Showing 54001 words to 57000 words out of 145917 words
da Tsarina akansa kamar yadda na Tsara..!
Ta karishe Fada tana kallon Anty Amarya wacce tayi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi da jin wannan labarin lalle Haj.Uwani ta fi su zama Shedaniya,Su ashe bakomai ma sukeyi ba,Shekaruna nawa ta kwashe tana Wahala ammh Lokaci kadan Uwani tana neman Tsawartata to bazata bari ba,Bazata yi Saurin karaya ba,sai ta nuna mata in ita a Tsaye take ita a tafe ta kwana..!
Ta kalli Uwani cikin Bakinciki kafin tace"meyasa Burinki ya yi kamanceceniya da nawa .?
Meyasa sai dole kin Tsawartsani Uwani meyasa haka..?
Haj.Uwani tayi kasa da Murya kafin tace"Ki yi kasa da muryanki mana marliya..Ai na riga na Fada miki Dalilina..Bake kadai na taba ba..Na Fada miki yadda na Raba Hajiya da ya"yanta a kusa da ita,Na maida Nasir mara amfani a wajen maallam na hanata ganin jikanta ta Tsatson babbar Danta ita meyasa batace ina so na Tsawartata ba sai ke da Duka Dagani har ke muna kan Turba Daya ne marliya..?
Anty Amarya na Huci tace"To baki isa ba..wlh uwani karyan ki ta sha karya..!
Haj.Uwani tayi Dariya kafin tace"Nama isa ai marliya..Kaawai ki yi Hakuri ki mara min baya Burina ya Cika in hakan ta faru nayi miki alkwarin Raba komai gida uku na Dauki Biyu na baki kashi Daya. !
Anty Amarya ta harareta kamar Idanuwanta zasu fado tace"Me kike nufi..?
Haj.Uwani tayi Dariya kafin tace"Ki hakura da Sai Sakina ta Haihu marliya..!
Anty Amarya ta Zumduma ashar kafin tace"Ina..Baki isa ba Uwani..Bazaki Hada baki dani ba..Kowa ya Tsaya da kafafunsa..Sannan kuma sai dai ki kare a muguntarki kina ji kina gani Sakina zata haifarma mallam da Hajiya jika sai dai bakin ciki ya kasheki. !
Tafada tana kumfar Baki Haj.Uwani ta tabe baki kafin ta Daga kaafadanta tace"Shikenan marliya..Kije ki cigaba da Wahala..Ammh ina mai kara gayamiki..in sau Dubu sakina zata samu Ciki sai ya Zube haka Sarood hakama Amina ke ko aure ya kara itana irin Tsarin dana Dora su itama akan shi Zan dora ta Marliya na Fada miki kan Cikar Burina zan iya aikata komai..!
Anty Amarya taji wani abu ya Tsaya mata a wuya kawai sai tayi kukan kura ta kara shako Haj.Uwani cikin Hargagi take fadin"Me kika baa sakina tasha..?
Ki Fadamin abunda kika Binne da kudin da kika kashe akan hana Sakina Haihuwa Uwani..?
Kwace wuyanta tayi tana Hararan Anty Amarya Lokaci daya tana Fadin"Wlh in kika kara saka hannunki kika rikeni sai na Sharara miki mari marliya..!
Ki kama kanki kafin Zuciya tajaki ki aikata abunda zaki zo kina Nadama..!
Anty Amarya na Haki ta nuna Haj.Uwanu tana fadin"Wlh kin yi kadan..Nayi alkawarin sai nayi sillar Tona miki asiri..!
Haj Uwani tace"To ai ban Hanaki ba..tunda baki min godiyar Taimakon ki da nayi ba akan Amina da Sarood ba, wato sakina kadai kike so ta Haihu ban da su ko..?
To tunda baki ga Hallacin da nayi miki ba Shikenan jeki fadama wanda zaki Fadamawa ammh ki sani in asirin ya tashi Tonuwa naki sai yafi muni Marliya ni iya ka dai mallam ya Sakeni ko..?
To in ya sakeni ai bai kare ba ina da Zaratan maza har uku ko da sun ji abunda ya faru basu isa su sauya ni a matsayin uwa ba marliya,Sannan kuma dole zasu neme ni kefa wa kike dashi..? Duka ya"yan ki mata ne baki da wani gata anan duniya iyayanki zasu yi Tir Dake ya"yan ki mata zaki bar musu abun kunya in ma bai taba auransu ba,Sannan Uwa uba kuma agaban idon ki Umar zai Saki Sakina kinga Daganan kin kare a Tutar babu..Wahalar ki tatashi a banza kenan kuma ke ahakan ma naki Tonuwar asirin mai kyau ne,akan na Balaraba ita wlh ko kaffara bazan yi ba kare sai ya fita Daraja in sirrin Boye ya fito Fili sai ta wulakanta ta Tozarta a wajen Sa"idu da Danginsa da kuma ya"yan Yaya da kukayi Sanadiyar barinta Duniya Saboda cikar naku burin..!
