Showing 228001 words to 231000 words out of 268365 words
Chapter 77 - Tana Tare da ni complete book document .txt
“gashi kiyi wanka semuci abinci I cooked your favorite.”
“Favorite wanne kenan? louisiana?”
“Yes sweetheart kishiga kiyi wanka ko in miki?” Towel d’in ta fisga daga riqonsa “haka kawai seka haumin wanka?”
“Barin iya bane?”
“Eh” ta fad’a tare da murgud’a mai baki. Gabanta yasha tare da d’agata sama chak! be direta ko inaba se cikin jacuzzi sannan yasoma raba ta da kayan jikinta. “A’a Habeebi wallahi zaka iya kayi hak’uri kabari please.”
“LOL shegen kunyan kinnan bansan ranan barinsa ba, ina jiranki” nan ya manna mata peck a kumatu sannan ya fice. Cikin kwanciyan hankali ta samu tayi wankanta ta fito zaune ta tarar da Anas gefensa wani baggi T shirt ne baby pink in color da hoton birds da flowers akai. “Come here” ya buk’ace ta, ba gardama taje ta zauna gefensa, akan cinyansa ya azata sannan yaciro lotion nata ya soma shafa mata sam bata hanasa ba bayan da yagama takallesa cike da so da k’auna tana murmushi sannan tace, “thank you Habeebi.”
“Its my job Flower in tayaki sa kayan?”
“A’a karka damu” a hankali tasa kayan daya cire mata wanda tsayin yamata daidai tsakiyar cinya. “Toh Habeebi ba leggings da zan sa taciki?”
“Babu I missed your sexy legs so yau inason inta kallonsu.”
“LOL” ta murmusa “baraka kasheni da kayan dariya ba Habeebi toh muje muci abincin” tayi maganan tana bin jikinta da turare bayan tagama ya rik’o hannunta suka fice daidai gaban d’akin babynsu ta tsaya hakan yasa Anas tambayarta ko lafiya.
“Flower wani abu ne?”
“Habeebi kawai na tuna da babynmu ne, I miss him/her” ta k’are maganar tare da aza hannunta kan cikin nata. Ganin zata fara masa kuka yayi sauri yayi hugging nata yana bubbuga bayanta. “Is okay Flower Allah ze kawo mana wasu in shaa Allah bar kuka kinji?” Hannayenta ta zagaye a bayansa a hankali tana gyad’a kai “I pray so Habeebi.” Sun d’au minti biyu suna manne da juna sannan Anas ya raba jikinsa da nata “muje muci abincin ko? Se kisha meds naki”
“Yes amman inason inshiga d’akin first.”
“A’a Flower banason kiyi kuka kuma nasan definately kika shiga zakiyi.”
“Please Habeebi” badan yanaso ba yabud’e masu k’ofan suka shiga. Daidai gaban babban gadon ta tsaya tare da sunkuyawa ta ciro d’aya daga cikin cute pink teddy bears d’in tana murmusawa, hawaye kawai tasoma zubarwa, kafin tasa hannu ta share Anas ya riga ya ganta.
“Flower kinga shiyasa nace banason kishigo.”
“Habeebi ka tuna lokacin da nace mu sayi blue ones kace a’a pink kafiso saboda jikinka na baka mace zamu haifa? Kasan wani name ya fad’o min alokacin?”
“No Flower tell me” ya juyo da ita gabansa tare da kwantar da kanta a chest nasa yana shafa bayanta. Kanta ta d’ago tana kallonsa *“HANAN* Habeebi. Kasancewar kanason baby girl nima na soma ji ajikina mace zan haifa and *HANAN* zanso muna kiranta dashi amman not anymore Habeebi...” sekuma ta rushe da kuka. Face nata yayi cupping yana share mata hawayen “kibar kuka kinji sweetheart? We will have another baby and many more kuma aduk lokacinda muka samu baby girl I promise you ke da kanki zakiyi naming nata *HANAN* kinji? Bar kuka.” Kai ta gyad’a a hankali tare da hugging nasa gagam a jikinta.
“I love you Habeebi, I love you so much.”
“I love you too Flower muje muci abinci.” Teddyn ya amsa ya ajiye sannan ya jata har a yanzu bata bar kukan ba, shida kansa yake bata abincin har ta k’oshi sannan ya b’allo mata meds nata ya bata bayan sun idar da Sallah suka fita waje garden dan shaqatawa kan wani dogon kujera suka zauna ya kwantar da ita ajikinsa me bala’in sata mance da dukkannin damuwanta.
