Showing 255001 words to 258000 words out of 268365 words

Chapter 86 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

44750

yayi da kallo yana cizen lips nasa, d’akinsa takoma haka tak’i binsu Sallah ita kad’anta tayi nata bayan nan suka soma jin yunwa sarai zata iya musu girki tace barata iya ba Amal ‘yar gata kam dama ba abinda ta iya yi koda Anas yace ze musu girkin Fannah ta b’ullo da dabara tace ita yau tuwo takeson chi tasan sarai ba iyawa yayi ba.
“Flower tuwo kuma yau?”
“Eh tuwo nakeso.”
“Toh Mom Hanan Amal jeki d’au mayafinki muje musiyo mata.”
“A’a Amal is staying with me akwai aikin danakeson ta tayani bayan tafiyan mu cleaners d’in ba kullum suke zuwa aiki ba d’akina duk yayi k’ura zamuyi dusting.”
“Flower bakida lafiya kibari gobe sukazo se suyi.”
“Don’t worry ai bawani aiki bane zaki tayani koh Amal?”
“Why not Ya Fannah.”
“Good muna jiranka kefa barakichi tuwon ba asiyo dake?”
“A’a banachi banaso.”
“Ya muku kyau keda wannan yayan naki wato bakiya chin tuwo kema? Seku nemi abinda zakuchi nide aje asiyo min tuwo da miyan yakuwa I’m hungry.”
“Toh Mom Hanan” yayi maganan tare da rufe gab dake tsakaninsu daidai zeyi pecking goshinta kenan taja baya sakamakon haka Amal ta k’yalk’yale da dariya “wai! Wai! Su Ya Anas ansha boncy, an kwashi shoki” itama Fannar bata san lokacinda ta qyalqyale da dariya ba. “Wato ni kikayi shunning a idan Amal ko Flower?”
“Ni kaje ka siyo min abinci abeg yunwa nakeji.”
“Kin kyauta kekuma Amal ina dariya kikemin nafasa bada iphone 7 d’in ma Shettima zan bada.”
“A’a Ya Anas please I’m sorry”***


Bayan tafiyan Anas Amal ta d’auko bucket da towel dan fara goge-gogen da Fannah tace zasuyi sede ta tarar da Fannah zaune a parlour. “Ya Fannah kince akwai goge-gogen da zamuyi.”
“Wasa nake babu zo nan ki zauna” tayi mata nuni da space dake gefenta “zamuyi wata magana” ba gardama taje ta zauna. “Amal ke ba yarinya bace yanzu you are 15 years old kinsan whats right and wrong koba haka ba?” Ta gyad’a kai “good” Fannah ta cigaba “inason ki saurari abinda nakeson fad’a miki da kunnen masu hankali ki ajiye duk wani abinda Ya Anas naki ya fad’a miki a gefe do you get me?”
“Yes Ya Fannah.”
“Mesa kika k’i ma Ummimi magana? Baki tausaya mata ne she lost 3 of her children, three fa Amal how does it feels ke lokacin da classmate naki nema yarasu ya kikaji balle ace ‘yan daka haifa har guda uku kana ji kana gani aka siyar dasu, just how bad does that feels?” shiru Amal tayi bata iya tace komai ba.
“Magana nake miki Amal.”
“It feels bad.”
“Good then meya kamata kiyi dan sata feeling better kuma?”
“Inyi condoling nata in bata hak’uri.”
“Exactly amman mesa bakiyi ba?”
“Ya Fannah ni kin manta abinda tamin ne danake baby? She hated me batare dana mata komai ba ko shayar dani batayi ba, to cut the crap har cewa tayi zata zubar da cikina kuma ga ciwon dataji ma Ya Anas nifa bana sonta.”

“Kai kai ya isa haka ya isa karki sake fad’in bakiya son Ummimi, kema Anas ya koya miki wannan banzan halin nasa ko? Ya cusa maki tsanan mahaifiyarki, waya gaya miki ana k’in uwa ne?”
“Ya Fannah nifa ba k’inta nayi ba ita ta k’ini, ita mesa baraki mata magana ba.”
“Ai na mata Amal we humans we are prone to make mistakes ko ke nan akwai mistakes da kikayi kuma akwai dayawan da zakiyi a gaba haka Allah ya hallice mu we aiint perfect amman kuma the best amongst us shine wanda yayi laifi yayi realising yakuma tuba kamar yadda Ummimi tayi kiga kukan data tayi mana d’azu akan yaran data haifa kinsan da zata bud’e baki ayau tace ta tsine muku gabad’aya bameyin albarka cikin ku kin sani?” Amal ta kad’a kai.
“Kinga shiyasa, Amal duk abinda zakiyi ma Ummimi aduniyan inma duniya zaki siya mata wallahi barekai kwatankwacin d’aukan cikin ki datayi ta reneshi har ta haifeki ba, kinsan azaban haihuwa kuwa? Ba zafin daya fishi se mutuwa fah shiyasa akace duk wacce ta mutu ta hanyan mutuwa ‘yar aljanna ce tayi mutuwan shahada, uwa uwa ce komin rashin dad’inta koda cikin shege tayi ta haifeku wallahi shima abu ne our mothers are priceless ba abinda zamu iya musu in return of abinda suka mana.”




