Showing 102001 words to 105000 words out of 145917 words
kawai har kan gabanta take yi Ranta Fes da Tunanin Burinta ya Cika sannan tana kan cin Duniyarta ne kamar yadda ta Tsara.
Abunda bata sani ba suna nasu ne Allah ya riga ya gama nasu..Basu sani ba Ranar tonon asirinsu ya kusa zuwa..Dama dama ace suna da sani da Allah wlh kafin Ranar hakan duk zasu gudu kafin bayyanan boyayyun Fuskokinsu.
Bangaran Amare kuma suna gidan su ya jafar Kamar yadda aka saba Su da sauran yan"uwansu su ya Zeenatu ya Abida ya zulaihat da su ya Ikram da su ya Sadiya har sa"adatu bata ware kanta ba wannan karom duk suna Tare ya Aisha Kadai ce bata iso ba,Abida tayi ta Kiranta sai tace mata tana tafe yau komai Dare insha Allahu.
Hanne da Hamida kam sai a hankali duk sun yi wani irin sanyi su Ya Abida nata musu tsiyan Amare,gwarama Sa"adatu ta saki jikinta ana ta harkokin yin Meatpie din walima da ita tunda su ya Abida ke yinsa anan gidan shi da Donut,su damuwar su Daya ayadda biki ya zo ammh ba Amina sannan ai Hajiya ta musu alkwarin Amina zata zo ammh basu ganta ba ko da Safen nan da suka je gidan sun mata mgana ta musu Dariya tace kada su damu Amina Zata zo insha Allahu.
Ya Danmallan kuma tunda suka Dawo basu hadu dashi ba Sunga dai Sakina,shima a shashen Anty Amarya,Sai sarood dake shashen Hajiya tuni Sakina ta Daina janta kusa da ita da sun iso garin zata janye mata sai dai ka ganta zaune bangaran Hajiya tana Bin kowa da kallo in taga mutum kuma ta fara mai Mirmishin ta din nan tunda ba jin abunda mutane ke cewa take yi ba.
Misalin karfe Daya na Rana Hajiya ta kira Wayar Danmaallam yana gida alokacin domin tun bayan da ya kawo Sarrod ya koma ya kwanta Gidan mallam ya cika da Hayaniya damam sun gama mgana da Aliyu kenan shima suna tafe shi da matarsa da ya"yansa sai Jibi asabar zasu koma sai ga Kiran Hajiya daman tunda ya Dawo ban da gaisuwan da sukayi Jiya basu yi wata mgana ba gwara ma mallam sun samu zama shi da Aba sun yi Hira sosai saboda gidan ya cika da Jama"a banda ma shashen Hajiya bai shiga ko"ina ba.
Da Hanzari ya sake yin wanka ya sauya kaya Cikin shigar Wani Farin yadi Dinkin riga da wando na Zamani da Hula,Allah ya taimakesa ko da ya iso ana salla nan masallacin mallam Duk da bai samu duka ba ya samu Raka"a Biyu mallam ma baya nan ya Shiga Cikin Collage din Gumel ta Fce suna da taron da aka gayyaceshi.
Ya Shiga gidan cike da Mutane Kansa na kasa yana gaisawa da duk wanda ya Hadu dashi har Falon Hajiya inda ya Duka yana gaisheta da goggon ninsu na maiduguri,sauran yara yaran matan kuma suna gaisheshi yagana ne tace mai Hajiya na Ciki yasa ya tashi ya shiga sarood na Dakin su Hanne ta shiga Sallah shiyasa bai ganta ba.
Koda ya shiga Dakin Hajiya suna waya da ya Aisha Shi dai baisan me tace ba yadai ji Hajiya na Fadin"Shikenan Allah ya kawo ku Lafiya zaku iya tasowa yanzu..Munyi mgana da mallam kafin ya fita..!
Daganan sukayi sallama shi dai yana Duke agabanta kansa a kasa Hajiya ta gama wayanta ta juyo tana Fadin"Mutanen madina..!.
Kansa ya shafa yana fadin"Hajiya mun same ku lafiya..!
Hajiya ta amsa da Lafiya lai daganan suka gaisa da Tambayan Hidima shuru yadan Biyo baya kafin Hajiya ta gyara Zama tana fadin"Kun yi mgana da Amina tunda ka dawo..?
Kansa na kasa yace"Eh Sau daya mukayi mgana da ita Hajiya..!
