Showing 96001 words to 99000 words out of 145917 words

Chapter 33 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83979

ya bata kudi 20k da zata tafi da harda kayan abinci yace ta tafi dashi gidansu tana ta godiya idi ya kaita washegari bai kwana ba Aranar ya Dawo.


Cikin Satin da mallam yayi ma su Hajiya mganar auransu hanne Tuni Labari yakai ko'ina tunda su hannen har masu auran dake wani garin iyayansu sun fada musu hanne da Hamida Hajiya ta kirasu ta Fada musu duk da daman ai susan haka zata Faru ammh sai da jikinsu yayi sanyi aure fa?tunda sukaji mganar basu da wani Walwala daman Amina na nan ne itace Cikin kowani yanayi bazata taba bari su damu ba Jidalinta kadai ai ya Ishesu Allah sarki Amina suna kewarta sun gaji da jiranta da saka ran Dawowarta har sun cire rai ma.
Bangaran Sa"adatu kuma kuka ta Dinga ma Anty Amarya wai bata son aure yanzu sai da Anty Amarya ta kusa Dukanta sannan ta kyaleta Domin ko ta kai wacece ita bata isa taja da Umarnin mallam ba Sadiya yayarta Anty Amarya ta Fadamawa ita kuma ta Kira waya aka bama Sa"adatun ta mata fada shiyasa Sa"adatun tadan Saki ita kanta Anty Amarya bata so ba ammh to ya ta iya..?
Mallam in ya Fadi mgana ai bamai Tada ita kuma sai Allah...
Mamanmu da Aba ya Fada mata Murna ma ta Farayi zata yi Biki na kece raini wajen aurar da autarta hamida Saboda Tasan mallam gangariyan mazaje masu Nagarta yake aurar da ya"yansa da nasu garesu Shiyasa bata da wata Damuwa in akwai abunda Hajiya da mallam ke yi suna Burgeta wannan Sadaukarwan nasu ne, basa numfasawa sai sun ga duka ya"yan agidan auransu mai Cike da Nagarta ne Shiyasa da Anty Amarya ta Kirata tana Korafin auran yayi kusa sai da Mamanmu taji Haushinta da Tunanin tana Bakinciki to in ba Haka ba menene. ?
Yara sun gama karatu to me zasu jira ai sai aure ammh tana neman ta nuna Bakinciki akan hakan,Sai dai bata Damu ba sanin ko me Anty Amarya zatayi Mallam dai bazai sauya mgana ba Sannan ai ita kakarta ce ta yanke saka Tunda tana ta amsan kudade wajen Aba da sunn siyama Hamida yan kayan kitchen tunda kayan gado da Sauransu mallam ke musu kowa ya sani ai ita fa Duniya sabuwa aranta tasha Fadin ko yanzu kasuwa ta Watse mata ai dan koli yaji Riba...


