Showing 207001 words to 210000 words out of 268365 words

Chapter 70 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54144

da ta sanar dani, toh ina take?
A rashin samun amsoshi ga wad’annan tambayoyin yasa ya koma ciki dan d’auko wayarsa ya kirata yaji daga bakinta yashiga kenan kasancewar ba takalmi k’afansa yaji kamar ya taka abu a nitse ya miyar da kallonsa kan right foot nasa inda yakejin ya taka abu bayan ya matsar da k’afan yaga paper ne aninke dudum! Yaji zuciyarsa ya sake bugawa fiye da na da se ayanzu yakejin something bad is happening to his Flower and baby ba tare da b’ata lokaci ba ya d’ago paper’n ya bud’e cikin sauri ya soma karantawa;


_Welcome back home Mr. Fauzi gida yayi kyau masha Allah nagode da riqe min amanan *whats mine* da kayi. I know baka mance ba whats mine is MINE 09011140607 you might get the chance to listen to her voice if you are lucky. Team F&F_


Rawa jikinsa ya soma a yayinda tunaninsa ya jaqule, wani irin gumin da ko ACn ma yakasa d’aukewa ne suka soma gangaro masa from nowhere, blue eyes nasa suka sake shiga darker tsabagen tashin hankali, migraine nasa ne ya bugo sa a lokaci guda wanda bare iya tuna when last rabuwarsa dashi ba. Hannu yasa ya dafe kan nasa cike da azaba ayayinda k’afafunsa ke rawa.
“FAROUQ!” ya furta a hankali cike da tashin hankali.


***** *FANNAH*
_Chan bayan garin Maiduguri_
Cikin wani abandoned uncompleted building me steps kusan biyar wanda ba’ayi painting ba windows ma ba’a gama sawa ba a floor na k’arshen. Irin tsagerun unguwa masu shaye shaye ne guda biyar k’ati a bakin entrance door d’in da alama gadi suke. Cikin gidan a second floor cikin wani d’an madaidaicin d’aki wanda yake nan da k’aramin rug seda sofas guda biyu da k’aramar fridge seda gado cikinsa. Fannah ne ke zaune kan wani kujeran katako hannunta da k’afafunfa duka d’aure jikin kujerar bakinta kuwa makeken cellotape ne anrufesa dashi hawaye ne ke gangarowa har yanzu kan lallausar kumatunta. Fuskar nan nata yayi ja dan kuka nishi take a hankali abin tausayi ayayinda Farouq ke tsaye a kanta yana shafa sajen fuskarta dayasamu fitowa dan yadda hijabin jikinta yayi baya.

“Wifey I told you to stop fighting amman kink’i inda kin bani had’in kai daduk hakan be faru ba, bakiga d’akin dana gyara mana bane dake 3rd floor? Just for me and you nasan kin saba da california bed agidanki but karki damu jiran call nake daga gun Anas yana turomin kud’i zan canza mana gida sorry you have to manage.” Y’unkurin magana take amman ba hali dan cellotape dake bakinta. “Shhh! Ba sekinyi magana ba so kike na cire miki wannan?” Yashafa kan celotape d’in ta inda bakinta yake. Kai ta kawar da wuri idanunta basu bar tsiyayar hawaye ba har a yanzu. ‘Yar murmushi ya saki “ya naga kamar kina zufa? Acire miki hijabin ne?” Yana tab’ata tahau shure shure da d’an k’arfin daya rage mata a jiki.
“Kunyar nan taki ta munafirci na nan LOL karki damu zan cire miki shi a first night namu” dawo da kallonta tayi garesa tare da watsa masa wani irin disgusting kallo a zuciyarta tana me tsine masa albarka.
“Sweetheart don’t look at me your husband like that banson raini.” Jakarta dake kan medim sized bed ya d’ago tare da zazzagewa. Kud’i ne almost a bundle na d’ari biyar ciki seda turaruka da d’an kayan kwad’ayi irinsu tuwon madara, tsami gaye, tsamiyan biri da sauran tarukuce sam hankalinsa bekai kan photo scan dake a gefe ba.

