Showing 126001 words to 129000 words out of 145917 words

Chapter 43 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83961

tunda akace Aba yayi aure zuciyarta ke zafi.
Anty Amarya ma kamar mujiya bata ko Fitowa,Chan duste labari duk ya bazasu kowa yasan abunda ta aikata shi dai mallam ya zura mata ido bai ce mata komai ba ballatana tasan mafitanta
Sannan duka ya"yanta ba wanda ya kara bi ta kanta har Sabeeha na wajen Hajiya sai jefi jefi take ganinta Turakan mallam kuma Daga Hajiya sai Haj.Nasara
Bangaran Hajiya uwa tana chan gidansu Cikin wani irin Hali Duk da ba wanda yasan abunda ya faru sun fara Zargin akwai wani abu saboda mallam bai zo ba ballatana ya"yanta ko Hajiya ma batazo ba ahalin in Lafiya lau Tare da Hajiya zata zo haka aka watse bakwai din Batula da tata ta kare Aka bar Uwani ita kadai Tana Faman da Bugun zuciya mutuwar Batula ya kara Raunanata Gata nan kawai ammh ita kadai Tasan Halin Data ke Ciki kuka tayi shi kamar Idonta zai Tsiyaye Kiran wayan su Nazeem kam har tagaji basa Dauka Shamsu ne ma ya taba Dauka yace kada ta kara kiransa Nazifa kuma Blooking dinta ma tayi,bata da karfin gwiwan komawa Gumel domin tasan zamanta achan ya Kare.
Rayuwa ta juya musu baya alokacin da basu zata ba,.
Sati Daya na Cika Anty Hadiza ta tare adakin Yaya,sai abunda ba"a rasa ba Hajiya ta kara mata sannan Aba yayi mata akwati Biyu na lefe su Yakaka ne gaba gaba yan raka Amarya ita da Haj.Nasara.
Aranar da Daddare Danmallan suka zo shi da Amina data matsa sai ya kawota taga Hajiya da Aba da Mallam,sai da suka zo sannan Hankalinta ya kwanta Shashen Hajiya ya barta yaje shashen Hajiya nasara ya ga Sarood Tunda tana wajenta yace ta koma gidansu na kofar arewa tace ya barta anan tasan ba wani Damuwa da ita zai yi ba yana da amarya Shi ko ba haka bane gani yayi ba yanzu zasu koma ba Sai nan da wata Biyu gwara ta koma gidanta zai fi in ya gama kwanakin sa wajen Amina sai ya koma mata ammh sai ta nuna bata so..!
Sai kawai ya kyleta ganin kishi take shi ko aransa ma tunani yake sarood bata iya kishi ba ai kishi na wajen Aminaa Jidali.
Shi tunda abun nan ya faru bai kara neman sakina ba,shi abakin ma Hajiya yaji Yan"uwanta sun maida ta Dutse daganan bai kara bi ta kan mganarta ba sai da komai ya bayyana sannan ya Fahimci bai taba Son Sakina ba komai ya kare acikin Ransa kwata kwata shi dai bai ma tsaya ya yanke wani hukunci akanta ba sai dai bata acikin Ransa kwata kwata.
Basu koma ba sai Sha Dayan Dare Har gidan Aba suka je,Mamammu ta window take lekonsu tana Kuka kukan Nadama da Bakinciki.
Amina Bakinta yaki rufuwa ganin Anty Hadiza Dakin Aba ta rumgumeta tana murna sosai itama ta riketa cikin Farimciki jawaad tana murna ya samu mama.
Haka kowa ke shigowa yana fita bawanda ya Damu da wata mamanmu mamakin karfin Halinta ma Aba ke gani data ke cikin gidan bata kara gaba ba.
Agaban idonta ya shigo gidan da Ledoji a hannunsa ga shi yaci Farar Shadda yayi kyau rabonta data gansa tun Ranar da komai ya bayyana..!
Agaban idonta Sa"idu ya Shige Dakin Yaya da wata mace suka Sakayo kofa sai taji jiri na Dibanta ta Daga kafa kenan Jirin ya yarfar da ita faduwar da zai yi Sanadiyar shanyewar barin jikinta Guda Daya..!












*Janafty**TFZB2029*




*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*




Wajen kwana Biyar Aba yana cin Amarcinsa hankalinsa kwance ya samu natsuwa da Anty Hadiza fiye da yadda ya Tsammanin samunta.
