Showing 66001 words to 69000 words out of 145917 words

Chapter 23 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83940

tana fadin"Ina da Dalilina mallam..Bana son cikin nan na Amina ya fallasa..Daga ni sai kai sai Danmallam shima don yakamata ya sani ne tunda shine Uban cikin..Mallam kamin wannan alfarman cikin matanka ba wacce Zata sani ko Sa"idu kada yasani mallam Don Allah..!
Mallam yayi shuru kafin yace"Duk naji Toh ammh meyasa kika ce haka..?
Miye Dalilinki..?
Hajiya tace"Zaka ji Dalilina ammh ba yanzu ba sai nan gaba Dalilin nawa zai bayyana kansa..
Mallam yayi shuru kafin yace"To sai yaushe Sa"idu zai sani..?
Balaraba fa..?bai kamata ta sani ba makafin uwa take ga mamana fa..?
Hajiya taji har Balaraban yanzu bata da yarda da ita ba yasa ta girgiza kai kafin tace"ya kamata ta sani..ammh a wannan gabar itama bai kamata ba mallam..Nidai kayi hakuri akwai Lokacin da zan fada maka Dalilaina nayin haka sannan zasu sani in lokacin su sani yayi..!
Mallan ya tari numfashinta da Fadin"Yaushe kenan..?
Hajiya ta kallesa Cikin ido kafin tace"Kafin abunda ke Cikinta ya Fito Duniya..!
Ya kalleta yana mamakinta meyasa Hajiya tace haka sai kuma yaga bazai iya Ture alfarmanta ba.
Yasa ya jinjinamata kai kafin yace"Shikenan..!
Hajiya tace"Ba shikenan ba..Alkawarin zakamim ba wanda zai ji sannan kuma ina so na Fada maka zan Dauke Amina Daga gidan nan zan kaita inda zata yi Renon Cikinta har Zuwa Lokacin da zai bayyana kansa shima bayan ni da kai da Danmallam ba wanda zai san inda Amina take..!
Mallam ya fara Tunanin da wani abu Cikin mamaki yace"Ina zaki kaita..!?
Kai Tsaye tace"Gidan Aisha Abuja..!
Mallam yace"Aishan ce zata iya kula da mai Ciki..?
Nawa take ko itama ta Haihun ne bansani ba..?
Hajiya tace"Ko Daya bansani ba ko tana da Ciki ammh ina da Dalilina na kaita Chan din ni na Haifi Aishan nasan Halinta Zata kula da Amina Sosai kuma ba ita kadai bace agidan yanzu akwai kakar megidanta da tadawo gidan da zama kaga kenan zata Tayata kula da Amina da abunda ke Cikinta..!
Mallam ya kalli Hajiya ya kara kallonta kafin yace"Duk me ya kawo wannan..!?
Sannan in tatafi karatunta fa kin san fa sun kusa fara jarabawar da kika matsa na Biya mata ita da yan"uwanta sannan mijinta ya kusa zuwa ya Dauketa kamar yadda kika basa Umarni..!
Hajiya tace"yanzu ba lokacin karatu bane..Ta Haifi abunda ke Cikinta Lafiya sai komai ya Biyo baya mallam..!
Zai yi mgana ta Riko hannayensa tana Fadin"Don Allah mallam.!
Idonta sai ya ciko da kwallah gani take in tayi wani Sakaci Amina Zata Shiga wani Hali..ganin haka yasa ya Jinjina ma Hajiya kai kafin yace"Naji na amince mijinta fa..?
Kinsan bazaki Dauke matarsa bai sani ba ko..?
Sannan ita Aishar ai ba ita keda kanta ba An nemi izinin mijin nata..?
Hajiya tace"Danmallam bai da matsala na Fadamai ya amince Megidan Aisha kuma Usman kai ne zaka kirasa kai mai mgana nasan ma bazai ce konai ba ni kuma zan kira Aishar na Fadamata komai zuwa gobe nake so mu tafi..Kada ka manta mallam iya ni dakai da Danmallam ko Sa"idu kar ya sani ballatana Sauran yaran don Allah..!
