Showing 129001 words to 132000 words out of 145917 words
ya Tabbata in ya Biye mata sai ya shiga Wuta.
Ganin yanayin Sarood din itama tana Fama da Laulayin jiki yasa ya Zage ya taimaka mata suka gyara Gidan suka share ko"ina Girki kuma yace kada tayi ta kwanta ta Huta zai taho mata Dashi Daganan Gidan mallam ya koma sukayi sallar Isha"i sannan yayi musu sallama ya nufi gidan Amina ya Iskesu afalo ta baje suna ta Faman Hira da yakaka Sai Hankalinsa ya kwanta..
Yana shiga Daki ta Biyosa Lokacin yana ta Tunanin abunda zai ce mata tana shigowa tace mai bari tayi Fitsari ya Bita da kallo Tana tafiya Dakyar ta Shige Tiolet sai ya fita Falo ya samu Yakaka ya roketa tayi ma Amina bayani ya kasa Yakaka tace kada ya Damu yayi tafiyarsa zata fadamata Tsorin Jidalin Amina yake yi shiyasa Daganan bai koma Falon ba ya Fice Tana Fitowa taji karan Rufe get dinsa ta kalli Yakaka tana Fadin"Hubby ya Fita ne..?
Yakaka tace"Ya koma gidan Yar"uwanki chan zai kwana..!
Tafada tana Hade rai tasan Halin Amina gwara a mata Zafi Zafi
Amina taji dan Cikinta ya motsa da Sauri tace"bangane ba..?
Ina kenan..?
Yakaka tace"Mallam yace ya Dauki matarsa su koma gidansu wannan balarabiyar kinga ai tunda suka zo tana gidan mallam ke kuna ba kuma Tare da shi anan ba..?
Sai Amina ta koma ta Zauna akasan Cafet ta Rushe da kuka tana Fadin"Shine ko yagayamin..Ya kama Hanya ya tafi wajen wannan banzar matar tasa..?
Yakaka ta saki Baki kafin tace"Yau naga Tsiya..ke da zaki godema Allah miji na sonki Yan"uwansa kowa naji Dake..Ita wacce kike kishi akanta uban wa ma ya Damu da ita Labarci nan dai kinsan ba kowa ke jinsa ba..Bata da wani Sakewa kamar mujiya ki godema Allah bawan Allah nan na tafe rawan jiki akan ki ke bakya gani kina wani shanshanci ke kika sani..!
Yakaka ta karishe da juya mata baya tana cire naman Daya makale mata a Hakori da tsinke domin Amina ta bata na zamani tace ta rabata tayi da wanda ta sani Amina mganar Yakaka bai sa ta Daina kuka ba Domin wani Kishi ne ya Rufe mata ido har wani Duhu Duhu take gani sai da ta gaji da kanta ta Daina gani kuma Yakakar tayi mata banza ta cigaba da Harkokinta yasa ta tashi da Turtsetesn Cikinta ta koma Dakinta ta kwanta tana Sauke Numfashi Yakaka ta Bita da kallo kamar tayi Dariya
Har Washegari a kumbure tatashi Yakaka kala batace mata ba bayan gaisuwa Tana da garin kuni da Hajiya ta saka aka Dakata mata Yakaka ta Dama shi Sannan tayi musu Fanke bata jira Amina ba Data gama ta Dibar mata tana Tura Baki tace ta koshi Yakaka ta Kalleta kafin tatabe baki Tana Fadin"Ke kika sani..!
Daga haka ta koma Falo ta sha kununta ta ci fankenta ta koma ta kwanta chan wajen sha daya na Safe Danmallam ya shigo gidan anan Falo yaga Yakaka ya Durkusa ya gaisheta ta amsa Cikin Fara"a.
Kansa na kasa yace"Yakaka ina Mutuniyar taki na ganki ke kadai..?
Yakaka ta tabe baki tana Fadin"Waya sanin mata..?tun jiya da ka tafi na Fada mata ka tafi wajen balarabiyar nan take kuka sai da taga na mata banza ta Rarrafa ta koma Daki yau fa Da Fushin tatashi ko abun karin da nayi bata ci ba..Dakyar fa ta iya gaisheni Danmallam..!
Umar yayi mirmishi Daman yasan za"a rina Kansa ya sosa kafin yace"Bari na lallasota zamu zo Biko Yakaka..!
Yafada yana mikewa Yakaka ta mele Baki kafin tace"ai kada kuzo kana tashi Tafiya kafata kafarka sai ta Zauna ita kadai.!