Kud’in ya d’aga yasa a aljihunsa duka sannan ya d’ago wayarta ganin new message from Habeebi yasa yad’an murmusa “wifey bari muga wani saqo Anas ya turo mana” nan ya shiga ya karance a fili kamar haka;


_How lucky I am. I am falling and falling deeply in love with_
_the prettiest girl in the world. I am not ashamed to say this. Infact, I am proud of you and I'm not going to let you go, remember those times when I woke up in the middle of_
_the night just to watch your innocent face while you sleep? Remember those times when I woke up very early in the morning just to to serve you coffee in bed?_ _Remember_
_those times when I hold your hands tight and find it difficult to let you go? It’s because I love you so, and I long to be with you more. This is no mere words, it's_ _from the depths_
_of my heart. I love you Flower._


Dariya sosai ya b’arke da “stupid kawai† yafad’a a fili. Nan k’arfin kukan Fannah ya dad’u kuka take sosai abin tausayi a yayinda son Habeebinta ke sake shiganta da zafi da zafi. “Ignore the bastard wifey” nan yayi deleting message d’inma kwata kwata tare da ajiye wayan a gefe sannan ya hau tattara tarukucan su tsamiyan biri gefe guda. “Wifey bansan ki da ciye ciye haka bafa, taya Mr. Fauzi ze barmin ke kina wannan ciye ciyen k’aza-” be k’are maganar ba idansa yakai kan d’aya daga cikin photo scan d’in, sam begane me aciki ba seda ya d’ago ya matso dashi kusa da idanunsa yana examining anan ne ya gano kan mutum ne ga kuma hannaye da k’afafu dara-daran idanunsa ya zaro waje disbelievingly kai ya soma kad’awa gudun kar abinda zuciyarsa ke sak’a masa yazamo gaskia cike da tashin hankali ya maido da kallonsa kan crying Fannah wani irin tafasa zuciyarsa ke ga kishi bayyane karara a fuskarsa tun ba yau ba abinda yake gudu kenan rananda Fannah zata d’au cikin wani ba nasa ba.


“Ke!” Ya danna mata kira cikin wani irin husky voice sosai ta tsorata amman tak’i koda d’ago kai ta kallesa. A fusace ya mik’e ya nufo gabanta tare da murd’a mata kai seda ta kallesa na dole “meh wannan?” ya d’ago hoton yana nuna mata. Bayan data kalli hoton sekuma ta sake fashewa da kuka babban tashin hankalin da take ta guduansa kenan, tun d’azu addu’a take kar Allah yakai Farouq jakarta tsoronta shine karyace ze illata mata baby she can’t afford to lose her baby ya mata komai amman karya tab’a mata baby.
“Magana nake miki ba kuka nace kiyi ba. What is this?” Tsantsan kishi yariga ya mamaye masa zuciya besan a lokacinda ya d’aga hannu yakai mata wawan mari a fuska ba dukda bakinta a rufe ne amman seda d’an k’ara ya fito a yayinda hawaye ke ambaliya kan fuskarta.


“Meh wannan nace? Ciki kike dashi? Ciki?! Waya miki cikin? Am talking to you! Anas koh? Hahaha...” ya sakar da wata muguwar dariyan bosawa. “Bazata saku ba, Fannah you are mine baraki d’au cikin wani mahaluqi ba a duniyan nan ba se nawa muddin ina raye. Ki ware kunnuwanki da kyau ki saurare ni” ya nunata da yatsa “zubar da wannan shegen cikin Mr. Fauzin zanyi in kinga kin haihu da d’an wani toh Farouq ya mutu baya duniya” shaking kujerar take tana kad’a masa kai tana hawaye sosai aranta kuwa ba abinda take se kwararo addu’a...




*© MIEMIEBEE*


beeenovels.blogspot.co.ke
[12:58, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
8⃣0⃣

















Daidai yakai da bakin k’ofa ya murd’a handle d’in a fusace kenan wayarsa dake aljihunsa yasoma ringing dogon tsuka yaja sannan yaciro wayar ganin new number yasan Anas ne dan kuwa beyi registering numban kowa kan sim d’inba. Wani shu’umin murmushi ya saki sannan ya maida hannun k’ofar ya dawo ciki tare da zama kusa da Fannah. “We are having a call from Anas wifey.” yasake murmusawa. Ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga tare da sawa a handsfree yana shafa hannun Fannah a hankali in a romantic manner se k’ok’arin shuresa take amman takasa.


