Showing 144001 words to 145917 words out of 145917 words
yana nan yake tayata Reno Sai Daga baya ne ya siya mata layin chan ta saka suna mgana da yan'uwanta Amina daman kusanta da son yawo ballatana an samu garin Madina tuni tasan ko"ina Ballatana ma da Surraya ta Kirata tazo gidanta ta wuni itama Ranar Danmallam ya kaita ta wuni Amina ta sami Sake tunda Danmallam bai mata shamaki da Fita ba Saboda wani Lokacin baya kusa ko yana cikin makaranta waya kawai Amina take mai tace zataje masallaci Kusan koda yaushe nan take sallar mangariba da Isha"i kafin kace me Fatar ta Goge ta zama kamar bakar Balarabiya atamfa sai tana Gida in zata fita kuma Jallabiya ce Ita da kyawawan yaranta gwanin ban sha"aawa..!
Watan Amina Daya da zuwa Madina Sarood ta Haifi Yar mace kyakyawa a gida ta Haihu sai daga baya sukaje asibiti aka Dubata Yarinya kamar tace sak kamar yar larabawa,Amina tana zuwa kullum saboda suna dan dasawa da Sarood Tsakaninta da Sakina kuma sama sama ne ko" ya"yanta sai a bayan idonta take Dauka In Amina na wajen bata bari Har Danmallam yaso yayi mgana Sanin Jidalin Amina yasa bai mata mgana ba..!
Ba suna akayi ba an dai yi taro na Murna Har Surayya sai da tazo wacce suka kulle da Amina suka zama kawaye Ballatana da Surayyah ke kaunar Amina Saboda Allah sannan tana son Haihuwa shekara tara da auransu bata taba ko batan wata ba..!
Agida Nageria an ta kira ana ma ya Danmallam barka da arziki sannan yarinya taci sunan Hajiya wato Zainab suna kiranta Banu princesss..!
Sai da aka tura musu Vidoes da Hotunan Bby kamar yar Labarawa to ai uwarta balarabiya ce..!
***********
*BAYAN SHEKARU BIYU..*
Bayan shekaru biyu da komawar Amina Madina da zama abubuwan alheri sun faru sosai ciki har da karin Haihuwan da Amina da tayi ta Haifi mai sunan Yaya Hadiza suna kiranta Iman,Sannan Amina ta koma jami"ar Madina tana karatun a bangaran Islamis studies,Sannan Yakaka tana wajen Amina Danmallam ya cika alkawari yayi ma yakaka takardan zama agarin na har abada tazo tana zaune a gidan Amina suna tare.
Sannan Sarood ta kara Haihuwan Namiji yaci sunan Kattab suna kiransa da Kattab dinsa..!
Sannan Danmallam ya cikama Amina Burinta taje Saudiya ta Sauke Farali Taga ka"aba tayi addu"a sosai addu"o"in da tayi Fatan ta roka ma kanta da iyayenta da mijinta sannan bangaran su Hamida duk sun haihu ita da Hanne wacce ke da wani Cikin ya Aisha ma ta Haihu su ya Zulaihat ma Duk sun Tara zura"a..!
Sannan an samu rashi Mamanmu ta amsa kiran Allah Rasuwarta ya girgirza Amina sai da tayi kuka basu je ba ammh ta Kira yan"uwanta ta Musu gaisuwa Hajiya uwa na nan kwance Jinya taki karewa sannan Anty Amarya kam ta Haukace abun dai ba Dadin ji sai ka tsausaya ma ya"yansu saboda Halin da iyayensu ke Ciki bayan tahowarta sun je gida Sau Daya dukkansu shima rasuwar Umaima ce ta kai su Umaima Allah yayi mata rasuwa wahala ta kare ance Mutuwarta ce ta kara girgiza Hajiya uwani Jikinta sai ya rikice..!
Sannan bayan Dawowarsu Hajiya da Mallam da Aba da Anty Hadiza da ya Jafar da ya Nasir da Aliyu suka zo Madina Aikin Hajji basu sauka agidan Danmallam ba suka kama Hotel kar su kara musu nauyi sai dai sun je sun ga inda suke Dukkansu har gidan su Sakinar sannan suna Haduwa a masallaci gabadayansu sannan a wannan shekaran ma suma sun isa makka sun kara Sauke Farali.
Basu Dawo ta Madina ba Daga makka jidda suka koma suka hau Jirgi suka koma Nageria cikin jin Dadin yadda suka ga Danmallam shi da iyalansa cikin Shiga mai kyau da muhalli.
Su Aba kuma suna Tafiya ba inda basa zuwa sun yi wayau suna da Shekara Biyu Cikin na uku ga Imam har tana Rarrafawa..,!
********
*MURFI..*
Yau tun safe Amina ta kasa sukuni ita ke da Miji yau,Sai shiga take tana fita,Tana Sanye da riga da wando na pakistan, Amina da ta zama babbar mace yanzu yar kimanin shekaru Ashirin da Daya a duniya.
