Showing 240001 words to 243000 words out of 268365 words
Chapter 81 - Tana Tare da ni complete book document .txt
yaranki abinda Ummimi tama Daddy’nki ba.” Daidai nan Hanan dake ciki tayi kicking take Fannah ta tashi “Habeebi Hanan ta motsa yanzu” murmushi ya k’irk’iro mata “yes Flower nima naji” hannunsu duka suka kai kan cikin nan Hanan tasake motsawa. Dad’i kamar ya cinyesu both suna feeling baby Hanan insu.
****
_Washegari 1:30PM_
Anas na tsaye a gaban mirror a bathroom fuskansa shaving cream ne da alama shaving zeyi danko riqe yake da shaving stick a hannu amman sam ya kasa yi, gabad’aya hankalinsa bayya a jikinsa ko bacci yakasa jiya se tunanin Ummimi yake, duk yadda yasan ze iyabi dan hana tunaninta yayi amman ya kasa the more yana hana kansa the more yake tunanin nata, Fannah ma takasa bacci ta zauna awake with him ko kad’an bayason maganan Ummimi koda Fannah ta taso da maganar masifa yake mata sosai wanda shima ba a son ransa yakeyi ba, he just can’t take it.
Ya zurfafa cikin tunaninsa next abinda yaji shine hannun Fannah akan nasa tana amsar shaving stick d’in kwata kwata besan lokacin da ta shigo ba. Sanye take dawani silky dogon riga me spaghetti hands. “Habeebi take it easy please banason ina ganinka cikin damuwa.” Juyo da fuskarsa tayi ta soma yimasa shaving d’in lightly kamar yadda take ganin yanayi. Bece mata komai ba har seda ta gama masa ta wanke mai fuskar tare da share ruwan da towel. Kallon kansa yayi a mirron, sosai shaving d’in yamasa kyau saboda bata kwashe gashin duka ba, tabar sajen da kuma beard nasa wanda suka had’e kad’an very light irin na larabawan nan sosai yayi kyau.
“Flower kin ma fini iya shaving d’in ban tab’a leveling haka ba” yayi maganar yana shafa kan gashin fuskar nasan. “Thank you sweetheart.”
“No big deal Habeebi” Hannayenta ya had’a gu d’aya tare da pecking nasu, “Flower ko baki fad’a ba nasani you are mad at me saboda abubuwan dana riga miki jiya, I’m sorry kinji? I’m sorry for shouting at you and Hanan”
“Na sani Abu Hanan you don’t have to be sorry komi ya wuce muje muci abinci amman yau ba anan nakeson chin abinci ba.”
“Fad’i duk inda ke da Hanan kukeso muje muchi.”
“A Restaurant Manhattan mukeso” (inda sukaga Ummimi jiya) kai ya girgiza mata “no Flower baramu je chan ba choose any other place amman banda chan.”
“Ayya Habeebi chan nakeso.”
“Flower NO! And that stays that bara muje chan ba.” Ba tare da tace komai ba ta k’wace hannayenta daga nasa ta fice zuwa d’akinsu tare da kwanciya kan gado tana jin footsteps nasa ta soma rera kukan qarya.
“Flower yanzu kuka kike saboda nace bara muje chan ba?” Yayi maganar yana k’ok’arin d’agota. Shuresa ta shiga yi “ka sakeni nikam bana so stop touching me.”
“Haba Mom Hanan I’m sorry kinji?”
“Banji ba ni ka sakeni.” Kunnuwansa ya riqe both “Flower I’m sorry kiyi hak’uri.” Da hanzari ta suk’e hannayen nasa “ni bance kabani hak’uri ka ka kaini Restaurant Manhattan kokuma karka sake min ko Hanan magana.”
“Flower kiyi hak’uri mana ki zab’i wani restor daban.” Banza dashi tayi tare da juya masa baya. “Mom Hanan magana fa nake miki...” Nanma shiru “Mom Hanan” still shiru “toh naji tashi muje Restaurant Manhattan d’in” a ransa yana me addu’an Allah yasa kada su had’u da Ummimi. Cike da ji dad’i ta miqe tare da brushing masa ligjt kiss a lips “thats my Abu Hanan! Lets go” kallonta kawai yake cike da adoration.
