Showing 249001 words to 252000 words out of 268365 words
Chapter 84 - Tana Tare da ni complete book document .txt
ciki sunada taurin kai.” pecking nata yayi a goshi wanda tuni ta tunkud’esa, killer smile nasa ya kashe mata “Shettima! Shettima!” Yau hau k’wala masa kira. Daidai nan Ummie da Abuu suke fitowa har Amal taje ta sanar dasu dawowan su Anas dawata mata me kama da ita da Anas harma da Shettima kad’an kad’an.
“Oyoyo! Mutanen New York ne a gidan namu, maraba lale!” cewar Ummie alokacin data ga Fannah, hugging nata tayi ahankali gudun karta jimata ciwo anan sukayi exchanging greetings. Ummimi dake a parlour ba abinda take se kallonsu hawaye na bin k’uncinta.
“Me kuke tsaye anan?” Abuu ya tambayesu.
“Uhm ruwa nazo d’aukawa Anas” Fannah tamai qarya “gashi Anas” murmushi ya saki sannan ya karb’a.
“Toh mu k’arasa parl-” be samu daman k’arisa maganan ba kasancewan ido hud’u da sukayi da Ummimi kwata kwata ya kasa amincewa da abinda idanunsa ke gane masa cewa ma yayi ko imagination nasa ne kawai, Ummie ma was at shock alokacin data ga Ummimi she couldn’t believe it either.
Cike da rashin yarda Abuu ya juyo yana kallon Anas fuskarsa d’auke da son k’arin bayani har b’ari bakinsa ke. “A.. An.. Annas wac..wacce wancan?” yana nuna Ummimi da yatsa, shida Ummie suka kasa kunne suna jiran amsar sa. Daidai nan Amal ta falfalo da gudu, Shettima na biye da ita yana huci sanadin d’aukar masa cookies dayayi niyyan kaiwa Afrah da tayi.
“Ai wallahi yau se jikinki yayi tsami, sa’an kine ni da zan ajiye abu ki d’auka har kichi?!”” Yayi maganar se binta yake a yayinda take ta gudu tana kiran sunan Anas “Ya Anas! Ya Anas! Shettima ze min duka.” Suna isowa dining area’n duka suka sa full stop tuni Amal tayi bayan Anas. Ganin Abuu Shettima ya dakata kaman ance ka juya ya juya idanunsa se akan crying Ummimi. Idanunsa ya zaro sosai kamar ze ciresu sam shima ya kasa yarda da abinda idanun nasa ke gane masa. “Abuu wace wancan?” Abinda ya iya tambaya kenan.
“Ya Anas meke faruwa haka? Ya naga su Abuu sunyi shiru.” Amal ta tambaya.
“Anas magana nake maka wacece wancan?” cewar Abuu.
“Abuu Nima bansanta ba Flower keda kika kawo ta seki musu bayani” anan duk suka maido da kallonsu kan Fannah suna jiran amsarta seda ta kalli Ummimi sannan ta kallesu bakinta ya bud’u “Abuu wancan Ummimi ce, Ummimin ku.”
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[13:00, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
9⃣4⃣
“Um... Waye?!”Abuu yayi maganar cike da k’in yardan abinda Fannah tace.
“Eh Abuu Ummimi ce” ta sake tabbatar masa, juyawa yayi ya miyar da kallonsa a gareta “Aysha?” Yayi questioning nata hawaye ne ke ambaliya kan fuskarta “nn..na’am Ya Ibraheem”
“Ummimi?” Cewar Shettima disebelievingly.
“Na’am Shettima.”
“Noo this can’t be wannan ba Aysha bace ko Nafeesa?” Abuu yayi maganar har yanzu be yarda ba.
“Ya Ibraheem ka kwantar da hankalinka please ba shakka zahiri wannan Aysha ce.”
“Meta kemin a gida? kice mata ta tashi tabar min gida tun kafin nakira mata securities banida wani alaqa da ita” yana kaiwa nan yayi ciki. “Ya Ibraheem ka tsaya please” Ummie tabi bayansa. Wani erin matsanancin kuka Ummimi ketayi abin tausayi ayayinda su Shettima suke kallonta kamar TV har a yanzu yakasa motsawa dan yadda mamaki ya ziyarce sa gabad’aya ashe dama ze sake sa mahaifiyarsa a ido?
“Ya Anas wace ita? Dagaske kake she is a bad person shiyasa Abuu yace tafita mana daga gida?”
“Yes Angel mushiga ciki in ta tafi se mu fito” Fannah ce ta dakatar dasu.
“Anas baka gani is about time Amal tasan gaskia itama?”
“Flower don’t you ever tell her a thing about it, am not asking you am ordering you banason kifad’a mata wani abu I hope am clear” yana kaiwa nan suka fice.