Hannu yasa cikin ¾ wandonsa yaciro wani heart-shaped pack tare da miqa mata. “Habeebi meh wannan?”
“Its yours bud’e kiga.” Excitedly ta amsa ta bud’e had’ad’d’en silver bracelet taga aciki meh chain d’an dogo seda toliyar heart a k’arshen wanda yake nan d’an babba. “Wowww its a beauty!” tayi exclaiming.
“Do you like it?”
“I love it Habeebi.” Hannu yasa ya ciro daga pack d’in tare da d’ago siririn hannunta ya sa mata chas ya zauna. “Just as I imagined it” ya fad’a tare da kissing hannun nata.
“Tsaya kiga wani abu.” Toliyan heart d’in ya bud’e mata _“FAHNAS”_ taga rubuce ciki in italics. “Habeebi this is way beautiful” fuskarsa ta riqo tayi pressing masa appreciating kiss daya kashe masa jiki lokaci guda, koda ta gwada sakesa kuwa holding lips natan yayi ya cigaba da kissing nata seda suka ji kansu problem free sannan ya saketa, murmushi ta sakar masa “I love you my sugar lips.” Murmushin shima ya miyar mata “sugar lips?” Yayi maganar da gira d’aya a d’age “ofcourse Habeebi I missed your lips and your body” kafin ya hankara ta sake pressing masa another hot kiss, se kissing juna suke passionately and hungrily tamkar yau suka fara tasting juna****
_some minutes afterwards..._
“I love you Flower.” yace da ita yana shafa dogon sumarta. Sake shigewa jikinsa tayi;
“And I love you too Habeebi like bohot bohot!” ta sakar masa da best smile nata me mugun amsar ta dakuma birkita wa Anas lisafi.
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[12:59, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
8⃣7⃣
“Yauwa Habeebi nace ya labarin Moosa ne? Har yanzu shiru ba’a samesa ba?” yatsunsu yayi interwining;
“D’azu munyi magana da police sunce suna kan investigating har yanzu, kinsan Farouq shege ne Allah kad’ai yasan inda yakaisa.”
“Allah sa a samesa a raye Habeebi nasan danni Ya Farouq ya masa duka haka saboda yak’i shigo dashi ciki.”
“You are right Flower in shaa Allah zamu sam-” besamu daman k’arisa maganan ba sakamakon ringing da wayar sa yasoma ganin number’n Inspector General yayi saurin d’agawa.
“Hello Inspector.”
“Yes Mr. Fauzi I will like to congratulate you.”
“Yes... About what Sir?” Yayi maganar cike da neman k’arin bayani.
“Mun samu Moosa your driver achan Mongunu wai gidan Bad Boy achan Farouq ya kaisa ya b’oyesa.”
“Alhamdulillah, Alhamdulillah this is indeed a great news.”
“It is kuma shima Bad Boy d’in yana a hannu yanzu according to record babban drug dealer ne partner in crime na Farouq kuma dan da miliyan biyar nasa akayi bailing Farouq a prison 2 weeks ago.”
“Okay... Thank you Sir ina Moosan yake yanzu?”
“An kaishi asibiti dan duba lafiyarsa I guarantee you ba abinda suka masa.”
“Ina godia Sir zamuyi magana anjima.” Nan ya katse wayar tare da juyo da kallonsa kan Fannah dake kallonsa fuskarta d’auke da tambaya. Kafin tayi magana ya aza yatsansa kan lips nata “nasan me kikeson tambaya, an samu Moosa? Ko ba haka ba?”
“LOL eh haka please an samesa?”
“Yes sweetheart an sami Moosa yana asibiti yanzu as we speak yakamata inje in duba sa, I will be right back.” peck ya manna mata a goshi kafin ya miqe ta riqo shirt nasa. “Habeebi nima zanje.”
“Zakije ina?” ya tambayeta disbelievingly.
“Asibitin mana nima in duba sa kasan fa nice sila.” Kai ya kad’a mata “inaaa! you are going nowhere ko kin manta kema yau aka sallamoki? Bafa kida lafiya ki zauna ki huta barin d’au lokaci ba zan dawo kinji Flower?”
“O’o” ta shakwab’e fuska.
“Flower please kiyi hak’uri ki zauna zan isar masa da saqon gaisuwanki bareyi ki bini ba.” Badan tana so ba ta gyad’a kai wearing a sad face.
“Flower ba goodluck kiss?”
“Eh babu” ta fad’a ba tare da ta kallesa ba.
“Oh common! Flower.” Alokaci d’aya ta d’ago fuskarta tana mai murmushi “Habeebi na gabad’aya ze fita barin basa goodluck kiss ba? Impossible!” a hankali ta had’a musu lips tare da kissing nasa a passionately. “Off you go take care okay?”