Iman tana rarrafe nan tsakar Falon Yakaka na zaune gefenta Mallam ke hawa bayanta yana Sauka Aba kuma na rike wuyanta Yakaka na fadin"Sai kun karisa ni kenan..!
Take fada tana Dariya Iman ta Rarrafo Tana turesu Yakaka tace"Yauwa uwar Hakuri Korar min su..!
Amina na jinsu hankalinta baya kansu Alkubus take yi ma Danmallan yau da Miyar agusu saboda da sukaje Gida tazo dashi,kuma ya Kirata yace yana so tayi mai shi haduwarta da Surayyah yasa ta kara kwarancewa wajen girke girke da Sannin siirukan Zama da miji Har gobe tana godema Allah tana godema Hajiya domin sune Sillar Inganta rayuwarta ita da mallam.!
Hankalinta bai kwanta ba sai da gama komai ta gyara gidan yana tashin kamshin Turarukan wuta masu kamshi Sannan yakaka tama yaran wanka suka Fito Tsab suna tashin kamshi suma Sannan banda Yakaka bamai ma yaran Hausa Babansu Larabci yake musu ita kuma Amina Tana musu labarci da Turanci Kuma yaran sun iya domin sun fi iya yaran fiye da Hausa sannan suna zuwa wata Tahfiz su Aba tun Safe sai yammah shiyasa harshensu ya tashi da Labarcin sosai.
Yakaka ce ma ke fadan meyasa basa musu hausa suna Hausawa suna wani iyayi ita dai Amina sai dai tayi Dariya bata mgana.
Iman ce suke bala"in kama da Banu din Sarood itama kamar Sarood din ta Haifeta ga gashi gata kamar yar larabawan wasu ma Dauka suke Sarood din ta Haifesu Amina ta yarda da komai banda Sakin Ragamar mijinta da ya"yanta wajen kishiya abunda ya Faru agidansu ya zame mata izinina..!
Bata dai mufin kowa da Sharri..Ammh Sama sama ne gwarama Sarood har lambar wayar juna suna da ita banda Sakina da Amina bata ma son tana Daukan mata yara Ita kuma ga son yara wlh kamar kayi mata kuka akwai ranar dasu Amina sukaje chan gidan Iman ta rarrafa wajenta ta Dauketa Amina ta karbe yarta abun yayi ma Sakina zafi tayi ta kuka har sai da yakaka ta mata Fada Sannan ta Sanar ma da Danmallam ya mata Fada ai Amina data Fara Fushinta sai da Danmallan ya raina kansa ya koma yana Lallashinta abunda ya Faru ya sa ma Amina rashin yarda kuma shi bazai iya Cire mata wannan abun acikin ranta ba sai dai ya tayata da addu"a..!
Yau bata shiga mkaranta ba sai gobe take da karatu kuma tasan sai bayan Isha"i zai shigo gidan shiyasa kafin Lokaci ta shirya Cikin Riga da wandonta,Masu roba sun kama jikinta Sosai ta taje gashinta ta Daureshi Tana gayu dashi yaran sunci abinci da yakaka Iman kuma ta bata Nono har tayi barci tana Dakin yakaka su Aba nata Damunta da Hayaniyarsu sai ga ya Danmallam ya Shigo Gidan Amina taje ta Tarosa kamar yadda ta Saba ya rumgumeta yana Kiran sunanta.
Noor nayi kewarki..!
Itama tace nayi kewarka Hubby..!
Danmallam daya kara zama babban mutum kimanin shekarunsa na Haihuwa Arba"in da biyar kenan ya kara haske sannan Hutu da jin Dadi da yanayin zaman garin madina yasa ya koma kamar balarabe sannan uwa uba kulawar matansa garesa musamman Amina sun taimaka wajen bayyanar da kwanciyar hankali ajikinsa da zuciyarsa.
Jansa Amina tayi zuwa Ciki bayan ta taimakamai yayi wanka suka fito Falo sannan yaran sukaji muryansa suka Fito suma na mai oyoyo.
Ya rumgume su yana Murnan ganinsu Yakaka ta fito suka gaisa sannan ta Janye yaran suka koma ciki Sai Amina ta Fara Cinyar da Mijinta kamar yadda ta Saba yana ci yana kallonta aransa yana saka mata albarka.
Suna gamawa ta kwashe komai takai Kitchen sannan suka Tallafi juna zuwa Cikin Bedroom dinsu
Suka Zube kan gado Amina ta Haye saman ruwan Cikin ya Danmallam tana sukuwa Dayake ya Cire Jallabiyan jikinsa Dagashi sai karamin wando..!
Danmallam na nishi yace"Noor kefa ba yarinya bace yanzu..shekarunki ashirin fa..!
Amina tace"Kama ragemin na shiga da Daya..!
Dariya ya sakamata yana Shafa Cikinta yace"Ammh har yau kina nan kamar yar sha shidda awajena Menene siirin..?
