Showing 30001 words to 33000 words out of 145917 words
kafin tayi mgana ya mike yana fadin"Ki rike su a hannunki..Ni yau zan koma..!
Zaro ido Amina tayi kafin tace"Ina..?Madina..?
Kai tsaye yace mata"Eh tafiyar ma bata yuyu bane da Tuni na tafi..Jafar zai kawo miki waya zamu rika mgana ..!ina dai gargadinki kada ki Fadama kowa..!
Amina bata ma jinsa Tunaninta na kan yadda zata zauna ita kadai agidan nan gashi bata san ina gajeran matarsa taje ba tun ranar bai kara mganarta ba..kafin ya ankara Amina ta Fashe da kuka cikin mamaki yake kallonta kafin yace"Kukan me kike yi..?cikin kuka tace"Wlh bazan iya zama agidan nan ni kadai ba Tsoro nake ji ka maidani gida..!
Kai Tsaye yace"Nima naso hakan sai dai Hajiya da maallam bazasu bari ki koma ba..!
Amina na Jan majina tace"Gidammu zan koma bazasu sani ba..!
Dariya mganarta ta basa da sai ya Dara kafin yace"In jiwa..? ai da gidanku da gidan mallam Duka Dayane Dole zasu sani..Ki daina kuka zan kira Hajiya ko Hannatu sai tazo ta Zauna Dake kafin Sakina ta Dawo..!.
Jin sunan Hanne Daya ambata yasa ta bar kukan ta Dago tana kallonsa kafin tace"Da gaske..?
Kai ya gyada mata wani mikewa tayi kafin tace"Yauwa harda Hamida don Allah ya Danmallan kaji..?
Ashe tasan sunansa kallonta yayi kafin yace"Wato ku hadu ku fara rashin ji ko..?
Kin san dai yanzu ba da bane ko..?
Da Sauri Amina tace"eh wlh babu abunda zamu yi..!
Kai ya jinjina mata kafin yace"Shikenan sai su zo..!
Tsalle ta Daka tana Hawaye tana Dariya zafi taji a kasanta yasa ta Duke tana Wash wash Kallonta yayi kafin yace"Ki rika kula da kanki fa..Kina da Sauran Rauni..!
Bata Dago ba ta mikamai kudinsa tana Fadin"Babu abunda zan yi da kudi..!.
Shi kuma yace"Ki rike a hsnnunki. zaki koma makaranta Dis Coming monday ki rika yin kudin Break sannan in kina Bukaar wani abu in Sakina ta Dawo ita zaki rika tambaya kina jina ko..?
Kai ta gyadamai ammah aranta tace Tab wannan matar muguwa din.
Afili kuma cewa tayi"Allah ya kiyaye hanya..!
Ya amsa da Amen yana kallonta kanta ya Dafa kafin yace'Allah yayi miki albarka..Na tafi sai in kuma na Dawo..!
Sai kuma taji kamar kar ya tafi yana mata Kirki na kwana Biyu wayarsa ya Dauka anan wajen kayan kallo ya Fice ta rakasa da kallo sai da ya Dade da Fita sannan ta koma ta Zauna da kudi a Hannunta tayi Tagumi haka kurum taji kamar kar ya tafi sai dai kuma taji Dadin da su Hanne zasu zo Dadi ya isheta.!
Shi kuma yana Fita Tasha ya wuce Direct Allah ya taimakesa ya samu Motar kano ta kusa cika ita ya shiga kuma Motar nada Lafiya sun yi gudu kuma koda biyar tayi yana Filin Jirgin Aminu kano,bayan yayi sallah ne ya kunna wayarsa ya Kira Hajiya..
******
Hajiya na Cikin Bedroom dinta tana Duba littafin 40 Rabbana Hanne na Tsaye awajen Wardrope dinta tana gyara mata kayanta Jiya mai wanki da guga ya kawo wayar Hajiya Dake kan madubi ta fara kuka alamun kira Hanne tafi kusa da wayar yasa Hajiya tace ta miko mata.
