” zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyan aza yatsansa kan bakinta “shhh! Flower na fad’a miki ni ba’a Nigeria nakeson ayi rainon babyn mu” tana murmusawa ta gyad’a masa nan ya fice da murmushi d’auke a fuskokinsu both seda gate ya ruhu ta dawo ciki.
****_10:30AM_
Dai-dai nan driver yazo d’aukan Fannah kamar yadda Anas ya buk’ace ta haka tayi dasuka isa asibitin ma ta kirasa again bayan angama dubanta driver yadawo da ita gida ko jakarta bata ajiye ba ta zaro wayarta ta danna masa kira bada jimawa ba ya d’aga.
“Halo Habeebi”
“Yes Flower... Har ya dawo dake gida ne?”
“Eh yanzu shigowa na ko jaka ma ban ajiye ba nace barin kiraka.”
“Thank you honey, so how is our baby?”
“Its fine Dr tace in pregnancy’n yakai 4 month za’a iya gano sex d’in.” Cike da jin dad’i yace, “wow! Great news I can’t wait.”
“Me either I have a suprise for you.”
“Again? Flower bakiya gajiya da bani suprises and I love them.”
“Saboda ina sonka Baby yau zan baka hint na suprise d’in.”
“Really? Toh inaji”
“Its regarding our baby.”
“Ohh wow! What about it?”
“Kai Habeebi kanamin wayo kanason in sanar dakai koh?”
“Please Flower...” Yayi pleading.
“Okay nasa anyi mana printing photo scan d’in.”
“Haba! I can’t wait indawo gida.”
“And guess what?”
“What?!” Ya tambaya ba tare da b’ata lokaci ba.
“Legs and hands na baby namu sun k’ara tsayi kuma har sun fara girmar da faracu.”
“Dagaske Flower?!” Yayi exclaiming cike da jin dad’i.
“Wallahi Habeebi its soo cute karka damu nayi printing out 3 pictures in kadawo zan nuna maka.”
“Happy us Mammy and Daddy, kinsan wani abu?”
“A’a Habeebi seka fad’a.”
“In nadawo we will think of wani suna zamu bawa baby’nmu.”
“Habeebi ai toh bamusan gender d’inba.”
“Nifa na fad’a miki mace ce.”
“Toh inkuma na miji ne fah?”
“Se muyi suggesting 5 names na maza 5 names na mata ciki semu zab’a two dayafi dad’i na both sexes.”
“Yeyy! to seka dawo I love you.”
“I love you so much more Flower yanzu kije ki kwanta kihuta kinji?”
“Yes Baby bye.” Nan tayi hanging hannu tasa zata zaro photo d’in dan sake gani aka danna door bell “wayene?” ta tambaya daga nesa.
“D... Dr... Driver ne Hajiya.”
“Moosa?” Ta tambaya tana nufowa bakin k’ofar.
“Eh.. Ehh shine” yayi stammering again.
“Toh meya faru haka?” Ta tambayi kanta ba tare da b’ata lokaci ba ta bud’e k’ofar ganin fuskarsa tayi duk jini ga idansa d’aya daya kumbura sakamakon bugin daya sha ga dukkan alamu. Hannu ta aza a bakinta tare da zaro idanunta waje “Ya Salam Moosa meya same ka haka? Innalillahi wa inna ilaihi r-” bata k’are salatin ba taga mutum from nowhere ya b’ullo a bayan Moosa rik’e da bingida a hannusa ya d’aga sama.
Wani erin mumunan fad’i gabanta yayi wanda ta jima batayi erinsa ba da yazo da mumunar k’arshe da cikin dake jikinta ma seya zube take a wajen dan yadda ta tsorata, takuma tsure, zuciyarta se bugun d’ari-dar’i yake a yayinda bakinta ke b’ari ko kiran sunan mutumin ma takasa dukda kuwa bayau tasoma ganinsa ba...
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[12:58, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕, Ummee, Anee and Lilmeerahcute.*
7⃣9⃣
Alokaci guda k’wak’walwarta tabar aiki dan irin matsanancin tsoro da fargaban da ta shiga ji take inama ace mafarki ne. B’ari sosai both jikinta da bakinta suke “Fff.. Fa... Ya Farouq?” Ta kira sunansa cike da tashin hankali dakuma rashin yarda gashinan zahiri a gabanta amman jikinta yak’i yarda mata shid’in ne. Bakin bindiga ya sake bugawa kan Moosa seda ya fad’i sume a wajen. K’ara ta saki sosai tare da toshe kunnuwanta wani irin la’anannen murmushi ya saki yana nan kamar yadda yake ba abinda ya canza tattare dashi illa duhun daya k’ara.
