Showing 42001 words to 45000 words out of 145917 words

Chapter 15 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83969

ki Hakura da zuwa Bikin su Abida Tunda ba an gama sha"anin bane akwai wasu masu zuwa kika jin mganata kika kuma Zuga Sarood itama ta Tada min rigima Duk Saboda nace ki Zauna bani da kudi sosai sai wani lokacin..!
Sakina ta kwaso Rantsuwa bai bata Dama ba ya cigaba da Fadin"Ita mahaifinta ya Dakatar da ita bata Biyoni ba..Ke kuma kika Biyo ni kikazo to kuma Miye na jin Zafi Domin nace sai nan da wani Lokaci zaki koma..?
Ai kina son zaman nan din ne shiyasa nayi miki abunda kike so..Wlh itama Data sake ta Biyoni Dukkan nan zan barku nayi Tahowata lokacin da na Sanu Dama da Hali sai nazo na Taho Daku a kallah dai nayi muku abunda kuke so kada kuce nayi miki rashin Daidai..
Kinsan Wlh rantsuwa ce ko..?
Sakina sai in na Samu Lokacin nazo sai mu koma Tare in kuma kika ce zaki Biyoni bansani ba to ba da Izinina ba..!
Daga haka ko cewarta bai jira ba ya Katse kiran yana Faman kokuwa da Bacin ransa Sakina kuwa kamar tayi Hauka haka ta mike tana Laluban wayar Anty sai dai bata Sameta ba Kasa Zama tayi ta mike tana Safa da marwa acikin Dakin tasan Waye Umar kaifi Daya ne in yayi mgana baya Sauyata ammh sai da ts saki jiki da Anty da ta tabbatar mata da cewa zai zo su koma Tare,sai dai wannan Jadadda mganar tasa yasa ta kara Sarewa a baya ma acikin ranta har ta Tsara in bai zo ba zata yi Visa da kudinta ta bisa sai dai ya ganta ai tasan Hanya ba inda bazata kai kanta ba A madina ba.!
Sai gashi furucinsa ya sa wannan Tunanin ya bace mata tasan kuma tunda yace bada yawunsa ba in ta Sake ta taka wani abun ne kuma zai Faru na Dabam wanda bata Fata wayar Anty Amarya tayi ta Kira kamar zatayi hauka bata Sameta ba