Tana Dauko wayar tace"La Hajiya ya Danmaallam ke kiranki..!
Hajiya ta ijiye abunda ke hannunta kafin tace"To ya natsa kenan tunda ya kira..!
Bata Tsaya Duba lambar ba ta Daga Kiran Lokaci Daya tana amsamai Sallamarsa cikin Sanyinsa ya gaisheta ta amsa tana Fadin"Kun sauka lafiya..?Mallam nata kiran ka bai samu ba Nima har da Safe na gwada layinka nachan ban samu ba..!
Cikin Taushinsa yace"Hajiya ai ban tafi ba..Sai yau ne zamu tafi jirgimu zai tashi da karfe takwas na Dare. !
Hajiya ta Bude baki kafin ta Dago wayanta tana kallon Lamba sai Lokacin ta Lura lambarsa ta nan ne saboda ta chan Danmallam2 ta sakamai.
Cikin mamaki tace"Ikon Allah to meya faru ba wanda yaji labari don ko da Safe Jafar ya shigo nan nake tambayansa yace shima bai samu wayarka ba..!
Umar yace"Matsalan hazo ne Hajiya shiyasa tafiyar bata yuyuba aranar..!
Hajiya tace"To Allah yasan hakan shi yafi Zama alheri..!
Ya amsa mata da Ameen kafin yayi shuru itama jinsa shuru yasa bata yi mgana ba sai da taga bai da niyar mgana sannan tace"Danmallam lafiya kuwa..?ka kira kuma kayi shuru..?
Ya sosa kansa kafin yace"Hajiya ina Filin jirgi kanon tun dazu..!
Hajiya tace"Madallah Allah ya Tsare..ya wajen su Aminar ina Fatan Lafiya ko..?
Cikin Kasa da Murya yace"Suna lafiya Hajiya..Daman zence ne in ba Damuwa Hannatu da Hamida su tafi yanzu su je su zauna da ita gidan ba kowa..!
Hajiya tace"Bangane ba kowa ba Sakinar fa..?
Kai Tsaye yace"Bata nan Hajiya..!
Bata Damu da tace ina taje ba tace"Allah ya kyauta..To yammh tayi kuma mallam baya gida sannan Gobe jumma'a suna da makaranta Danmallam..
Kai Tsaye yace"Hajiya kiyi hakuri su bar makarantar ta gobe su je su kwanan mata Biyu..In sakina ta Dawo Shikenan sai su dawo gida..kinga tayi kankanta da Zama ita kadai.. sannan ita ma Ranar monday sai ta fara zuwa makarantar..!
Hajiya tace"Shikenan bari na Tura su yanzu Daman na bari ne sai Asabar sai su hakura da Haddar su je mata tunda kuma ga wannan laluran bari na nemi ko Uzairu ne ya kai su sabod maallam da idi ya fita..!
Danmmallam yace"Uzairu ya Dawo ne..?
Hajiya tace"Eh jiya ya Dawo..!
Kai Tsaye yace"Hajiya ki basu keys din gidanan su tafi dashi..!.
Hajiya bata da bin Diddigi kai Tsaye tace shikenan daganan sukayi sallama ta bisa da Fatan isa Lafiya..tana gama wayar Hanne data kasa kunni taji ta cikin jin Dadi tace'Hajiya wajen Amina zamu..?
Hajiya ta mike tana fadin"Eh da naso sai jibi ne ammh yace kuje yau sakinar bata nan..!.
Hanne ta Daka Tsalle tana Murna Hajiyw tace"Daman na gama Hadamata komai jiya ma kinsan a kawo Dinkunanta da mallam yayi mata Sabbi yanzu shiga gidan Sa"idu kice ma Balaraba zaku wajen Amina in tana sako ta bada..!