“I will and you too Flower, in shiga dake ciki ko zaki iya?”
“Don’t bother zan iya I love you”
“I love you too Flower.” har ya soma tafiya ta tsayar dashi “wait wait tsaya in d’aukemu selfie so I can be starring at my husband’s handsome face kafin ka dawo.” Murmushin jin dad’i ya saki tare da dawowa baya ta d’aukesu sannan ya fice, anan yashiga ya fito da key’nsa ya fice itama bada jimawa ba tashiga ciki.
*****_3:10PM_
Daidai nan Anas ya dawo gida rashin ganinta a parlour ya tabbatar masa a d’aki take aiko yana shiga d’akinsu ya sameta zaune kan dressing mirror se sosa cikin gashinta take da comb tsantsan k’aik’ayi.
“Flower” ya kira sunanta anan ne tasan da shigowarsa ta juyo tana kallonsa cike da so da k’auna “sannu dazuwa Habeebi.”
“Thank you, me kikeyi haka?”
“Wallahi kaina k’aik’ayi na kwana biyu ban wanke ba, ya jikin Moosa’n?”
“He is okay alhamdulillah.” Yayi maganan yana dosowa gabanta.
“Toh masha Allah, aha! Mami ma ta kira tana gaisheka” tacigaba da sosa cikin gashintan.
“Ina amsawa” yace tare da karb’e comb d’in daga hannunta. “Habeebi bani please k’aik’ayi” ajiyewa yayi kan mirron tare da rik’o hannunta “muje in wanke miki kan Flower.” Dariya sosai ta tsaya yi wanda sakamakon haka Anas ya tsaya kallonta yana admiring nata, dariyan sa na mugun kashesa.
“Habeebi baraka isheni da kayan dariya ba, yaushe kazamo hair dresser da zaka wanke min kai?”
“Aww bakisani ba Flower? I can be anything fo you, Dr, hair dresser, cooku, servant komi da komi ma, muje.”
“A’a please kabari.”
“Flower banason dogon surutu” hannunta ya sake ya shiga cikin wardrobe ya ciro mata vest tare da miqa mata “sa muje in wanke miki” anan shima ya rage kayan jikinsa ya ragar da singlet se ¾ wando zallah.
Ba musu ta cire T- shirt d’in tasa vest daya kawo mata acikin jacuzzi ta zauna ya karkato da kanta direction guda. “Welcome to FAHNAS beauty salon how can I help you Mrs. Fauzi?” Dariya sosai take “thank you, wash and set nakeso.”
“You are at our service.” Daga farko seda yayi combing dogon sumanta sannan ya wanke thoroughly da ruwa sekuma da shampoo, a hankali yake mata massaging kan wanda ke mata dad’i sosai cikin d’ank’ank’anin lokaci ta nemi k’aik’ayin ta rasa. Bayan daya gama wanke mata ya d’aure mata kan da towel sannan ya miqa mata babban towel ta nannad’e jikinta dashi. Gaban dressing mirror ya ajiyeta ya ciro hand drier ya kunna sannan yasoma drying mata gashin bayan ya gama ya mata oiling sannan yayi mata packing gu d’aya harda style na donurt.
“Wow! Habeebi you are amazing!” tayi maganan tana duban kanta cikin mirron. “Wai nikam ya akayi ka iya komai neh?”
“LOL!” yasoma feeling. “Kin manta inada sister ne?”
“Thank you so much for making my hair.”
“Always Flower.” Yayi maganar yana mata murmushi miqewa tayi tare da pecking nasa a both kunatunsa, sekuma tip na hancinsa kafin ta kai kan lips nasa ya dakatar da ita. “Uhn-uhn Flower I know where this is going.” Murmushi cike da kunya ta saki “then let it happen.”
“A’a Flower kin tuna meh Dr. Yace? Cemana yayi kina buk’atan atleast 3 months na hutu before you can get pregnant again.”
“Toh ai hutun d’aukan ciki yake nufi bawai totally mubar yin...” Sekuma tayi shiru “ai ka gane me nake nufi.” light red lips nasa yayi pouting “ban gane ba” yayi maganar da gira d’aya a d’age. Bugi cike da shakwab’a takai masa a hannu “wallahi qarya kake ka gane.”
Dariya yake sosai “toh naji na gane but even still Flower muyi hak’uri.”
