Showing 141001 words to 144000 words out of 145917 words

Chapter 48 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83944

nasan zasu dawo dashu..!.
Danmallam yace"Yakamata aa Hada muku Solar Duhu ai ba Dadi..!
Yakaka tace"Dayake ma suna barin wutar..Sannu da zuwa kasha Hanya...bari na kawo maka ko ruwa na yau bamu yi girki ba Takwara makaranta ta wuni sai da zamu Dawo ne muka biya gidan mallam muka Dauko waina gatanan in zaka ci na Zubi maka...
Danmallam yace"Bakomai yakaka wanka ma nake so na farayi..!
Yakaka tace"Eh to ya kamata shiga Ciki Aminar na ciki ina ga sun kwanta daga ita har yaran sun gaji..ya amsa mata da Toh ya juya kenan Tace"ahf kaga na manta ya wajen su Sakinar ne da mai juna Biyu..?
Fatan dai suna Lafiya..!
Danmallam ya juyo yana amsa ma yakaka da Lafiyarsu kalau sannan ya shige Dakin Amina a gaban gadon ya Tsaya kawai yana kallon Amina tana Barcinta Cikin kwanciyar Hankali ta saka Hannunta ta rumgume ya"yanta su Aba yake mamakin girmansu da kibansu wani Annuri na shiga cikin Ransa yana kallon Amina aransa yana auna yarda yar yarinyar nan ta Hanashi Sukuni
Zama yayi gefen gadon bayan ya Sauke karamar Jakar Hannunsa yana kokarin Dauke hannun Amina kan yara saboda ya Samu ya Daukesu Caraf ta Rike Hannunsa da Karfi Lokaci Daya tana Bude idonta sai ya Fada kansa suka kura ma juna Ido na wani Lokaci shi na murnan ganinta ne da wani sonta da sha"awarta ita kuma na Bakin ciki da Takaici ne Daya Taimaka wajen Dakushe Zumudinta.
Kauda hannunsa tayi ta mike Zaune Fuskarta ba Fara"a tace"Mallam Lafiya..?
Girman Idonsa ya kara yana kallinta Cikin mamaki kafin yace"Mallam kuma..?
Kawai sai taga ma zai raina mata wayau ya sake kai hannu zai Taba yaran da Sauri ta make hannun nasa ya Dago Cikin mamaki yana kallonta kafin yace"Amina ni kike bige ma Hannu don zan Dauki ya"yana..?
Amina tamai wani kallon Tara saura kwata kafin ta sauko Daga kan gadon batayi wata wata ba ta Dauki Aba ta goya ta saka showel din Dake gefe ta Daureshi dashi sannan ta Dauki Mallam a Hannunta ta juya zata bar Dakin da Sauri ya mike yana kiranta,


"Amina..!


Da farko taso tayi Ficewarta ne sai kuma ta ja ta tsaya bata juyowa ba Da Hanzari ya taka har gabanta ya ja ya Tsaya yana Binta da kallo ita kuma ta Kara Hade rai cikin mamaki yace"Me kika yi haka?
Amina tace"Dani da ya"yana bamu da Muhalli a wajenka..saboda banga amfani Daukan su da zakayi ba..!
Baki ya saki yana kallonta Duk da yasan za"a rina Daman rigima sai wacce ya gani sai dai bai nuna ya karaya ba ya mika mata hannu yana Fadin"Bani su..Sai muyi mganar Daga baya..!
Amina ta kallesa Daga Sama har kasa kafin tace"Wadanan ya"yan Amina ne sai ka bari in Sakina ko Sarood dake da Mutumci a idonka sun haifan maka sai ka Dauka..Bani waje na fice kafin Raina ya kara baci kaga abunda baka Taba gani ba wlh..!
Sai mamakinta ya kamasa yadda take kallon Tsabar idonsa tana mai rashin kunya sai ya tsawarta mata yana Fadin"Ban sauke kaina kasa don ki raina ni ba Amina ki shiga Hankalinki..!.
Wata Dariyan Rainin Hankali ta sakamar kafin ta raba ta gefensa ta Fice Daga dakin ransa ya baci yabi bayanta yana Fadin"Amina ki dawo nace..Nace ki dawo ko..?
Amina ko Sauraransa batayi ba ta Fada Dakin Yakaka shi bai yi zaton Yakaka na Dakin ba ya bi bayanta kawai sai suka Hada ido da yakaka Amina na Tsaye ta Cika kamar ta Fashe Daman Yakaka tasan yadda Amina ta Zuciya Danmallan bazai ji Da Dadi ba.