*© MIEMIEBEE*


beeenovels.blogspot.co.ke
[13:00, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💞*


9⃣6⃣












“Toh ni yanzu me kikeso in mata Ya Fannah?”
“Kema ai kinsani Amal kidena biyewa Ya Anas kibata chance da take nema to hold you and be your mother bawai nace kiyafe mata bane amman kibata wannan chance da takeso dakanki zaki yafe mata in kikaji dad’inta ke bakison kisan mamanki ne?”
“Ai nasan Ummie.”
“Ummie ba itace mahaifiyarki ba Ummimi ce mahaifiyarki...” haka Fannah tariga ma Amal nasiha seda ta kashe mata jiki.
Dawowan Anas ya taho ma Fannah da tuwonta nan tasamu ta kora yunwa shikuma da Amal suka wuce kitchen dan dafa nasu kamar Anas yasani ya tambayi Amal ko Fannah tamata maganan Ummimi bayan fitansa, bata b’oye masa ba ta fad’a masa zahirin gaskia. “Ya Anas don’t you think is about time mu bawa Ummimi chance to be our mother? Wallahi wa’azin da Ya Fannah tamin ya mugun tsorata ni.”


“Ai dama nasani, nasan hakan ze faru kinaji na ba bawani chance da zakibawa Ummimi am I clear?” Baki na rawa tace “yy.. Yes.”


_Washegari..._
Da sassafe Ummimi ta tashi tayi wanka sannan ta rok’i Ummie data rakata kitchen dan nuna mata inda postions na plates da sauran utensils suke hakan kuwa akayi breakfast me rai da lafiya favorite na Abuu ta had’a wato doya me k’wai a jiki bayan tagama ta had’a kan dining. 8:30AM Abuu yafito daga d’akinsa cike da ladabi da biyayya ta sauk’a har k’asa ta gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa. “Ya Ibraheem ga breakfast chan na had’a maka dan Allah kar kace bara kaci ba kayi hak’uri please” kai ya gyad’a mata sannan yabita dining d’in taja masa kujera ya zauna sannan tasoma serving nasa tana bud’e flask d’in k’amshin girkinta wanda he can’t tell how he missed it ya buga masa hanci bayan tayi serving nasa ta had’a masa tea sannan ta koma gefe tana kallonsa a hankali yasoma chin abincin har ya k’are. “In k’ara maka ne?” Ya gyad’a mata kai dad’i sosai taji a ranta “ashe har a yanzu baka dena son doya me k’wai ba.”
“Mesa zan dena so bayan kin riga kin saba min dashi, kefa barakiyi breakfast d’inba?”
“Zanyi amman nafison duk ku karya tukuna, Shettima fah? Har yanzu yana kai goman safe kafin ya tashi kokuwa ya rage bacci?”
“Keda d’anki kuma kina iya zuwa kiduba d’akin sa ai shine first room by your right.”

“Toh nagode sosai Ya Ibraheem.” Seda yagama chi ta masa Allah kare ya fice office sannan ta dawo ta d’iba wa Shettima nasa a plate da tea nasa ta nufa d’akinsa a hankali tayi knocking. “Waye ne” ya tambaya. Da k’yar bakinta ya iya cewa “Ummimi ce Shettima.” Daga nan be sake cewa komai ba.
“Shettima yi hak’uri ka bud’en kaji? Yi hak’uri please.” Nanma shiru “Shettima barin bar nan ba har se in ka bud’en k’ofan nan.” Tafi minti goma tsaye a wajen sannan Shettima ya tashi ya bud’e mata ba tare da yace mata komai ba, bayansa tabi ta ajiye masa breakfast d’in akan centre table dake d’akin.
“Ina kwana Shettima?” Nanma be amsata ba gefensa ta nufa ta zauna kan gado. “Shettima barin iya forcing naka kayimin magana ba saboda na kasance me laifi amman kayi hak’uri ka tashi ka karya kaji Babana?”
“Ummimi why are you doing this?”
“Saboda inason ka Shettima, ina sonka fiye da yadda nakeson kaina.”
“Shine kika tafi kika barmu alokacin da muke buk’atanki?”
“Barin ku danayi shine babban kuskuren dana tafka kuwa Baba na shiyasa nakeson inyi making up for the last 15years da mukayi ba a tare ba, yi hak’uri ka karya kaji?” Hannunsa taja ta zaunar dashi sannan da kansa ta soma basa abincin yana karb’a har yagama chi. “Thank you so much Shettima na wannan dama da kabani Allah ya saka maka da alheri yakuma maka albarka.”
“Ameen” ya amsa. Daidai nan wayarsa yasoma ringing kasancewar wayar na kusa da Ummimi tasamu daman ganin wake kira ‘honey boo’ taga rubuce kan screen d’in. Da sauri ya d’aga wayar daga dubanta sede yakasa amsawa ganin Afrah ke kira, d’an murmushi ta saki “haka Baban nawa ya girma? D’aga wayar mana to ko se surikar tawa tayi zuciya ne?” Besan alokacinda ya murmusa ba.