Shi kuwa yana katse kiranta ya Kira Aliyu saboda yanayin Yan"uwansa duk suna Nageria ne yasa yake saka Kudi mai yawa saboda yafi Sauki shi ya Kirasu da su Dagachan su kirasa.
Kiran farko Aliyu Dake wajen aiki shima acikin Office dinsa ya Daga kiran yana Fadin"Ango..Kaga angon Amina Larabawan Madinatul munawwara..!
Umar yayi Dariya kafin yace"Taka Sallamar kuma kenan..?
To Allah ya shirya Sallamu Alaikum..!
Aliyu na Dariya yace"Wa"alaikas salam Shehi mun tashi lafiya..?
Daganan suka gaisa kamar yadda suka saba kafin Umar yace"naji hayaniya kana wajen aiki ne hala..?
Aliyu yace"Eh wlh tun Safe ma.!
Umar yace"Daman mgana nake so mu yi..!
Tana da muhimmanci sosai..!
Aliyu yace"To ina jinka ai ina Office dina ne.!
Umar ya gyara zama kafin yace"Matsalace dani na rasa wa zan Tunkara shiyasa na zabi na Fadamaka..!
Nan ya fadamai Halin da suke ciki shi da Sarood.
Aliyu ya Saki baki ya Rufe sau ba Adadi bai sani ba kafin yace"Bangane ba ita Sakinar kuma Lafiya kalau kake in ka Rabeta..?
Umar yace mai eh Aliyu yace"To Amina fa ka jarabata ka gani..?
Sai ya kasa mai mgana sai da yaji Shuru sannan Aliyu yace"Common Mutumina Saboda mu gano matsalan ne yasa kaji ina Tambayanka..!
Sai da ya Runtse kafin yace"Itama Lafiya kalau..!
Aliyu yayi ajiyar rai kafin yace"Umar kune malamai ya"yan malamai adan Sanina da ilimina na hasaso wani abu..!
Umar yace"Me ka Hasaso..?
Aliyu yace"Al"amarin ka kamar Sihiri kamar kuma shafan Aljanun mutanen Boye..!
Umar yayi shuru yana wani Tunani kafin yace"Sihiri kuma..?
A"a sai dai in Shafar aljanun in na rabeni bazan musa ba..ammh ni kam wazaimin Sihiri ni bani da abokin Fada kai Sheda ne Aliyu..!
Aliyu yace"Hakane sai dai shi Rayuwa bata ga haka..Kana zaman zamanka baka Damu da kowa ba wani na chan yana Bakinciki da duk wani Cigabanka..!
Umar yayi ajiyar rai kafin yace"Sai dai shafar Aljanun Aliyu..Bazan musa ba Ammh ina Tunanin ko ta bangaran Sarood ne..?
Ina da yakinin yadda na tsare kaina da addu"a azakar Safe da Rana da Karatun Qur"ani da Ibada aljanu bazasu Shafeni ba insha Allahu..!
Aliyu yace"Duk zai iya yuyuwa hakan din ma.!
Danmallam ya Dafe kansa kafin yace"to menene mafita.?
Aliyu yace"Ni dai a a shawarata ka Shawarci mallam na Tabbata shi zai san wani abun da bamu hango ba..!
Umar yace"Ina jin kunya fa..!
Aliyu yace"Lalura ce Shehi..Sannan Maallam ba kunya Tsakaninku..!
Umar ya jinjina kai kafin yace"Hakane Shikenan zan yi Tunanin hakan nagani in munyi mgana zan kiraka kaji yadda mukayi Dashi..!
Daganan sukayi sallama bayan Aliyu yace yana jiransa.
Duk yadda Danmallan yaso ya Kira mallam sai yaji ya kasa yafi dai yadda da mganar Aliyu na shafar Aljanun yafi kuma yarda data bangaran Sarood ne ya yanke shawaran in ya koma gida zasu yi magana yasan wasu mganguna anan madina na irin haka da kuma addu"o"in Tsarin Shafar mutanen Boye zai saka ta Jaraba ta gani in abun bai yi ba bai da wata Mafita sai na kiran mallam din.
Aliyu kuma mamaki ya cika sa na wannan lamarin ya fi karkata ga Sihiri ne saboda wani abokin aikinsa da suke Tare anan hakan kusan ya Faru dashi da ya kara aure shi ma Ba wani motsi tun yana shuru har mgana ta kaima Manya Mahaifiyarsa ce yar gidan malamai nan aka gano Shihiri ne sannan kuma ana Zargin Uwargidansa tayi mishi da aka Mike Tsaye da addu"a da mgungunar karya Sihiri Tuni aka wuce wajen shima yaso Shehi ya yarda da mganar sa ammh sai yaga bai amince ba sai ya bar sa a Inda Tunaninsa ya karkata sai dai yana Fatan In ya kira Mallam din adace.!


********


Bayan sati Daya..!


hajiya bata samu Tafiya Biki ba sai Ranar alhamis idi ya kai su ita da Hajiya uwa datace zata rakata ba wanda yayi mamakin hakan daman in dai sha'ani na Hajiya ne Hj.uwa tana gaba gaba sanin tasu tafi zuwa Daya da Hajiya babba ba kamar su Nasara da Anty Amarya ba kafin su tafin Jafar ya kawo mata 30k in ji Danmallam ta kar ba tana ta godiya ta nuna ma mallam ya saka albarka shima ya bada kudi da kayan abinci suka tafi dashi Kwana Daya idi yayi ya juyo sai sun gama Biki zai Dawo ya Daukesu
Su Amina sun so Hajiya tatafi dasu tace su yi Hakuri su zauna Saboda makaranta sannan kwana Daya Tsakani Ranar jumma"a Mamanmu ta tafi Gusai Biki Amina da Hamida da Hanne sun so su bita Tunda Hajiya bata tafi dasu ba ammh itama tace su Zauna Saboda makaranta Daman Amina ta ma mallamm gana ya basu Hakuri yace su bari wani Lokacin saboda karatunsu,Dole suka Hakura ammh Tundaga Ranar ganin Hajiya bata nan Amina ta share Kafa Tayi zamanta Daganan suke zuwa makaranta da Aba yayi mgana Mallam yace ya kyaleta watarana ba sai an mata mgana ba zata san muhimmancin gidan auranta har yanzu Amina yarinya ce.
Amina kuma Harkan gabanta take yi kamar ba matar aure ba in ba gidan ta koma ba mantawa take yi da wani aure ballatana Danmallan ko Sakina Abu Dayane bata manta dashi ba Har yau shine Abunda ya Faru Tsakaninsu Ko barci ta kwanta sai ta Tuna abun kunya take ji da nauyi in ta Tuna abunda ya Faru Ranar yau itace kan gado ita da Danmallam har wani babban lamari ya faru Tsakaninsu sannan bazata manta da yadda yagama gane mata jiki bakincikinta Daya yan nonuwamta Daya gama gani Tasan ya gama rainata Haushi take ji nata sunki girma ga Hamida Da Hanne har Hajiya ta siya musu Braziya ita kuma sai vest saboda ba su da wani girma sosai in ta tuna Haka sai ta Tura baki tana kunkuni kamar yana jinta ko yana ganinta.
Yanzu Ta rage tsoro tunda Tare da su Hamida take kwana sannan koda aka shiga Damina ko ana ruwa Tsakar Dare ba ruwanta tana makale bayan Hanne ko Hamida hankalinta kwance.


