Showing 45001 words to 48000 words out of 145917 words

Chapter 16 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83966

a makarantar boko satin daya gabata Gabadaya Revision sukayi.
Amina ke fadin Dama islamiya ma ta bata da Hutu ai da sun ji Dadi.
Ba"a basu Sakamakon su ba sai Sun dawo Hutu sannan.
Anan Shashen Hajiya sukayi sallah Sukaci abinci Hajiya na ciki bata san Amina da Hamida sun koma gida ba Tana zuci zucin ta Kirata sai ta Kira Danmallam din ta Hadasu ko da ta Fito sai Hanne kawai ta gani a Falo ita ke Fada mata Su Amina sun tafi gida kai Tsaye tace Hanne taje ta kira mata Aminar.
Hanne ta mike ta saka Hijabi ta tafi tana zuwa ta iske su acikin Dakinsu har Amina ta kwanta bata ga mamanmu ba tana cikin Dakinta ta kwanta in ji Hamida jawaad ke ta wasa da Karamar kwallo a Tsakar gidan.
Da Farko Amina Dataji Hanne na Tashinta kin tashi tayi sai da tace mata Hajiya ke kiranta sannan ta Mike tana fadin"Kice Wlh Hanne..!
Hanne ta mike tana fadin"Au nace ma Wlh..!?
To ki zauna kin ga tafiyata..!
Amina ta mike tana fadin"Tsayani Hanne mu je..Fatana Allah yasa ba gida zata saka Idi ya kaini ba..!
Hamida da Hanne suka kalli juna kafin Hanne tace"To in chan din ne fa..? Ai kince gidan mijinki ne..!
Amina na saka Hijabi batayi mgana ba sai da ta gama sakawa sannan ta Dago Tana fadin"Ni yaushe na Fada..?
Allah ya isa na, wuta bal bal in ban Fada ba..!
Hamida na Dariya tace"Daman chan Allah ai ya ishi kowa Amina..!
Harara ta balla musu kafin ta bangaje Hamida ta wuce fuu hamida da Hanne suka.bita da kallo Hanne tace"Kamar an kara mata bala"i wlh bayan auran nan..!
Hamida tace"Kowa ma haka yake fadi..ya danmallam zai yi mganinta bari su koma Madina ki gani nan ta raina achan Ubanwa zata mawa .!
Hanne na Dariya tace aifa Daganan ta bi bayan Amina zuwa gidansu.
Koda Taje Amina da Hajiya na kuryan Daki Hanne na shiga Hajiya Data Kira Danmallam bai Dauka ba ta kalli Hanne ta nuna mata kofa Tana fadin"Jirata afalo..!
Hanne ta Tura baki kafin ta fita Amina ta Fakaici idon Hajiya tayi ma Hanne gwalo ita azatonta wani abun Dadi Hajiya zata bata sai da wayar Hajiya ta shiga kidan larabawa taga Hajiyqn ta Dauka ta mika mata tana Fadin"Karbi Mijinki ke son mgana Dake..!
Ta fada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Dakin Harda Rufo mata kofar Bedroom din Amina gabanta ya Fadi tabi wayar da kallo ga sunan Danmallan nan baro baro na kan Layi sai jikinta ya fara rawa aranta tace na shiga uku ni Amina Allah yasa ba wani Abu akace mai nayi ba..
Jikinta a sanyaye ta kara wayar kunne Daidai Lokacin da Sanyayyiyar Muryansa ta Doketa Cikin Sallama da Hausansa daya Cakude da Larabci.
Sai da ya kara maimaita Sallamar sannan ta amsa Bakin da jikinta na rawa Tun kafin ya gama rufe baki Tace"Ina yi..yini..!


Ajiyar zuciyar daya sauke har sai da ta jisa a kunnenta Dayaji muryanta sai yaji Salama da natsuwa Cikin Taushinsa yace"AMINA...!
sai taji kamar yafi kowa iya Fadar sunan nata jin yadda ya kirata ita bazata iya tuna ko yama taba kiran sunanta ba Haka ba, jin tayi shuru yasa ya kara cewa"Amina kina lafiya..?
Cikin Sanyin Jiki tace"Na"am..eh lafiya kalau..!"