“Shettima” Fannah ta kira sunansa a nitse. “Shettima nasanka kai kam I know baraka yi shunning Ummimi ba dan Allah ka mata magana kama mahaifiyarka magana” kai kawai ya girgiza sannan shima ya koma d’akinsa. Wajenta Fannah ta nufa tana bubbuga bayanta tana bata hak’uri tana me tabbatar mata da cewa evrything will be okay.
****
A d’akin Abuu. Zaune yake a bakin gado ya had’a uwa uba tagumi yayi shiru ko kad’an yakasa comprehending abinda ke faruwa gani yake wane a mafarki wai Aysha ce ta dawo matar da har a ayau yakasa son wata mace bayan ita, matar da har a yau yakasa maye gurbin ta da wata, Aysha his first and last love, toh me tazo yi? Ina mijinta dakuma ‘ya‘yanta? shekara goma shabiyar dole ace ta haihu.
“Ya Ibraheem bekamata ba kace ta fita maka daga gida nasan yadda abin yake da ciwo da zafi amman hak’uri yazama dole, dole kayi hak’uri kaje kaji dame ta taho meya kawota? Dakuma me takeso”
“No Nafeesa kije ki sameta kice mata ta fita min daga gida, banason sake ganin fuskarta.”
“A’a Ya Ibraheem nasan you don’t mean what you said, Aysha cefah matarka daka fiso fiye da komai, cool down kaje ka sameta muji dame take tafe please.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin Shettima inda ta samesa miqe kan gado yayi jugum se hawaye yake zubarwa.
“Ahhhh namiji dakai kake wannan hawaye Shettima gaskia ka badani yanzu in Afrah taganka haka me makeso tace? Saurayinta rago ne saboda yaga mahaifiyarsa yake wannan kuka?” Tashi yayi a lokaci d’aya yayi hugging Ummie gagam yana fad’in “kece mahaifiyata Ummie, ke kika raineni ke nasani ba itaba, she gave birth to me but you played the role as my mother, ta tafi ta barmu alokacin da muke tsantsan buqatar ta kece mahaifiyata ba itaba Ummie.” Bayansa ta hau bubbugawa a hankali “shhh! is okay Shettima inhar kamar yadda kace nice mahaifiyarka inaso kamin wannan abu guda d’aya yau kaje ka zauna a parlour ka jirani, kamata yayi kabawa Ummimi chance ko explaining kanta ne tayi muji menene amfanin dawowanta kaji son?”
“Noo Ummie I don’t want to banason sake ganinta, Ummimi bata sonmu bata tab’a sonmu ba ta tafi kawai.”
Breaking hug d’in tayi ta riqo fuskarsa “banason suratan banza kaji ko? Man up! Haba na Afrah ba haka fa na sanka ba tashi kaje parlour kajirani kaji? Don’t say no tashi! Tashi! ina ganinka” ba gardama ya share hawayensa sannan yafice izuwa parlon inda ya tarar da Ummimi se kuka take da Fannah a agefenta ba tare da yace dasu komai ba yanemi waje ya zauna.
****
“Anas ka bud’en k’ofan nan kaji koh?” Ummie tayi maganar tana buga k’ofan d’akin Anas dayasa lock ya rufesu da Amal ciki.
“Amal tashi ki bud’e.” Ido yamata nufin karta tashi aiko ta maqe tayi shiru.
“Anas wai baraka bud’e ba? Sa’arka ceni nace ka bud’e!”
“Toh Ummie ki fad’i me kikeso inhar maganan Ummimi zaki mana save it bamuwa so.”
“Anas abinda kake be dace ba ka bud’en please.” Badan yana so ba ya tashi ya bud’e tashigo. A kan gado a gefen Amal dake kusa da Anas ta zauna tare da riqo hannayen Amal cikin nata tana mirzawa a hankali.
“Amal d’ita.”
“Na’am Ummie.” Kafin Ummie ta sake magana Anas ya dakatar da ita “Ummie please don’t tell her karki fad’a mata komai banason wannan yazamo silan lalacewar rayuwar Amal I can’t afford it.”
“Ya Anas meke faruwa ne please ku sanar dani, meneh Ummie?”
“Amal sweetie kinga matan data shigon nan ko wacce Abuu yakira da Aysha?”
“Eh naganta.”
“Ummie please don’t” Anas yayi pleading.
“Bakiga kuna kama da ita ba? Dukanku da Ya Anas naki harma da Shettima?”
“Nagani Ummie wacece ita?”
“Ummiminku ce.”
“Ummimin mu? Meaning?” Juyo da ita Anas yayi “listen to me carefully kinji Angel?” Kai ta gyad’a.
“Good kinga Ummie nan ko?” Nan ma ta gyad’a kai “who is she to you?”