“Ohh what a sweet voice I’ve been missing ashe matan nawa barata manta da suna na.” Da k’afansa ya shure Moosa gefe guda dan wucewa ganin hankalin Fannah tashe akan sumemmiyar jikin Moosa yasa yace, “wifey karki damu dashi, kuma haka ake karb’an baqo ne? ba ko sannu dazuwa toh shigo da kaina inga wannan one in town mansion da ake ta maganansa a gari.” Nan ya miyar da bindigan aljihunsa yazo shiga kenan wani erin k’arfi yazo mata alokaci guda ta ture k’ofar sede aikin gama yariga ya gama hannu yasa ya kareta daga rufe k’ofar d sauri “wifey wai haka kike karb’an bak’i? oh please don’t be like this.” Baya baya ta soma yi har yanzu se b’ari take ganin haka ya cafko hannunta da k’arfin dayasa hawaye suka ciko mata a ido.
“Ina zakije wifey?”
“Yyy... Yya Farouq dan Allah ka sakemin hannu ba kyau ka sakeni please na rok’eka da Allan da rana ke hannunsa let me go...” Ta k’are maganan cikin sautin kuka.
“Ohhh wifey don’t cry please kinji? Banason ganin hawayen nan” hanky yaciro na k’arfi da yaji ya share mata hawayen har a yanzu bata bar k’ok’arin k’watan hannunta ba.
“What a wonderful house inhar Mr. Fauzi ne yayi desging to gaskia kudos to him gidanku yayi kyau sosai baraki d’an zagaya dani ciki ba nima in d’an gani wifey?” Ya k’are maganan dawani maqirin murmushin daya karkato ta gefe d’aya a fuskarsa. Hawaye take har a yanzu “Ya Farouq I’m not your wife kuma dan Allah kayi hak’uri ka koma inda kafito, ka sakemin hannu please matar aure ce ni ba kyau” ta sanar dashi cikin murya me rawa.
“Ohh wonderful wifey ya kike magana haka? Rabuwa na dake tun yaushe amman ace wannan kalamu zaki fad’a mun don’t you miss me? Ko kad’an bakiyi missing d’ina ba?” Hannunta ya ja da k’arfi seda ta fad’a jikinsa. “I missed you wifey, kullum da tunaninki nake kwanciya in tashi inkuma sake yini dashi.” K’irjinsa take bubbugawa da k’arfin da Allah ya bata tana kuka tana had’asa da Allah amman ko a jikinsa se sake matseta yake yana shunshuna daddad’an k’amshin jikinta dukda haka bata bar kaimasa bugi ba seda yagaji ya raba jikinsa da nata hannunta still rik’e da nasa a hanakli ya murza hannun nata.
“What a soft skin wifey, kinga wani fresh da kika k’ara kuwa? Mr. Fauzi ya riqe min amanar ki...” D’an hamma ya saki “yunwa nakeji nasan gidan Mr. Fauzi ba’a rasa kayan dad’i” hannunta yaja zuwa dining space ya bud’o fridge tare da ciro bufallo wings guda biyu da chapman drink, kan dining ya zauna ya buk’aceta da tayi hakan itama sam tak’i. Bindigan aljihun nasa ya ciro nanma tak’i se b’ari take duk yadda tayi dan kwantar da hankalinta ta kasa batason tsantsan tashin hankali tayi miscarrying babynsu, murmushi kad’an ya saki cike da mugunta “ko ki zauna kokuma in bindige kan Moosa dake waje.”
“Ya Farouq mesa kake haka? When will you ever stop dan Allah? Me Moosa ya maka da zaka masa haka? Shin bakada imani ne?”
“Imani? Yes Fannah banidashi sabida na siyar wa shed’an akanki Fannah kowa ze iya mutuwa bakisan yadda nakesonki bane shiyasa kike min wannan banzar maganar” rigan shirt nasa ya sauk’ar ya nuna mata tattoo dake hannunsa “ko ban fad’a ba kema kinsan hat F&F stands for, now sit!” Ya daka mata tsawa cike da tsoro ta zauna gefensa se hawaye take kamar lalacaccen famfo cikin kwanciyar hankali yagama cin abincinsa sannan ya kora da drink ko kubya babu.
“Tunda kink’i zagaya dani I think its time to go” ya sanar da ita a lokacin daya mik’e yana k’ok’arin rik’o hanunta. Hannun nata taja ta sa cikin hijabi sannan ta hsare unstoppong hawayenta, “go where Ya Farouq? Where are you taking me? Dan girman Allah karka min haka ka tausaya min please.”