Shidai yana yar Dariya ya shiga Bedroom din Amina ya isketa zaune da waya a kunnenta suna mgana da Hanne sai da ya zauna kusa da ita ya Fahimci da Hanne take mgana
Saboda ganinsa yasa taja Hiran taki karewa har tana cewa ta bata Aminu in yana kusa su gaisa yana kusa kuwa Hanne ta basa karo na Farko suka gaisa da Amina Danmallan yaji bazai iya ba suna cikin gaisawar ya karbe wayar ya Kasheta ta Kuramai ido Cikin Kishi kafin tace"Miye kuma na kashe min waya..?
Hararanta yayi kafin yace"Bansani ba..Baki ganni na shigo bane kike waya da wani kato..?
Amina zan saba miki fa..!
Shima ya mata jan ido daman jira take kawai sai ta saka kuka ta mike ta Fara jijjiga Jikinta tana Fadin"Dama kamin Fada mana..Kaje ka kwana da ita kazo kana min ihu akai..Tunda kamin Ciki ban da wani amfani awajenka..!
Kuka har da majina Baki ya Saki yana kallonta Jidalin Amina yanzu shi kawai ke Diban fire akansa ganin abun nata nayi gaba gaba yasa ya Mike ya rumgumota yana Fadin"Wayace miki baki da amfani a wajena..?
Amina har da wage baki wajen kuka ta kasa mgana kawai sai yayi mganinta ya Hade bakinsu waje Daya Dole ta natsu acikin kirjinsa Sai da ya Dauki Lokaci duk ya gama Shanye Hawayenta da majina sannan ya Dago Fuskarta yana Fadin"Ke ce abu mafi Daraja da kima awajena..Ina sonki AMINA..INA SONKI AMINENE..!
Ido ta Bude tana kallonsa ranta yayi Fari,Idonta ta ware mai kafin tace"La.Har da Aminene..?
Hancinta Yaja yana fadin"Sosai ma..Duk da Jidalin Datake min hakanan nake son kayana..!
Rumgumesa tayi Da Sauri tana Dariya tace"Ni ba ruwana..!
Yana jinta bai ce komai ba ya shiga wata Jahar kuma Duk da Nauyin Cikinta batamai gaddama ba Har sai da suka samu natsuwa sannan ta fara mai kukan bayanta ya kage shi kuma yana lallashinta haka ta kwanta yana ta Faman Matsa mata baayan da Kafafun nata bawan Allah.
Ita dai Yakaka tunda taji su shuru ta Shige Dakin Data sauka ta kwanta afili Ta Furta"Gulmammiya.. !
Ranar ma gidan Sarood ya kwana ko Sallama bai yi ma Amina ba Daga bari yazo taji shuru,Da Safe sai chan rana ya Dawo gidanta Harara kam da Turen Turen baki yashashi yana shiga da ita Daki kaji shuru shiyasa in tana ma Yakaka Jidalinta sai ta kalleta tace"Nama Lura ni kika raina..Meyasa shi baki mai..?
Yana zuwa kuka shige Daki sai naji shuru..!
Amina sai taji kumya ta rufe ido tana Fadin"Ai ina mai acikin Dakin..!
Yakaka ta mata Dakuwa tana Fadin"Raina min wayau..!
Amina ta fara Dariya Yakaka na Hararanta kafin tace"Allah ya shiryaki Amina..!
Ta amsa mata da Ameen haka suka cigaba da zamansu Lafiya Ranar dayake gidan Sarood ba sa sallaman arziki da Amina in kuma ya Dawo ya Dinga Fama da lallashi kenan ga Sarood din Cikim na bata wahala sai da ya kaita aaibiti komai taci sai amai Ga Jidalin Amina wlh baya kaunar ma ya Bata mata rai Tsoron kukanta yake ji.
Amina na cikin Farinciki da kwanciyar Hankali ta kara Kiba ta zama katuwa Danmallam ya siya mata Sabuwar waya samsumg Tana waya da duka yan"uwanta har su ya Zulfa bata yada su ba Tana kiransu susha Hira tun basa Sakin jiki har suka zo suka saki Tunda duka ya"yan yaya basu nuna musu kyama kan abunda Uwarsu ta aikata ba Jadwa ne ta Dauki Zafi itama Daga baya ta Saki arana kuwa ita dasu Hanne sa yi waya fin sau hudu Har sai da Danmallam ya musu Fada yace basu da Hankali ne nan fa ba gida bane..?