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[12:59, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
9⃣1⃣
Cike da so da qaunan juna suka shirya suka fita chin lunch a restaurant Manhattan kamar yadda Fannah ta buqata, bayan Anas ya kawo musu order’nsu suka soma ci cike da jin dad’i, sosai Fannah ta zage ta gabza abincin se kewaye kewaye take ko zata ga Ummimi daga bisani k’ofar restaurant d’in ya bud’u atare Fannah da Anas suka miyar da kallonsu wajen Ummimi sukaga tsaye wajen tana rik’e da leda da alama shopping tayi sanye take da rigan cleaners, mamaki ne fal kwance kan fuskokinsu musamman ma Anas _bade Ummimi aiki take anan as a cleaner ba?_ ya tambayi kansa disbelievingly. Sun d’au tsawon minti biyu suna kallon juna sannan daga bisani Anas ya kawar da kallonsa daga gareta ganin hawaye sun soma ambaliya mata a fuska.
“Flower tashi mutafi.” Dagangan tace, “Habeebi ban gama chi bafa.”
“Nasani zanje in siya miki wani lets leave now” yayi maganar tare da miqewa, kafin Fannah ta sake samun daman magana Anas ya d’agata badan tanaso ba tasoma binsa sunzo daidai bakin k’ofan kenan zasu wuce Ummimi tasa hannu ta tare Anas ta hanyan rik’o hannunsa chak! ya tsaya ba tare da ya juya ya kalleta ba.
“Anas dan Allah karka min haka nasan banida iko akanka nasan banida daman tambayar yafiyanka amman dan Allah kabani daman baka hak’uri dan Allah Anas” ta k’are maganar cikin sautin kuka. Shiru Anad yayi totally speechless ayayinda zuciyarsa ke raya masa kar ya kuskura yabata wannan dama zuciyan nasa kuwa yabi ya fisge hannunsa daga nata yakama tafiya, dawani erin force Fannah taja kanta baya tare da k’wace hannunta dake a nasa cike da tashin hankali ya juyo yana kallonta.
“Flower lets go!” Yayi demanding.
“No Habeebi I’m not going anywhere with you se inhar ka tsaya ka saurari Ummimi, haba mana Habeebi wannan fa mahaifiyarka ce ita ta tsuguna ta haife ka bekamata kana wulaqantata kamar kashi ba, Habeebi nasan kanason Ummimi please give her this one chance to explain herself please for Hanan.”
Alokaci d’aya Ummimi taji tana son Fannah dan yadda ta burgeta, “nagode ‘yata, Anas dan Allah kaji maganar matarka kabani daman baka hak’uri dan Allah Anas.” Hannunsa Fannah ta rik’o a hankali tana mirzawa “kaji Habeebi? Zaka iya bawa mahaifiyarka daman baka hak’uri, can you? Please...” Kallonsa ya miyar kan Ummimi daba abinda take banda kuka yana ganinta kawai se last incident daya faru tsakaninsu ya soma masa yawo a k’wak’walwa seyaji he can’t give her the chance she is asking for, gabad’aya ya riga ya dawo daga rakiyarta da ace 15years back ta dawo da yayi accepting nata amman banda yanzu. “No I can’t Flower I can’t mutafi nace!” Yayi maganar a tsawace.
“Habeebi is okay calm down okay? Calm down” tayi maganar cikin salon dake kwantar masa da hankali. _*“INA TARE DA KAI Hanan NA TARE DA KAI*_do this for me please just listen to her” badan yanaso ba ya gyad’a mata kai.
****
Zaune Anas da Fannah ke kan wani d’an dogon kujera a yayinda Ummimi ke zaune opposite them fuskarta jik’ap da hawaye. Cikin kuka ta soma magana;
“Anas nagode daka bani wannan dama nagode sosai Allah maka albarka” ko kallon direction nata baiyi balle yace ameen.
“Nasan banida izinin da zan fara rok’ar gafararka saboda abinda na muku, bansan ta ina zan fara baka hak’uri ba wallahi barin ku danayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwata Anas, kuskuren da har a yau ina nadamar sa kuma har in mutu zan cigaba dayi, wallahi sharrin shed’an ne it wasn’t my intention to leave you guys my family.” Ta tsaya ta share hawayenta tare da jan hanci “Anas I love you, wallahi ina sonka fiye da yadda nakeson kaina, tun tafiya na a kullum da tunaninka dana mahaifinku dakuma na k’annenka nake kwana nake kuma tashi dashi, da abinda na muku tun aduniya na fara ganin sakamakon sa ina ace na tafi lahira ban nemi gafararku ba? Anas dan Allah kayi hak’uri, baka bani dama ba amman ni na baiwa kaina kayi hak’uri ka yafemin please na tuba Anas ka tausaya min mahaifiyarka dan Allah d’ana barin iya samun kwanciyan hankali ba har se in ka yafemin ka tausaya min please.” Ta rushe da kuka miqewa Fannah tayi takoma gefenta ta tsaya tana shafa bayanta cike fa tausayi idanunta itama sunyi jazir. “Ummimi please kibar kukan haka nan ya isa dan Allah.”
