Showing 39001 words to 42000 words out of 145917 words
bata lafiya..bari na tafi..!
Haj Uwa tace"Bazaki tafi ba sai kin sha wani abu muje..!
Ta kaita har falo ta zaunar da ita kan kujera tana fadin"Umaru dai ana Madina ko..?
Amina tace"Uhm..!
Daganan bata kara mgana ba mamaki abun ke bata Duk da Tasan Hajiya uwa bata da matsala ammh bata janta ajiki kamar na yau sai kawai taji bata yarda da ita ba.
Tana nan zaune sai gata ta fito da Jug da kofi ta kawo gaban Amina ta ja Center table ta dora lokaci Daya tana Fadin"Lemon kankana nayi tun Safe kinganshi nan yayi sanyi zaki ji Dadinsa Amina..!
Amina ta yi kasake tana kallonta ganin haka yasa ta Zauna gefenta tana Fadin"Kada ki damu nan Umaru ke karyawa indai yana gari dagashi har matansa abinci shashena basu da Shamaki dashi..!
Amina dai batace komwi ba ta Dauka ta Tsiyaya kadan Ta Daga kofin takai Bakinta Hj.uwa na kallonta zuciyarta Cike da Farinciki zata aiwatar da Tsarinta Cikin Sauki kamar yadda ta Saba.!
Amina acikin ranta taji bazata sha wannan abun ba,ba domin tana Zarginta ba sai domin cikinta ya cika sannan in ta fada mata bazata yarda ba Sai dai kamar an kwato bakinta Ta Furta.
Bismilallahi..!
Sannan ta Kurba kadan Haj.Uwa taji kamar an sakata acikin Aljannah Ta Bude zatayi mgana kenan Kukan Umaima ya katseta tatashi da gudu tatafi Dakin tana cema Amina tana zuwa..!
Tana shigewa Amina ta Dawo da na bakinta wanda bata gama Hadiye ba jin wani makaki a makogwaronta waige waige ta farayi ganin Haj.Uwa bata fito ba yasa tatashi Sadaf Sadaf ta shiga Kitchen dinta ta Juyesa a wajen wanke wanke taga yana wani yauki mamaki ya kamata da sauri ta Bisa da Ruwa ya wuce sannan ta samu ruwa ta Kuskure bakinta ta koma Falo da Sauri ta ijiye kofin ta zauna kenan sai gata fito Idonta kan kofin tana ganinsa ba komai ta wani Saki ajiyar rai kafin ma ta zauna Amina ta mike tana cemata zata tafi Cikin Murna da Cikar Burinta tace"To shikenan Aminatu Sai na shigo shashen Hajiyar..!
Harda Dari biyar ta bama Amina tace bazata karba ba ta matsa mata ta karba Amina ta fice cikin mamaki sannan uwa uba kuma Makogwaronta bai yi mata Dadi ba Tunda tasha wannan lemon
Tana Fita Haj.Uwa ta Daga Kofin kafin ta Sheke da wata Dariya a Fili ta Furta"Kema kin Hau keken beran kamar yadda na Dora na bayanki..!
Sai ta wani Saki shewa Duniya Sabuwa..burinta ya kusa cika Nazeem Sauransa wattani kadan ya gama makaranta Uzairu kuma ya gama Degree dinsa na farko Services ma yake shirin tafiya ta fara Hango kanta a matakin datake Wahala Shekaru masu yawa.
Abunda bata sani ba Kafin nata Tsarin Ta manta Allah ma da nashi..?
To nashi ya riga nata sannan abunda Allah ya rubuta shi zai faru wannan gudan jinin sai ya fito Duniya wannan Cewarsa ne..!
Amina haka taje Shashen Hajiya ba cikin natsuwarta ba cikinta nata Juya mata sai dai bata cema kowa komai ba suka gaisa da Hajiya tana ta Tambayanta ko ba matsala tace mata eh Dakin su hanne suka shige suna Hira Amina ta kasa natsuwa sai da ta shiga Tiolet ta dinga Tura Hannunta Cikin baki sai da ta samu Wannan dan Lemon daya shiga Cikinta ya fito harda Abincin data ci sai da ta Amayar dashi tayi sauri ta wanke wajen ta fito su hanne suna chan suna Hira basu ji karan Kakwazon aman nata ba.
Sai alokacin ta samu salama.
Allah yayi ikon sa Ko tasha wannan nganin bazai zauna acikinta ba sai ya fita saboda ba koda yaushe kake aikata abu kaci nasara ba daga Lokacin daka fara Hango nasara Daga lokacin kila Lokacin bayyanan wasu abubuwan ne.