Har Abuja sun ji Labarim auran su Hamida da hanne watan Gobe Aisha da kanta ta fadama Amina aranar Amina wuni tayi bakinta har kunne Domin ta Jiyo kamshin zuwanta Gumel sai dai takaicinta Daya bata nan ai da mutane sun ga Hura Hanci a Bikin Hamida da hanne ko su ya Abida sai ta rama suma wulakancin datake musu in ana Biki ita ko Cikin jikinta bata Duba ba hango kanta kawai take suna Kara"i ita dasu Hanne Tun kuma Daga ranar bata da wani Hira sai wannan Bikin yakaka har ta gaji da Haddace Labarin Bikim nan a bakin Amina shi kanshi Danmallam Topic din kenan kullum sukayi waya sai tace ranar Bikin su Hanne Hmm kaza kaza yana so yace da Cikin zaki yi kaza..?
Yana tsoron ya ballo ma kansa Ruwa sai dai yana Tausayinta in Hajiya tace bazata zo ba ya zatayi..?
Ai ya tabbata wannan Jidalin na Amina in ta fara shi ko mallam to sai kila sai dai shin zai iya lallashinta yadda taci burin Bikin nan ya tabbata bata ci burin haihuwarta haka ba.
Shima ai yasan da labarin bai Fada mata ba Tunda Mallam ya fadamai haka Hajiya ma duk sun yi mganar su sakina ma bashi ya fada musu abakinsu ma yake jin suna kara zencen yace musu Hakane Sakina sai Murna take yi Nageria tayi kira abu nasu to Har Sarood ta Shirya wannan karon sai tazo itama shi dai ko ci kansu bai taba Ce musu ba kan Bikin ya zuba musu ido ne kawai yana kallon ikon Allah.
Haj.Uwani kusan sai da shafe wajen kwana goma sannan ta Dawo ta saki Ranta ana ta sha"ani da ita Domin mama tace mata ta kwantar da Hankalinta ana gama wannan Bikin Itama Umaima za"ayi nata to shi yadan Sanyayamata rai sannan tana chan Tsafe Uzairu yazo gida Ya kwana Biyu bata nan daga Chan Delta in da yake Bautar kasarsa har ya tafi bata Dawo ba sai da sukayi mgana ta waya.
Haka take shigema Hajiya ana komai da ita Hajiya bata taba nuna mata tasan Wacece ita ba ta barta ne sai Ranar kin Dillaci domin ta nan zuwa Ranar da Allah zai tona musu asiri a bainar nasi.
Mazajen su Hanne sun zo kuma sun gana dasu,Manemin Sa"adatu ya fara zuwa Dan gombe ne ma"aikacin Costume mahaifinsa ne sukayi karatu da mallam a kano,Sai kuma na Hamida Dake lecutring anan Kango Abu Zaria shima yazo Cikin Daliban mallam ne da ya koyar da Mahifinsa tun zamansa a zaria yana Dalibi ma alokacin.
Sai na Hanne da Shine Karshen zuwa Haifaffan garin Adamawa kuma mazaunin yola ne.
Dukkansu ba wacce bata yaba da Zabin Maalllam ba,sai hanne da tun taga ta ganshi take kuka cikin Damuwa kuma taki Fadan Daliinta Hamida ne kadai ta sani kuma ita din ma batayi Zencen da kowa ba.
Shiryen Shiryen Biki fa ya kamkama ta kowani bangare mamanmu ta fi kowa Shiri domin tayi alkawarin kece Raimin da bata taba yi ba sai a bikin Hamida Autarta duk tana Barikin cewa Jawaad ne Autanta wanda yanzu suka fara JSS1 Shi da Sabeeha a kasan ranta ko nan bata ma kaunarsa bataki shima ya mutu ta koma Daga ita sai Sa"idu ko ba ko Hajiya ta Daukesa ta daina ganinsa kamar yadda ta Dauke Amina daga gabansu.
Danmallam da kansa ya Kira Mallam ya fadamai zencen gidan daya siya ma Amina mallam yaji dadi ya dinga sakamai albarka shi ya Kira Hajiya ya Fadamata addu"an da Danmallam ya sha kamar Hajiya zata goyasa albarka kuwa ya shata har sai da ya kusa kwallah yana Tunanin wanda bai Sakama iyayensa ba Allah kuwa zai barsa. ?
Aliyu yama mgana ya kawo ma Mallam Takardun gidan sannan ya Dauke shi da Hajiya kai suka ga wuri Hajiya kamar tayi kuka fadi take"Allah ya tsareka Danmallam..ya yalwata arzikinka..Allah ya Jibanci lamuranka Allah ya kara budi na Alheri yadda ka faranta mana ka rike Amina da Amana Allah kai ma Allah ya rike Hannayenka cikin Aminci..!
Mallam ma haka ya dinga sakama Danmallam albarka sai Tsausayinsu ya kama Aliyu da sukayi waya da Umar ya fadamai irin albarkar da ya sha Wajensu Hajiya Danmallam ya murmusa yana Fadin"Aminene ta mallam da Hajiya ce..Suna shiga farinciki matukar aka kyautatamata kuma kaunar Baba Sa"idu ce ta Shafeta. !
Aliyu yace"Ai kacigaba da kyautatama Amina..ka riketa Amana har ya'yanka sai albarkar Hajiya da mallan ya bisu..!
Umar ya saki kayattacen mirmishi kafin yace"Insha Allahu..!
Hajiya ta kasa auna farincikinta Daga ita sai mallam suka kara tsara kayan Gidan Amina kamar yadda mallam yayi alkwarin yima Amina kayan Daki kamar sauran yan"uwanta haka kuma akayi tare da nasu hanne aka bada Oder din kayan gidan sannan Hajiya ta Tsara in kayan sun iso ya"yan yagana yayarta zata kira ta bata aron su su biyu bayan sun tambayi izinin mazajensu su zasu taimaka mata cikin Sirri su gyarama Amina gidanta Sabida tana so duk ranar data dira agarin ta iske komai ya kamallah.
Hajiya ta kudiri niyyar sai da wannan Bikin Amina zata bayyana sirin Boye zai bayyana a kuma Lokacin take Fatan Allah ya bayyana mugayen Fuskokin Dake tare dasu domin ba Shakka bayyana Amina da Ciki Sai ya Razana su kuma ita ta sani shiyasa bata yarda da kowa ba yanzu Daga ita sai mallam suke sirrinsu ko matan sun Lura da hakan sai dai daman ba wanda yasan Tsakanin Hajiya da mallam tare aka gansu irin su Hajiya Uwani da Anty Amarya sai Bakinciki Daga nesa..!
Hajiya ta zama kadagaren bakin Tulu basu da yadda suka iya da ita. !
















