Showing 99001 words to 102000 words out of 145917 words

Chapter 34 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83943

kuma ki bari in kin yin Haihu Lafiya sai kiyi na suna..!
Amina ta kauda kai tana Fadin"Sai na tambayi ya Danmallam in yace yana son Kitso sai nayi..!
Ya Aisha ta rike Baki tana Dariya kafin tace"Ina yakaka tazo taji..Eyye masu miji manya..!
Amina tayi mirmishi batace komai ba ya Aisha tace"To har yanzu bai tashi Daga ya Danmallam din bane..?
Amina ta hura hancinta Daya kara Girma kafin tace"To ai nima bai sauyamin suna ba da Aminata yake kirana..!


Ya Aisha tace"To ai ke zaki sashi ya Sauya miki ina ruwanki da sai kin jirasa..Shi da yake da mata Biyu kowacce da sunan data ke kiransa kema sai ki samu naki tunda dai shi balarabe ne ki rika cemai HAbibi..!
Amina ta kalleta a karkace kafin tace"Allah ya tsareni..Habibi fa..Sunan da wannan gajerar matar tasa fa take kiran sa dashi kenan..!
Sai nima na Dauka..!.?
Ai na tasani kwaikwayo sai ta Rainani ma ya Aisha in taji ina kiransa da haka..!
Ya Aisha na Dariya tace"Oh ai bansani bane da gaskiyanki tobari mu sami wani suna ki rika kiransa da Norul kalbi mana..!
Amina ta yamutsa fuska kafin tace"Bai yi ba chanza wani..!
Ya Aisha tace"To Hubby..!
Amina tayi shuru kafin tace"Hubby..?
To har gwara ma wanman..!
Ya Aisha tayi dariya kafin tace"Yayanmu ya shiga uku..ya fada komar Aminenen hajiya da mallam..!
Amina na Dariya tace"Ko zaku Cirosa ne..?
Ya Aisha tace"Ina fa ai muna jin Dadi..Acigaba da kula mana dashi Allah ya kara kauna da soyayyah..!
Amina tace"Shi yace miki yana sona..?
Ya Aisha tace"Basai ya fada..Kowa ya ganki ai yasan kun fadama juna..!
Amina ta Hura hanci kafin tace"Ku ke gani ba..Ammh ai matansa yafi so akaina..!
Ya Aisha Dariya kadai take ma Amina Cikin zolayarta take kara gayamata Wasu sirrukan zama da miji,Amina ta Bude kunne tana Saurara bata da kalmar da zata gode ma Ya Aisha da yakaka zaman ta dasu alheri ga Rayuwarta har Abada bazata manta da gudumuwarsu ba.
Ta Dade a Dakin ya Aisha Sai azahar ta fito ta koma Dakinsu ita da Yakaka tana Shigowa yakaka na goge goranta ta kalleta tana Fadin"Ki rika dan yawatawa Takwarata sai kafafuwan naki su saki sannan ita mai juna Biyu ba"a son ta rika kumewa waje Daya .!
Amina tace"To yakaka ai baki rakani ba yau..!
Yakaka ta mike tana fadin"To Dauko mayafinki mu taka zuwa Haraban gidan..Ai bana ki takama Takwarata ba..!
Duk da dai kishiyatace ke domin kinsan dani komawa madina ba tashi..!
Amina na Dariya tace"Sai kun dawo..Ai ina nan zaki dawo ki sameni in wadanan guzumayen matan nasa suka koroki..!
Yakaka tace"Su har sun isa..?
Ai mu in muka shiga mun shiga kenan Asiri ko tsafi bai isa ya Girgizamu ba..Allah muka rike shiyasa gamu nan a Tsaye ga Kafafunmu..Kainuwa dashen Allah..!
Amina sai dariya take yi ta saka mayafinta tana fadin"Kwarai yakaka mu ikon Allah ne da na mutum ne da Tuni sun Shafe babinmu..!
Yakaka tace"Af keda kika san komai..!
Da haka suka fito daga Dakin Yakaka ce ta leka ta fadama Aisha sun fita takawa ita da Amina ta musu fatan Dawowa lafiya haka suke yi tunda Cikin Aminar ya tsufa.
Yakaka kitchen ta shiga suka gaisa da Saude ta Daukan musu ruwa suka fice Tunda in Amina najin tafiyar har karshen Layi Yakaka take janta iyaka in sun gaji su zauna Amina ta sha ruwa ta huta.