Su matan aure ne yanzu wani Shirmen dole sai sun barshi Baji sukayi ba aboye suna wayarsu barin ma in baya gidanta sai gashi yau Amina ke bama su Hanne wasu Shawarwarin sannan Fanin girki abunda ta iya ma basu iya ba Shiyasa har yau har gobe bazata manta da Hajiya da ya Aisha ba Duk tayi salla sai ta rokar musu Fatan gamawa da Duniya Lafiya.
Haihuwa dai shuru har EDD dinta ya wuce sai dai bata Damu ba Tunda Daman Before ne ko after har asibitin sun koma Dr.Ghali ya tabbatar musu da komai lafiya sai hankalinsu ya kwanta.
Bangaran Aba kuma komai Lafiya lau Anty Hadiza na kula dashi ta karbo Jawaad wajen Hajiya ya Dawo wajenta Abun yayi ma Aba Dadi tazo Ranar ta yinin ma Amina da Daddare Aba yazo ya Dauketa Dakyar ya shiga Gidan Amina yasa albarka Amina baki har Kunne saboda Murna Aba yazo Ruwa kadai ya sha ya saka albarka suka tafi Yakaka itama ta Bisu da saka albarka.
Bangaran mallam kuwa acikin Satin nan ya samu Lokaci Yaje Tsafe Idi ya Tukasa yayi ma yan"uwan Uwani Gaisuwan rasuwar Batula,Akwai mahaifiyarsu agidan da abokan zamanta Biyu bayan yayi musu gaisuwa nan ake fadamai Uwani na kwance ba Lafiya an je asibiti an yi Duk Gwaje gwaje an kasa gano abunda ke Damunta sai tace kirjinta da zuciyarta ke ciwo an ta neman Lambarsa afadamai ba'a samu ba..!
Sanda ya shiga inda Uwani take sai da ya kusa mata kuka tana kwance ta Zabge ta rame ta lalace Ba wannan kibar yau gata kwance ba kwalliya ba kayan kawa tana ganinsa ta fara kuka tana Fadin ya yafe mata.
Mallam ya jinjina kai yana kallonta kafin yace"Na yafe miki uwani..Saura ke da wanda ya Hallicceki..Sannan zan yi mgana da su Nazeem zasu zo su Dubaki..!
Daganan ya mike bayan ya ijiye mata Takardan daya rubuta mata Sakinta ya Fice ko bai Fadaa mata ba tasan ko na menene yasa ta Dinga kuka Tari ya Sarketa iyayanta yayi ma sallama da kudi 50k ya basu domin suna cikin yanayi don ma yaran maza na taimakawa.
Sai bayan fitarsa mahaifiyar uwani ta shiga Dakin ita ta karanta Sakin da mallam yayi ma Uwani Sai ta saka kuka tana fadin daman tasan za"a rina Domin zaman uwani bana Lafiya bane ba ya"yanta ba Dangin mijinta tasan wani abu ta aikata aranar Duka yan"uwan Uwani suka taru tana kuka tana Nadama ta basu labarin duk abunda ta aikata,Sun ji tsoron Duniya sannan sun yi Tir da ita har ta mahaifiyarta sai da tayi tir da ita tana kuka tana Fadin Batula ta rasu a Hanyar Shirka wannan wani irin tabewa ne sun fito daga babban gida ammh sun watsar da Tarbiyansu Tundaga ranar harta mahaifiyarta ta Daina bi ta kanta tana yashe Cikin Daki sai wanda yaga Allah yaga Annabi ne ma yake lekota yau ina ya"yan nata Datake yin komai Saboda su..?
Sun gujeta saboda mugun Halinta sannan ba mallam din ya Saketa ballatana ta hango cikar Burinta gata kwance ba Lafiya tana girban abunda ta Shuka kaiconta tayi kuka kamar ranta zai fita bamai lallashinta
Aranar da mallam ya Dawo Daga Tsafe ya Kira Anty Amarya Har Shashensa ya bata takardan Sakinta Ko da bata karanta tasan Dalili ta Fadi gabansa tana kukan ya yafe mata ya kalleta yace"Na yafe miki marliya..Yanzu Tsakaninki da Ubangijij ne..!
Daga haka ya shige ya barta nan tana kuka kukan nadama da rashin Madafa.
Bata zauna ba Kayanta ta Hada ta Rufe Shashen ta bama su Lami key din tace su kaima Hajiya ta Fice Daga Gidan tana kuka yau ina Burin nata..? Ta biye ma rudin zuciya ta karre a Tutar babu Tana kuka ta isa tasha ta samu Motar Dutse lokacin data isa Gidansu sai da tayi nadama.