“Ko kunyan Ummiminsa yake ne?”
“Ummimi fa ba budurwa ta bace.”
“Awww shine akayi saving lambarta da honey boo, d’aga mana kose ya tsinke ne.”
“Zan kirata anjima.”
“Toh wace ita? Wata lucky girl d’in ne ta sace min zuciyan one in town son d’ina?” Murmushi sosai Shettima ke “sunanta Afrah k’anwar Fannah.”
“Wow aiko ina da tabbacin itama tana da hankali kamar Fannah, Allah tabbatar mana da alkhairi yabar ku tare.”
“Ameen Ummimi”
“I will love to know you better Shettima”
“Don’t worry” yayi maganar yanasa shirt nasa.
“Toh Babana ya naga kamar kana shirin fita?”
“Eh makaranta zani inada lectures.”
“Oh okay me kakeso kaci da rana?”
“Babu ba sekin dafamin komai ba zan siya a school.”
“A’a mahaifiyarka na raye bara ka chi abincin waje ba fad’a min meh kakeso.”
“Ina irin macronin da kike dafa mana? Irinshi nakeso.”
“Toh angama son Allah kiyaye kaji? I love you.” So yake yace mata he loves her too amman kuma yakasa dan haka ya gyad’a mata kai zallah. Bayan tafiyan Shettima ta share masa d’aki tayi mopping tsatsaf haka d’akin Abuu ma sannan tasake yin sabon breakfast masu Anas tare da Ummie suka fita dankai musu sede Ummie tak’i shiga tabar Ummimi ita kad’ai, securities suna ganin Ummie suka bar Ummimi tashiga door bell ta danna alokacin Anas na aka kitchen shida Amal suna had’a musu breakfast ita ya tura da taje ta bud’e ganin Ummimi ce ta bud’e tare da gaisheta kamar yadda Fannah ta buk’ace ta. Dad’i sosai Ummimi taji “Amal my princess ya kike?”
“Lafiya.”
“In shigo?” Daidai nan Anas yafito “waye ne Angel?”
“Ummimi ce Ya Anas” apron d’in jikinsa yacire sannan ya k’ariso “ina kwana Anas” kamar wanda bare amsaba ya amsa “lafiya” tare da sake tare k’ofan dan kar ta samu daman shiga “wani abu ne?”
“Breakfast na kawo muku.”
“Ai da baki b’ata lokacinki ba we are making breakfast already zaki iya tafiya.”


Hannu tasa ta taresa daga rufe k’ofan “Anas please karka min haka dan Allah” tayi maganan hawaye na ciko mata a ido daidai nan Fannah tafito daga d’akin sanye take da kayan bacci iya guiwarta, ganin alaman baquwa bakin k’ofan yasa takoma ta sanya hijabi sannan tafito “Habeebi meke faruwa anan?”
“Ya Fannah Ummimi ce tazo.” Amal ta amsata.
“Shine baku shigo da ita ba?” tayi maganan alokacin datake tsaye gefen Anas. “Ummimi please kishigo” wani kallo ta watsa wa Anas sannan tashigo da Ummimi ciki anan suka gaisa.
“Waya miki kwatancen gidan namu?”
“Tare da Ummie muka taho tana waje tana kuma gaisheku duka, dama breakfast na kawo muku.”
“Allah sarki Ummimi da gajiya haka ai da baki wahalar da kanki haka ba, Anas d’an karb’i mana” yi yayi kaman be jita ba “Amal karb’i flask d’in kinji?” Ba gardama ta amsa takai kitchen hira kad’an suka tab’a wanda ciki ko uffan Anas be furta ba haka Amal ma kasancewar taga idon Anas daga k’arshe ma kitchen ya koma ya cigaba da abinda ke gabansa da Ummimi tazo tafiya takira Amal tare da miqa mata wasu hada’d’d’en porches na iphone 7s. “Gashi Habibti wannan naki ne naji Ya Anas ya siya miki iphone 7 koh?” Ta gyad’a kai “toh gashi bansani ba ko kinason maroon and red colour? best colorn Basmah da Barrah kenan I was thinking ko kema haka kinaso” amsa Amal tayi tana k’are musu kallo “sosai inason red and maroon colour Ummimi thank you.”
“Always Habibti” ta bud’e mata hannu da nufin hug ba gardama Amal taje tayi hugging nata wani erin yanayin da bata tab’a tsintan kanta ciki ba tayi yau, tunda take bata tab’a jin dad’in hug ba kamar na yau gaskiyan Fannah our mothers are priceless sunjima a haka se kallonsu Fannah ke cike da jin dad’i ina ma Anas zebawa Ummimi chance d’innan ta zame masa uwa kamar yadda take buqata. “Toh zan tafi seko gobe in dawo kinji?” Amal ta gyad’a kai.
“In na dawo gobe zaki bani labarin ki, kinga yanzu nasan favorite colors naki inason insan komai about you zaki min?” Shiru tayi chan ta gyad’a kai “thank you so much Amal Allah miki albarka yamuku albarka gabad’aya zan tafi” ahaka sukayi sallama. Dawowan Amal ta wuce kitchen “Ya Anas kalli porches da Ummimi ta kawo min na wayan daka sayamin amazing how tasan favorite colors d’ina koda shike tace favorite colors na step sisters namu Allah jik’an rai Barrah da Basmah ma kenan, Ya Anas Ummimi isn’t bad.”