Hajiya ta jinjina kai tana Fadin"Daman kan mganar tahowar su ne ita da Amina..Sun gama shirin su ni na Tsaidasu saboda Wani Dalilina..Naso Da sun sauka Amina ta wuce gidanta sai mallam yace bai kamata ba nan zata sauka tukunnah Shiyasa sai na sauya Shawara yanzu dai nace su taho ita da Aishar ne da Aminar sai yakaka da zasu zo tare da Direba..!
Danmallan kansa na kasa yace"Allah ya kawosu lafiya..!
Hajiya ta amsa da Ameen tana Fadin"Yau dai abunda muke Boyewa zai bayyana..Amina Zata dawo ammh ba ita kadai ba da abunda kowa zai yi mamaki..!
Shidai bai ce komai ba kansa na kasa Hajiya tace"Shikenan tashi kaje kiran da nayi maka kenan daman..!
Ba musu ya mike yayi mata sallama ya Fice yana tunanin murnan da Amina ke Ciki jiya da sukayi mgana sai shagwaba take mai kan sun gama shirinsu Hajiya tace su Dakata shi ya Lallasheta da fadin kada ta damu da ita za"ayi wannan sha"anin.
Yau kuma bai samu ya Kirata ba,Zumudin tafiyar ne yasa ko kiransa ma batayi ba sun dai yi mgana da Aisha da Safe kan asibitin da Amina ke zuwa awo sun je sun amso Takardun duka report dinta sannan ya basu shaidar ko a ina Amina zata Haihu in suka nuna wadanan takardun Babu matsala.
Yaji Dadin Hikimar Aminar da Mijinta Saboda shima yana Tunanin ba lalle Amina ta koma ba,Duk da Hajiya bata fadamai ba ammh ai tace gidanta zata Zauna ta Haihu tayi jegonta.
Yana fitowa daga shashen Hajiya suka ci karo da Anty Amarya ta fito Daga kitchen nan suka gaisa har tana cemai bazai shiga ya duba Sakina bane..?
Sakina na ciki kwance Zazzabi ya rufeta bai damu ba yace zai mata waya mata sun yi yawa ya samu ya fice aransa kuma bai yi niyyar kiranta ba ai tasan dashi tun shekaran jiya bata nemesa ba Shima ya shareta ai ba ita kadai garesa ba balle ya Damu sannan Ciki kuma ai ba kanta Farau ba shi Allah ya tuba ma ko ZUMUDI bai yi ba wannan karln to me za"a a nuna mai shi da ke da mai Ciki haihuwa ko yau ko gobe..?
Ai karyar barazana kuma ta kare yadda ta ke wani tsirfa ma mamaki take basa shiyasa tunda suka zo tace wajen Anty Amarya zata zauna bai damu ba Ko a kwalar rigarsa.
Dakin su Uzairu ya shiga suna taba Hiran inda yake sarvice daya ke shima ya Dawo shima da Safen har shamsu ya iso Dazu shima wannan Bikin fa na musamman ne kowa da kowa yana nan Saboda bikin mata ne kuma Sune na layim karshe daga su sai maza su Nazeem in sun tashin yin kenan nan kusa Har Mutanen bazanga mata da basu Cika zuwa ba sun zo wannan karon Bikin su Hamida kan kowa yasan yayi goshi.
Sun Dade suna hira dashi tare sukaci Abincin Rana da Hajiya ta aiko musu dashi Tunda tasan suna cikin Gidan sai La"asar suka fita Danmallam ya bada salla bayan sun idar ne sai ga Aliyu sun iso ya fita ya tarbesa Suka gaisa da Aliyu ya Dauki karamin yaronsu Hammad ita kuma Aliya da yar macen da Cikin jikinta Daya fara fitowa suka nufi Cikin gida.
Sai da ta fara zuwa shashen Hajjya suka gaisa har taga Sarood tana ganinta ta fara bashe mata baki taga wanda ta sani ammh Aliya ko kallonta batayi ba Ko Dadewa batayi ba ta baro Shashen Hajiya zuwa na Anty Amarya wajen sakina daman sun yi waya tun kafin ma su fito Daga gida.
Anty Amarya sai ina ka saka da Aliya take yi ita kuma Sakinar na kwance Dakin su Sa"adatu wai bata jin dadi Zazzabi ne ya rufeta Ammh ganin Aliyan sai ta mike tana wani yamutsa Fuska.
Aliya na kallonta tana Dariya tace"Masu Ciki..Yan Laulayi..!
Sakina tayi far da ido kafin tace"Kedai bari tunda muka iso ban jin Dadi..komai ma baya min Dadi..Chan gidan fa warinsa tadamin Hankali yake yi na baro sa na dawo nan..!