A jidalinta kam babu abunda ta Rage sai Dambe ne kadai ta Daina ammh Fada a makaranta da siyan fada ko bada ita akeyi ba sai abunda yayi gaba Ballatana gata ga Hamida ga Hanne bata da wani Danuwa ranar ma A Hadda suka yi fada da Samira ta kan kujeran zama Amina ta mike ta Chakume Wuyan Hijabin Samira zata Jata da Dambe Mariya ta kada baki Tace Amina yanzu fa kin girma tunda ke matar aure ce wannan abun da kike yi bai kamata ba..Ku su hanne ku Fadamata gaskiya in zataji to..!
Amina sai taji ta Muzanta Ido ya Dawo kanta sai taji kamar ta Shake mariya ta kalleta ta murguda mata baki kafin tace"Ubanki na aura ammh ko..?
Wannan mganar yasa mariya ta kai kara wajen Mallam Datti akan Amina ta Zagi babanta Case din da sai da ya Jafar yazo makarantar mallam ya aikosa ya kashe mganar Tunda Mallam Dattin ya kira mallam awaya ya Fadamai.
Ranar ya Jafar yaso ya Daki Amina sai Mallam ya hana ya kuma yi musu gargadin har Abada Amina ta wuce Duka awajensu..ko ba domin darajan auran Dake kanta ba Domin Darajan Danmallam Dake mijinta bazai ji Dadin su daketa ba in yaji Labari.
Ya kuma fada musu suma Amina Uzuri Amina har yanzu yarinya ce dole ya kyaleta ita kuma sai ya Bita da Nasiha tamai alkawarin Insha Allahu bazata kara ba,Daga dai ranar ta kulla Gaba da mariya sannan Sa"adatu ta sha Habaici kala kala Domin ita ta yada Labarin Hanne da Hamida su dai yan bada Hakuri ne Amina bama jin mganar su take yi ba suna dai bata Bakinsu ne.


Hajiya sun yi mgana dashi Danmallam din tana chan maiduguri yana so ya kara mata mgana ammh kuma ya kasa ita kuma tana Sane ta bari ne sai ta Dawo tamai bayanin abunda mallam yace.
Har Haj.uwa sai da ta Fadamawa itama tace shawaran mallam tayi saboda Kada a rabama Amina hankali Daga karatunta,aranta kuma Tana Tunanin meyasa Danmallan ya Damu da Amina alhalin kowa yasan wannan auran ga yadda yazo sai dai ta kasa sanun amsa.


Sati Daya Hajiya sukayi Idi yaje ya Daukosu suka Dawo Mamanmu kuma sai da tayi kwana goma sannan ta Dawo Amina kuma Hajiya na Dawowa ta Tattara ta riga komawa gidanta tana kwana sai su hadu da Sakina ammh basa ma juna mgana Sakina gabadaya Tsanar Amina take ji Saboda gani take yi komai ya Faru ita ce sila Anty Amarya tace ta cika gajen Hakuri ta Daina kiranta in bata da mgana mai Dadi Ita kanta Anty Amarya a Rude take abubuwa duk sun shagule mata Tafiyar mamanmu Gusai sun hadu a Dutse sun koma wajen malamaminsu ya Tabbatar musu da cewa Umar zai dawo ya tafi da Sakina Sannan Burinta zai cika itama mamanmu ya Fadamata Sa"idu na hannunta sai abunda tace suka Zubemai makudan kudi Anty Amarya ta koma Gumel ita kuma ta koma Gusai saboda kada a Fahimci Tafiyarsu Daya.


********


Umar sunyi mgana da Sarood itama ta yarda kila shafan Aljanun ne suka fara amfani da mganin da ya siyo mata a Islamic Chamet na irin abunda suke Hasashe shima ta bangaransa ya Dake da Addu"a ammh bai kara Jaraba kusartar ta ba ya bari sai ta gama amfani da mganin sannan.
