Ai da gudu Hanne ta fita Tana murna Hajiya kuma ta fara Hadaa Sabbin kayan da mallam ya Dinkama Amina kala goma da Hijabai sai ita kuma ta mata Turaran wuta da Humra sai Dambun nama dasu Samosa duk an yi package dinsu sai kamshin girki kala kala har da curry har da su Cake sannan ta Siya mata Sabbin panta da sikat da Vest.
Ba jimawa sai ga Hamida da Hanne kamar bakinsu zai Tsage saboda murna Hamida ta Dauko kayanta kala Biyu Hanne ta bama Hajiya Turaran Tsinke guda Daya a ledansa wai inji mamanmu akai ma Amina..
Hajiya mamaki ya kamata ko jiyan nan Sa"idu ya sake fadaa mata ya bama Balaraba kudi ta yi ma Amina siyayyan abun Bukata shiyasa ta aika mata ammh sai taga wannan abu haka..?
Abun ya bata mamaki ace wajen Amina fa za"aje koda Sa"idu bai ce ya bata kudi ba ta Dauka kayan da zata Hadama Amina sai yafi ma wanda ta Hadamata ammh sai bata saka kokonto aranta ba ta barshi a kila bata siyan mata bane tukunah sai Daga baya..!
Hajiya batace komai ba ta Hada Cikin kayan sannan ta Dauko musu keys din gidan ta basu sannan tace Hanne ta Diban ma Amina sinasir din da sukayi da Miya su kai mata jiki na rawa suka Diban mata a coolers suka saka miya Dabam sai murna suke yi Hajiya ta Jaddada musu ranar Lahadi idi zai Zo ya Daukesu sannan taja kunnensu da su natsu da sakon su gaida Amina..bata yi gaban kanta ba sai da ta kira mallam sukayi mgana da Farko cewa yayi"Hajiya yara nan su kadai agida kina ganin zai yuyu.?
Kodai Aminar ta dawo gida kawai har Sakinar ta dawo..!
Hajiya tace"Hakan ba mafita bace in mukace haka bazata saba da gidan auranta ba gwara ta zauna watan watarana zata saba..!
Da haka mallam ya yarda da Hujjanta yace su Hamidan su tafi da kanta ta Kira uzairu yazo ya kaisu da Daya daga Cikin motocin gidan Daman tun jiya daya Dawo key din motar ke hannunsa.
Har suka tafi Hajiya bata Daina mamakin Balaraba ita sai kawai taji abun yayi mata wani iri.
Sai da ta koma shashen nata ta ga Sinasir din datace su hanne su dibar ma Amina saboda sauri sun manta dashi kawai ta girgiza tana mirmishi suna ta zumudi dole su manta.
Ita kuwa mamanmu Rana Tsaka kawai hanne tazo tace Hajiya tace ta bada Sako zasu wajen Amina..
Ita har ga Allah mantawa ma take da wata Amina kudi kuma tabi ta kansu Shiyasa ta Dauko wannan Turaran Tsinke wanda mamata ma ta bata shi ya Dade bata taba amfani dashi ba tamikama hanne domin bata taba Zaton Sa"idu yayi zencen ya bata kudi da Hajiya ba. ganin suna ta Murna yasa batace komai ba gwara Hamidan taje ta gano wani irin Halin da Amina ke Ciki don ta tabbata Sakina bazata mata wasa ba ita fa a gayyas gida yanzu ya Rage daga ita sai mijinta Jawaad yanzu in Aba ya Dawo yadaina zuwa saboda samunsa tayi tajamai kunni yaro kuma da Tsoro ko Aba ya Dawo ko ya kirasa daya zo sai yace yana da Homework sai ya tafi hakan yafi ma Mamammu Duniyarta take so taci ita kadai bata san Takura.