“Mesa kika karb’a?”
“Ya Anas I’m sorry.”
“Bance karki mata magana ba?”
“Ya Anas she is our mother.”
“Naji zan karb’i iphone d’ina se muga aina zaki sa porche d’in.”
“Ya Anas I’m sorry.”***


★★★★
Haka nan tun daga ranan Ummimi tacigaba da musu girki, da sauran ayyukan gida dukda abinda Anas ke mata hakan be hanata ja da baya ba saboda tasan dalilin dayake hakan alokacin data tafi shine me wayon chan dole abin yafi affecting nasa, addu’arta a kullum baifin Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting nata as his mother ba, duk yadda yayi dan hana Amal alak’a da Ummimi yakasa as the saying goes ba a shiga tsakanin uwa da d’a, shak’uwa me k’arfi ne yashiga tsakanin Ummimi da Amal har fiye da nata da Shettima koda Amal takoma gida d’akin Ummimi ta tare, atare suke kwana da Ummimi, tamata tsifa tamata kitso har wanki haka ma Shettima tuni suka daidaita a tsakaninsu daman Abuu abinda yake jira kenan bayan ya tabbata everything is cool tsakanin Ummimi da yaranta ya dawo da ita d’akinta dad’i sosai Ummimi taji harda kukan murna her biggest dream is now a reality su Ummie da Fannah duk sunji dad’in wannan re union d’in har small party suka had’a inda Fannah tayi introducing Ummimi wa Maminta anan Ummimi taga Afrah in-law to be nata abinde se wanda yagani they turn out into a one big happy family banda Anas da duk wannan abubuwa da akeyi baima zuwa bale yaga kayan bak’in ciki har a yau bayajin ze iya yafewa Ummimi yariga ya dawo daga rakiyarta gabad’aya sede hakan be hana Ummimi fita daga harkansa ba ita ba.
Musamman Abuu ya kira Fannah yamata godiya in person in da badan ita ba yasani da bare sake had’uwa da Ayshan sa ba, dabadan Fannah ba da Amal won’t get the chance to see her mother again, da badan Fannah ba da Ummimi won’t get the chance to see her family ever again har ta nemi gafararsu dan haka yayi mata godiya sosai tare sanya mata albarka ba iyaka. Shak’uwa na haqiqa ne ya cigaba da shigewa tsakanin Fannah da Ummimi, yadda Ummimi tad’au Amal haka tad’au Fannah tamkar ‘yar data haifa saboda irin ladabi da biyayyan da Fannah ke mata itama sekace wa Mami.


Ummimi da Abuu dasu Shettima ne duk sukaje gidan iyayenta, alhamdulillah iyayen nata na nan da rai dakuma lafiya anan duk suka nemi gafarar Abuu akan abinda suka yi masa shekaru da dama da suka shud’e.
Tun daga wannan rana rayuwa tayi turing perfect ma wannan family kan Ummimi da Ummie a had’e sekace ba in laws ba sosai Ummie kebawa Ummimi girma bata kuma dena yiwa Anas wa’azi ba itama fatanta Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting Ummimi.
Cikin Fannah se girma yake masha Allah a yanzu haka cikin nata ya tsufa yanada 8 months da sati d’aya, sosai cikin nata yayi girma yazamo ko k’wararren motsi zatayi setayi dagaske, ga wani erin tsoron haihuwan datake cikin yi a kullum


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login