Bai taba zaton balaraba tana cikin gidan nan ba, bata kara gaba ba,saboda Dakinta yana rufe ne sannan bata fitowa yayi zaton tayi ma kanta Hisabi ne ta kara gaba Acikin ransa kuma wannan kuncin da bakinciki da Tsanar Balaraba baya jin zasu sake shi nan kusa yana jin har duniya ta Nade bazai iya Yafe mata ba.
To shi kanshi baisan tana cikin gidan ba,ballatana Anty Hadiza da bata Dade agidan ba,Sai ranar kwana na shida ne Wari ya rika fitowa Daga Dakin da Kakarin mutum kamar zai yi Amai Lokacin Aba ya fita gidan Gona Anty Hadiza ke tsakar gida tana Shara taji wannan abun sai hankalinta ya tashi ta tsorata sai dai bata bar kiran sunan Allah ba Mayafinta ta Dauka ta je gidan mallam Shashen Hajiya ta gayamata abunda ke faruwa ita kuma Hajiya ta Sako Hijabi ta Biyo bayanta.
Koda suka zo Dakin yana rufe ne ta Ciki ba yadda zasu yi su shiga sai an balle kofar sannan Hajiya tana da Tabbacin Balaraba na ciki Saboda ai ita tayi waya da yan gusai a manganganunsu bai nuna balaraba ta koma chan ba sannan tana da yakinin kunya da Nadama ne suka sakata ta kasa fitowa kamar yadda ya Kanannaye Marliya itama ko Kamshinta bamai ji itace ma Sarkin Tsausayi take umartan su Lami da in sun gama girki su shigar mata dashi Cikin Shashenta kada yunwa ta mata Illah.
Hajiya mallam ta kira awaya bai yi nisa ba yana makarantar Haddar su Amina suna taro yace ga shi nan zuwa Daganan sai ta kira Aba tace ya Dawo gida shi har ya rude ya zata ko wani abu ne ya faru da Hadizar shiyasa yazo Hankalinsa tashe ko kafin ya kariso Mallam har ya dawo sannan ga Jafar ga Nasir su suka kira mai Balla kofa kafinta yazo ya Balle kofar Gabadayansu sai da suka toshe Hanci suka samu shiga Dakin Halin da suka Iske Mamanmu aciki Dole bawa ya kara Tsoron duniya..
Tana kwance a kasa inda ta Fadi Jiki ya jirkice Baki ya karkace Anan tayi kashi da Fitsari bazata iya tsshi ba Idanuwanta sun kafe saboda kuka sannan ta galabaita da yunwa da kishi Tana ganin Hasken rana ya shigo ta Fara laluban inda zata Hango mutane sai idonta ya koma yana ganin Duru Duru bakinta ya bushe ba"a kajin me take fada sai mgana take yi ba wanda ya Fahimta ashe ruwa take fadin a bata Anty Hadiza ce ta karkata kunnenta har taji abunda take fadi ta Ruga Kitchen ta Dauko ruwa Tsausayinta har ya kamata Idanuwanta ya ciko da Hawaye ta kasa ma Daga kanta ita kadai kuma ba wanda ya taimaka mata hakanan ta Zuba mata ruwan wani ya shiga Bakinta wani kuma ya Zube a kasa.
Hajiya ta kalli mamanmu ta kara kallanta kawai sai ta gyada kai ta Girgiza kafin tace"In bawa bai ji Tsoron wannan rayuwar ba yayi asara..Allah ka Tsare mana Imaninmu..!
Aba ko na tsaye yana kallonta aransa yana jin Dadi samnan yana mata Fatan abunda zata gani sai ya fi haka Ya Jafar ko nadaga bakin kofa bai ma kariso ba domin in akwai Hallitar Daya Tsana to ya ga mamanmu ne yanzu nan komai zai Dawo mai acikin kansa Nasir ne ke gefen Aba Mallam kuma Duke yake gaban Mamanmu ya kasa mgana Acikin ransa kuma Kabbara da Kirari yake ma Allah yana Tunanin yaushe bawa zai gane cewa Duniya ba matattaba ne. ?
Yaushe zamu san cewa rayuwar nan tana cike da tashin Hankali ne..?
Kai ya girgiza kafin yace"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un..!
Haka kawai yake fada Aba kuma kawai sai ya juya baya zai fice Daga Dakin Mallam ya Daga kai ya kallesa kafin ya kira sunansa shiyasa ya Tsaya kafin ya Juyo yana kallon Mallam din.
Mallam ya mike yana Fadin"Ina zakaje..?
Baka ga Matarka cikin wani mawuyacin Hali bane..?
Kallon Baba mallam yake yi Cikin mamaki kafin ya cije baki yace"Balaraba ba matatace bace..Tun Ranar da nagnee ita wacece na Tsinke saura igiya biyun Dake Tsakanina da ita..!