Sai da suka kai karshen Layin Maitama sannan suka juyo suka Dawo suna tafe a hankali suna Hira sama sama har suka dawo kuma Amina hakan ba karamin taimaka mata yake yi ba sai da suka dawo sukayi sallah Sannan suka zauna suka ci abinci Amina tuwo taci miyar kuka wacce Tun jiya Saude ta mata shi.bayan tashi ta koshi sai kuma ta kwanta ta Huta Daganan sai barci karar wayarta me ya Tada ita Daga barcin daman bata wani barci mai Nisa Tunda Cikinta ya tsufa..yakaka Dake Dakin ta miko mata wayar tana Daga kwancen tace"Gashi nan tun dazu ake ta kira..Ina jin mijinki ne to ban da ma shi ba wazai kira..?
Amina ta amshi wayar yakaka sai ta fita kamar yadda ta Saba ta bata wuri.
Sai da ya kara kira ta Dauka Cikin Shakewar murya suka gaisa jin yanayininta yasa yace"Meke faruwa ne..?
Kai Tsaye tace"Me ka gani..?
Dagachan bangaran yace"nayi ta kira baki Dauka ba..Sannan yanzu kuma kin Dauka naji muryanki ta Chuse fata dai ba jikin bane..?
Amina ta muskuta ta mike Zaune tana Fadin"Lafiya lau na dan kwanta ne shiyasa ban ji kiran wayar ba..!
Kai ya gyada kafin yace wani abu kawai yaji tace"HUBBY..!
Tsayawa yayi yana Tunanin ko dai bada shi take ba sai da yaji ta kara maimaitawa"Hubby..nayi kewarka sosai yaushe zaka taho..?
Danmallan Dake Cikin Office dinsa bai san sanda yayi baya da kansa kan kujeran Dayake zaune har da sabule Hula yana Shafa gashin kansa..
Cikin wani yanayin Farincikin Dayake Ciki yace"Yau nine Hubby Amina..?
Yaushe na tashi Daga ya danmallam din..?
Bakinta ta Tura kafin tace"To ko baka son sunan ne..?
Da sauri yace"Wa ne ni..?
Sosai sunan yayimin dadi..Sannan nima ai ina kewarki sosai..Zan dawo Cikin Satin Bikin insha Allahu kada ki Damu nima ina son nazo na ganki ke da Abunda ke Cikinki..!
Amina ta murmusa kafin tace"Ammh ai nima baka sauyamin suna ba..!
Dariya ta basa yasa ya Murmusa yana Fadin"Waya fada miki..?
Amina tace"Ai ban taba ji bane..Da fa Amina kake kirana..!
Kai Tsaye yace"Uhm kece dai baki Taba jiba..Ni nasan sunan da na saka miki Acikin raina sannan dashi nayi Saving din lambarki a wayata. !
Amina tace"Don allah ka fadamin..!
Make kafada yayi kamar tana gabansa yace"Naki bazan fada ba. !
Amina ta fara Shagwaba tana Fadin"Don allah fa nace..!
Kuma ai ni na fadamaka sunan da na saka maka..!
Jin zata faramai kukanta na Fama yasa ya Dakatar da ita yana Fadin"Tsaya Tsaya.kafin ki faramin wannan kukan naki da bayajin Lallashi..Ai ke NOOR ce..Haske ce ke Amina acikin Rayuwata Tun da kika shigo Rayuwata nake ganin haske kan komai nawa sannan nake ganin Daraja kima da martabawa wajen Iyayena sannan suke kara sakamin albarka da godiya gareni..Daga nan na Fahimci ke haske ne ga Rayuwata..!
Amina sai ta fara Hura Hanci tana jin Dadi sai wani Blushing take yi Cikin Fara"a tace"Da gaske ni Haske ne awajenka..?
Yana shafa kirjinsa yace"Ki bari nazo ,zan kara tabbatar miki Noor..!
Amina ta washe baki ta kasa mgana Dadi take ji akan ranta Cikin wani yanayi yace"Ya Bby na..?
Yau yayi motsi kuwa..?
Amina tace"Dazu muna dan takawa ni da yakaka sai naushi na ake yi aciki..!
Tafada Cikin yar shagwaba har da Jan hanci Danmallam yayi dariya Amina na jinsa sai ta sakamai kuka tana Fadin"Dole kamin Dariya tunda kamin Ciki ka tafi ka barni da wahala kana chan kai da matanka kana jin Dadin ka shine har kana min Dariya..!
Ya rude Hankalinsa ya tashi ya fara Lallashinta yana fadin"Wani jin Dadi baki kusa dani..?kinsan Allah ni fa kina Haihuwa zan taho Dake nan bazan jura zama baki kusa dani ke da abunda zaki haifa ba. na riga na samar Miki Shaidar zama a kusa dani..!