*Janafty**TFZB2008*
*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*
Amina tana rakube a falo tsoro duk ya cikata tunda Danmallam ya fita take duban idon su hanne ammh har Dare ya fara shiga ana gabda kiran sallar mangariba bata gansu ba Tsoronta Allah kada Dare yayi basu zo ba bazata iya kwana ita kadai ba Tana jin tsoro.
Tana zaune kan kujera a rakube saman kujera tana fiki fiki da ido,kamar mara gaskiya ko kwakwaran motsi bata yarda tayi ba, saboda tsoro,Saboda yanayin Datake ciki yasa ko karan Bude get bata ji ba sai ihun kiran sunanta da Hanne da Hamida suke mata kamar daga sama haka taji tana kyalla ido kawai taga Hanne da Hamida da kaya niki niki a Hannunsu,bata san sadda ta Diro daga kan kujera ba duk da yanayin Datake ciki bai sa ta tsaya ba Cikin Farin ciki da murnan da Rabonta da tayi har ta manta ta fada Jikin Hanne Tana Fadin"Oyoyo..oyoyo..!
Haka take fada sai hawaye sharr kafin ta Saki hanne ta Rumgume Hamida tana Fadin"Nayi kewarku..Nayi kewarku ba adadi Hanne da Hamida..!
Ta fada tana sharan kwallah suma sai da kwallar ta kawo musu suka kara Rumgumeta suna fadin muma mun yi matukar kewarki Amina.
Hannunsu taja tana fadin su kariso mana Bakinta yaki Rufuwa Saboda Murna basu Tsaya a falo ba sai Dakin Data kan gadon suka yada Zango Hanne da Hamida suna ta bin Gidan da Dakin da kallo.
Amina Murna yasa ta rasa me zata basu kallonsu tayi tana fadin"Kuna jin yunwa.?
Ga Abincin chan da ya danmallan ya siyomin kafin ya tafi zaku ci na Dauko muku..?
Binta kawai suke da kallo har ta Fice sai gata ta Dawo da shi a Hannunta Hade da maltina,tana shigowa Hamida tace"Mufa mun koshi Sai dai anjima..!
Amina ta Dago tana fadin"Hanne kema bazaki ci ba..?
Hanne tace"Mun ci abinci agida..Sannan ni ba abincin siya zan ci ba girkin Amarya Amina zan ci..!
Hararanta Amina tayi kafin tace"ai sai ki ci abinci bayan matar gidan ta Kulle Kitchen dinta ta tafi bansan inda taje ba..!
Hamida ta zaro ido kafin tace"Bangane ba..?
Hanne ta karbe da cewa"Naji Hajiya na Fada ammh inaga ya Danmallam ya mata mgana ga keys din gidan gabadaya na wajen Hajiya tace nazo miki dashi..!
Amina ta tabe baki batayi mgana ba, Hamida da Hanne sai binta suke da kallon kurillah Amina sai ta Tsargu ta balla musu harara kafin tace"Wai kallon fa na miye..?
Hamida ta kalli Hanne suka Tsintsire da Dariya Amina sai ta sha kuni Tana Fadin"Bana son munafunci hanne da Hamida..!
Hamida tace"Ba wani gulma munga kinga sauya ne Amina kin rame sannan kinyi wani sanyi kamar bake ba..Eye Amarya Amaryan Ya danmallam to ya amarcin ne da Dadi ko ba Dadi..?
Amina sai Hararanta take yi kafin tace"Sai dai ango..Sannan ba Amarci ba amaro..!
Gabadayansu suka saka Dariya Farimciki ya cika Amina bakinta yaki Rufuwa Hanne ce tabi Dakin da kallo kafin tace"Dakin waye wannan hala..?
Amina tace"Na Sarood ne..!
Hamida tace"To ba kayanta a Dakin ne..?
Amina tace"Dillah kun isheni ko bari ma na Tambayi mutanen gida baku yi ba..Hamida shegen son jin kwakwaf to da kayanta zaki ganni aciki ne..?
Hamida na Dariya tace"Allah ya baki Hakuri Daga tambaya..!