Mallam ya jinjina kai Daman so yake ya tabbatar da hakan duba da yadda Sa"idun bai kara Tadamai da mganar ba,Hajiya tace"To yanzu ya za"ayi da ita..?
Aba zai yi mgana kenan Mamanmu ta fara zakuda jikinta tana kuka tana mgana bamai gane me take fadi Sai da Hajiya ta Duka da warin Dake fitowa Daga Jikin Balaraba haka ta Daure tana Fadin"Me kike son kice Balaraba..?
Cikin Daba daban mgana tace"Kuu u....yaaaa...fee ee..min..!
Sai Hawaye Daga gani ta gama galabaita Hajiya ta Dago tana kallon su Aba kafin tace"Yafi yar ku take nema Sa"idu ni dai na yafe miki balaraba haka ma mallam..Sai dai Sa"idu da yaran nan..!
Aba ya juya kawai yana Fadin"Har Abada bazan iya yafe ma wacce ta Cutar da rayuwata ba..Da yardan Allah kin fara gani kenan kafin ki Mutu sai Allah ya Dandana miki azaba mafi muni akan abunda kika aikata muguwa kawai..!
Daga haka ya fice Daga Dakin a Fusace Jafar ya mara mai baya domin shima bazai iya yafe mata ba Anty Hadiza na gefe tsausayi duk ya Cikata sannan ta kara jin tsoron rayuwa da Duniya gabadaya.
Ba wanda ya iya taimaka mata cikin wannan Halin suka barta Hajiya da mallam a falonsa suka shiga suka Zauna mallam yayi jigum Domin har yanzu abunda ya faru bai sakesa ba,Hajiya ma Tagumi kawai tayi tana kara Jinjina al"amarin kafin ta Daga kanta tana kallon Mallam cikin wani yanayi Tace"Mallan yanzu ya zamu yi da ita..?
Ayadda Sa"idu ya fice bazai taba Sauraran kowa ba..!
Mallam ya Sauke Numfashi kafin yace"Nima abunda nake Tunani kenan..Bazan taba takura ma Sa"idu akan wannan al"amarin ba kamar yadda ban takura ma kaina ba..Zan Kira chan gusai na Fada musu Halin da ake ciki yan"uwanta da suke Dolenta su zo su tafi da ita..!
Hajiya ta jinjina kai alamun gamsuwa nan take ya kira Kawu salisu bayan sun gaisa ya Fadamai abunda ke faruwa shima Dagachan barayin yace kadan ta gani sun yi mgana kan zai Fadama yan"uwanta gobe zasu zo su tafi da ita Domin ta fara girban abunda ta Shuka ne da wuri.
Bayan sun gama wayar Hajiya tace"Ya kuka yi dashi..?
Mallam yace"Yace zai fadama yan"uwanta gobe zasu zo su tafi da ita.!
Hajiya ta Sauke Tagumi kafin tace"AllAh ya kyauta..!
Mallam ya amsa da Ameen Cikin wani yanayi Hajiya ta gyara zama tana Fadin"Mallam ya batun yaran nan..?.
Kasan dai uwa ba abun wasa bane sannan duk abunda iyayansu suka aikata basu isa su sauyawa Tuwa suna ba..Na lura daga ya"yan Balaraban har na Uwani da Marliya tun da abun nan ya Fallasa suka gujema iyayan nasu kana gani Harta Umaima ina jin yan"uwan sun fadamata tana shashena ko Damuwa da uwar ma batayi ba..!
Mallam na jinta kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Me kike so ayi..?
Hajiya tace"so nake ka kira su kayi musu nasiha kan Muhimmancin Uwa awajensu sannan su yi hakuri su yafe musu su tallafesu domin su kadai ne yanzu suka Rage musu..!
Mallam yace"Zan yi musu mgana Insha Allahu. !
Hajiya tace"Ya kamata gaskiya..!
Gani tayi mallam na nemsn shigewa Ciki yasa ta kallesa tana Fadin"Mallam ya batun Uwani da marliya..,?
Gwara Uwani tana gidansu Marliya kuma ta nan ko Fitowa batayi nine ma nake saka su Lami suna shigar mata da abinci..!
Mallam ya Dakata yana kallon Hajiya kafin ya koma ya zauna yana Fadin"Duk da Sakin aure ba Dabi"ata bace..Ammh kuma ya zama Dole ne Bazan iya Cigaba da zama da Uwani da marliya a matsayin matana ba..Dukkansu zan tsinke igiyan aure koda Dayan Dake Tsakanina dasu ne Su je na yafe musu ni ban taba Cutar dasu ba..Allah suka ma Laifi sunemi gafara a wajensa..Zan samu Lokaci naje chan Tsafe gaisuwa zan sanar ma ita Uwani marliya ma zan sanar da ita abunda na yanke..!