*Janafty**TFZB2023*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


*Gumel..*


Yau ta kama laraba ne da wuri suka dawo daga islamiya saboda anyi rasuwa ne Baban wata yar ajinsu Samira yahaya ne ya rasu sai aka zabesu su goma sha biyar maza biyar mata goma sukaje gidansu samira gaisuwa,bayan sun dawo mallam Ahmad yace kowa ya wuce gida sai Ranar asabar.
Dayake sun cigaba da zuwa islamiya da Haddarsu kamar yadda suka saba suna dawowa ba su wuce gidan Baba mallam ba sai suka yada Zangonsu gidansu Baba Sa"idu Sa"adatu daman bata je islamiyar ba wai batajin Dadin haka sukaji Sabeeha na fadama kawarta mariyan ajinsu.
Mamanmu na cikin Daki ta baje a Tsakar falonta ta baje wasu Sabbin kaya sababbin Dinkunanta ne da tayi Domin da gaske take yi sai ta shiga ta Fita ta kece raini a wannan Bikin.
Tana cikin Duba Dinkunan taji Sallamarasu kafin ta kauda kayan sun Daga Labule sun shigo Da fara"arta ta Tabersu tana fadin"A"a Amare ne da kansu Ashe daga ina haka..?
hanne gefen Mamanmu ta Zauna yayinda da Hamida ta zauna kan hannun Kujera tana Fadin"Daga makaranta .!
Mamanmu tace"To naga kun tashi da wuri Lafiya..?
Hanne tace"Rasuwa akayi mukaje gaisuwa daganan mallam Ahmad yace kowa ya tafi gida sau ranar asabar..!
Mamanmu tace"Oh..Allah ya jikan musulmi..!
Suka amsa da Ameen kayan take Dagawa Bakinta Har kunne tana Fadin"Kayan da zan ci fitar Bikin ku ne fa..Kun gansu nan ba"a Dade da aikomin dasu daga wajen Dinkin ba..
Less din take Dagawa har Hanne ta amsa tana fadin yayi kyau Hamida kuma kayan take kallo da mamaki ita dai bata saba gani ba ko ana Biki mallam ke ma kowa kaya daga manya har su yara sannan kwananan mamanmu Facaka kawai take da kudi yawancin Suturunta duk ta sauya su Taoffinta kuma ta aika dashi Gusai Tana ta sota mata mgana kuma ta kasa bata san ta ina zata fara ba Sannan ko Jiya taje kasuwa ta nuna mata Dinbin kayan data siya mata na Kitchen da sunan ita ta siya mata alhalin Hajiya ke siyan komai bama haka ina Mamanmu ta samu uban kudi haka datake ta kashewa..?
Abunda bata sani ba Aba yake bata ko Da bai yi niyya ba da tace ya bata bazai iya mata gaddama ba ko nawa tace ya bata haka zai dauka ya bata.
Hanne ce kadai ta Daga kayan ta gani ta yaba Hamida kuma daga inda take tace sun yi kyau basu wani jima ba suka tashi suka koma Dakin su Hamidar Hanne kan gadon Amina ta kwanta daman ko gidan ta kwana nan take kwanciyarta Hamida kuma tana Tsaye tana ninke Hijabin jikinta Data Cire ta ga Hanne tayi tagumi tana Tunani.
Sai da ta maida Hijabinta Cikin Dirowarta sannan ta isa kusa da Hanne ta Dafata da Sauri Hanne ta Dago tana kallonta cikin wani yanayi Hamida ta sauke Nunfashi kafin tace"Haba hanne wai wannan mganar har yanzu bata daina damunki ba .!?
Hanne sai kwalkwal kamar zatayi kuka Cikin wani yanayi tace"Hamida ya Zanyi..?
Da wani ido zan kalli Amina in ta Dawo taji yadda abubuwa suka koma..!
Hamida tace"Na fada miki ki daina Sako mganar Amina a wannan mganar..Amina fa yanzu ba kamar da bane..Matar aure ce kinga kuwa Igiyar aure ai ya kore komai Hanne..Ayadda nasan Amina Zata fi son kwanciyar hankalinki fiye da nata Hanne ni shaida ce irin kaunar dake Tsakaninmu..!
Hanne ta Saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta na wani Lokaci Hamida ta rike hannayen nata tana fadin"Dom Allah ki daina damuwa..Matar mutun fa kabarinsa Wani ai baya auran matar wani..haka ita ma matar wani bata auran mijin wata..Ga misali da Amina waya taba Zaton zata auri ya Danmaallam..?
Ammah dayake matar sa ce tun daga Launil Mahafuz ba gashi ya faru ba..Ki kwantar da Hankalin ki hanne Hajiya da mallam bazasu taba Zaba mana Abunda zai cutu garemu ba..!
