Showing 63001 words to 66000 words out of 145917 words

Chapter 22 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83952

ita Uwanin ta shigo sai ta Sanar da ita sai dai tana Daga kafarta da niyar Fita taji Uwani na Fadin"Haba ni ce fa Batula kar kin manta ni..Ai marliya bazata kara kiran mai alewa bata da kudi ba..Alokacin da nake fadama Marliya Irin Tuggu na sai ta ga nata ai bakomai bane Batula na Fadamata zan yi shekaru aruru ina bin bayan Hajiya ne kamar wata Sakarya..?
Na Fada mata na riga fara aiki akan biyan Bukata saboda haka sai da ta hakura da nata Cikar Burin ta barni na cika nawa in burina ya gama cika zan sallameta sai ta nuna Taurin kai cewa ita bazata yarda ba sai na Fadamata me nayi ma Sakina da yasa ta ke Barin duk cikin data samu. ?
Nace mata ta kwantar da Hankalinta ba Sakina kadai ba, har ita Balarabiyat da ita kanta Aminar ko sau D'ari zasu samu Ciki sai yabi Rariya alkawari ne na Daukan ma kaina Nazir ya fara Haihuwan ma mallam Jikiko guda Biyu hakan ya Zama kuskure ammh yanzu bazan kara maimata kuskure na ba..Duk da Haka sai da nasa aka maida su mara sa amfani a wajen mallam kamar yadda aka maida Nasir yanzu abubuwa nawa akeyi agidan nan kafin kiji mallam ya kama sunansa an Dade..? Kamar yadda na saka Mama ta sa Nazir yayi nisa da Gumel din da har Abada bazai iya zama na Sati Daya acikinta ba na saka ta Lula kurciyar Danmallan madina yadda bazasu zauna ma agarin bama ballatana Mallam ya gansu ya ce zai Dorasu kan dukiyarsa Batula kin san yadda na sha Wahala shekaru aru aru kan ganin ya"yana akan gaba akomai agidan nan to Wahalata ta kusa zuwa karshe Nazeem sauran kadan ya karisa ya Dawo uzairu kuma yana Bautar kasa kafin ya gama Nazeem ya Dawo daganan zan Dora harshashen Burina ya fara cika ga Shamsu shima ya fara nasa karatun kina ganin zan bari marliya tazo ta rusamin Shirina na ne..?
Shine na Tauna Tsakuwa domin aya taji Tsoro Batula na tabbata na Saka tsorona azuciyar Madina,bama ta da wayau ne ni da ya kamata ta godemin Batula..? Nan ta maida balarabiyar nan kamar Hoto wajen Umar kan Tariyan Amina kuwa babu abunda basu yi ba ita da mai tayata din saboda kar ta tare ammh sai da ta taren sai ni kuma na karisa musu aikin na Dorata kan Tsarin dana Dora Sauran..Domin na Riga na fadamata indai ina Numfashi Cikin matan Umar ba wacce ta isa ta Haihu ya"yana basu fara Haifama mallanm jikoki ba Domin Tunda Mama ta Fadamim mallam ya son ganin Ya"yan Umar tunda yafi soyuwa wajen ya'yansa ni kuma na mike Tsaye na hana Faruwar hakan sai dai ya Mutu bai taba Haihuwa ba batula. !


Hajiya tsabar mamaki da Rudewa sai da ta Bude baki kamar sau goma tana Rufewa Jikinta yayi wani irin sanyin mamaki da al"ajabin jin kalaman Dake Fitowa Daga Bakin Uwani Duniya Haka ta lalace bata sani ba..?
Kana Zaune da Mutum Tsakani ga Allah shi kuma yana nan yana Cutarka ta karkashin kasa duk da bata Fahimci wasu mganganun ba ammh ta Fahimci Daga marliyan har Uwanin basu da zuciya mai kyau sannan Duk Jirgi Daya ya kwasosu sannan abunda ya Faru jiya wannan Tsakaninsu ne sannan Daga baya Uwani ta maida abun kan Marliya..?
Ashe Uwani ke zubar da Cikin Sakina..?
Ita tayi ma su Nazir kurciya kin zama a kusa da mallam..?
Gabadaya sai taji kanta ya kulle ta kasa wani Tunani har zata tafi ta koma Shashenta sai ta fasa so take taga Idanuwan uwani taga ko zata iya Hada ido da ita Hajiya mace ce mai Juriya da Takwalli shiyasa koda taji haka Razanan Dake zuciyarta bai nuna a saman Fuskarta ba Murya ta Bude kadan ta kara yin wata sallaman tana Fadin"Uwani ko bakya Ciki ne..?
Haj.Uwani Dake waya taji kamar mganar Hajiya afalo gabanta ya fadi ko sallama bata yima Batula ba ta Datse kiran ta fito falo da Sauri har Zaninta na neman Faduwa har ga Allah sai da gabanta ya fadi data ga Hajiya Cikin Daburcewa da kinganta kinsan bata da gaskiya ta washe baki Tana fadin"Hajiya ke ce daman..?
Yaushe kika shigo. ?