Hajiya sai taji wani iri sai dai tasan mallam ya tsorata da wannan al"amarin yasa kawai tace"Allah yasa hakan shi yafi zama alheri su kuma Allah yasa hakan ya Zame musu izna..!
Ya amsa mata da Ameen kafin yace"Me Saratu take yi agidan nan ne..?
Bata koma gidan mijinta ba..?
Hajiya tace"Na tambayi Danmallam din yace min yamata mgana ta koma taki tace ya barta anan..!
Mallam yace"Wannan mganar banzace..Bazai yuyu ba Dole yayi adalci Tsakanin matansa Raba musu kwana zai yi Saboda yayi adalci a Tsakaninsu ki Fadamata ta shirya ta koma Gidan auranta zan kira Umarun zan mai mgana..,!
Hajiya tace"Shima yaso ta koma itace taki..Kasan ita kadai ce yanzu ko Rashin Sakina agidan yasa taji wani iri..!
Mallam yace"Ita Sakinar tana chan Dutsen kenan wajen Danginta..?
Hajiya tace"Eh sadiya ta fadamin tun washegari suka Dauketa Daga asibiti suka tafi da ita..Ta kara barin cikin nata ne..
Mallam ya jinjina kai kafin yace"Allah ya kyauta na gaba..Shi ya matsayin auran nasu da Sakinar..?
Ko baku yi wannan mganar dashi ba..?
Hajiya tace"Bai taba min wannan mganar ba..!
Mallam ya koma ya jinginar da kansa Jikin kujera yana Fadin"bari zan Tuntubesa naji..Bazan mai Dole ba Sai dai zan bashi Shawara a matsayina na Uba a wajensa..Ina Fatan abubuwan da suka Faru su zama izna garemu da yan baya..Sannan ina Rokon Allah ya Tsaremu da zuru"armu gabadaya Daga Fadawa Halaka..!
Hajiya ta amsa da Ameen Ameen basu wani Dade suna mgana ba ta koma Shashenta ta bar mallam zai kwanta Saboda tun faruwar abun nan bai wani Cikin natsuwarsa abun ya tabasa sosai,Ita kanta sai a Hankali ta gama tsorata da Duniya da mutanen Cikinta Har ita kanta Nasara sai ahankali gidan gabadaya sai yayi kamar ba kowa,shuru kowa kumazaka gansa baya cikin Walwalarsa.
Hajiya bata yima Sarood mgana ba Illah ce mata tayi taje mallam na nemanta Sai da taje ne Mallam yayi mata Nasiha Daga karshe yace tayi Hakuri ta koma Gidan mijinta ta zauna kafin su tafi ta tabbarar mai da Insha Allahu zata koma sannan ya Sallameta Kai Tsaye kuma ya Kira Danmallam yace yazo yana nemansa Tun da yammah bai samu zuwa ba Sai Dare saboda Rigimar Amina wai sai yazo da ita bazata iya zama ita kadai ba yasan in yazo da ita sai ya shafada wajen Hajiya kamar yadda akayi Ranar shiyasa ya zauna ya lallabata Dakyar da Sharadin bazai Dade ba Sannan ta barsa ya fito.
Sai da suka Idar da Sallar Isha"i sannan Suka gana da mallam a Falonsa mallam bai nuna mai ya san wani abu ya tambayesa zaman me Saratu take bata koma gidansa ba..?
Sai ya karantamai yadda sukayi da ita Mallam yace"Wannan ba Hujja bane Umaru..ita macece kai kuma Namiji ne Shugaba..Kada ka manta adalci ne aikinka Tsakanin matanka..Kada ka bari Daya ta Rinjaye ka domin Ranar Lahira zaka tashi da Barayinka daya ne yana Rinjayan Daya. kada ka Duba wai Tare kuke achan duk wannan ba Hujja bace..Zaka raba musu kwana ne har Lokacin da zaka koma shine adalci..!
Danmallan kansa na kasa yana gyada kai bai ce komai ba Mallam ya Cigaba da fadin"Na kira ta na mata mgana saboda haka yanzu ka Dauki matarka ku tafi gidanku..Allah ya zaunar daku lafiya..!
Danmallam sai Lokacin ya Dago kansa yana Fadin"Naji Duka mganar ka mallam..Sai dai ina so kamin afuwa Zuwa gobe da zan cika Sati Daya awajen Amina sai na koma wajen Sarood din..!.