Mallam bai da tacewa illah gyada kai kafin yace"Shikenan nayi alkawari..Zan kira Usman din muyi mgana..Allah yasa hakan shi yafi Zama alheri bazan ja da mganarki ba Domin baki taba aikata wani abu Sabanin Tarbiyan gidana ba na baki Dama ki kula da Mamana da abunda ke Cikinta Allah ya raba su lafiya..!
Cikin jin Dadi Hajiya ta amsa da Ameen Ameen sannan ta mike tana Fadin"Nagode mallam..Ka taya mamarka da addu'ar Allah ya Tsareta ita da abunda ke Cikinta ya rabata da Sharrin mugum mutum da aljan..!
Wannan karon bai boye mamakinsa ba sai da yace"Hajiya kodai wani abu ya Faru ne..?
Da Sauri ta girgizamai kai kafin tace"Ko Daya..Kasan duniyar ne ta lalace..Ba kowa ke zaune dakai don Allah ba..Sannan ba kowa ke son ganin cigabanka ba. !
Daga haka ta Bude Dakin ta fice ya Bita da kalli yana kara nazarinta aransa yana Tunanin me ya faru..!?
Hajiya bata Cika irin wannan mganar ba.?
Tabbas wani abu ya faru sai dai bazai matsa mata sai yaji ba yasan ta bata aikata wani abu bata da Dalili mai karfi shiyaasa zai bata goyon baya insha Allahi zai kuma taya Amina da addu"a kamar yadda tace Duk da bai taba gazawa da mata addu"an shirya da Daidaituwa Tsakaninta da Umaru ba..!










*Bakina yayi kadan wajen nuna godiyata ga masoyana..Nagode kwarai da gaske ina ganin Addu"o'in ku gareni Yadda kukemin Fatan Alheri nima ina bin ku dashi Godiya ta musamman ga Masoyan da suka siya wannan Littafin Allah ya rubanya muku da Alheri Allahu ya bar zumunci Ameen..*










*Janafty**TFZB2016*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*




Hajiya Shashenta ta koma cikin wani yanayi,yanayin da take ciki tun Lokacin dataji wayar uwani da kanwarta,wani irin dakiya da kwarin gwiwa tare da yakinin babu wani mai yi sai Allah ne suka shigeta.
Ta samu sukuni da sukayi mgana ta Fahimta da mallam yanzu zata jira har ya Kira shi Usman din mijin Aishar duk da tasan ba matsala Aisha kuma sai sun isa goben zata mata bayani haka kurum taji Hankalinta ya kwanta da Aishar saboda tana da bambamcin Hallayar da sauran sannan Halinta kamar Halin Danmallam ne, bata da Hayaniya ballatana yawan surutu.
Ta yi ta leka Amina tagani ko tatashi bata tashi ba sai wajen sha biyun rana Data Sake lekata ta ga ta tashi Hajiya da kanta ta shiga Tiolet ta Hada mata Ruwan wanka ta taimaka mata ta shiga tayi wanka bayan ta fito ita ta Dauko mata wata Doguwar riga ta saka Duk ta rame ta wuya idanuwanta sun kumbura kadan Saboda kuka.
Tea Hajiya ta sake hado mata da sauran Doyar da suka karya dashi da Safe,Kadan Amina taci Doyar Tea din ta Shanye duka domin cikin jikinta na son shan Tea musamman ma Dayake akwai madara aciki.
Sai da Hajiya ta barta ta natsu sannan ta Dawo domin tayi mgana da ita Amina na Zaune Saman Cafet ta jingina da gadon Hanne tana maida numfashi Lokacin da Hajiya ta Sake shigowa Amina kuka take yi domin bata Zaman mintina goma bata tuna da Yaya ba da irin yadda mamanmu ta Dai'dai'ta Rayuwarsu.