Hajiya ta kalleta na wani Lokaci ganin yadda take zufa yasa tayi wani Mirmishi aranta tace ruwa ai ya kare ma Dan kada kuma Uwani a Fili kuma cewa tayi"Eh shigowata kenan ina ta Sallama shuru..!
Ajiyar zuciyar data saki sai da Hajiya ta jita ta sauke Numfashi tana Fadin"Eh wlh ina cikin Tiolet ne Fitowa ta kenan naji sallamanki..Sannu da zuwa hajiya..
Ki zauna mana kina Tsaye..?
Hajiya ta kada kai kafin tace"A"a ba zama nazo yi ba..Naga duk yau baki Fito bane shine na leko naga ko lafiya.?
Haj.uwani na sosa kanta tace"Lafiya lau barci ne a idona Hajiya jiya ban samu barci ba Umaima tatashi tana ta Kuka cikin Dare..!
Hajiya ta kada kai kafin tace"Allah ya Sauwake ya bata lafiya..!.
Uwani ta amsa da ameen Cikin Fuskar Tsausayi taso taja hajiyar da Hira sai hajiyar tace mata tana wani abun ne bari ta koma Shashenta sai ta shigo Suka Rabu da Uwanin akan zata shigo har da raka Hajiya tana fita ta kulle kofar Shashenta lokaci Daya tana Sauke Nunfashi Fatanta Daya Hajiya bataji wayar ta da batula ba ai da aikinta na Shekaru ya rushe alokaci Daya bata ma san meyasa ta bar Falon nata abude ba..!
Hajiya har ta kai Shashenta mamakin Abunda taji Uwani na Fadi bai bar ranta ba ko iya karisawa Dakinta batayi ba ta samu saman kujera afalonta ta Zauna tayi Tagumi tunani take ko Tun Zamanta da uwani tun suna Gusai tataba Cutar da ita ne..?
Balle itama ta rama ta Hanyar abunda take Fadin ta aikata..?
Sai taga bata samu komai ba sai Mutuntawa da girmama juna da Tarin Alherinta ga Uwani ashe daman alheri na komawa sharri..?
Allah Sarki Danmallam Uwani ta Curar dashi wajen salwantar mai da Cikinsa bama ita kadai ba tace har Amina in ta samu Ciki sai yabi Rariya..To ita Allah ne..?
Ta isa da taja da abunda yace ne..?
Sai jikinta ya fara rawa kada Uwani ta Farga da Cikin Amina shima ta ga bayansa Domin bata da Imani Allah Sarki Nasir bawan Allah har da shima bata barsa ba..?
Ba ruwansa mai Sanyi da Hakuri Duniya ma bata Damesa ba duk Cikin ya"yanta shi kadai ne tabbas maallam bai wani Damu da lamuransa ba ashe da Dalili .?
Ga Nazir da ya"yansa suma din badai kaji mallam na mganarsu ba duk da yake son ganin jikikinsa a gabansa shima ashe da Dalili..?
Sai dai Uwani tayi kuskure tana Takama da Boka da mallam ne su kuma Allah suka Rike ko Daya abunda tama ya"yanta bai Dameta ba don sun yi nesa da ita bashi ke nuna sun manta da iyayensu ba Bata bakinciki da Haka Tunda suna chan suna neman na kansu ne kuma tana da yakinin addu"arta garesu shi ke Tsare dasu Duk kwanan duniya sai sun kirata sun gaisheta sannan haka mallam sannan Duk wata Daga Nazir har Danmallam suna aiko ma ta da kudi hakama mallam koda basu Cikin wahala ammh Basu manta cewa iyayensu dana Hakki akansu ba ko Nasir sai dai tace Allah ya biyasa da gidan Aljannah Shi da Jafaru ga Sa"idu wh Tallahi yau ko mutuwa Umaru da Naziru sukayi bazata ce tayi kukan maraici ba Domin sa"idu da ne kamar da goma sannan ga Nasir da Jafaru da bai Taba sakawa ta Ji zafin Rashin Zaman ya"yanta Biyu kusa da ita ba ga matansu Tsakaninsu sai mutumtawa da Martabawa har ta Matar Nazir Hidiya in bata kirata yau ba zata kirata gobe ta gaisheta kuma in suka zo garin bata Sauka a ko"ina sai shashenta sai in itace tace taje shashen Uwani ko Nasara tafi ma Darajata Fiye da Sakina domin kaf Cikin Surukanta bama wacce ta raina ta irin Sakina to me zai Dameta..?
Ita Allah ta rike kuma dashi ta Dogara boka ko mallam basu isa su ja da Ikonsa ba..!
Zata numa Uwani da dukkan mugaye irinta su Marliya da ma wasu Boyayyin wadanda Allah bai bayyanasu ba Domin ta tsorata Ta kasa ma yarda da kowa gani take Tunda Uwani ta Cutar da ita to wanda batayi Tunani ba shima zai iya Cutar da ita kafin Su farga da Cikin Amina ya kamata tayi wani abu a matsayinta na Uwa yau dai ta cire kawaici da kunya da nuna ikonta in takamar su boka da mallan ita ta rike Allah sannan bawa bai isa yayi ma Mutum abunda Allah bai masa ba.