"Ya jikin ki..? Ina fatan kin warke babu kuma inda ke miki ciwo..?
Ya fada kai Tsaye domin baya Fatan ace wani abu kuma ya tashi bayan Tafiyarsa kunya ta kama Amina ta Dukar da kanta kamar yana ganinta ta kasa mgana sai gabansa ya Fadi da Sauri yace"Ko da wata matsala ne..?
Da Sauri tace"A"a na warke..!
Afili ta Furta"Alhamdulillah..!
Kafin yace"Naji Dadin haka ina Fata kamar yadda kikamin alkawarin baki gayama kowa ba ko..?
Sai da ta gyadamai kai kafin tace"Eh ban fadama kowa ba..!
Cikin jin Dadi yace"Dakyau naji Dadin Haka..Ya karatu fata kina maida Hankali wajen karatu..?.
Da Sauri tace"Eh yau ma mun yi Hutun Hadda..Gobe ma zamu Fara Jarabawa a boko..!
Kai ya gyada kafin yace"Allah ya bada sa"a..ki rika maida hankali kinji ko..?
Ta gyada kai ya cigaba da Fadin"Sannan ban da wasa ban da Fada ban da gujeguje ke yanzu ba yarinya bace kin tashi Daga su Hamida ke matar aure ce ba Daya kike Dasu ba kina jina ko..?
Nan ma kai ta gyada mai yace"Baki da baki ne..!
Ba nace ki daina min mgana Da kai ba .!
Da Sauri tace"Naji insha Allahu..!
Ajiyar rai ya Sauke kafin yace"Kina Bukatar wani abu..?
Tace bakomai kai Tsaye yace"Ki rika gaida Sakina in kun hadu tana gaba Dake kinji ko..?
Amina ta Tura baki kafin tace"Ni fa in na ganta batamin mgana sai tayi ta Hararana har zagina ma tanayi..!
Cikin mamaki yace"Ita Sakinar..?
Amina tace"Eh shiyasa nafi son zaman nan fiye da chan sannan achan ina jin Tsoro da Daddare bana iya barci don Allah ka Fadama Hajiya ta rika barina ina kwana anan in ka Dawo sai na koma achan..!
Kawai sai ta sakamai kuka sai yaji Hankalinsa ya tashi meke Damun yarinyar nan ne Cikin Tausasa Murya yace"Naji ki daina kuka zan mata mgana..Daman baki daina Firgita cikin barci ba..?
Tace mai eh sai da yayi shuru kafin yace"Ki samu mallam yau da Daddare in ya natsu ki Fadamai abunda kike jin in zaki Firgita kin ji ko..?
Tace"Na Fadamai..?
Yace"Eh ki Fadamai sannan mganar Zagin ki da Sakina ke yi kada ki Fadama kowa har su Hajiya zan mata Fada insha Allahu zata Daina ke dai in kin koma gidan kun Hadu ki rika gaisheta saboda ko bakomai Tana gaba Dake kuma a islamiya an koya muku yin biyayya ga na gaba da ku ko ba Haka ba..?
Tace eh ya cigaba da fadin"To ki rika bata girmanta kin ji ko..?.
Ta amsa da toh bai Tsawaita mganar ba yace"Zan ce ma Jafar a Cefanan wannan watan ya siya miki Goldenmorn da Cornfkles Saboda Saukaka miki Wahala sai ki Rika sha in zaki tafi makaranta..!
Tace "To nagode..!
Ya amsa ta da Fadin"Kada ki damu komai kike Bukata kada ki tambayi Hajiya ko mallan ki yi ma Jafar mgana ko kuma ki Dauki wayar Hajiya ki kirani kinji ko..!
Nan ma tace mai da toh tagode Dagnan yace ta maida Hankali a karatunta ta amsa mai Daganan ya mata sallama ya kashe wayar.
Tabi Wayar da kallo Tana Tura baki wai ta rika gaida Sakina Tab wannan mara mutumcin ne zata gaisheta..
Shi kuwa sai da sukayi mgana yaji Hankalinsa ya kwanta har ya natsu ya Cigaba da Duba Takardun Dalibansa da sukayi gwaji.
Da suka gama wayar kunya ta Hana Anina fitowa sai da Hajiya ta Shigo Daukan abu ta ganta zaune tayi shuru tace"A a Mamah tunda kun gama wayar ki fito falo hanne na jiranki mana sai ki zauna ke kadai..!
Jin haka yasa ta mike ta mikama Hajiya wayar, ta karba ta Fice da Sauri Hajiya ta bita da kallo tana Mirmishi a Cikin aranta tana Fatan addu"an su Allah ne ya karba na amitar da Ruhin Amina da Danmallam waje daya.