Tana ganin Hajiya sai tayi Dubara ta share Hawayenta,Bata sani ba Hajiyar ta gani ammh sai tayi Tunanin Sabida yanayin datake Ciki Domin abubuwa sun faru ne duka Tsammanin abunda basu yi Tsammani ba dukkansu.
Gabanta Hajiya ta Zauna ta Tankwashe kafa Amina tana kokarin gyara Zamanta Hajiya ta Dakatar da ita da fadin"A"a mamah yi zamanki..!
Kanta ta maida kasa domin kunyar Hajiya take ji.
Hajiya ta kalli Amina Lokaci Daya ta Kira sunanta ta amsa jin muryan Hajiya Daga gani mganace a bakinta.


Hajiya ta cigaba da fadin"Amina ina so kiyi hakuri ki kuma Dauki Rayuwa yadda tazo miki. domin bawa bai isa ya Zabama kansa wata Rayuwa ba illah wacce Allah ya Zaba masa..!
Amina dai batace komai ba Hajiya ta kara Gyara Zamanta tacigaba da Fadin"Ina so na fada miki..Gobe zamu Tafi Abuja gidan Aisha chan zaki Zauna kiyi Renon Cikin ki Zuwa wani Lokacin..!
Amina ta Dago da mamaki tana kallon Hajiya kafin tace"Hajiya gidan yaya Aisha..?
Hajiya ta gyada kai kafin tace"Nan Amina nasan zaki yi ta mamakin meyasa haka..?
Ina da Dalilina Amina akan hakan Dayasa bazaki zauna anan ba..Sannan bana so kowa yasan da mganar Cikin ki Mamah ko Hanne da Hamida ne kada ki Fadama kowa sannan shima Batun Tafiyarki ban ce ki sanar dasu ba..In na Dawo goben Daga kai ki Zan musu bayani bana son koken koken nan naku..!
Kiyi hakuri Jarabawarki bazaki yi ta yanzu ba sai in kin haihu nayi miki alkawarin karatu zaki yi shi har sai kin gaji..Danmallam ma bazai taba Tauye miki Hakki ba..!
Amina sai ta fara Tunanin ko Hajiya tasan wani abu ne kan mamanmu da Anty Amarya..?
Sai dai bata ga wani alama ba,Ita yanzu zata iya yin komai Saboda Cikin jikinta sannan Zatayi komai Saboda Tonama mamanmu asiri da Anty Amarya kuma Cikin jikinta ne makami shiyasa bayanin Hajiya bai Dameta ba Hawaye suka kawo Idanuwanta in ta tuna Shekarun data kwashe bata san Dadi da muhimmancin Uwa ba,Gashi yanzu tana Cikin wani Siradi,Siradin da uwa ce kadai Zata tallafamata sai dai ina Mamanmu ta yanke wannan abun Saboda son zuciyrta da kuma Mugunta da zalunci.
Ganin Tana Hawaye Yasa Hajiya tayi Tunanin Rabuwa da su hanne da karatunta yasa ta saka Hannu ta Rumgumo Amina kan kafadarta Tana Lallashinta Lokaci Daya tana Fadin"Kiyi hakuri Amina..ki daina kuka na dan Lokaci ne watarana sai Labari..!
Amina na Shesshekan kuka tace"Hajiya ba ina kukan hukuncin ki bane..
Ina kukan rashin yaya ne..ayau bata a Duniya ina jin matukar kewarta..!
Hajiya Tsausayinta ya kamata ta Dagota tana share mata Hawaye lokci Daya Tana fadin"In kin Tunata ki mata addu"a kin ji ko..?.Sannan in kin ji kewarta ki tuna Dani Domin tamkar Uwa nake gareki ina nan Saboda ke Amina ni ba Uwar Umar nake ba Har Abada ni ina matsayin mahaifiya gareki ne nayi kuma alkawarin Kareki da yardan Allah ke da abunda ke Cikin ki..!