Mallam ya kallesa kafin yace"Shikenan daman na Tunasar Dakai ne..Itama akwai Hakkinta akanka Umaru kuma ina yi maka kwadayin Zama mutum adali Allah yayu muku albarka ya wajen ita mamar tawa..?
Fata dai ba wata Damuwa ko..?
Danmallam yace"Lafiya lau mallam..!
Daga haka shuru ya Biyo baya sai Danmallam din ne ya gyara zama yana Fadin"Mallam daman ina so nayi ma Hajiya mgana..Yakaka kakar mijin Aisha da bata koma ba tunda sun shaku da Aminar me zai hana ta koma chan Gidan Aminar su zauna tare..Ga Halin Datake ciki sannan in ina gidan Sarood bazan dinga Fargaba ba..!
Mallam acikin Ransa Hamdala yake yi Saboda yaga kaunar Mamar tasa a cikin Idanuwan Umar.
Kai Tsaye yace"Kayi Tunani mai kyau..Kada ka Damu zan yima Hajiyar mgana gobe sai ta saka Idi yakaita Yakaka akwai kirki da karamci Sosai shekaran jiya ta na nan har Dare muna ta hira da ita..!
Danmallam yayi godiyar har ya mike zai tafi Mallam ya saka Baki ya ka kirasa ya Dawo ya Durkusa a gabansa Mallam ya kallesa Kafin yace"Ya mganar Ka Da Sakina..?
Naji har yanzu baka ce komai ba..Sannan kana jin labarin Halin Datake ciki domin an ce ta kara rasa wannan cikin shima..Allah ya kyauta na gaba..!
Danmallam kansa na kasa yace"Mallam ni bansan komai ba tadai Kirani Sau biyu shekaran jiya ban Dauki kiranta ba..!
Mallam ya gyada kai kafin yace"Kaje kayi Tunani Umaru..Duk abunda ka yanke sai ka sanar dani..Ammh ina so ka Sani ka Bude zuciyarka Dakyau ka gani ko zaka bama Sakina Dama har ga Allah ina Tsausayinta domin Sharrin Marliya ne ya koma kanta Barin Ciki ga mace abun jin Zafi ne..Sannan abubuwa Dadama ba Laifinta bane..Kayi tunani kagani ko zaka iya yafe mata..Ban takura maka ba..Shawara ce Tsakanina Dakai..!
Danmallam kansa na kasa yace"Nagode Mallam Insha Allahu zan karbi mganarka..!
Daganan ya sakamai albarka sukayi sallama ya fito,Shashen Hajiya ya Shiga suka gaisa da yakaka da Hajiya nan yaga ma ya"yan Goggo Yagana sun zo wato yan"uwan Anty Hadiza sun kawo mata kayanta dake chsn da wasu Dake Dake daga mahaifiyarta Dazu da rana suka iso shiyasa bai Dade ba suna gaisawa yayi musu sallama ya fito a haraban gidan suka Hadu da Aba suka gaisa sun dan Taba Hira sama sama kafin ya shige motarsa ya bar gidan shi kuma Aba Falon mallam ya shiga.
Koda ya koma Amina ta cika kiris take jira tayi kuka,Allah ya tsaresa da Jidalinta shiyasa ya kasa gayamata Zai koma wajen Sarood har washegari Suka je asibiti da Duka Fayel dinta na Aaibitin datayi awo a Abuja wajen Dr.Ghali suka je inda ya Taba kaita Farko al"amarin.
Dr.Ghali nata mamakin wannan al"amarin Sha"awa suka basa har ya kasa Dauke ido Daga kansu ganin yadda Amina ke shagwaba Umar na Biye mata ya Dubata yace ba matsala Sai dai Jininta yayi Low sosai taci kayan ganye,Daga asibitin Da suka Dawo suka sake fita da kafa suka Zagayen anguwan saboda kafaduwan Amina su Saki suna Dawowa ba Dadewa sai ga Idi ya kawo Yakaka Murnan sai ya Dauke Hankalin Amina har ya sake wanka ya fita bata Damu ba.
Koda yaje abakin Hajiya Yaji abunda ya Faru da Maamanmu da Labarin yan"uwanta yau sun zo sun Dauketa tana Fadamai irin yadda Duniya ta juyama Mamanmu abaya har ga Allah bai wani Tsausaya mata ba,Aransa ma yasan Kadan ta fara gani
Da yammah ya Dauki Sarood suka koma gidansu batare daya Fadama Amina ba saboda bai son me zai ce mata Amina yadda take da kishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login