Hanne ta cire hannayenta a kan Fuskarta lokaci Daya tana kakalo Mirmishi Hamida ta saka hannu ta Share mata hawayen tana Fadin"Bana son na ganki cikin Damuwa duk nima sai naji na shiga damuwa..!
Hanne tayi yar dariya kafin tace"Nagode Hamida..Na rasa Amina ammh baki barni nayi kewarta sosai ba..!
Hamida tace"dukanmu muka rasata Hanne..Kuma junanmu ne bamu bari kewarta ta mana illah ba..Sai dai Amina wata aba ce awajen mu da mantawa da ita abu ne mai Wahala..!
Hanne tace"Ni damuwata har da yarda za"ayi auran mu hamida ba Amina..!
Hamida tayi shuru kafin tace"Nima abun na raina..ko xamu je mu roki Hajiya ne don Allah Amina tazo mana Walima ko bayan Bikin namu ai sai ta koma inda basu san mu sani din..!
Hanne tace"Kin kawo shawara mu yi sallar mangariba sai mu shiga. !
Haka kuwa akayi suna Idar da Sallah suka ma mamanmu sallama wacce ta idar da sallah ta amsa musu da sai da Safe saboda tasan har Hamida ba lalle ta Dawo ba Jawad ma ya shigo ya Cire Kayan makaranta ya saka na gida ya fitaa masallaci domin wannan tarbiyan ta salla Cikin jam"i ko yaro karami ne yasan da ita agidan mallam yunusa Bazanga.
Sanda suka shiga shashen Hajiya sun sameta tana addu"a ne bayan ta idar da sallah sai da suka jira ta shafa Daman tun da ta ga shigowarsu sun wani uban buga Layi agabanta aranta ya bata mganar Amina ne domin shi kadai ke sakasu kaga sun zama kalar Tsausayi..
Tana rike da Cashabanta ta kallesu tana Fadin"Lafiya na ganku haka..?
Ko duk Tunanin barin gidan ne ya"yan Hajiya..!
Kansu na kasa suka gaisheta ta amasa Cikin Fara'arta tana fadin"Amaran namu duk sun rame sai dan wuya..!
Mirmishi kadai sukayi kansu na kasa kafin tace"Nasan da mgana a bakin ku ko..?
Hanne ta Dago tana fadin"Hajiya mganar Amina ce..haka za"ayi Bikin mu Amina bata zo ba Hajiya..!
Hajiya sai da tayi dariya Har Hakoranta suka bayyana Cikin Girgirza kai tace"Daman ai nasan Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki..Daman ai labarin kenan Amina..Amina ita ma tana chan duk mganarta da Zencenta Hanne da Hamida..Wannan kaunar junan naku Allah ya barta har ya"yan ku da jikokin ku su hadu a aljannah Firdausi..!
Suna Mirmishi suka amsa mata da Ameen kai ta gyada tana Fadin"Amina ce dai damuwar ko..?
Atare suka Daga mata kai Tana jan Casbahanta tace"To ku sha kuriminka..Amina na nan tafe da yardan Allah da ita za"ayi sha"anin auran ku..!
Ido suka zaro a tare suka ce"Da gaske kike yi hajiya..!
Cikin Yar dariya tace"Insha Allahu..Itama tana chan tana shiri..Bikin Hanne da Hamida bazai wuceta ba insha Allahu..!
Saboda murna sai da Hamida da Hanne suka rumgume juna kafin su saki juna suna ma Hajiya godiya ta amsa musu cikin sakin fuskar tana ce musu sai su sudaina ramewa Amina Zata Dawo haka suka fice suna Murna ammh bayan Hajiya ta gargade su kada su fadama kowa sukace ba wanda zasu fadamawa.
Ita kanta Hajiya bata isa ta hana Amina zuwa Gumel ba wannan karon Duk taso sai Amina ta Haihu ta Dawo da ita ammh Mallam ya nuna mata kada su kwari Amina da yawa bata da Zence sai na Hanne da Hamida in har sukayi aure bata zo ba abun zai mata Ciwo suma haka sannan Mijinta ma yabada goyon bayan su taho tare da Aisha shiyasa ta amince bayan tayi wani Tunani sai taga haka din shine Daidai.
Hanne da Hamida jin Labarin zuwan Amina wajen Hajiya Bakin da bazai musu karya ba yasa suka saki jikinsu Damuwasu ta ragu,Shiryen shiryen Biki kuma babu abunda aka fasa su dai basa wani shiru tunda basu da kawaye daman Amina ta fisu gayyar kawaye sai Sa"adatu su bama su fadin zasu yi aure da Bakinsu koma tambayansu akayi shuru suke yi abunsu.saboda lamarin yazo musu ne alokacin da basu taba zato ba ballatana Tsammani ba..
Daman ai haka rayuwa ta gada..Sau Tari abubuwa da dama suna Faruwa damu ne bamu tsammaci Faruwarsu ba..Haka lamarin Ubangiji yake.