La"asar nayi suka shirya suka tafi islamiya irin su mariya sai kallon Amina suke domin Sa"adatu ta Fesa musu Amina ta auri yayansu mijin Anty Sakina to sanin Halin Amina Shiyaasa ba wanda ya Tareta da mganar har aka tashi.
Suna Dawowa gida Amina taso ta Tsaya wai taga Aba da Mallam Hajiya tace maza ta wuce idi ya maidata gida Mallam yana Hadeja sun je bude wani masallaci ba yanzu zai dawo ba shi da Aba Dole Amina taje tayima mamanmu sallama ko mangariba agidan ta tayi ta sai kunci take yi.
Aranar dai bata Hadu da Sakina ba sai Washegari da Idi ya maidota da yammah ta ganta afilo suka kalli juna kasa kasa kowacce ta kauda kanta bata Damu da abinci ba, tana ciko Cikinta Kafin ta Dawo da Safe kuma Tea kadai tashe sha watarana ma haka take Tafiya.
Asatin nan kaf haka Rayuwar Amina ta cigaba da gudana kudin hannunta sai da ta gama kashe ma su hanne gbadaya sannan Hankalinta ya kwanta Ranar jumma'a daga makaranta bata koma gida ba Ta jira sai da Mallam da Aba suka Dawo ta gaisheshesu Aba sai mamakin Amina yake a idonsa yaga kamar ta kara mishi girma sannan tayi hankali Kadan Mallam kuma kamar ya maidata Ciki saboda so Shiyasa bata koma gida ba sai Ranar Lahadi da yammah Mallam yace tayi kwana Biyu saboda Har da Hajiya bata so ba Ammh Tunda mallam ya saka baki shikenan.
Jafar kuwa sam ya manta da Kudin wayar da Danmallam ya barmasa ya siya ma Amina sai da Umar din yaji Shuru ya kirasa sannan ya Tuna Hakuri ya basa aranar bayan ya Dawo Daga wajen aiki ya biya ya siyama Amina waya karama Nokia sai washegari ya siya mata layi yayi mata Rigister sannan yazo ya kawoma Hajiya wayar Tunda Aminar na makaranta Hajiya ita har ta ma manta da Batun wayar sanda ya kawo mata Cikin wardrope dinta ta saka wayar sai kuma Allah ya mantar da ita har Amina ta dawo ba ta bata ba.
Wajen kwana Hudu da Jafar ya sanar ma da Danmallam ya siya waya ya kaima Hajiya ta bama Amina sannan ya Turama sa Layin Aminar sai dai tun Washegarin ranar yake ta faman kiran wayar a kashe sai ya fara Tunanin kodai Hajiya bata bama Amina wayar bane.?
Shi kuma ya kasa Hakuri ya rasa meke Damunsa Daidai da rana Daya Tunda ya Dawo madina Zuciyarsa bata manta Amina ba.
Wannan yarinyar daya ke kira kazama Kwaila itace ya kasa mantawa da ita ko Sakina da suka Dade tare baya jin nauyi da wani Damuwa da ita akan yadda yake ji kan Amina wani al"amari ne da Ubangiji ya barma kansa sani abu Daya ya sani yana matukar son yaji muryanta sannan yaji lafiyanta baya fatan ace yau yabar baya da kura.
Sannnan yarinyar itace ya Hada Abu mai muhimmanci da ita abunda bai Taba Hasaahen zai iya Faruwa Tsakaninsa da ita ba..
Abunda bai sani ba Addu"an Hajiya da Mallam ne Allah ya amsa sannan Addu"ar yaya ce Allah ya amsa ya Amintar da Ruhin Amina da Umaru waje Daya..Aminci na har Abada..!
*Janafty**TFZB2010*
*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*
*Bayan kwana biyu..!*
_Area:Prince Naif ibn Abdulaziz Road,Aljami"a P.O Box 170,Madina Saudi Arabia_
Shigowarsa kenan Cikin kayataccen Office dinsa mai girma da Fadi yana Hawa na Hudu ne a bangaran ofishin Malaman makaranta ta Madina bangaran Shashin Qur'an and islamic Studies babban Shashi ne mai Dimbin Tarihi a cikin babbar Jami"ar ta Musulunci Dake madina.
Littafan hannunsa ya zube bisa Babban Tuburin dake cikin Ofishin kafin ya samu waje ya zauna Hular kansa ya cire Lokaci daya yana shafa Sumar kansa data fara Tohowa.!