Amina jin haka yasa tace"Da gaake..?
Yace"Sosai ni dai kimin alfarman ko Hajiya tace bata yarda ba kice ke Zaki bi mijinki abunki..!
Amina ta fara Dariya tana Fadin"Wlh ba ruwana..!.
Wai shi zai mata wayau yana Fadin"Au baki son ki koma garin da Monzon Allah sallahu alaihi wasallam ya Zauna..?
Baki son zuwa makka ne kiyi Hajji..!
Amina tace"Ina so naje..In na ganni a gaban ka"aba Hubby kasan me zan fara roka..?
Yace"A"a Noor..!
Amina tacigaba da Fadin"Zan duka in Dafa ka"aba in rokar ma yaya Afuwa da salama sannan na roki Allah ya Hadamu a darussalam..!
Kai Tsaye yace"Allah ya Amsa ina jinki sai me zaki roka..?
Amina tace"Zan rokar ma Hajiya da maallam gamawa da duniya lafiya..Sai kuma Aba shima zan rikor masa kwanciyar hankali da Zama lafiya da wadata..!
Danmallan yayi Tagumi kafin yace"Sai kuma me zaki Roka..?
Amina tace"Sai kuma na roki Allah ya bama mijina Wadata na alheri Allah ya Zaunar damu lafiya Allah ya karamana kaunar juna ya shiryamana abunda Zamu haifa ya bamu ikom Musu Tarbiya bisa Amana da koyarwan addinin islama..!
Ayadda take mgana sai da yaji ajikinsa Cikin mamakinta yace"Wani mijin naki..?
Kai Tsaye Amina tace"Kai mana Hubby..dole zan gode maka..Domin kaima ka bani Taimako wajen dawowa da Rayuwata daidai sannan ka aureni Cikin wani yanayin da bakowani Namiji zai iya ba..Nagode kwarai Allah ya baka ikon yimana aldaci..!
Danmallam sai yaji kamar yayi kwallah ashe haka Amina ke da Hankali..?
Kai tsaye yace mata"Ameen Ameen Noor..Allah yayi miki albarka Allah ya Saukeki Lafiya insha Allahu Buriinki Zai Cika kin ji ko..?
Ta amsa mai Cikin jin Dadi,Shuru na wani Lokaci kafin taji yace"ANA BEHABBIK YA NOOR.....!
Amina ta ji mganar kamar Daga sama yasa tace"Me kace..?
Shi a tunaninsa bata ji me yace ba Sabida Labarci ne ya fada sai yayi saurin cewa"Bakomai..!
Kawai sai ta murmusa batace komai idonta ya kawo kwallah haka suka gama Hirarsu sukayi sallama Suna gama wayar ta rumgume wayar akan Cikinta tana Fadin"Ina son babanku..Wlh nima Ana Behabbak Hubby Umar..'
Hawaye ya kawo mata tayi saurin sharewa tasani tana son mijinta so mai tsanani data bata san yaushe ya fara ba Sannan yadda take kishin sa ko matansa basu kaita ba shiyasa ta Tsani ko jin sunansu kamar ma ya sani in suna Hira baya mata mganarsu shine zaman lafiya.
Washegari suka tafi asibitin tunda yanzu duk sati suke zuwa saboda Cikinta ya tsufa.da suka Dawo ne suka Tsaya Shagon salloon aka musu gyaran kai da Gyaran kafa Daman Amina ta Fadama Ya Danmallan yace kada tayi kitso ta bar mai gashin nan yafi son ya gansa haka ya fi bashi sha"awa ita kuma Amina duk abunda Zata Burgesa shi take yi bata Damu da kowa da komai ba sai shi sai Cikinta ke gabanta.


*******


Ana saura Kwana goma Bikin su Hanne Oder din kayan Dakin su ya iso har da Na Amina,Kowacee kuma Dakinta inda zata zauna aka wuce mata dashi Hamida dai yayarta Zulfa taje ta taimakama ma"aikatan aka Gyaran kayan aka saka komai a muhallimsa anan zaria zata zauna Gaskiya Layout.
Ita kuma Sa"adatu Gombe Kanwar Anty Amarya A"i sai Haj Nasara da Hajiya Babba suka je aka gyara Inda Sa"adatun zata zauna Sai washegari suka Dawo na Hannatu kuwa Haj.Uwani ce taje da Anty Amarya har Yola suka yi Jerin su,Tunda sun tafi da Kayan Kitchen din da Hajiya ta siyama Hanne da Hamida duka da Sauran na Hamidan da Mamanmu ta siya a mota ta saka ta aika ma Zulfa bata bari ko su Hajiya sun sani ba kada ta bar wata kafar da Za"a Zargeta.