‘‘Yata dan Allah kimasa magana ya tausaya min ya yafemin.”
“Anas Habeebi ka tausayawa mahaifiyarka please.”Kai ya girgiza cike da takaici “mahaifiya? Yanzu ke Ummimi bakiji kunya ba da kike kwatanta kanki da mahaifiyata nikuma da d’anki? Bakiji kunya ba? As far as I’m concerned Ummie itace mahaifiyata. D’an da kika tunkud’esa kamar kashi 15 years ago, d’anda kika k’yamata d’an da kika masa permanent tabo a hannu” ya yi rolling hannun shirt nasa ya nuna mata tabon tabbas ta tuna itace taji mai ciwon danko kafin ta fice daga gidan taga yadda hannunsa ke yoyon jini amman saboda yadda shaid’an yafi k’arfinta alokacin ta fice ta barsa. Wani sabon kukan ta rusheda.
“Kin tuna ciwon?” Ya tsamota daga duniyar tunanin data fad’a. “You think you still have the right to call me your son? Kinsan kalan k’uncin rayuwan da mukayi witnessing bayan tafiyarki? Kinsan ya akayi aka girmar damu aka girmar da Amal jaririyan da kika turo bayan tafiyarki precisely? Kinsan ya aka tarbiyyattar damu?” Zuciyanta taji yawani buga tare da sarin da kanta ke mata tana me k’ara tsanan kanta.
“Kinsan ya akayi muka taso ba gatan uwa har muka fara mancewa da labarinki? Kinsan dare nawa muka kasa bacci saboda tunanin ki? Kinsan kwana nawa na d’iba inayi a waje ina tunanin ko zaki dawo mana? Kinsan what hell you made Abuu went through? The answer is No baki sani ba saboda alokacin kina chan da sabon mijinki kina more rayuwa. Its all over Ummimi I’ve loved you, we’ve loved you so dearly bu not anymore banida gurbin da zan sake ajiye soyayyan ki a zuciya na saboda na dawo daga rakiyarki, ke kika haifeni I can’t change that amman abinda nakeson kisani shine ki sa a mind naki baki tab’a haifan d’a me suna Anas ba, so nake ki mance dani kamar yadda na manta dake a rayuwa na cause I can‘t forgive you I will NEVER forgive you.” Yana kaiwa nan ya miqe da sauri tare da juyawa gudun kar hawayen dayake maqewa su fito seda ya shanyesu sannan ya juyo alokacin kuka sosai Ummimi ke wane zata cire ranta ayayinda Fannah ke bata hak’uri.
“Anas tabbas ba k’arya cikin kalamunka tabbas nasan namuku laifi, laifin da yayi babban tabo duka a zuqatanku wallahi nayi nadama Anas kabani dama in biyaka 15years that passed, let me make it up for the past 15years da mukayi ba tare ba please kar ka hanani performing obligation d’ina as your mother.”
“You are not my mother so you don’t have to saboda I don’t need you ko ayau akace Ummie wacce ta girmar dani wacce nake regarding nata as my mother ta rasu zan cigaba da rayuwa na balle ke, because I’m a grown up now as you can see I’m married saboda haka I don’t need you na yafe miki tsawon 15 years da mukayi ba a tare ba, ba sekin biyani ba, kitafi ki koma inda kika fito banasonki a rayuwa. Flower lets go” yaja hannunta suka soma tafiya, k’ok’arin jan hannunta daga nasa take amman takasa har seda suka isa mota tana kuka tana mai magana “haba Habeebi ban tab’a sanin your heart is as cold ba se yau, mahaifiyarka ce fa your own mother koda laifin kisan kai tayi be kamata ka mata haka ba, ka duba yadda tayi nadama mana kodan haka baraka saurara mata ba?”
“Yes Flower barin saurara mata because I don’t need her 15years danayi ba ita yasa na mutu ne? No saboda haka bana buk’atar ta taje tasamu family’nta we don’t need her.”
“Hab-” katsesa yayi “enough okay?!” Yayi maganar cikin sautin tsawa ganin yadda ta firgita sekuma yaji ba dad’i hannayensa ya aza kan shoulders nata “Flower I’m sorry banason ina miki tsawa, banason muna musu banason Ummimi ta zama sanadin samu fad’an da bama yi please stop crossing me kibarta let her be kinfi kowa sanin kalan k’uncin data jefa mu especially me, data tafi ta barmu without turning back. Ko kin manta saboda ita nasoma shaye shaye har ya kaiga nayi raping naki Flower duk kin manta? It because of her you suffered itace silan komai Ummimi batada advantage se disadvantages.”