In kin yarda da duka Faruwar wannan shikenan u can go..Ki je ki Fadama Hajiya sai mu shirya bankadewar siirikan namu dani da ke da balaraba alokaci Daya ko banza na San Dagani har ke bamu samu cikar Burukan namu ba..!
Tafada tana wata yar Dariya Anty Amarya duk yadda taso kada ta nuna Rauninta sai da ta nuna Hawaye ya wanke mata Fuska ta nuna Haj.Uwani da yatsanta Cikin Kaushim murya mai Cike da karkawa tace"Ki Rubuta ki ijiye Uwani Indai ban samu abunda nake so ba..Na rantse ko Zan yi yawo Tsirara sai naga kema baki samu abunda kike so ba..In juran ki sammako ni madina a tafe na kwana mu Zuba mu gani..!
haj.Uwani ta bata amsa da cewa"Shege ka fasa marliya..!
Daga haka Anty Amarya ta murza key din ta Bude kofar ta Fice tana kuka Duk yadda taso ta shanye kukanta ta kasa bakinciki da Takaicin sun taimaka wajen Fitar Da ita daga natsuwarta uwa uba kuma da yadda Gabadaya sirrukansu yake tafin Hannun Haj.Uwani
Hajiya ta fito kenan Daga Shashenta zata shashen Haj.Uwani suyi mganar wani Turaran wuta da suka je Bikin nan maiduguri tace tana so yagana ta kirata kan mganar ne yasa tace bari ta shiga ta fadamata..
Ta sawo kanta Falon kenan Anty Amarya na fita da gudu tana kuka Hajiya sai ta Rude hankalinta ya tashi ta rika fadin"Subhanallah Amarya Lafiyanki kuwa..?
Ina ko jinta batayi ba batama ganta ba Domin kuncin datake ciki ya Rufe mata jinta da ganinta har ta fice Hajiya na Kallonta sai jikinta ya kama rawa tana Fatan Allah yasa ba wani abun ne ya Faru da Sakina ba kamar ta bi bayanta sai kuma ta fasa ta karisa Cikin Falon Haj.Uwani tana Fatan taji abunda ya faru Daga bakinta.
Ita kuma Haj.Uwani Anty Amarya na fita ta yi shewa ta kara Sakin shewa kafin tace"Mu zuba mu gani marliya..Karki fara ja da Uwani Domin ni walkiya ce ban Fito ba sai da na shirya..!
Haka take ta fada tana Dariya tasan Daman zatayi mamakin yadda tasan komai nasu Mama hatsabibiyar Bokanyance Dake Niger ita take Sanar da ita duka aikin marliya ita da Balaraba ita kanta da Farko ta Razana da jin sunan mamanmu domin bata taba Zaton matar mugun halinta yakai haka ba, sai dai batayi mamaki ba Sanin yadda Idon kowa yake Rufewa kan neman Duniya..sannan Ta kara jinjina ma wannan kalmar na rai ba abakin komai yake ba wajen Biyan Bukata Tunda Balaraba ta saka aka kashe yaya Matar data Zauna da ita Tsakani ga Allah ta bar mata gidanta da ya"yanta kawai saboda Cikar Burinta na mallakan sa"idu..!
Tana wannan Tunanin kamar Daga Sama taji muryan Hajiya tana Sallama sai ta Rude ta mike da Sauri ta fito Tana kokarin Daidaita yanayinta Hajiya dake tsaye Tsakiyar Falon Uwani ko Zama ta kasa ta kalli Uwanin Yadda ta fito tana abu kamar wani abu dai ya faru yasa da Sauri tace"Wai ni Uwani me ya faru ne acikin gidan nan bansani ba..?
Naga Amarya ta fita Daga shashen ki da Gudu tana kuka ina ta mgana bata jini ba kema mayi sallama kin Fito kamar kina ma a firgice ne Hankalina ya tashi muke Faruwa..?
Haj Uwani na jin haka kawai sai ta Zube saman Cafet din Falonta ta Fashe da kuka yi take yi ba Saurarawa ta kara Tadama Hajiya da Hankali Cikin Rudewa tace"Ko Cikin yaran mu ne wata ta rasu kuke Boyemin..?