Amina na fita Hanne ta taso tana Tambayanta da wa tayi waya Amina ta balla mata Harara kafin tace"Bansani ba..!
Hanne na Dariya tace"Nasani Ya Danmallam ne..ko..?
Amina ta mata wani kallo kafin tace"In ma shine sai na Fada miki..?
Sirrin miji da mata..!
Hanne ta saki Dariya kafin ta Ja Hijabinta tana fadin"Bari naje na gayama Hamida..Sabon Update..!
Amina tayi Tsaki kafin tace"Ai ke Hanne mijinki ya shiga uku..duk wanda ya aureki ya auran ma kansa sai kin hada Fada a Family din mijinki Saboda munafuncinki..!
Hanne bata bi ta kanta ba ta fice Amina tayi zamanta Falon Hajiya chan sai gasun dawo Tare Hamida sai kara maimaita abun da Hanne ta gayamata take yi Amina ta musu wani banzan kallo kafin tace"kusan dai ni yanzu ba Sa"arku bace ko..?
Igiya uku ne akaina..Taimaka muku ma nake yi ina yawo da yara. !
Hanne da Hamida suka saki baki ganin haka yasa ta Musu gwalo tatashi da gudu ta Fada Dakin su Hanne Tana Dariya suka mara mata baya suna fadin yau sai ta gayamusu su waye yara..?
Ranar dai anan suka wuni Shashen Hajiya suna abunda suka saba sai bayan sun dawo islamiya ne Hajiya ta saka aka maida Amina gida tana kunkuni Tana komai bata samu yima Baba mallam bayani ba sai washegari da suka dawo makaranta ta Fadamai ya Dade yana mamaki ya tambayeta yaushe ta fara tsorata tace tun tana karama ta dade mallam ya Dinga Fadin Sakacin mamanmu da Aba da Amina na Fama da wannan Laluran ammh bsu sani ba Hajiya ce ma ta Lallasheshi ya bar mganar da yace har Aba din sai ya kira da mamanmu ya musu Fada.
Shi ya Rubuta mata addu"o'i ya bata yace ta Rika karantawa Duk Dare in zata kwanta Tare da Sauran addu"an barcin da Annabi ya koyar damu.
Amina yadda Taga Mallam ya Dau abun ne yasa itama bata Dauka da wasa ba sannan Danmallam ma sun sake mgana da wayar Hajiya Data Fadamai yadda sukayi da mallam ya mata Fada kan ta Dage kada wasa ya Dauke mata Hankali ta rika kwanciya bata karanta su ba.
Shiyasa ta Dake bata kwanciya sai ta karanta sai gashi kuma Cikin ikon Allah tunda ta Dage sai ta samu Saukin Firgita din sai abunda ba"a rasa ba Danmallam har da mallam sun yi mgana Mallam nata fada yana Fadin da Haka Umaima ta Fara gashi nan suna so su taba mata kwakwalwa Dannallam yana so ya Fadama Mallam bayan haka ma yana Zargin akwai wani abu Tattare da Amina sai dai kuma bai da Hujjan hakan ammh yana so sai in ya kara Dawowa ya Zauna ya Fahimci matsalanta Domin Ranar da abun nan ya Faru tsakaninsu da Washegarin nan da Safe yaga tana wasu abubuwan da Dole tana da wani abu a Tattare da ita.




*******


Kwantashi ba wuya a wajen Allah su Amina har sun gama Jarabawarsu sun yi Hutu taso ta zauna anan tayi Hutunta Hajiya ta hanata sai ta Roki Baba mallan kan su Hanne su Bita ko Sati Daya su yi da Farko Hajiya ta Hana sai da Mallam ya saka baki Sannan ta amince suka Tattara suka koma chan da Niyar Sati Daya zasu yi Saboda islamiya basu yi Hutu ba.
Mamanmu bata Damu ba da akace Hamida zata je gidan Amina Domin alokacin tana Tsakar Cin Duniyarta ne Domin komai tace Aba ya bata baya Gaddama Kudi yake sakar mata bana wasa ba ta zama Tauraruwa a wajen sa Mamanmu ta samu Cikar Burinta Fiye ma da yadda take fata shiyasa ta manta da kowa da komai ko Anty Amarya ta kirata bata ma kaunar Hakan gani take tana neman Takura mata Shiyasa Amina ma bata gabanta Ta barta da Anty Amarya chan itace Zatayi mganinta ita yanzu Sa"idu ne agabanta yanzu shawaran komai sai yayi da ita sai abunda tace koda yace Jafar yace kaza ya kamata ko Hajiya sai tasan yadda tayi ta Kushe mganarsu ta sauya da nata Shiga kawai take tana fita Daga kayan alfarma kamar wata Yarinya sannan Malaminsu tana sakarmai kudi sosai Domin ta yaba da aikinsa
Anty Amarya kuma tana nan tana Jiran gawom Shanu domin ta yarda da aikin Malam ya sanar da ita Nasara tatace shiyasa bata Damu ba ta koma ta Zauna tana jiran tsammani kamar yadda ta basa duka yardanta Shiyasa ko Sakina ta kirata tana mata Korafi take mata Fadan bata da Hakuri aiki nawa suka basa kuma ya Biya musu Bukata..?
To wannan ma ta Zauna ta Jira komai zai zama Daidai da yardan Allah abunda basu sani ba Daga wannan Lokacin aikin ya kuskure musu sannan zasu cigaba da jiran majirata ne Jiran da zai kai su ga Ranar Nadamar su da Tonon asirin su..!