Amina tamai Fari kafin tace"Kai ne Sirrina Hubby..!
Kansa ya shafa yana Fadin"A hakan..?
Na fa fara Furfusa Noor Shekarata arba"in da biyar fa..?
Amina ta kwanta akan jikinsa tana Fadin"ahakan kafi min dan shekara Ashirin da bakwai kai ai Jarumi ne Hubby..!
Yana Dariya yana kara shafa Cikinta yana Fadin"Ko nayi ajiya ne..?
Da sauri tace"Ba ruwana ni karatu nake yi.!
Danmallam ya marairaice yana Fadin"Karatu yafi ki haifamin yara ne Noor..?
Kinsan yadda nake jin ki a zuciyata kuwa..?
Wlh ina miki son da bansan kwatankwancinsa ba..Abu daya na sani kin FITA ZAKKA Amina..A ko"ina ke Zakka ce..!
Amina ta runtse ido Dadi na Ratsata kafin tace"Na sani Hubby..Nima zolayarka nake yi..Bani da wani Buri sai na yi ta Haifa maka ya"ya ina saka ka cikin Farinciki da Annushuwa..!
Danmallam ya rumgumota sosai kafin ya Hade Bakinsu waje Daya Amina ta Tallabesa na wani Lokaci kafin su Dago su kalli juna Danmallam yace"Ana Behabbeki Noor..!
Itama tana kwanciya saman kirjinsa tace"Ana Behabbika ya Hubby..Behabbeka Kathiran..!
Daga haka ya sakata Cikin jikinsa sosai suka lula wata Duniyar da ya Danmallam kadai yasan inda take...!
*Tammat Bihammdulillah..Alhamdulillah Alhamdulillah Allah ne abun godiya Salati tare da Tsira su tabbata ga Annabin Rahma Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wasallam Tsira da gafara da salama su tabbata kan iyalansa gabadaya Nagode ma Allah da yau Laraba 26 ga watan October na sauke Nauyin hakkin ku dake kaina Masha Allahu naji salama da sukuni Ina godiya gareku Dimbin masoyan Labarin Aminene bakina yayi kadan wajen nuna muku godiyata naga soyayya da kauna har ba iyaka ni ban isa nasan Karshenta ba sai Ubangiji ne ya sani Sannan jinjina da godiya ga Masoyana masu son cigaba na da suka iya cire wani abu daga cikin kudinsu suka siya karishen wannan Labarin ina matukar godiya yan group din TFZB2BANDGROUP,Allah ya bar Zumunci Nagode sosai sannan ina Fatan zaku min afuwa Saboda duk Dan Adam Tara yake bai gama cika goma ba Ubangiji Shi kadai ne ya cika Cif dari bisa Dari ni yar Adam ce kuma mai Kuskure ce kila acikin Rubutun nawa akwai inda nayi muku Daidai kila kuma akwai inda na Saba muku to ina mai baku hakuri ku yafemin Ajanci ne na Dan adam sannan ban isa na Rubuta Daidai Dari Bisa Dari ba kila ba haka kuka so Labarin ya tsaya ba sai kuma ya tsaya a hakan to ku sani kuskure irin ne da ajanzi na dan adam,Ina Fatan zaku yi amfani da abunda kuka karanta mai amfani zaku zubar da na banza,Sannan ku tayani rokon Allah ya Hadamu cikin abunda na Rubuta na Lada acikin wannan Tafiya kuskurena da zunuban da na Rubuta kuma Allah ya yafemin su domin bada gangan nayi su ba acikin Rashin Sani ne Daga karshe zan mika sakon godiyata ga yan"uwana Janaf gabadayansu tare da Daukacin BA"ARE'S Family Allah ya bar zumunci Sannan ina mika sakon jinjinta ga Masoyiyata Aisha muhammad Alto da uwata Ummi Khadija Salisu yusuf ina gaisuwar ban girma gareki Besty na Halima yusuf gwarzo dake da Tawaganki gabadaya irin su Suwaiba,Mrbb,Saratu,Da Duka wadanda ban ambata ba ina godiya da karamcinku da kaunar ku gareni ku sani Janafty mai karban masoyanta ne Hannun biyu da kuma Godiya garesu Bissalam nan zan Dakata sai kuma in Allah ya kara Hadamu a Wata Tafiyar in muna Raye da yardan Allah..Nagode..Nagode Nagode Allah ya bar zumunci Ameen..Sannan ku sani duk wacce ta cire kudi ta siya Littafina na adana Lambarta acikin wayata domin ku din masoyan gaskiya ne.*
_Kamar yadda na Fada TA FITA ZAKKA zai zama Softy Copy and Hardcopy to Softy copy ya kamallah saura Hardcopy ga masu Bukatarsa Bugaggensa zasu iya min mgana ta wannan Lambar domin jin yadda Tsarin yake 09069067488_
AMEENA 24 HOUR'S HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on
07014979567
WhatsApp ONLY