“Tabbas ba k’arya cikin maganganunka Anas” cewar Ummimi dake tsaye some inches away from them da alamun ta saurari dukkannin abinda Anas ya fad’a. “Tabbas duk wani abin haramun da ka aikata nima me laifi ce kuma nice sila saboda da ace ina nan da na hanaka aikata hakan, kayi gaskia da kace banida advantage se disadvantages all am asking for is kabani dama to be a mother to you again Anas koda baraka yafemin ba kabani dama insake rik’eka a hannayena in dafa maka abinci this is all I ask Anas please.”
“You should hace thought about this 15years ago kafin kika tafi, alokacin ne wad’annan kalamu naki zasuyi tasiri akaina amma banda yanzu da kika riga kika karya min zuciya in baki sani ba kisani I’m not the Anas you left 15 years ago wannan Anas bayida tausayi saboda tafiyar mahaifiyar sa yakoya masa rashin tausayi da imani, my heart is as cold as stone dan haka kibar b’ata yawun bakinki kina bani hak’uri barin tab’a hak’ura ba Flower lets go.”
“Okay Habeebi zan bika amman please kabani koda minti biyu ne inma Ummimi magana kaji?”
“Flower me zakice mata? Kibarta please.”
“Habeebi dan Allah fa nace please minti biyu kad’ai.¢ Kai kawai ya gyad’a mata “thank you so much my Lion.” Wajen Ummimi ta nufa taja hannunta suka b’ace daga kallon Anas bisa wani bench suka zauna Fannah na sharewa Ummimi hawaye. “Please kibar kukan hakanan ya isa dan Allah.” A raunane ta d’ago idanunta tana kallon Fannah “ ‘yata ya sunanki?”
“Fannah, Fannah suna na.”
“Masha Allah Fannah nagode da kulawarki a gareni Allah sak’a miki da alheri yakuma sauk’eki lafiya” (agarin share mata hawaye da Fannah ke hijabinta ya d’agu anan ne Ummimi taga cikin nata.) Mamaki ne ya mamaye fuskan Fannah taya Ummimi tasan tana da ciki? Cike da kunya tace, “ameen Ummimi please kibar kukan haka nasan Anas haka yake yanada taurin kai ne kuma sonki da yake yasa yake treating naki haka amman in shaa Allah wataran se labari Anas ze yafemiki nan bada jimawa.”
“Haka kike gani ‘yata Anas ze iya yafemin abinda na masa?”
“Allah ma muka mai laifi ya yafe mana balle d’an da kika haifa? Trust me ze yafe miki kidage da addu’a kawai nima zan saki cikin nawa.”
“Nagode sosai ya Shettima yake dan Allah?”
“Shettima nanan girmansa kusan d’aya da Anas yana kan karatu.”
“Masha Allah nasan da kunya ma in tambayeki ya baby’n dana turo musu da ita bayan tafiya na wanda ko halittan fuskarta ban k’arewa kallo ba.”
“Amal? Amal sunanta she is 15 years now itama ta na nan lafiya tana ss2 kinsan wani abu?” Kai Ummimi ta kad’a “sautin muryanku d’aya dakika fara min magana na zata ma Amal ce.” Murmushin takaici ta saki “Allah sarki Amal Allah yi mata albarka”
“Ameen barikiga pictures nasu” nan taciro wayarta tana gwada wa Ummimi, hawaye sosai Ummimi ke kamar ba gobe tana me sake tsanan kanta abinda ta ma family’nta. “Amal da Anas sak kaman ni na, Shettima ma ba laifi, ‘ya‘yan Albarka Allah ya cigaba da raya min su yamusu albarka, yamuku albarka gabad’aya” tafad’a tana share hawayenta. “Ameen Ummimi.”
“Ya Babansu yake? Wace Ummie da Anas yake fad’a kuma?”
“Babansu na nan k’alau, Ummie k’anwar mahaifinsu ce.”
“Ohhh Allah sarki nako ganeta itace ta girmar dasu?”
“Eh itace.”
“Allah sarki Allah ya saka mata da alheri, Babansu be sake aure ba?”
“Gaskia be sake ba”
“Allah sarki Ya Ibraheem, Fannah awani gari kuke yanzu da zama?”
“Dukan mu a Maiduguri muke.”
“Okay kunzo nan shaqatawa ne?”
“Eh munma kusa komawa zaman nan ya ishemu gida yafi dad’i.”
“Hakane ‘yata no place like home, dan Allah kitayani ma Anas magana nasan yana jin magananki koda bare yafemin ba yabani izinin zama mahaifiyarsa again, I want to make up for the past 15 years da mukayi ba a tare ba.”
“In shaa Allah Ummimi karki damu sede wani gudu ba hanzari ba am