Yan"uwanta basu karbeta ba haka suka gana mata tir da kaico har da uwar data Haifeta sai da ta juya mata baya ba yadda zasu yi su koreta ne ammh Kashi ya fita Daraja abinci sai dai yan aiki su bata tayi kuka tayi nadama Lokacin da bai da amfani ta Kira wayoyin su Sadiya ba wacce take Sauraranta.
Sakina kuma tana Gidan A"i ita ta Dauketa tana kula da ita bayan an sallamosu Daga asibiti Dayake nan kusa take aure Ranar da Anty Amarya Taje sai da ta raina kanta Har Marin ta sai da kanwarta A"i tayi abaya yadda suke jin mganarta Saboda auran Babban mutum kamar mallam..agaban idonta Sakina tana kuka tace itace ta cuceta ta rabata da auranta da kuma Halin Datake Ciki gashi sanadiyar barin cikin data dinga yi mahaifarta ta samu rauni Har ta fara Dagargajewa yanzu haka an cire mata mahaifa ita da Haihuwa har Abada ta Tsaneta bata son ganinta
Anty Amarya na kuka tana rokonsu gafara suka Tarkatota waje bayan A"i ta saka megadi ya sakar mata karnuka su suka kadata har waje nan bakin get din gidan ta durkushe tana wani irin kuka mai Cin rai kukan Nadama da nasani.
*******
EDD din Amina har ya tsallake da wajen Sati uku Bata haihu ba Sannan Cikinta ya fita wata na Tara har ya shiga goma sai kuma hankula suka fara tashi ita kanta Aminar ta kosa ta Haihu Cikin ya mata girma ya koma yana Rinjayanta.
Danmallam duk ya Damu ya koma yana matukar jin Tsausayinta Hajiya ta bada Shawaran su koma asibiti haka kuwa akayi da ita suka koma wajen Dr.ghali da Amina shi kanshi yanayin Daya ganta yasa yace zai sanya mata ruwan naguda ya gani.
Allah Sarki Duk mai imani sai ya Tsausayama Amina an saka mata Ruwan Naguda ta fara asa asa kamar abun zai yuyu sai kuma shiru sau Biyu ana saka mata sai nagudan ta Fara ta Tsaya anan asibitin ta kwana Tare da Hajiya da Yakaka Danmallam kuma duk hankalinsa a tashe yake washegari asibitin ta cika da su Anty Hadiza da su Aba har da ya Jafar da matansu..
Mallam ma yazo ganin yadda Amina ke kukan azaba tana fadin acire mata Ckkin jikinta zata mutu yasa yace bari ya koma gida ya yi mata addu"a a ruwan Zamzam ya kawo mata tasha tagani shi ya hana asake mata alluran nagudan ganin yadda take wahala kamar zata mutu kuka reras haka Danmallam ke yi saboda ganin Halin da Amina ke ciki hatta Sarood da tazo asibitin sai da ta tsausayama Amina da kuma kanta Tunda itama ai cikin gareta
Tafiyar mallam ba Dadewa sai gashi ya aiko Hajiya Nasara da ruwan zam zam din da yayi ma Amina addu"a shi kuma yana gida yana cigaba da taya Amina addu"an Allah ya sauketa Lafiya Hankula duk sun tashi.
Kamar an kara ma Amina azaba tana sha ruwan zam zam din nan abubuwa suka taso mata haikan tana kamkame jikin Hajiya hannayenta cikin na Danmallam tana kuka tana Fadin su yafe mata mutuwa zatayi Aba duk Dauriyansa bayan rasuwar yaya da abunda Balaraba tayi mishi wannan ne karo na uku Daya ji ya raunana Waje ya fita chan haraban asibitin yana kuka tare da Fatan Allah ya Sauke Amina lafiya..
Anty Hadiza ma har da kwallarta Kowa fa jiki yayi sanyi ganin Haka yasa Danmallam yace ma Dr.Ghali a yi ma Amina aiki a ciro mata abunda ke Cikinta.
Nan da nan kuwa aka fara shirin yima Amina C.S,Bayan Danmallam ya saka Hannu kudin aikin ma su jafar sukayi ta Zirgan Zirgan Biya Hajiya ta amince da hakan saboda Amina ta Wahala har mallam data kirasa ta Fadamai ya amince yace indai za"a samu mafita ayi din yafi Alheri.
Koda aka shiga da ita Dakin Tiyata Amina ta fita Daga Hayyacinta Danmallan ko addu"a ya kasa yi ya Fara Hango kansa Rayuwarsa ta lalace in ya rasa Amina sai da Yakaka ta yi bashi baki sannan ya iya fita hataban asibitin ko Sallar da yaso yayi ya kasa Cikin Mota ya koma ya Dafe kansa kawai yana kiran sunan Allah hatta Hajiya ta kasa mgana Saboda itama ta Shiga Dimuwa..!