A matsayinta na Babba yasa ta mike Daga zaunen Datake ta mikama Amina Hannu tana Fadin"Bani yaran..Ki koma ku cigaba da Rigimarki kada ku saka yaran da basu san me Duniya ke ciki aciki ba. !
Sanda ta Fadi haka sai Danmallam yaji kunya ya koma da Baya ya fice Daga Dakin Amina sai ta sakama Yakaka kuka ita kuma ta karbi Aba ta kwanto Mallam Dake baya tana Fadin"Ban son Sakarci kin gama kuma Nuna mai Matsayinki ya tako ya Biyo ki sai ki Bata wayonki..?
Maza Share hawayenki kada ki sake mai kuka kije ki karbi Lallashin shi ko Banza yasan Darajan ki yanzu..!
Amina ta Share Hawayenta sannan ta juya ta Fice Yakaka ta bita da kallo aranta tana Fatan Allah ya Daidaita Tsakanin Ma"auratan..!
Amina na komawa Dakin ta iske shi Zaune gefen gado yayi Tagumi yana ganinta ya taso zai riketa ta kauce ta sakamar Jajayen idanuwanta tana Fadin"Bana so..Kada ka tabani..!
Sai ya Janye mata Kan gadon ta koma ta kwanta ta Juyamai baya sai kawai ya koma ya zauna ya kara yin Tagumi.
Yana mamakin Amina zata Haukatasa ganin kamar ma batasan yana Dakin ba yasa ya Sauko Ya Duka a Gaban gadon inda yake kwance yana Kiran sunanta..!


Amina..!
Noor..!


Kamar yana kiran Dutse haka tayi mai yasan Laifinsa yasa ya fara mgana"Amina kiyi hakuri Ana Asif..Nasan ban kyauta ba da na tafi ban Fada miki ba..Ammh kema ai kinsan kin batamin ko..?
Kamar tana jiransa ta juyo Lokaci Daya ta Mike zaune tana Fadin"Au nama bata maka ko..!?
Saboda ban je nayi ma Hajiya Rashin kunya nace zan bika ba ko..?
To ai da nayi hakan da nagane bani da wayau domin ka nuna min Tabbas ku maza baku da Tabbas haka zan bika kuje ku Hadu da matanka kuna wulakantani Tunda ka nuna musu ban da Daraja..duk lalacewar naka ai naka ne. watarana Hajiyar dai itace Uwata kuma wajenta zan koma bari kaji na Fada maka har yau ban yi Nadaman Kin binka ba..Indai kan Umarnin Hajiya ne da kai ma ta isa Dakai bama niba..!
Ta fada tana bayyana bacin ranta Danmallam sai ya kasa mgana yana kallonta Amina taji hawaye sun kawo mata sai tama kasa Cigaba da mganr
Danmallam ya Bude baki yana Fadin"Amina n...!
Dakata..!
Tafada tana Dagamai Hannu kafin ta kallesa Tana fadin"Ba sai kace min komai ba..Ka nuna min matsayina amfanina ya kare Tunda kamin ciki na Haihu ni Aikina kenan shiyasa Domin ka nuna min ni din ba wata bace yasa ka Dauki matarka kuka koma Tare bansani ba.?
Saboda ka nuna min in ban bika ba kana da Biyu irina ko..?
To ai bakomai yanzu ma sai ka koma wajensu ni ban kira ka ba sannan ban aika maka da katin gayyata ba..!
Daga haka ta juya zata kwanta ya riketa da karfi tana so ta kwace jikinta yaki barinta sai ma gadon da ya hau ya Rumgumeta sosai Duk yadda taso ta kwace kanta yaki barinta sai kawai tayi Lamo sai kuka Danmallam ya kamkameta yana Fadin"kiyi Hakuri Amina na Tuba nabi Allah..Na biki..Nasan ban kyauta miki ba ni Haushina da na shirya tafiya Dake kika bi na..Wlh Amina na kasa zama in baki kusa dani ina Bukatarki kusa dani Amina..Noor ina sonki..Wlh ina kaunarki ki yafemin..!
Amina ta kara sakarmai kuka Tana Fadin"Baka sona ka nuna ka fi son matanka akaina..!