Amina ta mata banza ta zauna kusa da Hanne tana Fadin"Hanne ya su Hajiya da Baba mallam..ke kuma Hamida yasu Mamanmu da Aba ina Jawaad su ya Zeenatu sun san an kawo ni nan..?
Ta fada a marairaice kamar zatayi kuka Hanne ta tura mata Ledan Hannunta tana fadin"Kowa lafiya..Ga Sakon hajiya tace mu kawo miki Sannan tana gaisheki sosai..!
Hamida ma tace"Mamanmu ma na gaisheki Aba da Jawaad duk suna lafiya sannan kowa yaji kina gidan ya Danmallam sunce duk a gaisheki..!
Sai Amina ta jawo leda ta fara fito da kaya bakinta yaki Rufuwa Fadi take yi Duk ni kadai wannan..?
Tana Daga kaya da Hijaban tana fadin"Wannan nasan aikin baba mallam ne..!
Ta daga su yaji da kayan da Hajiya ta Hadamata tace"Wannan kuma na Hajiya ne..!
Hanne tace"Kamar kin sani ta kasa sukuni komai sai tace na Amina ne..!
Amina sai hawayen Farinciki Fadi take nagode nagode sosai Kafin ta kalli Hamida tana fadin"Hamida ina abun Dadin da mamanmu ta bada ki kawo min bana son wasa fitomin dashu kafin raina ya bci..!
Tafada tana mikamata Hannu Har da shan kuni.
Hamida sai taji wani iri ta kasa mgana Domin ita dai mamanmu bata bata komai ta kawoma Aminar ba Hanne ce ta ceceta ta Dauko mata Turaran wutan da mamanmu ta bata ta Saka ma Amina a Hannu tana fadin"Ga shi in ji mamanmu..!
Amina ta karba tana jin Dadi tace"Kai nagode sosai nayi kewarta sosai Allah Sarki mamanmu..!
Haka take ta fada suna Binta da kallo Sai da tagama gani duka sannan zata kwashi kayan ta maida a ledan Hamida ta hanata ta karba tana fadin"Bari na jera miki Cikin Kwabarki..!
Amima tace"Wayyo Anty Hamida i miss u..!
Ta fada tana Rumgumeta Hamida ta kwace jikinta tana fadin"Ni sakeni..Dole kiyi missing dina anan bamai miki nasani..!
Amina tace"Wlh kuwa kamar kinsani..Ya Danmallam ne in yayi mun masifarsa nake dan ninkewa shi baya son ganin Datti..
Hanne tace"Tab baki san kyamkyamin ya danmallam bane baya shiri da kazami sam Amina sai a Rage son jiki..!
Amina ta Harari Hanne kafin tace"In an ki fa..!?
Hanne ta mike tana Dariya tace"Sai a Daku..Don Wlh keda megidan ne ba ruwana.!
Jin haka yasa Amina tayi shuru su kuma suna mata Dariya Hamida ta Bude Wardrope din taganshi Tsab Cikin mamaki ta juyo tana kallon Amina kafin tace"Amina kece yau da gyaran kayanki..Lalle aure dabam ne..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Bani na gyara ba shi ya gyara ni fa tunda nazo gidan nan ban saki jikina ba sai yau dana ganku..!
Atare Hamida Da Hanne suka Hada baki wajen fadin"Shiwa..?
Amina ta kallesu kafun ta ce"Bansani ba..!
Lokaci Daya tana juya musu ido Dariya suka kwashemata da shi Hamida tace"Soyayya ruwan zuma ka sha ka bama masoyi..!
Amina taki cewa komai ta kyalesu suna ta mata iskanci Hanne ta taya Hamida suka gyara ma Amina kayanta suka jera nasu suma da suka zo dashi suka tsinke da labarin makarantar su da Amina sai dai ta tambayi wance da wance sai jin Dadi take yi Amina ta Dauka Aminene ta tafi kenan sai ta gane cewa har yanzu Aminene na nan Rayuwa ce ta sakata tayi sanyi nan da nan kewar makaranta ya kamata Cikin Jin Dadi tace"Ai ranar monday nima zan koma in ji ya Danmallam..!