Tana Fada tana share mata Hawaye wasu na Bulbulowa Hajiya fadi take"ki daina kuka nasan zaki ji Dadin Zama da Aisha na dan Lokaci ne Zaki Dawo in Lokacin hakan yayi.!
Amina ta gyada kai tana Fadin"Hajiya ke da mallam nasan har Abada bazaku kai ni inda Zan cutu ba..Sannan duk abunda kuka Zartan kan Rayuwata ina maraba dashi..Na yarda da Hukunci ku kuma Insha Allahu Zaki Sameni mai Bin Umarninki..!
Hajiya taji Dadin haka ta Dinga shafa kan Amina ta saka mata albarka kafin ta mike tana fadin"Kayan ki duk suna gida ko..?
Amina tace"Eh akwai wasu anan hajiya..!
Hajiya tace"To ai ba kaya da yawa Zaki Diba ba nan gaba ma kadan zasu yi miki. Sai ta Dinka miki wasu achan kawai..!
Har Hajiya ta Fice Daga Dakin Amina bata kara mgana ba,wani irin Dakiya ne da Taurin zuciya ke shiganta da kwarin gwiwan da bata san tana Dashi ba Duk da tasan zatayi kewar su hanne da makaranta ammh Gaskiyan Hajiya ne datace na dan Lokaci ne watarana sai labari.
Daya da wani abu na rana su Hanne suka Dawo sun ji dadin ganin Amina taji Sauki basu damu da yanayinta ba sun Dauka saboda bata da Lafiya ne ita kuwa kallon su kawai take yi Tana Tunanin sai dai suga Hajiya ta Dawo ita kadai zasu yi kewarta kamar yadda itama Zatayi kewarsu Hamida kuma Tsausayinta take ji domin in ta kalletasa sai taji kuka ya taso mata ya Zataji in taji Abunda mahaifiyarta take aikatawa..? Bazasu iya Daukan wannan abun ba su take Tsausayi domin ba d'an da zai so uwarsa ta kasance bata gari ba abun akwai taba Zuciya ammh Dolen wata watarana Allah ya Tona musu asiri kamar yadda ya Fara Tona musu awajenta.
Kamar sun san Amina zata koma wani wajen Ranar wuni sukayi tare ko Hamida bata ko leka gida ba suna Tare har Dare,Da mallam ya shigo har Shashen Hajiya ya Dubata ya Dafa kanta yana fadin"Allah yayi miki albarka..Allah ya Saukeki lafiya ya kareki mamana..!
Ta amsa kanta na kasa kafin ya Sake fadin"Kina tsorata Cikin barcin ki har yanzu ko kin bari..?
Amina tace"Yayi sauki baba..!
Malam ya jin jina kai yana Fadin"Zai bari gabadaya ki Dage sosai ki Daina kwanciya ba alwala sannan ki Rike addu"o"in nan da yawaita karatun Qur"ani..!
Amina ta amsa da toh ya Dade yana mata Nasiha kafin ya fita,Dakin Hajiya ya shiga sukayi mgana ya Fadamata ya Kira Usman mijin Aisha yace ba wata matsala sannan bayama gida yana Lagos,Daganan sukayi mgana sama sama kafin ya fice Daman shi da Aba suka shigo shima ya shiga ya gaida Amina bai Dade ba shima ya fita Amina bata Damu ba Sai ma wani Tsausayinsa Daya kamata Mace tatasa shi gaba da makircinta.
Mallam nan ya bar Aba Hajiya tamai mganar Zata kai Amina gidan D'aya Daga Cikin yaran nan tadan koyi wasu abubuwa tunda ga yanayin yarintarta bata koyi wasu abubuwa ba sannan nan da Lokaci kadan Danmallan zai zo ya tafi da ita madina..