Yana kara riketa cikin jikinsa yace"A"a kada kice haka.. Kema kinsan ina sonki..Tunda na koma bana cikin natsuwata na gama Fushin na Sauko na nemeki baki bani Daman kare kaina ba..Sannan ki duba na kasa zama a madina saboda ke..Hankalina ya tashi ko Barci bana iyawa..!
Wannan duk ba so bane. ?
Wannan duk bai sa kisan kina da Daraja ba..?
Amina na jinsa ta masa banza sai Faman mata rantsuwa yake yi yana Lallashinta Amina na karamai Bore Gajiya yayi ya Hade Bakinta da nashi Duk yadda taso ta hanasa ta kasa Domin itama ai ta gyaru tana Bukatar Mijinta a kusa da ita tun ana Lallashi har aka Sauya salo Danmallan yadda ya Samu Amina yasa sai da ya raina kansa kuka reras ya Dinga rairamata Albarka kuwa tashashi har sai da tagaji Sai da suka samu natsuwa sannan sukayi wanka tare bayan sun fito taje ta Hada masa Tea ta kawo mass Yakaka da yaran Tuni har sun yi barci.
Sai janta da Hira yake yi taki Sakarmai Fuska sai dai eh ko A"a shima yasan ai yaga karshensa ina shi ina kara ma Amina Laifi..?
Irin wannan Hukunci haka..?
Duk Fushinta kafin wayewar gari ta Sauka sannan ya Lallabeta suka koma Ruwa wajen Danko yake mai Amina tasha gyaran da yasa Danmallam ya kara raina kansa da duk abunda yake Takama dashi.
Amina sai yanga take mai sai da Safe ne ya Dauki su Aba bayan Yakaka ta musu wanka Allah yasa bata da Paper ranar ammh taso tana dashi tayi Tafiyarta ya karata shi kadai
Tunda ya Dawo bai fita ba ko Sallah acikin gida yake yi wayarsa ma kasheta yayi saboda yasan Halin Amina da zafin kishi yanzu ya samu ta Dan Sauko ai sai su Sakina su Ballomai ruwa ya shiga uku..!
Yakaka sai ta koma zaman Daki Ta bar ma"auratan su ci Lokacin su Taji Dadi Data ga sun sasanta kansu.
Allah ya taimaki Danmallam kwana Hudun da yayi Amina bata da Jarabawa da su yayi amfani ya Gurji Amarcin sa sannan ya samu ya Nuna ma Amina matsayinta duk da ta gamsu bata wani Sakin mai sosai shifa Jidalin Amina shi zai bada Labari Domin shi yaga komai ganin Idonsa..!
Ranar kwana Biyar tana da Jarabawan Safe sai da taje tayi ta Dawo bai Fita ba har tace mai ko gidan mallam bazai leka ba saboda ya wanke maata zuciya yasa yace Zuwan nata ne baki ta tabe bata nuna mai tawani ji Dadi ba aranta kuma ai tasan ko yanzu kasuwa tatashi Dan koli yaci Riba..!
Sati Dayan da Danmallam yayi komai ya Daidaita Tsakaninsa da Amina Saboda kada ya kara ballo ma kansa ruwa yasa yace in ta gama jarabawar ta shirya tafiyan ta gaya masa sai yasa Jafar ya nema mata Visa sannan ya Sanar da ita ya Sama mata Takardan zama achan na Dindin bata wani Nuna murnanta ba sukayi sallama Ta Abuja ma wannan karon ya kara tashi Sai washegari ya isa jidda Daganan mota ta kaisa garin Madina Ya kirata ya samu ta Daga wayan Daman kafin ya Tafi sai da ya roketa alfarma shi yanzu Lallaba Amina yake tasha shi ya warke..!
Yar ya tafi su mallam basu san yazo ba bai gayamusu ba sannan kuma itama Aminar bata gayamusu ba tayi gum da Bakinta itama Yakaka bata Fadama kowa ba..!
Danmallam Daya koma sai ya Fara Cukun Cukun sama ma Amina gida sun yi shawara da Aliyu akwai kudi a Hannunsa zai siya mata gidanta ne ya Fasa,karban na cikin makaranta Yasan ko giwan wake yasha bazai Hada Amina zama dasu Sakina ba..!
Tafi su kishi da Jidali zaman ma bazai yi Dadi ba,Sannan Aliyu ya bashi goyon bayan ya samata gidanta ita kadai Saboda tana da yara sannan kuma hakan ne ma ya Dace zai fi Samin kwanciyar Hankali da hakan suka Tsaida mgana da Taimakon Abu Kattab ya samu karamin gida nan cikin gari kusa da Masallacin madina..!