Aliya tace"Sannu sai Hakuri..Zuwa gaba zaki ji Dama dama in Laulayin ya ragu..!
Sakina tace"Allah yasa ya hanya..!
Ina Aliyun da hammad..?
Aliya tace"Suna wajen tare da Umar..!
Sakina tace"Yazo kenan..?
Aliya tace"To nadai gansa a waje fa..!
Sakina tace"Rabona da ganinsa tun shekaranjiya da muka zo nan..!
Bai sake nema na ba. !
Ta fada cikin wani yanayi Aliya tace"To kinsan kila saboda mutane..!
Sakina tace"Waya fa..!
Ai sai ya Kirani yaji ya nake duk wannan wahalan da nake sha duk shine Sila fa..!
Aliya tace"Kuma fa hakane..kimai Uzuri dai ammh ai naga kishiyarki dana shiga Shashen Hajiya sai wani washe min Baki take yi nayi kamar ban ganta ba. !
Sakina tayi tsaki tana fadin"Bar munafuka ita wai ta ganki ta ganeki mana..!
Aliya tace"Ta gane Ubanta..!!?
Aiko taga wulakanci domin ko kallo bata isheni ba..!
Sakina tace"ai tunda muka zo bata kara ganina ba..Na yakiceta ajikina..!
Aliya tace"Ai hakan ya kamata ina Wani Cigaba ka hada kai da kishiya..Duk fa Kirkinta sunanta Kishiya..!
Sakina tace"Ai saboda na sami abunda nake so ne..kuma na samu shiyasa na yakiceta Daga jikina..!
Aliya tace"Wlh hakan ma yafi..!
Daganan suka cigaba da Hirarsu suna ta zagin Sarood Aliya ce ta kalli Sakina tana fadin"Wai ina ita Labarin Kazamar yarinyar nan .?
Sakina tace"Wace wai..?
Aliya tace"Amaryanki mana..Waa ma take da suna..?
Amina take ko wa..?
Sakina ta ja wani Dogon Tsaki kafin ta mike tana Fadin"Ina na sani..!
Nifa na manta ma da ita kwatakwata sai da kikayi mganarta..!
Aliya tace"Wato ma kin manta da ita..!
Ni fa ina mamakin ina Hajiya ta kaita..?har Aliyu na Tuntuba yacemim bai sani ba bama suyi mganar da Umar ba. !.
Sakina tace"Ai hashashemu ya tabbata. inaga ba auran nan..!
Aliya ta zaro ido tana fadin"Ta ya akayi kika sani..?
Sakina ta Bude kofar Tiolet tana Fadin"To in da auran da baki ganta ba. ?ai ba haka ake aure ba Aliya.
Bari nayi alwala ban yi sallah ba .!
Aliya ta bita da kallo tana fadin"Nima ki fito nayi muna hanya ta same mu..!
Ammh a kasan ranta tana Tunanin Ta yaya Umar zai saki Amina..?
Hajiya da mallam kuma sun sani basu ce komai ba..? Gaskiya tunanin hakan bai zauna mata ba sai dai in wani abun ne Dabam ammh banda mganar Rabuwa.
Sakina na fitowa itama ta shiga tayi alwala sukayi sallah bayan sun idar Aliya taci abinci suka kimtsa Sakina tace su leka wajen Walima ana ta Tafiya,Koda suka fito duk an watse har Anty Amarya ta tafi da wasu yan"uwansu Daga Dutse Hajiya ce kadai ya rage bata tafi ba sai wasu yan maiduguri,Sakina gaba sukayi ita da Aliya sai a hanya ne suka hadu da su Zulfa da Yara sun dauko musu waina da za"a raba awajen Walimar suka Dumguma zuwa haraban makarantan koda sukaje har an fara Amaren ma sun iso sun yi shigar bakaken jallabiya da Farin Hijabi Sa"adatu ne dai Fuskarta acike ammh Hanne da Hamida sai kwarmin ido,sun yi wani Zuru zuru dasu su ya Aisha ne kan gaba ke ta Hidiman Baki.
Aan basu kyauttuka Hamida an bata na Tajweed da Kira"a am bama Hanne na Larabci da sanin Nahahu sai Sa"adatu ita kuma na zuwa makaranta ba Fashi Hanne sai da tayi kuka sun farota da Amina ammh yau ba ta awajen da zasu yi bankwana da makarantar su haka ma Hamida sai da sukayi kuka,su ya Abida duk sum san kukan da suke yi na rashin Amina ne suma ai sun damu sai dai ba wanda yama Hajiya mgana, ba Tarbiyansu bane yin katsaladan a Hukuncin babba sai dai su hanne sun Fada musu Hajiya tace zata zo insha Allahu.