*Janafty**TFZB2011*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*




Bayan Sati daya da dawowar su Hajiya Daga maiduguri Ranar wata lahadi da misalin karfe goma na Safe sai ga Aliyu a falonta Danmallam ya aikosa tun daga Dutse har gumel wajen Amina.
Hajiya mamaki ya cikata Lokacin da Ta fito falo suka gaisa da Aliyu yake sanar da ita yazo neman Amina ne mamaki bai bar Fuskar Hajiya Babba ba ta kalli Aliyu Dake zube saman Cafet din falon nata kansa a kasa cikin ladadinsa kamar abokin nasa
Sai da ta gyara zama kafin tace"Amina..?
Cikin sigar mamaki kansa na kasa yace"Eh Hajiya..Yace nazo ne na kawo mata waya yana so zasu yi mgana..
Hajiya tayi wani kayattacen mirmishin su irin na manya kafin tace"To ban da abun Danmallan don wannan sai ya Tadoka tunda ga Dutse har Gumel..haka ake yi..?
Ai da ya kirani sai na basa Aminar suyi mgana sannan ni nace zan kirasa nayi mai bayanin yadda mukayi da mallam kan wayar da jafar ya kawomin sai na manta zuwana Bikin nan sannan da na dawo ma ban zauna ba Sabga tayi yawa..!
Aliyu kansa a kasa bai ce komai ba shima so yake ya gama da Hajiyar ya fita ya Tsitsiye Shehi yaji Dalilin sa na neman yarinyar daya gama Cema kwaila kazama.
Hajiya tacigaba da Fadin"Tashi ka tafi abunka Aliyu Amina bata nan suna Hadda Yau ma inaga da wuri zasu dawo Saboda hutu zasu yi sun fara Jarabawar tun awanchan satin ne In ya kiraka ka Fadamai ya kirani muyi mgana..!
Aliyu kansa na kasa ya mike yana Fadin"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma mungode..!
Ta amsa da Ameen da Fatan ya gaida iyalansa daganan ya fice zuwa shashen maallam yamai sallama suka Hade da Anty Amarya ya gaisheta cikin Ladabi ta amsa tana kallonsa cikin mamakin ganinsa da Safe haka sai dai bata Tsawaita mamakinta ba Sanin Aliyun yana zuwa gaida Hajiya da mallam Lokaci bayan Lokaci koda Danmallam din baya kasar
Shashen mallam ya koma yamai sallama zai koma domin nan ya fara shiga suka gaisa bai dai zauna bane ganinsa suna mgana da Aba yace bari ya shiga ciki ya gaida Hajiya Mallam bai kawo ma kansa shima wani abu ya kawo Aliyu ba sanin Yadda yake Darajasu Dalilin kawai suna iyayen Abokinsa Umar.
Sallama sukayi yana ta sakamai albarka da Fatan Allah ya kaisa gida Lafiya kiran Danmallam bai shigomai ba sai da ya bar Gumel ya dau hanyar Dutse Gefen titi ya samu yayi fakin sannan ya Daga kiran nasa Daga chan bangaran Danmallan yayi mai sallama kamar yadda kowa yasan shi da zarar ya Dauki waya da sallama itace Farko a bakinsa
Aliyu bai wani amsa sallamarsa ba yace"Shehi wai miye sirrin ne..?
Umar yace"Sirrin na mene..?
Aliyu yace"To gani nayi ka bi ka Rude kan karamar yarinya sa"ar yarka ta Fari kuma kwaila..kuma kazama ka tadani Tundaga Dutse zuwa gumel haka Hajiya ma ta Dinga mamakin wannan aikin naka..!
Umar ya Dafe kansa dagachan bangaran kafin yace"meyasa ka bari kuka Hadu da Hajiya..?
Aliyu yace"Dole kuwa mu hadu don Daga Falon mallam shashenta naje neman Amina ta tabbatar min da batanan suna makarantar Hadda..!
Umar yace"Kash..Da tace haka sai kayi Tahowarka ba sai ka fadamata Dalilin zuwanka ba..!
Aliyu yayi wata Dariya kafin yace"Ai aikin gama ya riga ya gamu Shehi tuni na Rattafamata komai tace in munyi mgana Dakai na sanar maka ka kirata zaku yi mgana .!
Umar yayi shuru kafin yace"Kai dai baka da biyan Bukata duk ka bata komai ni fa kunyarta nake ji shiyasa ban kirata ba ita da mallam..!
Aliyu yace"Oho zakace haka mana Tunda na gama Biya ma Bukata akwai ai watarana ba agama ba..!
Umar yace"Naji bakomai dai nagode zan kirata yanzu..!
Aliyu yace"Ni fa baka Fadamin sirrin ba..!
Umar yace"Wani sirrin kenan..?
Aliyu na Dariya yace"Sirrin abunda ya susuta ka kan Aminatu mana..!
Umar ya saki karamin Tsaki kafin yace"bansani ba..!
Aliyu ya saka Dariya kafin yace"To to..Nagano Sirrin ma..Shiyasa jiya daka kirani bakace min wannan kazamar yarinyar ba kai Tsaye ka kira sunanta Tabbas yanzu ta tashi Daga kazama kwaila ta koma Sweet Amina..Ko Honey ce..?
Umar ya tsaki again kafin yace"Kai fa Dan iska ne..!
Daga haka ya Datse kiran Aliyu yabi wayarsa da kallo yana Dariya sosai in ya Tuna sanda aka aurama Umar Amina yana ta fada yar cikinsa ne ina zai kaita sai gashi kaji sa shuru ya shiga komar yara ya kasa sukuni.
Duk da yayi matukar mamakin yadda Komai ya faru Tsakanin Amina da Shehi sai dai bai Tsananta ba Sanin Tsakanin miji da mata sai Allah ammh Shehi ya bani a wajensa ya Dinga Tsokanarsa kenan.
Yana Mirmishin ya Tada motarsa ya bi hanya yana kara Dariyan Abokin nasa yana kuma Fatan yasa Amina ta mai mugun kamun da sai ya raina kansa.!