“My mother mana Ya Anas, she is all our mother, Ummie mamanmu ne dukan mu koba hakaba Ummie?” Shiru Ummie tayi takasa amsa Amal tsantsan tausayi yau shekarun ta goma shabiyar amman ace batasan wace asalin mahaifiyarta ba, batasan ta ina zata fara mata bayani ba. Kanta ya karkato zuwa direction nasa.
“I’m sorry Amal.” abinda ta iya cewa kenan.
“Ummie ba mahaifiyarmu bace Angel, ba ita ta haifemu ba she just played the role as our mother amman ba ita bace asalin mahaifiyar mu Ummie is our foster mother Ummimi wanda Abuu yakira da Aysha a while ago itace mahaifiyarmu ita ta haifemu kingane?” Hawaye tasoma zubarwa alokaci d’aya sam k’wak’walwarta yakasa comprehending abinda ke faruwa kamar ya Ummie ba mahaifiyar ta bace.
“Ya Anas bangane ba, bangane me kake nufi ba? Taya zakace Ummie ba mahaifiyata bace, ba mahaifiyarmu bace duka? Taya zakace wancan matan datazo wanda ban tab’a ganinta ba se yau itace mahaifiyata? Why Ya Anas?” Hannu yasa ya share mata hawayen.
“Angel banason ganinki kina kuka.”
“Then tell me you are not telling the truth” cike da tashin hankali ta juyo tayi hugging Ummie. “Ummie you are my real mother right? Kece mahaifiyata bawata daban ba Ummie you are my mother please say yes, Ya Anas be gane bane you are my mother and no one else” itama Ummien kuka take sosai na sosai da k’yar ta d’aga Amal daga jikinta tasa hannu ta share mata hawayen.
“Amal I’m so sorry kinji? Ban tab’a sanar dake gaskiya ba, na tauye miki hak’k’inki na sanin asalin mahaifiyarki amman kisani nayi hakan ne for your sake, wanki Anas ne yahana a fad’a miki gaskia sabida yadda yakeson ki bayanson abinda ze lalata miki rayuwa, bani bace mahaifiyarki Amal Ummimi ce ta haifeki itace mamanki na asali.”
“Noo Ummie ni kece mahaifiyata and no one else kece ba ita ba she is a bad person banasonta ban santaba.” Ta rushe da kuka, hugging nata Anas yayi yana bubbuga bayanta har seda tayi shiru.
“Ya Anas inhar ba Ummie ce mahaifiyata ba then wacece ita? Mesa take zama damu kullum?”
“Ummie sister’n Abuu ne bakiji Abuu na kiranta Nafeesa ba? Asalin sunanta kenan but ana cemata Ummie shiyasa time da ta dawo zama damu tun kafin a haifeki muke kiranta Ummie, dalilin daya sa ta dawo zama damu kuwa shine sanadin barin mu da Ummimi tayi”
“Toh in haka ne mesa ban tab’a sanin Ummimi ce mahaifiyata ba? Inhar dagaske kai da Ummie kuke wancan matar itace mamanmu mesa bata zaune damu?”
“Kinason kisan dalilin Angel?” Ta gyad’a mai kai.
“Saboda batada imani Angel, bata da tausayi bata sonmu.”
“Anas don’t talk about your mother like that” Ummie ta katsesa “uwa uwa ce komin rashin dad’inta.”
“No Ummie kibari in sanar da ita dukkannin abinda Ummimi tayi mana sabida kar ta tausaya mata.”
“Anas I said no.”
“I’m sorry Ummie amman ya kamata Amal tasan abinda mahaifiyarta ta mata” nan ya cigaba “Amal Ummimi bata tab’a sonmu ba zaki iya tuna ciwon dake a hannu na wanda nace miki agarin ball aka jimin?” Nanma ta gyad’a kai. “Its a lie kinga matar dake parlourn, Ummimi ita tajimin ciwon, she left us for another man 15 years ago...” nan ya kwashe labarin komai yabata ba tare da yabar komi a baya ba.
Kuka sosai Amal take Ummie takwantar da ita a jikinta. “Ummie mena mata? Mesa ta tsaneni? Mesa bata bari naji d’uminta ba?”
“Shhh! is okay sweetheart ya isa kinji? Bar kukan haka, duk abinda ta miki she is still your mother-” katseta Amal tayi tare da d’agowa daga jikinta “No Ummie you are wrong Ummimi ba mahaifiyata bace, ita ta haifeni amman ke nasani as mahaifiyata saboda haka you are my mother right Ya Anas?”
“Yes Angel come here” nan ta matso jikinsa yayi hugging nata “is okay bar kuka kinji?”
“Ya Anas promise me Ummimi batazo dan tafiya dani bae, bana sonta kamar yadda tak’i ni tun ina baby, Ya Anas karka barta ta tafi dani please.”