Su ya Zeenatu aka bari da lallashin su Sai da suka saki ransu,Sannan suka koma Bangaran sallaman Baki su da sauran yan ajinsu na Hadda sannan kawar Hajiya tazo tayi ma Amare nasiha sosai sai shidda na yammah aka tashi Sakina anan suka Hadu da Sarood tana ganinta ta manne mata sai Hararanta suke ita da Aliya ita ko Allah Sarki bata sani ba tana tare dasu da zuciya daya ne,Har Hajiya tazo wajen Walimar chan gabda za"a tashi mamanmu kuma ai suna gaba gaba ita da Anty Amarya sun saka kayan alfarma Anty Amarya Shadda ta saka itama mamanmu shadda ce taji aiki ammh kalan kowa Dabam kafafunsu sun ji Lalle kamar wasu yara har yan gusai nama mamanmu Tsiya ta koma yarinya tace a wajen Sa"idu ai ita yarinya ce Danya sharaf
Sai Dariya take yi cikin Nishadi suma suna tayata da tsiyan da suka saba mata musamman ma abokan wasan Aba Na gusai.
Ana tashi daga wajen walimar aka Dumgumo zuwa gida Amaran dai Gidan su ya jafar suka koma su da ya Zeenatu da Abida sauran kuma sun koma gidan baba mallam wasu kuma gidan Aba Dayake ana ta kiran sallar mangariba suna komawa sai kowa ya fara shirin salla a waje kuma su ya Danmallan sunyi alwala suka Shiga masallaci duk da mallam ya Dawo shi ya bada salla da mangariba suna da Karatu yasa duk suna cikim masallacin suna Sauraran karatun Baba Mallam Har Nazir da shima Gabda mangariba ya sauka Daga Lagos.
Adaidai Lokacin misalin karfe bakwai da yan mintina na Dare Motar Usman Mijin Aisha prado mai lambar Abuja ajikinta ta yi Diran cin Taya a kofar gidan Baba mallam Dake Dauke da Haske Tar domin an kunna Gen da wuri saboda Sha"anin da ake ciki ko"ina Haske ya bayyana sai dai kofar Gidam ba kowa duk suma masallaci Tsit mata kuma duk suna Cikin gida.
Ya Aisha ta fara fitowa bayan Direba ya Bude mta kofar Mota ita agidan gaba ta Zauna yayinda Amina da Yakaka ke gidan baya.
Tana fitowa tace"Salihu bude booth ka Fito da kayan Dake Ciki Duka..!
Ba musu ya amsa mata ya nufi Booth din ya Bude ya fara Fiddo da akwatunan Amina Sabbi yana jerawa a kasa ita kuma Aisha ta Bude bangaran da Yakaka take tana Fadin"Yakaka Bismillah mun iso..!
Yakaka ta Fara fitowa tana Salati Lokaci Daya tana Fadin"Mun isa barka..Tafiya ai yankin azaba ce..!
Lokaci Daya tana kare ma gidan mallan kallo da yanayin anguwam ta Furta"Masha Allah..yau gani agidan mallam..!
Take fada daidai Lokacin da Amina ta Fito Daga Motar kofofin Hancinta na Budewa da Shakkar Iskar gumel din Data Dade bata shaka ba,Gabadaya Sai taji ta kamar ba ita ba,Sai taji kamar bakuwa ce ita tana kallon kofar gidan Mallam da nasu gidan wasu abubuwan da suka shude a baya suna Dawowa mata Daki Daki kamar yanzu komai ke faruwa Sai da taji Hawaye sun kawo mata.
Tana Sanye da Doguwar riga Baka na Saudiya cikin Tsaraban Danmallan ne sai jan hijabin Dake jikinta Tunda adon Rigar ja ne,hijabin gwiwarta kadai ya Rufe Cikinta gashi nan ya bayyana Kafarta sanye Cikin Takalmi mai Saukakken Tudu kafafun sun kara kumbura saboda Zaman mota Fuskarta ta kara Cika tayi kwaba kwaba kamar Danyen Nama.
Duk wanda yasan Amina abaya in ya ganta yanzu da wahala ya ganeta komai nata ya sauya.
Tsaye kawai tayi tana bin gidajen nan guda Biyu data yi Rayuwarta aciki da kallo acikin Ranta tana jin wani Farimcikin da bata taba ji ba Dazu suna Hanya sun yi mgana da Danmallam yace mata dukkansu matan suna wajen Walima har suka iso Bata kara mgana ba taso ta samu Walimar su Hanne ammh Allah bai yi ba.