Allah mai hikima ana shiga da Amina Dakin Tiyata Nagudan gaske tataso mata Sai dai su Hajiya suka ga Nurses suna kai da kawo da gudu suka zo suka karbi akwatin kayan Haihuwa suka shiga dashi Dr.ghali yayi matukar mamakin Lokacin Daya Duba Cm din Amina yaga Saura 2cm sannan kan yaro na kokarin fitowa Kananun shekarunta yake kallo yana Tunanin Haihuwa da kanta zai ja mata Tsinkau Tsinkau ko yoyon Fitsari sai gashi Cikin Hikimarsa Amina ta fara kokarin Haihuwa da kanta Nishi kawai take yi da kakari da Taimakon Dr Ghali da Nurses dinsa Amina ta Sintalo manyan ya"yanta guda Biyu abun mamaki Kusan atare Jariran guda biyu suka Sulmiyo Daya na Fitowa Dayan ya Biyosa sai kuma Amina ta koma ta yi yaraf kamar bata da rai Dr.Ghali ya taimaka mata Uwar ta fito Nurses suka fara aikin gyara wajen Wasu kuma suna faman goge yaran bayan sun yanke musu Cibi Amina kuma Dr.Ghali ya samu natsuwa ganin tana Da rai allurai ya Hada yayi mata sannan ya fara kokarin gyara mata jikinta bai cika Tsayawa Irin haka ba da zarar mace ta Haihu ya gama mata abunda ya dace yake barin ma Nurse sauran ammh Amina ta Dabamce Matar Bazanga ce..!
Yaran duka maza ne sannan sun fito a wahale yasa basu yi kuka ba sai da Nurses din suka Daga su sama suka Daki bayansu sannan atare suka Callara kuka Gabadayansu sai suka washe Baki Dr.ghali na mirmishin jin Dadi yace"Alhamdulillah..!
Su Hajiya kuwa kamar amafarki sukaji kukan jarirai daga Dakin Tiyata sai suka fara Tunanin aikin ko yayi Sauri yanzu fa aka shiga da ita Hajiya tayi Hamdala acikin ranta suna nan dai Zaune suna jiran tssmmani.
Rabin Sa"a kafin Nurses guda Biyo su fito da Jarirai guda Biyu Cikin kayan Sanyi Farare masu kyau Hajiya ta kasa gasgaata abunda ta gani Amina ta Haifi yara Biyu duka maza..?
Allah mai iko Annabi mai Dubun Daraja.
Hajiya Nasara ta karbi ya"yan tana Hamdala daga ita sai su Nasir da Aba da Anty Hadiza da matan su ya Nasir Baki yaki Rufuwa Hajiya kuma Hannu ta Daga sama tace"Alhamdulilah..Godiyata tabbata ga Allah Shugaban Duniya..!
Sai hawaye tana sharewa sai ga Dr Ghali ya Fito Hajiya na ganinsa ta karisa tana Fadin"Sannu likita mungode fa..Ina Aminar ina fata Lafiya take..?
Dr Ghali yace"Lafiyanta kalau mama..Na mata alluran hutu ne sannan ga karin albishir ma Amina da kanta ta Haihu bamu riga ma mun yi aikin ba..!
Hajiya bakinta Har kunne take fadin"Alhamdulillah..Allah mun gode maka..Ashe yan Biyu ne acikin Amina bamu taba sani ba..?
Nidai nace cikin nan yayima Yarinyar nan girma ashe ashe..!
Dr Ghali yace"Hakan na faruwa Mama..ammh ni sanda suka zo na mata Scan na gani.Sai dai ban Fada musu bane ina Tunanin sun sani..!
Hajiya tace"To mudai bamu sani ba.kila dai Aishan ta sani Dayake chan wajenta ta zauna har cikin girma...!
Mungode Likita..!
Ya amsa mata kafin ya karisa su gaisa da Aba da ya Jafar sai.Nasir sannan ya koma Office dinsa ba Dadewa aka Gunguro Amina kamar gawa sai numfashi zuwa Dakin da zata Huta.
Hajiya Bakinta har kunne ta kira mallam tace mai tayi mazaje Shima Hamdalan yake yi Danmallam kusam shine na karshen sani Sai da Jafar ya Kirasa a waya ya Dawo Cikin asibitin.
Ya kasa yarda Amina