Gajiya ce ajikinsa domin yau tun Safe ya bar gida yana da ajin karfe takwas na Safe zuwa goma sannan bayanan ya shiga na goma zuwa sha biyu daganan kuma suna da meeting da zasu yi na malaman shashin Dayake koyarwa gabadaya
Sakamakon yau Alhamis ya tashi da azumin Lada kamar yadda ya saba so yake ya tashi ya isa babban masallacin Cikin makaranta yayi karatun Qur"ani kafin lokacin Sallah yayi ammh ya kasa tashi kasala Tare da Gajiya sun Taru sun lullubesa.
Kansa ya kwantar kan kujeran Dayake zaune idanuwansa suna lumshe kamar mai jin barci nan kuwa ba barci yake ji ba Tsabar Tunanin abunda ya faru tsakaninsa da Sarood jiya da Daddare ne ya Addabesa
Shi bai taba Daukan matsalan sa da Sarood mai girma ba sai jiya daya kara jaraba Kusanta ta abu yaci tura kamar dai baya da ya riketa ajikinsa tafiya ta fara tafiya sai yaji komai ya koma ya kwanta a duba da abunda ya faru tsakaninsa da Amina ya Dauka Komai zai yi daidai tsakaninsa da Sarood sai kuma yaga akasin haka,Bai taba Daukan abun da Serious ba sai jiya Saboda abun kamar zai yuyu sai kuma abu yaki yuyu shiyasa wani Lokacin baya son rabarta kar yajamata matsala tunda ita macece Tana da Rauni Fiye dashi sannan shi yana da wata matar ita fa..?
Shi ne kadai mijinta kuma Wanda zai Biya mata Bukararta in ta taso.
Ajiyan ya dauka komai yazo karshe Ganin yadda abun nasu ya fara kamar gaske sai dai ina Yana zuwa gabar sai komai ya kwanta yaji bai iya Tabuka komai abaya ya Dauka Sha"awan ce ke Daukewa shiyasa girman nasa bata Mikewa alokacin ammh Daga Jiya ya fara Zargin da wani abu Saboda shi kanshi yayi mamakin yanayin da ya shiga jiya da Taimakon addu"a ne kawai ya iya Sarrafa kansa.
Sarood kuma kwana kuka tayi bai ga Laifinta ba tayi hakuri wajen wata bakwai ba wani labari Tabbas akwai Cutarwa acikin zamansa da ita Dakyar ya samu ya lallasheta bayan ya mata alkawarin zai Binciki kansa Domin ya sama musu mafita da wannan Tunanin ya barta agida ya fito zuwa makaranta ya kasa samun Mafita,ya rasa da wa zai Tattauna wannan matsalan da Farko kamar ya Kira Mallam kunya da nauyi bazai barsa ba yayi Tunanin Baba Sa"idu kuma sai ya fasa Tuna yanzu ba Da bane..In abaya yana yayansa ne yanzu har da karin Surukanta Tunda ya aura masa yarsa ta Cikinsa da Kunya ya Kirasa yana Fadamai bai iya kwanciya da wata mace Abokiyar zaman yarsa duk da yasan Waye Baba Sa"idu auran Amina bazai taba Chanza Tsakaninsu ba Sai dai shi din ne Bazai iya ba yana jin nauyi,Hajiya kuma ba wannan Sakewar Tsakaninsu,koda ma akwai ita uwa ce bazai taba iya fadamata wannan mganar ba Aliyu ne ya fadomai arai aboki kuma Amini garesa da shi kadai ne ya kamata ya Tattauna wannan matsalan dashi.
Shawaran kiran Aliyu ya Zauna aransa bai Tsaya ba ya tashi Zaune Dakyau ya Fiddo wayarsa cikin Aljihun Wandon Pakistan din Dake jikinsa kafin ya kira lambar Aliyu layin Amina ya kara kira wanda Jafar ya Turo masa ammh kamar kullum ana Kara fadamai wayar tana kashe ne. damuwarsa ba Daya bace har da Damuwar rashin jin Aminaa har Jafar ya sake kira a jiyan yana kara tambayansa ko ya kaima Hajiya wayar..?