“That will never happen Angel.”
“Anas ya isa please be kamata kasawa Amal tsanan mahaifiyar ta haka ba koda meh Ummimi tayi she is still your mother yanzu ku tashi muje mu sameta a parlour banason jin no ku tashi.”
****
A parlour. “Shettima, Shettima d’ana dan Allah kamin magana I’m sorry for what I did to you dan Allah kayi hak’uri.” Anan ta miqe ta nufo inda yake zaune ta dafe kafad’ansa, hannunsa yasa yacire nata shima yana hawaye “Shettima please kayi hak’uri.”
“Ummimi why? Mesa zaki dawo bayan mun mance dake? Why do you have to mess up our lives always? Why Ummimi?” Ya rushe da kuka tsugunawa tayi gabansa tare da hugging nasa sam be hanata ba sede beyi hugging nata back ba, yana kuka tanayi Fannah na kallonsu sun kusan minti biyu a haka sannan ya raba jikinsa daga nata. “Shettima wallahi ba’a son raina na tafi na barku ba I love you guys so much” ta yi maganan hannunta dafe akan fuskarsa tana shafawa a hankali. “Sharrin shaid’an ne ba komai ba Shettima dan Allah don’t stop me from being a mother to you kabani dama in biya wannan shekaru goma shabiyar da mukayi ba’a tare ba please this is all I ask nasan barin iya tambayan gafarar ka ba saboda ban cancanci hakan ba ni kawai kabani dama in zame maka mahaifiya again please Shettima.” Shiru yayi bece komai ba.
“Shettima kayi shiru” Fannah tayi maganar tana d’ago Ummimi daga k’asa. Daidai nan Abuu yafito idanunsa sun mugun kad’awa bayanshi Ummie ne da Amal sekuma Anas. Bayan sun zazzauna Abuu yayi gyaran murya; “Aysha meke tafe dake? Me kika zo yimin a gida? Ko ban tambaya ba nasan sharri ne tattare dake saboda haka in kinayi wa Allah kitashi kifita min daga gida, nida yarana bamu k’aunan ganinki, bak’in cikin da kika bamu da abaya kad’ai ya ishemu basekin k’ara mana.”
“Ya Ibraheem please ya isa kayi hak’uri” cewar Ummie. “Amal taho nan” Abuu yakirata seda ta kalli Anas yabata nod tukuna taje tasamu Abuu, a gefe dashi ya zaunar da ita. “Zaki iya tuna wannan?” Ya tambayi Ummimi da tuni kuka yafi k’arfinta. “Zaki iya tuna ‘yar da kika k’yamata kika turo ta kamar shegiyar da batada uba acikin basket? Zaki iya tunawa?”
Har k’asa ta sauqa kan guiwanta tana roqan Abuu.
“Ya Ibraheem dan darajan ubangiji kayi hak’uri, kayi hak’uri dan Allah wallahi baroku danayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa na, d’an Adam ajizi ne we all make mistakes nasani kuskuren danayi babba ne wanda se me imani da tausayi ze iya yafemin, Ya Ibraheem wallahi nayi nadaman abinda na muku musamman ma abinda nayi ma Amal.” Nan ta dawo da kallonta kan Amal.
“Amal dan Allah kiyi hak’uri kiyafewa mahaifiyarki I’m so sorry Amal please forgive me, give me the chance to hold you in my arms Amal tunda na haifeki ko k’are miki kallo banba nasa aka nad’eki cikin tsumma aka turoki ban tab’a riqeki ba Amal wannan abu har a yau yana damuna barin tab’a samin sukuni ba a rayuwa na har se in na riqeki as mothers do dan Allah karki hanani please my Amal.”
Hannu Amal tasa ta share hawayenta sannan ta miyar da kallonta kan Abuu. “Abuu mena tab’a mata ta tsaneni haka? Mesa baka tab’a fad’amin inada wata mahaifiya ba bayan Ummie? ”
“Amal kiyi hak’uri kinji? Nasan mun miki laifi wanda yake babba na hanaki sanin asalin ki, kisani nayi hakan ne saboda ina sonki Amal banason ki tashi kina kewar mahaifiyarki, I’m sorry kinji? Bar kuka” yasa hannu ya share mata hawaye. “Angel zo abinki” Anas ya kirata ba gardama taje ta samesa. “Abuu nida Angel zamu d’an fita in kun gama abinda kukeyi call me se in d’au Fannah.”
“Anas dan Allah karka tafi kabari in nemi gafarar Amal please.”
“Amal zaki iya yafe mata tauye miki hak’k’in datayi? Zaki iya yafe mata wulak’antaki da tayi since you were a baby?” Kafin Amal ta amsa yacigaba “no that the answer daga