Hajiya Uwani na jan majina da Hanci tace"Ai gwara ma Mutuwa da wannan Zargin da Amarya ke jifana dashi Hajiya..!
Hajiya tace"Wani Zargi kuma Uwani..?
Haj.Uwani na kara saka kuka tace"Hajiya wai ni Amarya tazo ta sama tamin zagin kare Dangi da Zargina wai ni nake asiri ina Zubar ma Sakina da cikinta..Fitar nan da kika ga tayi ni tazo ta kare ma Tanadi Hajiya..!
Hajiya ta Zaro ido kafin ta saka Salati ganin haka yasa Haj.Uwani ta karkace baki ta Cigaba da fadin"wai malaminta ya mata Duba yace ci kin matan mallam ne..kawai hajiya sai tace ni ce..Nan tazo ina ta mata Rantsuwa taki yarda dani ina Fadamata kada tayi saurin yarda da irin mallaman nan na karya masu Hada Fada bata Saurareni ba Hajiya haka ta fita tana kukan da Ikirarin sai ta ga Baya na..!
Hajiya nan da kika gani daman wajenki Zani Na fada miki abunda ke Faruwa naji Ciwon wannan abun sannan na Fadamiki bazan kyale Amarya ba sai ta san tayi min kazafi..!
Ta karishe Fada tana kuka Wurjajan..hajiya kuwa sai Faman Salati take yi kafin tace"Kinga Uwani bar kuka..wannan mganar ba tawa bace..Bari naje na kira mallam na Sanar dashi abunda ke faruwa wannan mganar tayi muni da yawa Uwani..!
Haj.Uwani na jan majina tace"Ko kin gayamai Hajiya ni bazan yafe ba..Sai an Bimin Hakkina akan kazafin da Amarya tamin..!
Hajiya bata Saurareta ba ta Fice tana Jimamin wannnan abun aranta tana Jin Haushin Anty Amarya bata taba Zarginta da shiga malamai ba ammh jin abunda ta aikata sai taji duk ta Zube mata ina amfanin wannan aikin..?ta Biyema mallaman karya suna neman hada fada acikin gida.
Hajiya na fita Haj Uwani ta mike ta Share Hawayenta ta yi Dariya kafin tace"Marliya tun a yau zaki san kin Hada Hanya da Uwani Diyar Hamza Tsafe..!
Ta fada tana Dariya har ta Hango yadda Marliya zata gane bata da wayau a falon mallam Dakin da Umaima take ta leka barci take yi Domin yanzu ko Makarantar Haddar ta Daina zuwa saboda Ciwon nata ya tashi gadangadan ana ta dai fama da mgunguna ne.
Hajiya ko na fita Bedroom dinta ta shige nan ta bar Hanne da Hamida afalo suna rike da Littafansu bata ma Bi ta kansu ba ta Shige Daki wayarta ta Dauko ta Kira mallam bai yi nisa ba yana gidan mai anguwa ya Kirasa kan Cases din Filin wasu marayu da aka kawo mai mganar to daman mai anguwa in wani abu irin haka ya Faru na bangaran addini yana kiran mallam Domin su Tattauna.
Yana jin Hajiya tace yazo gida ba Lafiya yace mata suna ma kan Hanya.
Lokacin ana gabda kiran Sallar La"asar ne yasa suna Dawowa yace bari ya Tsaya yayi sallah kafin ya shiga Cikin gidan
Hajiya ta fito ranta a jagule sai yanzu ma ta lura bata ga Amina ba Tunda dazu da suka Dawo daga makaranta,yasa ta kalli Hanne da Hamida dake ta yin aikin da malamin Lissafinsu ya basu a makaranta tace"Ina Mamah yau. ?
Hanne tace"Tana gidan baba Sa"idu dazu da muka shiga gaida mamanmu ta kwanta sai ta fara barci mu kuma da Zamu tahilo bamu tashe ta ba..!
Hajiya bata ce komai ba ta kada kai kafin tace"ku tashi kuyi sallah Lokaci yayi..!
Daga haka ta koma Cikin Bedroom dinta Ammh aranta sai da tayi Tunanin barcin Amina yayi yawa kamar kasa yanzu ko da asuba fa Dakyar ake tashinta wani Lokacin da Daddare kafin takwas Amina ta kwanta sannan in suka Dawo makaranta sai tayi barci ammh sai bata kawo wani Tunani ba tafi Barinsa a Saboda Basa Zama a zirga Zirgan makaranta da Sauransu.