Jafar ya kara Tabbatar mai da wlh ya kaima Hajiya wayar ta kuma Ta tabbatar mai zata bama Amina wayar sai dai baisan meyasa har yanzu bata bata ba ammh zai je ya mata mgana sai Danmallam din ya hanasa yace zai kirata da kansa shi kanshi Jafar yayi mamakin yadda Danmallan din ya Damu da sai an bama Amina waya wannan yarinyar da baisan yaushe zatayi Hankali ba ko Shekaranjiya ya ganta sun dawo islamiya suna tafe ita su Hamida sai Mgana take cikin ihu Suna bakin masallaci kofar gidan Baba mallam har sai da Nasir ya kada baki yace Amina in aure bai gyara ba to bazata taba yin hankali ba shima ya yarda da mganarsa..!
Bai kira Aliyu ba kamar yadda ya kudira daga farko sai ya maida akalan kiran nasa ga Hajiya, mallam sun yi mgana dashi da Safe agogon Dake kafe a afishin nashi yabi da kallo yaga karfe 12 da wani abu na rana yana Tunanin achan Nageria yanzu Tara ne da wani abu na Safe.
Wayar Hajiya ta shiga gabda zata katse ta Daga kiran cikin Sallamarta ya amsa mata Cikin Ladabinsa kafin ya Fara gaisheta ta amsa tana Fadin"Lafiya lau Danmallan ya madinar da wajen aikin ka..?
Ina Saratu ina Fatan tana lafiya..?
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"Duk muna Lafiya Hajiya..aiki kuma alhamudulillah cikin Nasara da addu"arku..!
Hajiya tace"Masha Allah Allah ya taimaka..Allah ya kare ka Dammallam ya baka Zuru"a Dayyaba..yadda kake mana Biyayyah Allah ya jikan ka ya baka mai jin kanka kaima..!
Addu"a hajiya yasa yaji kamar yayi kwallah kaunar Mahaifiyar tasa na kara shiga ransa.
Cikin muryan sa mai cike da Zati da Haiba yake amsa mata da Ameem Ameen.
Mallam da mutanen gidan ya tambaya tace duk suna Lafiya kafin yace"Hajiya yau she ne tafiyarki maiduguri.?
Hajiya tace"Satin na sama ne zan tafi inaga Ranar Laraba..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kaimu zan turo ma Jafar sako..Ki kaima Goggo ta kara Allah ya bada zaman lafiya..!
Hajiya cikin Farinciki tace"Angode Allah ya kara Wadata Allah ya Dafa maka..!
Ya amsa mata da Ameen kafin su yi shuru na wani Lokaci jin shurunsa yasa sai ta Fahimci yana so yayi mgana ne.
Cikin Dattakonta tace"Danmallam me kake so kace ne..?
Ya sosa kansa kamar tana gabansa kafin yace"Hajiya jafar yace ya kawo miki waya ko..?
Hajiya tayi yar Dariya kafin tace"Eh wlh ya kawomin tun kwanaki na Shafa"a ne ban bama Aminar ba..Dayake bata zama Da sun Dawo makaranta abinci kadai suke ciki sai su tafi islamiya da sun dawo kuma nake sawa akaita gida ni kuma Shaf na manta..Ammh bari in ta Dawo yau zan bata insha Allahu..!
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"To nagode Hajiya Allah ya kara girma..!
Ta amsa da Ameen Daga haka sukayi sallama Hajiya ta zauna gefen gadonta Tana kara nazarin meyasa Danmallam ya Damu da Amina ta rike waya Daga baya alhalin ita ta kawo Shawaran siyan waya Daga baya da suka Tattauna da mallam sai ya nuna mata illar hakan saboda Har yanzu Amina yarinya ce sannan Karatu ne agabanta,in ta rike waya yanzu zai Shagaltar da ita daga karatunta in Saboda su rika mgana da Mijinta ne ga wayarsa ko ta Hajiya duk wacce shi Umarun ya kira zai yi mgana da Amina shiyasa bata maida kanta kan bama Amina wayar ba ko ayanzu ma Datace mai zata bata tadai cemai ne kawai ba domin zata Tsallake Shawarar da mallam ya bada ba.!
Danmallam kuwa suna gama waya da Hajiya sai ga kiran Sakina ya shigo Yana ma kokarin kiran Aliyu ne kamar bazai Dauka ba sai kuma ya Kashe ya Kirata Tuna yau kwana Biyu basu yi mgana ba Shifa har yau Haushinta yake ji kan abunda tayi mai In ya tuna yadda ta kulle ko"ina ta tayi tafiyarta shi abu daya ya Damesa yadda ta tafi ta bar yar Mutane acikin gida in da yunwa ya kamata ko kuma wani abu ya Sameta ai da ya shiga uku wajen Hajiya da mallam kila sai sun kusa mai baki.