Har Zulfa sai da tayi mata mganan ina ta samu kudin siyan wannan kayan saj tace ai kiwo tayi a gusai da Bikin Hamidan yazo sai ta saida tayi wannan Hidimar da ita Zulfa sai ta yarda bata kawo Tunanin komai ba na wajen Hajiyan wajen mamanmu aka barsu da niyar sai ranar Daurin airan in za"a wuce da Amarya sai a wuce dasu.
Bangaran gidan Amina kuwa batare da kowa ya sani ba Daga Hajiya sai Aliyu sai Mallam suka san an kawo kayan Dakin,Hajiya da bata samu kiran yar"uwanta yagana ba saboda Nisa Mallam ma yace ta kyalesu Fadila matar Nasir ta nema tare suka gyara gidan Amina ya fito Tsab komai an saka mata Labule ne kadai ba"a saka ba Aisha zata zo dasu Tunda tace ta siya ma Amima masu kyau oder dinsu tayi daga Dubai.
Har kuma aka gama gyaran gidan Fadila bata san ko gidan waye ba,Tunda dai Hajiyan ta nemeta da Nasir bai sani ba,sai bata ma Fadamai ba Tunda bata da Hayaniya,ta kama Bakinta tayi shuru ammh bata taba kawo Tunanin gidan nan da komai na Cikinsa na Amina bane Aliyum ma Data gani Tafi Tunanin ko nashi ne ko na wani nashi kila.
Shirye shirye ta ko"ina ya kamkama ana cikin kwanakin Bikin ne Sakina achan Madina tayi Zazzabi har da su Amaye amaye ana zuwa asibiti aka gwadata sai Ciki dan kimanin wata Biyu da kwanaki Labarin da ya yadu a Nageria abun mamaki shi Danmallan Da mallam kadai sukayi mgana ya fadamai hajiya ma mallam ya manta bai Fadamata a bakin Haj.Nasara take ji.
Anty Amarya haka take yada mganar Cikin tana Hura Hanci Hangowa kawai take komai ya kare ana gama auran Sa"adatu zata fara kokarin ganin bayan Haj.Uwa Ita kuwa daman Dariya take mata domin ta tabbatar da cewa kamar sauran shima haka zai bi Rariya Hajiya dataji labari Fatan Allah ya Tsayar tayi mata har aranta bata Fatan wannan karon Sakina ta rasa Cikinta ai mugunta Fitsarin Fako ne mai shi yake ci.
Amina ma taji labari abakin ya Aisha itama tace Sadiya ta kirata ta fadamata Amina sai taji Abu acikin Ranta ammh bata yarda ta Furtamai abunda taji ba shima kuma bai taba mata mganar ba sai mganar tafiyarsu Dayace Ranar Litini Jirginsu zai taso Daga jidda da Daddare zuwa Nageria shi da Sakina da Sarood.
Da farko yaso Sarood ta zauna Hajiya Dataji mganar tace bai yi adalci ba Sai dai Sakina ta Zauna shi kuma baya son Rigima yadda Sakina ta ke Hura Hanci da Cikin jikinta da kuma wannan sha"anin in yace ta zauna ai sai ta nemi mai hayaniya sannan yana da kudi a Hannunsa yasa kawai yaga gwara su taho gabadaya sannan yana su dan jima tunda hutun karshen shekara ne.
Su kuma su Amina suna ta shiri Ya Aisha bata siya ma Amina komai da kudin da Usman ya bata ba Daman kuma ta Bude Banki zuwanta Abuja sai da sukayi mgana da Hajiya tace ta barmata kudinta tunda kusan komai ta siya ma Aminar itama Aishan ta siya mata Zannuwan gado da sauran kayan Kitchen su blander Toster da Sauran su sai kayan Kamshin girki su kayan gyara kuma sai dai inda ta Haihu sannan har da Yakaka zata tafi gumel Usman baya nan yana Lagos za"a Yi Bikin Direba ne zai kawo su da kayan su.
Amina ta rasa Bakin godiya Data ga Uban kayan lefenta da kayan da ya Aisha ta siya mata sai da tayi kwallah Tace Gudummuwar malam da Hajiya ne suka Dauke ma Danmallam lefe tasani ba"a taba kawo lefen kowa ba sai dai in kaje gidanka ka gani ammh Sai gashi ita da nata Lefen zata koma Allah Sarki Rayuwa daman ai abunda ya baka Tsoro watarana shi zai sakaka kuka.