Bedroom biyu sai Falo sai Kitchen da karamin haraba kafin dai abubuwa su Daidaita,sannan yasa aka gyara gidan ya Zuba abubuwan amfani na Daidai misali Duk da ya Takura bai da kudi sai da Aliyu ya turomai wasu suna waya da Amina ta fadamai sun kusa gama Jarabawa.
Ya kira jafar suka yi mgana kan zai nema ma Amina Visa ammh sai ta amince sannan Jafar mamaki ya kamasa su ya Danmallan an shiga Hannun Amina sai Allah..!
Ko su Hajiya bai Fadama Amina yake jira ba sun zata fushin da yayi bai Sauko bane suka zubamai do suga iya gudun ruwansu..!
Amina sun gama jarabawarsu Cikin Sa"a sai Fatan Nasara asatim Matar Aliyu ta haihu Aliya jin haka yasa Danmallam yace ta shirya taje suna ta kwana Daya batamai musu ba ana Gobe suna Idi yakai su ita da Yakaka da yaran Aliya nata ina ta saka dasu sai Faman nuna ta take yi a matsayin Amarya abokin mijinta Amina dai Sama Sama domin ita bata da yarda ne kan wasu abubuwan sannan bazaka nuna mata ki da Farko ba Sannan ka Dawo ka nuna mata so ba, Daga baya baya ba..!
Kuma Aliya sukan yi mgana da Sakina ammh ba kamar baya ba Sai dai Sama sama kawai kowacce tasan matsayin yar"uwanta sakina kuma sai dai a gaisa da Labarin Duniya Tariga ta gama Shiga Taitayinta..!
Kwana Daya sukayi suka Dawo Gumel ammh sai da Amina taje ta kara Duba Anty Amarya abun sai addu"a Yanzu takai sai ana kulleta adaki Itama Daga Bakin window ta Lekata Sai da ta mata kwallah Mamanmu ma suna waya da su ya Zeenatu an sallameta tana gida sun ce dai da Sauki ammh ba Baki har yanzu ganin ma dai sai ahankali ita kanta Hajiyar uwar ma Duk ba wani Cigaba sauki sai na Allah itama har yau an kasa gane Cutar Dake Damunta..!
Amina batayi gaban kanta ba sai da ta Samu Hajiya ta Fada mata yadda sukayi da danmallam da yazo sai dai Ta Boye Rigimansu Hajiya tayi ta Dariya aranta Ta kuma godema Amina sannan ta godema Allah ko banza yarta nada Daraja Hajiya tace zasu Tattauna da mallam tana mai mganar yace ta shirya tabi mijinta Hajiya tace to..Anty Hadiza tama mgana aka Hada mata kayan gyaran jiki Sannan da Dake Dakem kayan kamshi da sauransu na Tafiya.
Sannan Hajiya ta kira Danmallam taji Tsarin Tafiyar na Amina da inda Zata zauna ya fadamata ya siya mata gida Hajiya taji Dadi tana ta sakamai albarka..Sannan ta mai mganar Yakaka yace sai in Amina ta Fara Tahowa sai yaga yarda za'ayi shima yasan zaman Yakaka da Amina taimako ne sosai
Danmallam bai saka a fara neman mata Visa ba sai da Amina ta Kirasa da kanta tace ta amince zata taho sannan ya yarda Jafar yazo ya amshi pasport dinta sannan yace ta Hada kayanta saboda jirgin yawo zai yi gaba Dashi..!
Jin haka yasa Hajiya ta siya mata Kamshin Girki kala kala da su garin kuni aka shanya mata wake surfaffen da Danyen shinkafa kaya da marasa Nauyi da su fulawa da Sauransu,Sai kayan sawanta dana yara duk da ba Duka ta Diba ba..!
Ansamar mata Visa zata su tashi nan da kwana goma ta Abuja,sai Amina ta Cigaba da shirinta ta kira duka yan"uwa awaya tayi musu sallama su Hanne suna ta Fadin zasuyi kewa da kuma Fatan in suka Haihu Allah yasa tazo tace tasan da wuya. !
Ana jibi zasu tashi Suka kulle gidan suka je gidan Baba mallam tayi sallama da Aba da Anty Hadiza anan ma gidan ta kwama itama Yakaka ta musu sallama Domin abuja gidan Ya Aisha zata koma kayan su Tuni suna Madina har Danmallan ya karba. !