Hajiya ta idar da Sallah kenan Kiran mallam ya shigo mata yace gashi ya shigo Gidan Hajiya batayi kasa agwiwa ba ta saka lullubinta ta Biya Shashem Hajiya Uwani Dake zaman jiran Kiran mallam suka tafi Falon mallam suna zuwa Hajiya tace ta fara gayama Mallam yadda taga Anty Amarya sannan tace Uwani ta maimata abunda ta Fadaamata Haj.Uwani ta gyara Zama ta Fara Rattafama mallam yadda ta Fadama Hajiya ta karishe cikin kuka tana Fadin"Mallam abu dayane in na Tuna yake min ciwo..Da Amarya ta Zargeni da laifin kisa Mallam..?
Ashe haka ta Tsaneni bansani ba..Ta rasa kazafin da Zatamin sai kazafin kashe gudun jini Tun kafin ya Fito Duniya..? Wannan in gaban yan Sanda za"a kai ai babban cases ne mallam..!
Mallam da ransa ya gama baci ko mgana bai yi ba ya Daga wayarsa ya kira Anty Amarya wacce ke cikin Bedroom dinta tunda ta Dawo Daga Shashen Uwani ta shige ta rufe kanta tana kuka kukan rashin mafita da madafa kukan takaici da gazawa a karo na farko ko sallah bata tashi tayi ba sai ga Kiran Mallam sai da gabanta ya Fadi balle Dayace tazo ta same sa afalonsa a kausashe.
Ai bata gama Sarewa ba sai da Sawo Hijabinta Fuskarta duk ta kode ta iso Falon mallam ganin Hajiya da Haj Uwani sai da yasa gabanta ya Fadi Jikinta ya fara rawa ta Tsaya Cak ta kasa gaba ballatana baya.
Mallam cikin kaushinsa yace ta kariso ita ake jira,Jiki a sanyaye ta kariso ta Zauna gefen kafar Hajiya a kasa tana kallon Uwani dake mata Dariya a kasa kasa Daganan tasan wani makircin ta kulla mata..
Kanta ya Daure sanda Mallam yake karanta mata abunda Uwani tace ya Kalletaa Cikin bacin rai yana Fadin"Marliya ashe ban Dade ina muku nasihan yarda da malaman tsubbu ba..?
Shine kika kai kanki bayan kin yarda dashi shine ya karanto miki karya kika zo kika Hadamin Fada acikin Ahalina alhalin na Dade ina gargadinku..?
Anty Amarya ta Tsure hankalinta ya tashi ta kalli Haj.Uwani dake matsan kwallar karya ta maida kallonta kan mallam taga yana mata wani kallo Sai kuka ya taso mata ta Fashe da kuka Tana fadin"Wlh ma..!
"Karki ce tak a nan wajen marliya..Baki da abunda zaki fadamin bana Kiraki Domin kimin karin bayani bane..na kiraki ne naja miki kunne Wlh Tallahi in na karajin mgana makammancin wannan sai na Saba miki in ma ban yanke Igiyan auran dake tsakanina Dake ba. domin ina kyamatar Zama Dake Marliya tunda kin zama Mushuruka mai bin malamai da yan Tsubbu makiya Allah..!
Anty Amarya ta tsorata ta Duka gaban Hajiya ganin yadda mallam yake mgana tasan ransa ya baci Uwani tayi nasara akanta tace"Hajiya don Allah ki bama mallam Hakuri ba Laifina bane kuskure ne..da sharrin Shedan..!
Sai kuma ta rike kafan Hajiya tana gunjun kuka Hajiya taji Tsausayinta ta Duka ta riketa tana fadin"Tashi ki Zauna marliya..!
Komawa tayi ta zauna tana kallon Haj.uwani Dake matsar kwallah tana mata Dariya ba wanda ya Lura
Hajiya ta kalli mallam kafin tace"Mallan kayi hakuri don Allah..Tace Sharrin shedan ne ayi mata uzuri..!
Kema Amarya ki gyara wlh bazan Boye miki ba kimarki ta Zube awajena tunda naji kina daga Cikin masu Bin malaman karyan nan ammh Tunda kin bata Hakuri ya wuce..Mallam kai ma kamata Hakuri..!mallan cikin bacin rai yace"Bani zata bama Hakuri ba Uwani gatanan baiwar Allah da ta zargeta tana zaman zamanta zata bama Hakuri in kuma wlh bata yafe mata ba sai Allah ya kamata !
Yafada cikin nuna bacin ransa lokaci Daya yana Kauda kai baya son kallon Anty Amarya
Hajiya ta juya tana kallon Anty Amarya tun kafin ma tayi mgana ta Zube gaban Uwani tana Fadin"Kiyi..hakuri sharrin shedan ne ki yafemin..!