Bayan Tafiyar Aliyu Hajiya tayi ta Tunanin me yasa Danmallan ke son mgana da Amina haka da har ya kasa Hakuri..? Bata samu amsar ta ba sai tayi Tunanin kila yana so yaji Lafiyanta ne sannan ya tambayeta ko tana Bukatar wani abu daganan ta watsar da Tunanin ta koma Bedroom dinta tana gyarawa ba Dadewa ta samu kira Daga Danmallam bayan ta Dauka sumgaisa kamar yadda suka Saba sai kuma yayi Shuru yana jin kunyar yayi mata mgana ta san Halinsa Tunda ita ta Haifesa.
Yasa ta gyara Zama tana fadin"Dazu Aliyu abokin ka yazo..akan kai ka aikosa ya kawo ma Amina waya zaku yi mgana ko.?
Dakyar ya iya amsa ma Hajiya gani yake kamar zata Fahimci abunda ya Faru Tsakaninsa da Aminar.
Cikin Dattakonta ta cigaba da fadin"To nace yayi tafiyarsa Sabgoginsa ka taso mutum Tunda ga nisan Duniya Danmallam..! Ai sai ka Kirani muyi mgana ko ba Haka ba.?
Kai tsaye yace mata"Kiyi hakuri Hajiya..
Cikin Ladabinsa bata Damu ba tace"Ni ba laifi kamin ba..gani nayi ka basa wahala..Daman ina ta so na kira ka nayi maka bayanin Dalilin Dayasa ban bana Amina wayar nan ba duk da ni nace ka siya mata mgana mukayi da mallam ya nuna min Rike waya ga Amina yayi sauri sannan Duba da har yanzu akwai kuruciya a tare da ita..hakan zai Dauke Hankalinta har ya Taba karatunta da muke Fata ta Samu,ya nuna min na bari sai zuwa gaba in kazo ka tafi da itan sai ka siya mata wayar Lokacin tana gabanka zaka kula da Motsinta yanzu kuma ya nuna min gaskiya a"a shiyasa kaji Shuru ban bata wayar ba tana nan na ijiyeta..!
Cikin gamsuwa da mganar ta yace"Hakane Hajiya..!
Hajiya tace"To kaji yadda mukayi da mallam da Dalilin dayasa kaji shuru..Sannan yace in kana son jin Lafiyarta ne ka kirani ko mallam din sai in ta na nan sai abata ku gaisa..!
Danmallam yace"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma..!
Hajiya ta amsa da Ameen kafin tace"suna Hadda ammah ina ga bazasu Dade ba in sun Dawo zan kiraka sai na Hadaku..!
Cikin Ladabinsa ya shiga Fadin"Allah yasa agama Lafiya Hajiya Allah ya kara Nisan kwana..!
Ta amsa da Ameen suka rabu bayan ta Tambayi Iyalansa da ayyukansa.
To sun ma gama wayar ba Dadewa wajen azahar sai ga su Aminan sun Dawo suna ta Murna an basu Hutun Sati ukun Dadinsu Daya gobe zasu fara Exam din second Semister

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login