Ko Hutun da su hanne suka tafi Sakina kamar ta Haukace saboda Bala'i Amina Mahaukaciya take so ta maidata,gwara ma su Hanne suna dan jin mganarta banda Amina sai ta gama masifarta sun ba'ta mata Falo ko Kitchen Amina ta mata gwalo ko Ta mata Tsaki ta shige Daki abunta Sakina taci ji Yatsa kamar me..?
Kamar yadda yace a Cefanan watan nan an kawo su Goldemorn su Amina an samu banza ana ta Wadaka madara kuma da kayan Tea kafin Sati sun kare saboda yadda suke barnan sa basa da aiki sai dan sululu ko Wainar Fulawa gashi Sakina bata son kazanta su kuma in suna aiki a Kitchen din sai sun yi kaca kaca dashi in tayi mgana Hanne da Hanida kadai ke Sauraranta banda Amina da take maidata ma mahaukaciya.
Sakina abun ya isheta kullum sai ta Kira Danmallan ta kaimai karan Amina da kannensa shi har ma ya gaji Saboda bai isa ya kore su ba Amina Matarsa ce sannan su Hanne kannensa ne ko ba aure suna da Damar zama agidansa watarana da abun ya ishesa sai yace ta bama Amina wayar da an bata ya fara mata Fada sai ta saka kuka tace In ta gaishe da Sakina sai taki amsawa ta bita da Zagi sannan bata barin su suna shiga Kitchen sai tace suna mata kazanta Ayadda take mgana ne yasa Dole ma ayadda da ita sannan tace ga su hanne ma yaji ta bakinsu su hanne kuma basu taba kwaye ma Amina baya ba, sai su karantamai yadda Amina tace Daga karshe sai abun ya koma kan Sakina yayi mata Fadan itace babbar banza tana Biyema yara sun rainata sannan kada ta kara Hanasu shiga kitchen ta bar su dafa abunda suke so itama ta Dafa nata baya son Fitina.
Tunda ga ranar ko Takai ma Korafin Amina ta mata kaza bai Sauraranta Anty ma Zaginta take yi tace ta Daina Danunta tunda ita Sakarya ce zata Zauna yara kanana su gagareta
Alhalin basu san yadda yaran nan suka Sakata gaba bane barin ma Amina in ta fito falo ta gansu ta rika waka kenan tana cema mata agwagwa in ta yi mgana ta maidata mahaukaciya sannan ba Tsayawa ma take yi ba,ballatana ta Daketa ta huce.
Su hanne wajen kwanansu goma Daga su Har Aminar basa zuwa makaranta da Hajiya tayi mgana ne Mallam yace ta rabu dasu Idi ya rika zuwa yana Daukosu yana kawo su makarantar Daganan,saboda dukkansu yara ne sannan nan gaba kadan In Aminar ta bar garin ina zasu ganta..?
Sannan kuma suma watarana gidan auransu zasu watarana sai dai labari..da Haka ta kyalesu suka zauna achan sai dai Idi ke zuwa yana Daukosu da an tashi kuma ya maida su.
Cin Duniyarsu da Tsinke suke yi ko ajikinsu Sakina ta koma zaman Daki bata Fitowa saboda su in tana son Tsira da Mutumcinta Ranar kwatsam sai ga Aliya matar Aliyu sun zo kawo Amarya wata Diyar kanwar mamanta ne shine tazo gidan ta iske Sakina cikin Daki Amina ta gagareta bata iya ma Fitowa sanda Sakina ke Fadamata tana kuka Sai taga Laifin Sakinar da ta Zauna yarinya karama ta gagareta.
Taja Sakinar suka fito su Amina na Falo sunyi Daidai ga Filets nan da Kofuna da gorinan lemuka da suka gama dasu nan basu Dauke ba suna Hira Ita a Dole sai ta kwatan ma Sakina yancinta..