Sama sama daman yake da ita in ya kirata shima saboda sauke Hakki da Nauyin Dake kansa ne ba da domin haka ba sai ta kara Raina kanta.
Tana Dauka ko Sallama batayi ba ta Fara fadin"Habibi..!
Rai ya bata kafin yace"Bana fada miki..Ki daina daukan wayata baki min Sallama ba..?
Tuna haka yasa tayi Saurin mai Sallama ya amsa mata yana tambayanta lafiyanta tace"Lafiya lau Habibi ya aiki..?
Yace"Alhamdulillah ya naji kamar kina kwance ne..?
Gyara kwanciya tayi kafin tace"Wlh kuwa ban tashi ba..Tunda nayi sallar asuba na koma barci..!
Cikin mamaki yace"To Haka Aminar ke tafiya makaranta bata yi kari ba kenan..?
Sakina ta bata rai kafin ta tabe baki Tace"Wacece haka..?
Yana jinta sai bai tanka ba Sanin Halinsa yasa tace"Kace min wannan kazamar matarka taka..Ohon mata Daman na Fada maka bazan dinga mata Bauta ba, ba zamanta nake yi ba..!
Sai kuma yaji bai ji Dadin sunan Data kira Amina ba Duk da shine silar saka mata sunan sai yaji bai Dace ba Domin karshen kazanta kenan ya Ratsa Amina ahakanta,aiko kazanta ya kare.
Tattare naman goshinsa yayi bai yi mgana ba yana kokarin Daidaita yanayinsa Sakina ta cigaba da Fadin"Da Safe ake zuwa Daukanta makaranta ni bana ma sanin Tafiyarta..Sannan bata Dawowa sai yammah ranar jumma kuwa in tatafi makaranta da saafe sai Lahadi da yammah take dawowa sai mu yi kwanaki bamu hadu ba in ma mun Hadu bata min mgana sai kallon banza Habibi yarinyar nan ta gama Rainani bata da kunya Ranar fa Har Zagin Ubana tayi bayan tafiyarka ba Dadewa..!
Yana jinta bai ce komai ba aransa yasan Amina zata aikata A dan Sanin da yayi mata da labarinta dayaji Sama sama Zata aikata sai dai bai yarda ba Sakinar ce ta fara Zaginta ba yasan ta Sarai Itama Sakinar bata da Hakuri.
Yana jinta tana cigaba da Fadamai Rashin mutumcin Amina shidai bai ce komai ba illah"Kiyi hakuri zan kirata zan mata fada..!
Sakina tace"To tana da waya ne..?
Kai Tsaye yace mata"A"a chan gida zan kira abata na mata fada..!
Sakina taji Dadi yasa ta gyara kwanciya tana kara shigewa Cikin blamket tace"Habibi yaushe zaka zo ka Daukeni..?
Ni in bazaka zo ba sai Su Jafar su Nemin Visa na taho..!
Yana jin mganarta yamata shuru Sai da ta fara magiya tana Fadin"Don Allah Habibi kayi Hakuri na tuba nabi Allah na bika..Wlh Daga yau bazan kara saba Umarninka ba..!
Ta karishe Fada Cikin kukan Shagwaba Saboda ko jiya sun yi mgana da Anty ta tabbatar mata da cewa mallam ya sanar da ita Umar zai zo ya Dauketa Dolensa..!
Shiyasa ta tadamai da mganar ita a Tunaninta komai ya zama yadda suke Fata abunda basu sani ba ba kowani Lokaci Allah ke basu nasara ba akwai lokacin da aikin da suke da yakini a kansa zai basu mamaki..!
Sai da ya gama jinta sannan yayi gyaran Murya yana fadin"Sakina na Fada miki abaya zan kuma kara Fadamiki a yanzu..in har ni mijinki ne mai baki Umarni ki bi to bazaki Dawo madina yanzu ba..Sai nan gaba in kin gaji da zaman gumel din..!
Sakina jikinta ya fara rawa gabanta na Fadi ta ce"Habi..!
Bata karisa ba ya katseta da Fadin"A wanchan Lokacin sai da nace kada ki zo..Kika jin mganata kikace sai kin zo..Biki nawa ake yi baki san zaki je ba Zan ce miki ki shirya mu taho..?
Abaya bake kika bani Shawaran Dauko ki na kawo ki garin nan ba Ni nayi Ra"ayin haka,kamar ni nace