“Halo Farouq?” cewar Anas. D’an dariya ya saki “huh! How smart you are Mr. Fauzi harka gano nine na ma wannan big suprise d’in kenan? Well bravo.”
“Shut up you bastard where is my wife? Ina ka kaimin matata?”
“You shut up Idiot ko kayi behaving kanka kokuwa har abada baraka sake sa Fannah a idanka ba, mschw!”
“What do you mean Farouq let her go ka saketa dani kake da problem ba Fannah ba niya kamata ka kama ba ita ba, why are you such a coward?”
“Coward? Dan na karb’o whats mine shine zaka cemin coward?”
“Fannah was never yours and never will be-” katse sa yayi “don’t you dare Anas karka sake katseni idan ina magana yanzu ba wannan ba idan kanason sake jin voice na Flowerka you do as I say.”
“Farouq don’t dare touch her karka kuskura ka tab’a Fannah wallahi I will kill you inhar wani abu ya sameta.”
“LOL” ya k’yalk’yale da dariya “kill me? Ashe I will dye along with your Flower saboda nikeda iko da ranta yanzu aduk lokacin dana ga dama ina iya kasheta inkazo nima seka kasheni kaga ko semuje mucigaba da soyayyar mu kamar yadda muka saba chan a lahira kaikuma a barka anan.”

“Farouq you are going straight to hell and don’t you dare touch her-”
“Then behave yourself” ya katsesa.
“Naji I will karka tab’ata please.”
“Hohoho did the mighty Mr. Fauzi just said please? Lallai fa kanason Flower nan taka sede ba kamar yadda nakeson taba.”
“Farouq please shut up kafad’amin inda take banida lokacin jin nonsense naka, ina ka kaimin mata?”
“In fad’a maka inda take? Karka damu very soon zaka sani sede you’ll pay an amount in return. Kuma the next time ka sake cemin nonsense ka yarda dani baraka sake sa Flowerka a ido ba” ya k’are maganan yana shafa fuskar Fannah.
“Me kake nufi Farouq? Ransom?”
“Brilliant sesa nakeson harka da mutane masu ilimi kamarku ransom nake nufi”
“Farouq kasan meh? You are going straight to hell.”
“And your Flower is going with me” nan ya d’aga hannu yasake shafo fuskar Fannah da sauri ta kawar da kanta.
“Ina take yanzu? Taya ma zanyi trusting maqaryaci kaman ka? Taya zan yarda Fannah *_TANA TARE DA KAI?”_*
“Smart guy barin maka proving” cike da mugunta yasa hannu ya b’antare cellotape dake bakin Fannah wani irin azabartaccen ihu ta sakar wanda Anas yaji har tsakar kansa sannan kuma ta rushe da wani erin wahalallen ihu. Cike da tashin hankali Anas yayi maganar. “Flower! Flower!... Farouq please karka tab’a ta I will do anything dan Allah nace don’t touch her please...”
“Shhh!” Yace da Fannah yana shafa bayanta har a yanzu bata bar kukan ba, nan ya dawo kan wayar.
“Mekace Mr. Fauzi?”
“Anything Farouq please karka tab’ata I will do anything ka had’ani da ita please.”
“Zan had’aku na minti d’aya in exchange of N500,000 (dubu d’ari biyar) inkuma kanason kaji muryar Flowerka fiye da minti d’aya sekayi multiplying kud’in per minute N500,000 and karka yimin wasa da hankali zan maka sendn bank details d’ina inhar banga alert ba zuwa yamma believe me baraka sake sa Fannah a ido ba.”
“Farouq are you crazy? Wani irin hauka ne haka?”
“Fine and good bakason jin muryarta kenan am hanging up” fuskar Fannah ya juya cike da muguntan da yasata sakar da k’ara.
“Please don’t okay, okay I will ko nawa kakeso zan baka please kadena sata kuka.”
“Good boy Anas ga Flower ku gaisa kunada minti biyu” nan yasawa Fannah wayar a kunne cikin sautin kuka ta kira sunansa “Habeebi”
“Shhh! Flower don’t cry kinji?” magana take cike da tashin hankali dakuma tsoro.
“Habeebi ina tsoro dan Allah stop him yace ze zubar min da ciki, Habeebi ze kashe mana baby, dan Allah ka barsa ka hanasa karka barsa please Hab-” bata k’are maganar ba Farouq ya ciro wayar daga kunnenta “munafirci kike agabana?” Nan ya mik’e “kuma cikin seya zube, sena zubar kina wasa da Farouq.” fashewa tayi dawani erin matsanancin kuka jin haka Anas ya sake kid’imewa
“Hello...?” Anas yayi maganar cike da tashin hankali.
“Hello Farouq please speak up.”
“Meh? Meh? Kana cika min kunne fah.” Cewar Farouq ganin Fannah nada niyyan sake magana yayi sauri ya toshe mata baki da hannunsa d’aya.