Haka ta Dinga surfama Amina Zagi tana kiranta kwaila kazama mara Tarbiya su hanne sukayi Tsuru Tsuru Amina ranta ya baci ta mike ta rama Zaginta da Aliya ke yi ita kuma tace Zata Daki Amina ai ko sun ga Hauka Amina ta Tsaya kikam idanuwanta sun juye ba baki sai Fari tace in Aliya ta isa ta tabata tagani Sakina ke jan Aliya tana ta bari kada ta tabata ta ja mata bala"in wajen su Hajiya.
Ita kan Aliyan ta Tsorata bata Taba Aminar ba suka koma Daki tana Borin kunya Amina kuwa ba wani Abunda ya Sameta Zafin ranta ne ya taso mata Taso ta tabata ne Daga Sakinar har Aliyan sai sun raina kansu Wlh sai kuma Allah yaso su su Hanne na tabata Hakuri ta balla musu harara tace sun cika Tsoro ba wanda ya isa ya Takura musu acikin gidan nan.
Aliya taso kwana ne ammh ganin yanayin Amina yasa taki kwana ta koma gidan Amarya ta kwana ko Washegari Datace zata dawo bata Dawo ba ko da Sakina ta Kirata tace mata gata a Hanya zata koma gida ammh Tana zuga Sakina kan Wlh in Amina ta kara mata rashin kunya ta kamata ta mata Dukan tsiya Sakina jinta kawai take ina ita ina taba wannan yar gold din ai sai Hajiya ta saka Umar ya Saketa.
Allah ne ya taimaketa suka koma makaranta Hajiya tace su Dawo gida idi yazo ya Dauketa sai ta Samu Sauki Bata ma haduwa da Aminar sai ta bar gidan take Fitowa sannan Daga ranar jumma"a sai Lahadi take dawowa tana ganin Lokacin Dawowarta yayi zata shige Daki karfi da yaji Bala'in Amina da jindalinta ya Saka Sakina ta kasa Sakewa agidanta.
Gashi Danmallam ya Daina Sauraranta indai kan Amina ne yace yana wata kasar ta daina tadamai da Hankali baya so in bazata kama girmanta ba bazai iya Hana Amina ta mata Rashin kunya ba abu goma da Ashirim ga rashin miji ga Fadan Anty Amarya Data Kirata sai tace laifinta ne sannan ga Amina ta Sakota gaba..!
Ana cikin Haka Sadiya Diyar Anty Amarya ta Haihu bakwaini yarinyar tazo ba rai anan Dutse su Sakina ana ji sune gaba gaba ita da Hj.Nasara da Hajiya Babba suka tafi suka Duba Sadiya Dake asibiti domin ance ta Zubar da jini sosai achan suka Rabota Tunda Danmallan ya barta ita ta zauna da Sadiyan har aka sallamota Daga asibiti duk da ga yan"uwa ammh Anty Amarya tafi yarda Sakina ta Zauna da Sadiyan.
Bayan sun Dawo gida ne Sakina ta Fara Zazzaabi har da su karin ruwa koda akaje asibiti akayi Test aka gano Tana da Shigar ciki kimanin wata Uku da kwanaki Ashe koda Danmallam ya Tafi ya jefa kwallinsa araga a maran Sakina basu sani ba.
Murnan wajen Anty Amarya da Sakina ba"a mgana kamar an basu aljannah Hajiya da mallam ma Tare da shi kanshi gogan Danmallam Domin yana matukar son yaga kwansa a Duniya,Sannan da kansa ya Sanar da Sarood ta tayasa murna Har dai yanzu shuru ne ba wani cigaba ammh basu sare ba suna cigaba da shan mgani shi dai har yanzu ne bai yarda da Shawaran Aliyu na ya kira mallam ba yana tunanin al"amarin nasu ba Sihiri bane.


Mamanmu dataji itama tayi murna sannan tasan yanzu tunda Cikin Sakina ya samu sai Madina ta barta taci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login