Washegari Idi yakaisu Abuja gidan ya Aisha suka kwana washegari karfe Uku na Rana su ya Aisha da mijinta da Yakaka suka Raka Amina Filin jirgi tana Sabe da ya"yanta daya a gabanta ta Sakashi Cikin Abun goyo Daya kuma yana Kafadanta suma yaran sun yi Bul Bul Dasu suna Daga mata Hannu Amina sai da tayi kuka Lokacin da Jirginsu ya Daga Tana Salati Allah yasa akwai wata Farar mata agefenta ita taimaka mata ta saka mata Belt sannan ta rike mata Aba Dake hannunta..
Amina jikinta sai rawa take yi yau gata ajirgi duk bata cikin natsuwarta addu"a kan har ta shiga bayi sai da tayi matar dake gefenta nata mata Dariya saboda ganin yadda take yi sai da Tambayeta ammh bata taba shiga Jirgi ba tace eh tayi Dariya tace kodaga gani to maatar ne ma yasa ta Saki jikinta ba kamar Farko ba suna ta Fira nan tasan sunan matar Surayyah a Nageria take itama aiki yakai mijinta madina suka koma yanzu ma tazo ganin gida ne su yan Abuja ne suna ta Hira da Amina duk da ta Girmeta itama ta Fadamata wajen Mijinta zataje sai santin su Aba take tana jin Dadin ta samu yar"uwa a Nageria..!
Sai Dare suka sauka a jidda Danmallam Daman tun tasowarta ya Sani yana Jidda shi da Sarood da Sakina suna jiran Saukan Amina Saboda ya gayamusu sai ko ga Amina ita da Surayyah wacce ke rike da Aba ita kuma mallam na Hannunta .!
Sakina baki ta saki tana kallon yadda Amina ta koma Cikin Abaya baka tayi Rolling jan gyale Takalmin kafarta ja ne da Jakarta ga yaranta sai dai kace Masha Allah Danmallam ya nufeta
Ya karbi Jakarta lokaci da mallam yana mata maraba har da Rumgomta sannan suka gaisa da Surayyah Amina ta Fadamai irin taimakonta da tayi a jirgi ya mata godiya itama Mijinta yazo Daukanta har suka gaisa da Ya Danmallam sai ma suka ga sun san juna suna Haduwa wajen karatu a masallacin cikin madina suka gaisa cikin girmamawa basu rabu ba sai da Surayya ta karbi Lambar wayar Amina da alkwarin zata zo har gida sannan ta shiga mota suka wuce ita mijinta, Amima kuma ta saki Fuska suka gaisa da su Sarood har da rumguma Sakina kuwa Amina sama sama ta amsa mata ko Hannun Datake bata,ta kauda kanta bata karbi Musabahanta ba,Motar Haya suka shiga zuwa Madina Danmallam na rike da Aba Sarood ta kankame Mallam itama cikinta har yayi girma Sakina na gefe kamar maraniya mamaki ya kamata jin yadda Amina da Sarood ke Hira Cikin Larbaci..!
Gidan su Sakina suka fara zuwa Sai da Amina tayi sallah taci abinci sannan suka Dumguma zuwa gidanta ta iske komai an gyara har kayanta da suka Rigata isowa Data tambayi Danmallam yace mata Sakina ce Sarood suka zo suka gyara bata kara mgana ba nan suka barsu ya rakasu suka Hau mota suka koma gidansu Yau dai ga Amina amadina Duk Gajiyan da ta kwaso na Tafiya Sai Da Danmallan ya Famshe sai washegari ya barta ta Fara barcin gajiya sannan shi ya Kira chan Nageria ya Fada musu saukanta .!
Saboda ita bai riga ya siya mata Layin nan ba,Amina kamar bugagiya wajen Sati tana Hutawa sannan ta Fara Fita ita da Danmallam gidansu Abu Kattab suka fara zuwa ta wuni mami Sara nada Kirki sannan Amina taga inda Sarood ta Dauko rashin Hayaniya har suka bar gidan Su Aba na hannunta tana wahala dasu Daga Ranar Amina bata zauna ba suna Fita Cikin gari yana nuna mata wurare Amina tayi kuka data ganta a msallacin ma"aiki Bata taba Zaton haka ba,Sannan sun raba kwana yana kwana Biyu gidansu Sakina ita yana mata kwana Daya Sai dai tana Wahalan Renk ita kadai ta Saba yakaka ta Saba mata duk sai ta Sangarce.
Ammh yanzu Reno kadai ya isheta sai in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login