“Farouq dan Allah kabar sata kuka, karka tab’a lafiyar Fannah I beg you ko nawa kakeso zan baka dan Allah karka mata wani abu she is sick already please karka mata wani abu.”
“Hohoho!!! Mr. Fauzi ashe ka iya rok’an mutum sede kash! Barin bar shegen ajiyar da kayi cikinta yaje ko inaba I must destroy it” jin haka Fannah tacize masa hannu da k’arfin da Allah ya bata take ya jefar da wayar wanda beyi landing ko ina ba sekan cinyan Fannah. K’ara sosai ya saki se buga hannun nasa yake a iska cike da azaba.
Anan tasamu daman magana “Anas Habeebi please help me dan Allah karka bari yamin wani abu Anas our baby please stop him.”
“Shhh! Flower bar kuka kinji its bad for your condition kuma in shaa Allah ba abinda ze miki. I won’t rest sena k’wato ki hannun Farouq bar kuka. Kinsan ina ya kaiki? Kinsan address d’in wajen?”
“Habeebi bansani ba a sume ya taho dani gidan all I know is babban buildin-” bata samu daman k’are maganar ba sakamakon marin da Farouq ya wanketa dashi wanda har cikin kunnen Anas seda yajiyo k’aran marin kuka tasoma papawa ba makawa abin tausayi.
“Ni zaki ciza? Eh? Bakida hankali ne?! Karki damu by the time na zubar da shegen abinda ke cikinki zaki shiga hankalinki mschw!” ya sake kallon hannun nasa a fusace sannan ya katse wayar tare da cire sim d’in ya taune sannan ya yasar. Kuka sosai Fannah ke kamar zata cire ranta. Wayanta dake kan gado ne ya soma ringing Farouq na dubawa yaga Habeebi wani dogon tsuka yaja sannan ya katse wayar nan Anas ya sake bugawa Farouq na katsewa kusan sau uku se a karo na haud’u Farouq ya d’aga.


Cike da tashin hankali Anas ke maganar “Farouq please karka ma Fannah wani abu, karka rabata da babynta ko nawa kakeso zan baka please don’t do such evil please karka rabata da abinda ke cikinta ka fad’a ko nawa kakeso zan baka please Farouq...”
“Huh! Let me see yanzu senayi tunani, zaman da zanyi dan gudanar da tunanin is 2 million sannan inna yanke hukunci sanar dakai zanyi nanma 2 million, kanaji na?”
“Inaji Farouq wannan ba matsala bane please karka mata wani abu batada lafiya she is your sister please karka mata wani abu.”
“Naji seka fad’a mata karta min misbehaving if not I might lose my patience.”
“Okay zan mata ka bata wayar please.”
“Kasani each minutes costs N500,000 d’azu kunyi 2 minutes 1 mil kenan.”
“Farouq yaushe mukayi 2 minutes ba katse wayar kayi ba?”
“Then fine zan kashe wayar-” da wuri Anas ya katse sa, “A’a please kar ka katse I will pay just give her the phone.”
“Good” nan ya maido da kallonsa kanta “ke! Gashi sauran kimasa wani munafircin kiga in ban rabaki da shegen dake cikin ki ba.” Hannu d’aya ya since mata tare da bata wayan sannan ya yi gefe guda a d’akin yana me zuba mata ido.


“Flower kinaji na?” cewar Anas. Cikin sautin kuka ta amsa “eh Habeebi.”
“Good kibar kuka kinji? And kiyi duk wani abinda ya buk’ace ki muddin be sab’awa muslinchi ba I promise I will let yo out of there, I love you.”
“Habeebi I miss you please karka d’au lokaci kazo ka d’aukeni, I don’t trust Ya Farouq dan Allah Habeebi.”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login