“Toh baby ba semuyi using protection ba.” Kai ya girgiza mata “I don’t trust in that, saboda sometimes suna bursting kuma kinga zaki iya samun ciki if that happens which is very harmful to your condition” ya tab’a tip na hancinta. Baki ta murgud’a masa “ina ni kayi rejecting yau Mr. Fauzi nima sena rama.” Hannayenta ya gwada rik’ewa da wuri ta fisge ita a dole tayi zuciya. Daidai zata juya masa baya kenan ya zagaye hannayensa a waist na tare da pulling nata closer to him. “Haba Mrs. Fauzi matar Anas, the mother to my awesome kids in shaa Allah. Taya zanyi rejecting the perfect woman I’m lucky to call my wife? Kema kinsan hakan k’arya ne, Flower ni kaina ina missing naki like hell I miss us on bed amman kinga lafiyarki ya fiye min komai, koda na shekara da shekaru akace inyi avoiding naki zanyi inhar hakan ne ze sama miki lafiya balle ma na d’an months, bawai nayi rejecting naki bane understand kinji? I’m sorry my sugar lips”
Kafad’a ta buga uwar zuciyar har yanzu bata sauk’o ba. “Flower meh kikeso in miki ki hak’ura?”
“Muje mu kwanta.”
“Zamu kwanta amman ba abinda ze shiga tsakaninmu its a deal.”
“O’o toh na fasa hak’uran.”
“Sena sauk’a akan knees d’ina zakiyi?” Ganin yasoma sauk’a tayi sauri ta hanasa. “A’a please baby don’t na hak’ura but can I kiss you atleast Mr. Fauzi?” Murmushi yamata “ofcourse Mrs. Fauzi” sannan yayi owning lips nata da kansa yasoma kissing nata.***
****
Tun daga ranan rayuwan masoya biyu ya cigaba da kasancewa kamar yadda ya saba da a baya ko inche fiye dana da ma, ba fad’a kullum cikin farintawa juna rai suke, ga uban lovely suprises da Anas yake cikin bawa Flowersa a kullum. A kullum wutan soyayyan junansu dad’a ruruwa ya ke a birnin zuqatansu.
★★★★
_6 months later..._
_Monday, 6:20AM_
Tsaye Fannah ke a kitchen da shiganta kusan minti uku kenan yanzu amman takasa tsinana komi ciki dan wani irin zazzab’in da takeji wanda ya fara mata tun jiya da daddare amman sam tak’i nuna wa Anas saboda batasan sasa cikin damuwa ‘cause ta lura aduk lokacinda batada lafiya Anas yafita damuwa. Tsugune take gefen sink takasa koda miqewa, tafi minti biyar ahaka sannan da k’yar ta miqe sanadiyar amai da yazo mata, cikin sink d’in ta riga kwararo amai wane zata harar da hanjinta seda tayi emptying cikinta kap sannan ta wanko bakinta, wane k’adangare tabi jikin bango har izuwa d’akinsu.
A kasalance ta miqe agefen Anas dake ta bacci hankali a kwance.
“Habeebi” ta kira sunansa ko motsawa beyi ba se a karo na uku yayi groaning “uhmmm Flower.”
“Habeebi ka tashi kaji? Yau Monday akwai office.” A hankali ya bud’e idanunsa kallo d’aya yama Fannah yagano batada lafiya she is looking so pale. Cike da tashin hankali ya shafa fuskarta “Flower are you okay?” Kai ta girgiza masa “Habeebi I’m sick ko breakfast na kasa had’a maka, I’m sorry.”
“Subhanallah, shhhh! Haqurin me kike bani?” body tempreture’nta ya tab’a yaji ya hau sosai yayi zafi. “Omg! Flower kinji tempreture naki kuwa? Ya kikeji?”
“Zazzab’i Habeebi sau biyu nake amai yau ko miyau ban iya had’iye.”
“Omg! Flower mesa baki fad’amin ba?” I’m sorry kinji?” Kai kawai ta girgiza masa dan batajin ma zata iya magana.
“Arghhh!” Ta saki wani irin k’ara hannunta rik’e da gefen cikinta, cike da tashin hankali yakai yana dubanta “Flower wani abu ne?”
“Habeebi ciki na tanan, wayyo!”
“Sannu Flower ina zuwa” bayi ya fad’a a gurguje yayi wanka sannan ya had’o mata black tea tare da b’allo mata meds. Duk’unk’une cikin bargo ya tarar da ita “Flower tashi ki zauna kisha magani kinji?” Da k’yar ya miqar da ita tare da jinginata jikin gadon, magunan ya miqa mata sam tak’i karb’a.
“Flower kiyi hak’uri kisha if not baraki