Hanne tace"Naji yana fadama Hajiya.!
Hamida tace'Yauwa gwara ki Dawo Wlh daga Unity har islamiya ba Dadi baki Amina..!.
Amina tace"Nima bakusan yadda nake kuka in na tunaku bane kamar in yi Tsalle in gani agida..!
Hamida tace"Wlh muma Hajiya take Lallabamu da mallam in sukaga muna kuka ko mun Damu Saboda baki nan..!
Hira ce kawai ta Tsinke kamar bakin su bazai gaji ba Daga Dakin Amina Kitchen sukaje suka Bude Hanne ta Sassaka ma Amina su Samosa da danbun namanta a Fridge kar ya lalace suka kuma jera maltinan aciki Duk da akwai lemuka kala kala aciki Sannan suka Diba samosan Hamida ta soya musu.
Sai alokacin sukaje sukayi sallar mangariba Amina kamar an bata Kujeran Hajji Saboda murna yau gata ga Hanne ga hamida
Bayan sun idar da salla su ka koma Falo sukaci Takeway din nan suka hada da samosa suka kuma sha Tea suka Dora da maltina ransu Fes gashi akwai Wuta basu Dauke ba Amina bata manta da shan mganinta ba bayan sun yi sallar isha"i ta Dauko Zata sha su Hamida suka tambayeta tace tayi Zazzabi ne basu matsa mata ba Tunda daman sunga ta rame kadan sai suka yar da da mganarta..
Afalo suka baje suna Hira Hanne ta kuna kallo gabadaya Tasoshin na wa"azi ne dana addini Ta kashe ta Dawo ta zauna tana fadin"Na manta gidan ustazai ne nan ba"a kallo..!
Hamida ta yi Dariya kafin tace"Ko agidanku ai ba kallon kike ba..!
Amina tace"Gulma da iyayin Hanne mana..ku wai ina Sa"adatu ne..?
Hanne tace"Tana nan mun manta da mun mata mgana mun zo da ita..!
Amina ta Harari Hanne kafin tace"Wlh da kuwa daga ke har ita ba matsiyaciyar da zata shigomin gida..!
Hanne ta Bude baki ita da Hamida kafin su kalli juna su hada baki suna Fadin"Uhm masu gida da miji..ammh nan ana kuka ana ba"a so..!
Ashe dai ana son ya Danmallam din..!.Hanne ta karishe Fada tana Dariya Amina ta karkace baki tace"Allah ya isa Tsakanina daku..Kuma Wlh wuta..!
Suka karisa mata da bal bal..!
Suna Dariya ta tashi tana jefansu da filon Kujera tana fadin"Munafukai kawai..!
Sai da suka gaji suka koma suka zauna Hamida tace"Wato Hanne Halin mutum zanen dutse Amina ko ta Sauya akwai wasu hallayanta da Har Abada bazata sauya su ba..!
Hanne tace"Kamar Taurin kai da Tsiwa da Fada..!
Amina ta kallesu ta harare su batayi mgana ita kanta ta zata ta koma Ruwan sanyi ammh Sanadin zuwansu yasa ta Fahimci Aminene bata Mutu ba Doguwar suma tayi ta Fara Farfadowa yanzu.
Sai kusan goma na Dare suka je suka kwanta achan dim ma wata Hirar suka Dasa tuna irin abubuwan da sukayi suke yi suna Dariya Amina in ta Fara Dariyan mugunta har da Hawaye yau gata ga Hanne da Hamida suna kwance waje Daya Amina ce a Tsakiya Hamida tace"Wai har yanzu baki daina shegen tsoron nan ba..Ke in ba kin