Ranar Talata da yammah Jirgin su Damallam ya sauka Filin saukan Jirage na kano Aliyu yazo ya Dauke su shi da Jafar suka kawo su Gumel gidansu suka sauka.












*Janafty**TFZB2024*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*




Saboda Gajiyan tafiya yasa ko washegari basu fita ko"ina ba Har shi Dannallam din bai iya fita ba sai Ranar Laraba suka zo gidan mallam Lokacin baki daga nesa duk sun fara Hallata irin su ya Fatima da su ya Nazifa,Mutanen Jordan kuma Suma Jiya suka iso Goggo Husai da Jadwa Sannan aranar Hidaya matar Nazir da Jaleela suka sauka suma da yammah kuma sai ga Mutanen Parthercourt su yaya zahra,Gida fa masha Allah ya fara shiga da Dangi na nesa dana kusa Sakina saiwani Hura hanci take yi tana iyayi ita a dole mai ciki sai Tsirfa take yi kala kala Saboda Sarood wanda ita batama nuna ta damu ba,Bangaran Anty Amarya kuwa itama Sai harkokinta take yi Cikin jin Dadi Saboda ai tana ganin ita yanzu bata da wata matsala ga Sakina na da Ciki gashi Zata aurar da Sa"adatu duk da abaya bata so hakan ba ammh zuwa yanzu ta hango hakan a matakin Nasararta.
Aranar bata koma gidan Danmallam ba nan ta kwana wai bata son kamshin Gidansu Danmallam ko ta kanta bai bi ba ya Dauki Sarood suka koma sai da Safe bayan sun Karya sun yi wanka ya Dawo da ita.
Aranar da Safe yan gusai suka iso da su ya Abida,ya zulaihat su ya Zeenatu da ya zulfa da su ya Ikram dukkansu duk sun iso domin in ba irin wannan Sha"anin ba baka samun damar zuwa gida har ka dan yi kwanaki mallam baya barin su suzo sai da wani Dalili mai karfi.
Hidaya wannan karon data zo Shashen Hajiya uwa ta sake sauka kamar yadda ta saba Hajiya bata nuna komai ba ko a Fuskarta,Shiyasa Hajiya uwa ta saki jiki anata kai da kawo da ita sai dai ta ciki na ciki in sun Hadu da Anty Amarya su rika ma juna kallon baki isa ba ita Hajiya Uwa Dariya Anty Amarya ke bata in taga tana wani iyayi saboda dai tasan Cikin Sakina ma wannan karon sai yabi Rariya kamar sauran ita kuma Anty Amarya tana takama da mallam yace Wannan matsalan ta kau har Abada.
Hajiya babba kuwa bata bi ta kansu ba harkan gabanta kawai take yi,Shashenta itama ba Matsaka tsinke Danginta yan maiduguri sun iso suma kwansu da kwarkwatansu Tunda ai Auta Hajiya zata aurar wannan karon Ita in kaga tana mgana ko Shawara da mallam ne ban dashi ta daina yarda da kowa Tunda ta lura yanzu Rayuwar ga yadda ta zama sai addu"a kawai wanda bakayi Tsammani ba sai ya Cutar dakai ko Hajiya Nasara da bata taba kamata da wani abu bata Saki Jiki da ita ba an ce Sau Daya ruwa yake dukam mutum yayi hankali ita kanta ya Daketa kuma tayi Hankalin Sosai.


Achan gidan Aba kuwa shima yana cike da Baki na nesa dana kusa yan Gusai Dangin Aba da Dangin mamanmilu Wannan karon yadda taci Burin Bikin nan yasa gayyata ba kama hannun yaro har da wadanda basu zo nasu Zeenatu ba sun zo wannan karon Mamanmu sai shiga take tana Fita Domin tun jiya ta fara sawa tana Cirewa Da Sabbin kaya Bakinta kamar zai Tsage saboda Fara"a kanta na Fashewa duk inda ta shiga ana Balaraba sannu da kokari Allah ya Biyaki da Aljannah.
Tana amsawa da Ameen tana kara jin Dadi ita ta samu Duniya,Domin yadda ta amshi kudade hannun Aba Allah kadai yasan yawansu data Mika hannu bai gaddama yake bata sannan Duk abunda tace ko bai kwantamai ba ta ZAuna Hajiyar banza ai yanzu ta sha gabanta ballatana wani chan Tsoho mallam da kansa A tunanin ta ayadda ta ci wannan Burin bata taba Hasaahen ko kawo kanta da wani abu zai iya faruwa da ita da zai Tsawarwata wannan Burin nata ba ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login