Haj.Uwani ta share Hawayenta kafin tace"Shikensn tunda Hajiya da mallam sun saka baki..Ammh wlh da naso ne sai na kai mganar nan gaba..Ammh Tunda kin bada Hakuri ya wuce sai ki kiyaye ki daina yarda da mganar makaryatan malama nan makiya Allah da addininsa..!
Hajiya tace"Tabbas Allah ya Karemu gabadaya..!
Haj.Uwani ta amsa da Ameen da karfi mallam ya mike yana Fadin"Sannan mgana ta karshe bayan mu Hudun nan kada naji wannan mganar abakin wani..Na kasheta Daga yau..!
Daga haka ko mgana bai kara ba ya shige ciki bakincikinsa Daya yana tafe wa"azi akan mata masu Bin malamai ammh yau agidansa ma ake yi wannan aikin..?
Tayaya ransa bazai baci ba..?
Hajiya kuwa sai da ta kara yima Anty Amarya Nasiha sosai da nuna mata illah rashin yarda da Allah da kaddaran da Illah barin Shedan ya saka mutum wasi wasi da kuma illar Bin malaman karya na Tsubbu.
Sannan ta sallame su Anty Amarya ta Mike kamar tana kan kaya ta Fice Haj.Uwani sai daga baya ta fito Hajiya kuma ta bi mallam ciki ta Rarrasosa..!
Haj Uwani har takai shashenta tana Dariya Allah Allah take yi ta Kira Batula ta labatar mata abunda ya faru yau sai ta Kira ta bata Dauka ba Shiyasa ta bari sai an juma ta Sake nemanta kan kujera ta kame a falonta ta Dora kafa Daya kan Daya tana Mirmishin jin Dadi da Nishadi ko banza yau ta bama Marliya Daya daga Cikin Tsoronta..!
Anty Amarya kuwa haka ta shiga Shashenta bata gani tana jin Sakina da Sa"adatu na kiran sunanta da suke
Falo bata bi ta kansu ba ta shiga Daki ta Bame kofa da key jikinta na Rawa da Hannunta ta Dauki wayarta Dake kan madubi ta Dokama Balaraba kira.
Mamanmu na cikin bedroom dinta bata Dade da tashi daga barci ba tayi sallah tana Zaune tana Tunanin irin girkin da zata Tsarama Aba da Daddaran nan Tunaninta ba kowa agidan Jawaad na Haraban gida yana Kwallo Su Hamida basa nan suna gidan mallam Domin bata Dauka Amina bata bisu ba dataji Fitansu ta Dauka gabadaya suka fita..shiyasa bata Damu data leka Dakin su Aminar ba da ba kowa acikinsa yanzu sannan Dazu da ta fita alwala taga kofar Dakin a Sakaye abunda bata sani ba Iska ne ta Dan Tura kofar Dakin Amina na ciki tana barci.
Wayarta Dake gefenta ne ya katse mata tunani ita azaton ta Aba ne Domin yanzu ko yana wajen aiki haka suke cikin waya yana tambayanta ko ba wata matsala sai taga Madina ne ke kiran Wani katon Tsaki ta saki kafin tace"Kai madina bazata barni na Huta ba..ya kamata ta Hakura tunda ita dai kamar bata da sa"a ne..matsaww...!
Sai da ta Daidaita kanta sannan ta Daga Kiran tana fadin lafiya"Madina Allah yasa lafiya kira da bayan la"asar haka..?
Anty Amarya cikin kuka tace"Dayyaba mun kade mun gama yawo..Ashe duk abunda muke ciki siirinmu yana Bankadane bamu sani ba..Tabbas muna Shuka a idon makwarwa Dayyaba. !
Mamanmu ta ce cikin mamaki"Bangane ba madina..?
Waye yasan sirrinmu..?
Anty Amarya tace"Hajiya UWANI 'ce Dayyaba..A tsirara take kallonmu Duka Sirrukanmu dani Dake yana Tafin Hannunta ne. !
Mamanmu ta mike Dafe da Kirji Tana Fadin"Mun shiga uku Madina wani irin labari kike son ki Fadamin..?
Anty Amarya ta share hawayenta tana Fadin"Ai bama uku muka shiga ba goma ne Dayyaba..!
Nan ta fara gayamata komai da komai Tunda daga farko da zuwar da tayi ta Samu Haj Uwami da yadda suka kare da Sharrin data kulla mata ta karishe da Fadin" Kinga yadda take kuka afalon mallam kyce ta Allah ce Dayyaba..Wlh Uwani ta shirya yin Fito na fito damu kuma in muka yi wasa..Tana gabda Kware mana Zani a Tsakiyar kasuwa..!
Mamanmu ta Mike