******


*ABUJA..*


Ya Aisha na cikin bedroom dinta tana gyara kayanta da aka karbo wajen mai wanki da guga nata dana Amina sai na yakaka tun jiya aka kawo bata samu Zama ta saka nata cikin Wardrope ba tana ta shirin tafiyarsu Gumel ita da Amina gashi Hajiya tace tare da kayan Lefen Amina da kuma kayan Haihuwarta zasu taho sannan itama Daga barayinta akwai abubuwan data siya mata sannan Darling ma ya bata kudi yace ta siya ma Aminar wani abu tunda in ta tafi ba Lalle bane ta Sake dawowa ba..jiya ma kasuwa taje bata samun zama Sosai shiyasa.
Tana Tsaye ne tana Shirya kayan nata acikin Wadrope din Amina tayi sallama ta shigo Dakin ta juyowa tana kallonta Lokaci Daya tana amsa mata sallamarta.
Kallon Amina take yi tana dan Mirmishi tana kara jinjina ma Ubangiji Amina da Ciki Haihuwa ko yau ko gobe domin cikinta ya shiga watan Haihuwansa ko scan dinta na Biya ya nuna EDD Dinta karshen watab nan ne sannan ai Tsarinsa befare ne ko after.
Ta kara Kumbura kafafunta da fuskarta sun kumbura sai da tana da Tsawo shi ya taimaketa ammh Cikin yayi girma sosai sannan sai yayi kasa soaai alamun ya kusa fitowa duniya.
Har ta kariso Aisha na kallonta ta samu gefen gado ta zauna Dakyar Aisha ma mata sannu Sanye take da doguwar riga baka cikin Tsaraban ya Danmallam ne ta madina Daya aikomata daahi Amina na son Rigar bata san Dalili ba.
Sai da ta zauna ta gama hakinta ya Aisha na mata sannu sannan tace"Ya Aisha yaushe zamu je gyaran kai ne..?
Ya Aisha ta na yar dariya tace"Oh yau watarana Aminene na tambayan yaushe za"a je gyaran kai..?
An girma an zama manyan mata an Daina kazanta raahin wanka da yin wata uku da kitso ba gyara kenan..!
Amina tayi dariya da Idanuwanta da suka Shige Ciki tace"Ko abaya ma ba Laifina bane har da Sakaci da kuma rashin kula ya Aisha..!
Cikin dan mamaki tace"Bangane ha..?
Amina tayi wani mirmishi takaici kafin tace"Bazaki gane ba..Ammh ki yarda da mganata ai hamida da Hanne tare muka taso ai ba haka suke ba ko..!?
Ko haka suke..?
Ya Aisha ta girgiza kai tana Fadin"Sukan tun abaya suna da kokarin gyara kam..!
Amina tace"ki barsa a yadda na Fadamiki..!
Ita dai ya Aisha bata damu da mganar Amina ba yasa tace"Kada ki damu ki bari sai gobe in muka dawo daga asibiti sai mu biya mu yi gyaran kan ko..?
Ni kitso zan yi kefa..?.ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login