Aba bai Tambayi ina Za"a kai Amina ba Sai kawai yabi Hajiya da godiya yana komawa gida ya Fadama mamanmu yadda sukayi da Hajiya anan nema take jin Amina bata da lafiya Mamanmu dataji haka shewa ta Saki aranta tace auran da Zai kare a gantali ne za"a je koyon zama da Miji..!?
Shiyasa kwata kwata bata Damu ba,ita Atunaninta Wahalar da kai kawai Hajiya take yi ammh Amina da Umar ai sai hange Daga nesa ammh a fili sai ta nuna Tasauyawanta da cewa da Safe zata shiga ta gaida Ameenan kafin su tafi ko aranta bata Damu da Sanin ina Hajiya zata kai Aminar ba wannan baya gabanta yanzu.
Adaran Hajiya Ta kira Aisha tace gobe tana nan tafe Aisha taji mganar kamar Daga sama murna ta Cikata Dayake Usman din bai riga ya Kirata ya Fadamata ba Hajiya ta rigasa sai taga kamar ta zama mai sa"a domin Hajiya basa zuwa gidan mutum hakanan sai da babban Dalili ammh ita yau gata Hajiya Zata zo gidanta Murnan ta ya kasa Boyuwa suna gama mgana da Hajiya ta tafi Dakin kakar mijinta Dake zaune tare Dasu da suke Kira Yakaka ta sanar da ita Hajiyarsu na tafe gobe.
Har gari ya waye su hanne basu san komai ba da Safen dai Hajiya tace ma Hanne zasu fita da Amina su shirya su tafi hadda sukace to basu yi wani tunani ba, sai sukayi Zaton Ko asibiti zasu koma basu damu ba.
Ammh Sanda suke shirin tafiya Amina na kwance na kallon Hamida na shiryawa ta fito wanka aran Amina tana tunanin Hajiya zata zame ma Hamida uwa kamar yadda ta Zame mata uwa,Idonta ya kawo ruwa in ta Tuna zatayi nesa dasu saurin share Hawayenta tayi ta kira sunan Hamida bata Damu data waigo ba ta amsa mata.
Amina tace"Hamida don Allah ki kula da Jawaad..!
Hamida sai da ta saka Rigar wata atamfar dake jikinta sannan ta Juyo jin abunda Aminar tace da yanayinta yasa Cikin mamaki tace"Wasiya kika fara bari ne Aminene .!?
Amina tayi Mirmishi tace"Eh mana kinsan Rayuwa haka ta gada..muna tafe ne bamu san muna tafiya da mutuwarmu ba .!
Hamida ta fara Dariya tana Fadin"Lalle Amina ta fara Tunanin mutuwa..Hanne tazo kiji..Hanne. !
Ta shiga kwalama Hanne kira sai gata ta Dawo da Faratin kayan karinsu tana Fadin"Kiran me kike min hamida kamar kin bani ajiya..?
Hamida na Dariya tace"Amina ce ta fara barin wasiyya..!
Hanne ta ijiye abun hannunta saman Cafet tana kallon Amina Lokaci Daya tace"Topa ta fara Tunanin mutuwa ne..?
Ko azara"ilu ta gani..?
Ta fada tana yar Dariya Amina ta balla musu harara tana fadin"Bansani ba. kufa yan iska ne baku san abun arziki ba.!
Hamida tace"Mu ko ke ne bamu san abun arziki ba..?
Ke Amina uban wa ya kaiki maida abun arziki na fada ma. !
Hanne ta Zauna tana Fadin"Ki zauna mu karya hamida kada mu makara..Amina inaga asibiti zasu koma da Hajiya. !
Hamida tace"Shiyasa ta fara barin wasiyya kenan. !