“Wifey ai tausayin ne yajawo haka” cike da mugunta ya miqar da ita daga saman hannunta wani irin wahalallen k’ara ta saki “Anas! Anas! Anas! dan Allah kazo ka taimakeni, Anas pleaze come.” ta fashe da kuka...
“Chill chill wifey Anas naki ba yanzu zezo ba saboda yana da meeting 1:30PM to 2:30Pm so kinga se k’arfe uku ko hud’u kamar yadda ya saba ze dawo dan haka kima bar kiransa for help.”
“Ya Farouq me kakeso wallahi in kud’i ne zan baka dayawa muje safe na Anas zan baka ko nawa kakeso amman dan Allah karka kaini wani wajan karka rabani da gidana da mijina please Ya Farouq ka tausaya min nasan I can’t fight you kaji k’aina please.” Ta k’are maganan tana kuka sharqaf sharqaf.
“Ohh wifey meyayi zafi haka? Bar kukan nan please zancen kud’i kuwa wanda kike kira da mijinki shi ze dank’a min arzikinsa gabad’ai yanzu lets go.” Bata bar rok’ansa ba har a yanzu se janta yake da k’arfi tana jan kanta baya tana ihu tana kiran sunan Anas har sun kai da bakin k’ofa ya dakata yaje ya d’ago jakarta da wayanta sannan yasa hannu a aljihunsa ya ciro wani ninkekken takarda ya ajiye gab da bakin k’ofar sa’annan ya bud’e k’ofar har a yanzu Moosa na nan a sume k’ara k’arfin sautin kukanta tayi tana me kiran sunan Anas har a yanzu. Cikin motan da driver ya turo Anas k’irar Audi jeep 2016 yasata ciki tare da zaro handcuff ya had’e hannunta da k’ofar ta yadda barata iya guduwa ba sannan yaje yaja sumemmiyar jikin Moosa yakai gefe d’aya daga cikin motocin da akayi parking nasu a lot kome ya sake canza masa ra’ayi se kuma ya sake jan Moosa yakai motar dayakeson tafiya da Fannah, cikin open booth ya jefa Moosa.
*****
Anas na zaune a office nasa dawasu files na Unity Global intercome yana going through kawai seyaji gabansa yayi wani irin mumunar fad’i wanda ya rasa dalilin hakan, coffeensa da Fannah ta had’a mai ya zuba kad’an a cup yasha amman inaaa yakasa samun sukuni rolex agogon hannunsa ya duba yaga 12:32PM har ya d’ago wayarsa dan kiran Fannah kuma se ya tuna ashe d’azu ya buk’ace ta takwanta tayi bacci bari ya tura mata text message kar ya tak’ura mata.
Da murmushi a fuskarsa yamiyar da wayan bayan yayi mata sending ya ajiye sannan ya cigaba da abinda ke gabansa...
*ANAS* _3:57PM_
Shigowan Anas gida kenan bayan ya miyar da k’ofan ya juya yana neman Flowersa normally inba wai bacci take ba she’s always around tamishi sannu da zuwa sab’anin haka yayi concluding a ransa koda bacci take har yanzu. D’akinsu ya nufa to his suprise be ganta ciki seyayi tunanin ko tana bayi, dining ya dosa dan ciro bufallo wings daya siyo wa kansa dankuwa Fannah bata ci sama da k’asa ya nema abinsa ya rasa mamaki ne kwance a fuskarsa. Yaushe Fannah ta iya chin bufallo wings da har zata cinye guda biyu? “Wow!” Yayi exclaiming a fili “bade cikin naki ze miyar dake glutton ba Flower.”
Packaged chicken yaciro yad’an ci kad’an dan bawani yunwa yakeji ba bayan ya k’are ya koma d’aki sede still ba Flowersa bayin ya dosa yayi knocking. “Flower?” Ya kira sunanta.
“Flower kina ciki ne?” Jin shirun yayi yawa ya murd’a hannun k’ofar ya shiga sede ba Flowersa ciki anan fa hankalin Anas ya fara tashi, d’akinta ya dosa a gurguje nanma ba ita ba alamunta haka ya duba d’akin babynsu nanma ba Fannah tirk’ashi!
Gidan kap ya zagaye yana kiran sunanta yana nemanta aman ba ita ba alamunta ba. Toh kode tafita ne? Ina ma zataje ai Flower bata zuwa ko ina kuma inda wani gun zataje