Tana jin ya Aisha na cema Yakaka bari ta kira waya a daukan musu kaya tunda ba yara a wajen kawai sai ga Ya Shamsu ya fito Daga gida zai shiga masallaci yaga ya Aisha ya tsaya suna gaisawa tana Fadin"Shamsu yaushe ka zo..?
Yace"Dazu da yammh ya Aisha sannun ku da zuwa..!
Ta amsa shi kuma ya juya yana gaida Yakaka ta amsa Cikin Fara"a.
Ya Aisha ke Fadamai kaya ne daman za"a dauka don Allah ko zai taimaka ya kira mata su Akilu su Daukan mata,Yace to bari yayi musu mgana suna Cikin masallaci da Hanzari ya tafi ya kirasu sai alokacin ya Aisha ta Daga kai tana kallon Amina Data jingina jikin mota batace komai ba..
Cikin kulawa tace"Amina kari so mana..Ko jikin ya rike ne zaman mota ko..?
Amina sai alokacin ta tako zuwa wajensu kafin tayi mgana Yakaka ta chabe da Fadin"Dafa gajiya..Ko mu da bamu da komai mun gaji ballatana ita mai Lalura..Jiki fa ya rike sai dai mun shiga ta samu ta watsa ruwa a shafe Jikin da man zafi taji Dama Dama..!
Amina ta tura Baki tana Fadin"Man zafi kuma yakaka..?
Yakaka ta Harareta Tana fadin"Shine zai sakar miki jiki har kiji Dadi wannan kumburin da kikayi duk ya Saki..!
Amina bata samu bakin mgana ba Sai ga Shamsu ya fito bayansa Akilu ne da Zubairu har suka kariso suka gaisa da Ya Aisha da Yakaka basu lura da Amina ba sai da Ya Aisha ta nuna musu Kayan da zasu shigar musu dashi Ciki,Saitin akwatina guda Bakwai sai kuma wani saitin mai Hudu suma Dabam sai kayan su da kuma wasu kaya a kwalaye acikin wani babban Buhu.
Ya Shamsu ne ya fara ganin Amina sai ya Tsaya kawai yana kallonta kamar Amina kamar ba ita ba ita kuma ganin Haka yasa tayi mirmishi tana Fadin"Ina yini ya shamsu..!
Da Sauri ya kara ware ido yana kallonta har su Akilu suma sai alokacin suka ganta da sukaji muryanta ganin ya kasa mgana ne yana kallonta Daga sama har kasa ga Muryan Amina sannan wannan kuma gata babbace ga kuma ciki ajikinta Sai da ya Aisha taga haka sannan tace"Shamsu Amina ce fa ke gaisheka..!
Dukkansu kusan Hada Baki sukayi wajen Fadin"Amina..?
Cikin Sigan Tambaya Yakaka tayi Dariya tana Fadin"Sun ga ta zama uwar mata ga Ciki ga shi ta yi kiba..!
Amina Mirmishi kawai tayi kanta na kasa kunya taji da Yakaka ta ambaci Ciki su kuma kawai ita suke bi da kallo mamaki ya kashesu.
Shamsu har yana cin Tuntube Daya Dauki kaya zai shiga gida yana waige su Akilu ma mamaki duk ya kamasu wai Amina ce ta koma haka..?
Kuma har da Ciki ikon Allah..!
Harda Salisu Direba a masu Daukan kaya da wasu matasa da suka gani zasu shiga masallaci Ya Aisha ta rokesu suka Daukan musu ita sai ta Dauki karamar akwatinta da na Amina yakaka kuma ta Dauki wata babbar Leda Amina bata Dauki komai ba Saboda yanayinta suka bi bayan su Shamsu zuwa Cikin gida har megadi yana masallaci wajen karatun mallam.
Su ya Nazifa da su ya Fatima duk suna Tsakar gida wajem kitchen ana ta Hidima hada Miyan gobe sannan wasu kuma suna ta gyaran kajin da aka kawo daga wajen Gyarasu,Hajiya na Shashenta Hajiya Nasara ne ke Madafin tana nuna ma su lami yadda komai zai tafidaidai sauran matan kuma duk suna Dakunansu kana dai jin Tashin Muryoyinsu suna ta Hira da Shewa.
Sai ga su shamsu na Shigowa da kaya ya Fatima ce ke fadin"Shamsu wannan sabbin akwatin fa Daga ina..?
Ya Shamsu