Duk tana jinsu batace musu komai ba illah tasowa da tayi tace su karya Tare harda Jawaad daya shigo yanzu gabadayansu suka karya suna yi suna Hira Amina tana tunanin shine na karshe Zaman su tare Indomie ne sai soyayyan kwai da Tea Amina kwan taci ya taso mata da zuciya sai da tayi Amai ta koma ta kwanta tana maida Numfashi su Hanne na mata sannu da Zasu tafi haka taji kamar ta Bisu har suka fice tana musu bye bye suka fita Suna Dariyanta wai Amina ciwo yasa ta fara Tunanin mutuwa
Basu san cewa Amina Zatayi nisa da su na wani dan Lokaci ba..suna fita ta Fashe da kuka sai da tagaji tatashi ta rarrafa tayi wanka sai a yanzu da aka Tabbatar tana da Ciki take jin wani Sauye Sauye ajikinta na masu juna Biyu.
Ta shirya Cikin Riga da zani na kayan da Hajiya ta Dinka musu ita da Hanne da Hamida abunda yasa ma rigar tayi mata daman tun farko dinki yayi mata yawa saboda Sizes din Hamida aka mata kuma tun Lokacin ba"a rage kayan ba Ta yi shirinta da wuri ne Sabida Hajiya tace da wuri zasu tafi Tunda ita ayau din zata Dawo.
Yan kayanta Dake nan kawai ta Hada kala uku sai Azakar da addu"o"in da mallam ya Rubuta mata' sai mangunanta,wasu kayan nata suna gidan Aba wasu kuma suna gidan ya Danmallam bata kwaso duka ba,Zama ta yi kawai tayi Tagumi tana Tunanin yadda Sabuwar rayuwa zata Bude mata ita da abunda ke Cikinta tana tunani tana Hawaye sai ga Hajiya ta shigo tayi saurin goge hawayenta saboda kada ta gani ashe ta gani sai bata nuna mata ba
Kallonta tayi tana Fadin"Mamah kin gama shiryawan .?
Amina kanta na kasa tace"Eh Hajiya ina kwana..?
Hajiya ta amsa tana fadin"To kin kar ya kuwa..?
Ta gyada mata kai tana Fadin"Eh hajiya..Tare da su hanne muka karya. !
Juyawa tayi ta Fice tana Fadin"To bari Idi ya dawo kai su makaranta sai mu wuce..!
Fitan ta ba Dadewa ta Leko tace ma Amina ta fito Dogon Hijabinta ta Saka Jakar data Hada kayan nata Hajiya ta karba ta farayin gaba itama ta shirya Tsab da ita,Hajiya na gaba tana Binta abaya har falon Mallam suka gaisa ya kara mata Nasiha sai ga Idi ya Dawo Hajiya ta mike tace zasu tafi mallam yace"Ko in kira Sa"idu ne su yi sallama..?
Hajiya tayi shuru kafin tace"kyalesa kawai ai na Fadamai jiya..
Mallam bai kara mgana ba shi ya rakosu har bakin mota sai ga Hajiya Nasara ta fito domin ita ke da Turakan mallam jiya ganin Hajiya da Amina yasa tace ko anguwa zasu je Hajiya tace eh ba Dadewa zasu yi ba mallam dai na gefe bai ce komai ba domin yayi alkwarin bazai ma Hajiya kaladan kan abunda ta Tsara ba ya yarda da ita fiye da duka matansa bazata taba aikata ba Daidai ba.
Agaban idon Hajiya Nasara da Mallam Suka fita Daga gidan idi ke jan su a Motar mallam din prado baka suka Dauki Hanyar Abuja Amina na ta sharan kwallah Hajiya na kallonta batace komai ba Domin bazata hanata ta koka ba.
Su hajiya basu yi nisa ba,Aba ya fito zai Tafi gidan gona mallam ke Fadamai su hajiya sun tafi yayi mata Fatan Dawowa lafiya bai Dade ba gaiswawa kawai sukayi da Mallam ya shiga Motarsa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login