Zata kare Amina da abunda ke Cikinta Har sai ya bayyana Lokacin da Danzaki ya girma basu isa su ga karshensa ba Umaru zai haihu Tabbas zai ga kwansa Daga Tsatso mai Daraja Tsatson Sa"idu da Hadiza ta sani addu"arta ne Allah ya amsa ta Dade tana Fatan Ganin Zuru"a mai yawa ta bangaran Umar da Amina tun kafin mallam ya Hada wannan auran Burin haka ke ranta.
Zata nuna musu ba su isa ba..Allah ya Fisu sannan suna Raye za"ayi komai Da yardan Allah sun fara ganin Rashin Nasara har abada acikin Rayuwarsu sannan burikansu bazasu taba Cika ba..!
Tsam ta mike Amina ta leka taga ta Samu barci kafin ta kada kai ta Shiga Dakinta wayarta ta Sake Dauka ta Kira Dannallam har alokacin yana Cikin Daki bai fito farimcikin abunda Hajiya ta Fadamai ya kasa sakinsa Tsammamin abunda baka Taba Tsammani ba wajen wanda bakayi Tsammani ba..!
Sarood na falo tana ta samu barci ya lekata ya gani shiyasa ya Dawo Daki ya Zauna kawai yana ta Tasbihi da yima Allah kirari Lokaci Daya soyayyar abunda ke Cikin Amina ya shiga ransa shiga ran da ko Sakina in ta Samu Ciki bai taba jiba Fata yake da Addu"am Allah ya bar masa wannan Ciki shi kadai yake tunanin Haihuwar Amina Zai faranta ran mallam da Hajiya da Baba Sa"idu fiye da Tunaninsa alokacin Kirjinsa ke Budewa Da sunan Amina da dukkan abunda ya Faru Tsakaninsu sai ga wani Kira Daga Hajiya gabansa ya fadi ya rika Allah Allah yasa ba cewa Zatayi wasa take mai sai da ta gama Ringing sannan yabi bayan kiran.
Sai a wannan karon ne Hajiya ta bari suka gaisa Cikin Yanayinta na rashin Dadi tace"Ina fatan mganar da na Fadamaka baka Fadama kowa ba ko..?
Kai tsaye ya amsa mata da Eh Hajiya ta gyara Zama tana fadin"To ka min alfarman bazaka fadama kowa ba Ciki kuwa har da matanka da Sa'idu da abokinka Aliyu ko yan"uwanka ban amince ka Sanar da kowa Amina dana Ciki ba .!
Cikin mamaki yace"Hajiya har da mallam..?
Hajiya tace"Ni zan sanar dashi Dakaina wannan..Ta bangaranka ka bar mganar nan asirri Umar..Ban yarda da kowa ba za"a iya Cutar da Abunda ke Cikin Amina nayi alkawarin da sunan Allah zan bata kariya saboda haka kayi shuru da bakinka ..!
Cikin gamsuwa yace"Na Fahimta Hajiya..Allah ya saka da alheri..!
Hajiya ta amsa da Ameen ta Cigaba da Fadin"Sannan zan Dauke Amina Daga idon mutane..Saboda wasu Dalilaina bana son bayan ni dakai da mallam wani yasan da mganar Cikinta da kuma inda zan kaita ajiya har zuwa Lokacin da Cikinta zai isa Haihuwa..!
Cikin mamaki yace"Hajiya ina kenan..?
Kai Tsaye tace"Abuja zan kaita Wajen Aisha..Chan zata Zauna na wani Lokaci kafin abubuwa su Daidaita..!
Danmallam mamaki ya cikasa sai dai baya yima iyayensa gaddama yace"Shikenan Hajiya kiyi duk abunda ya kamata..!
Ta jinjina kai kafin tace"Kada ka Damu zuwa Lokacin duk zaku san Dalilina na hakan sannan zan bata Wayar nan a hannunta in ta koma chan ku cigaba da mgana ta waya..!
Cikin girmamawa ya amsa mata kafin Cikin wani yanayi yace"Tana Lafiya ko..?
Hajiya tayi Mirmishi kafin tace"Lafiya kalau..jiya ne ta kwana da Zazzabi shine yau mukaje asibiti likita ya auna jininta sai ga Ciki kaji abun Allah ko..?ko ni Da nike Tare da ita Allah bai bani ikon gano hakan ba..Shiyasa na yarda akwai abunda Allah ya Boye kan cikin nan na Amina..Umaru ka Dage da addu"a don Allah azkar safe da yammah da Karatun Qur"ani na yarda Bawa bai isa yayima Mutum abunda Allah bai mai ba addau"armu gareku bazata taba Faduwa kasa banza ba duk Salolinka kada ka manta da Rokar ma Amina Tsarewar Allah da ita da Abunda ke Cikinta kaji ko..?
Sai duk jikinsa yayi sanyi da kalaman Hajiya duk da tana yawan fada musu su dage da Addu"a ammh na yau na Dabam ne Cikin Sanyinsa ya amsa mata ta Dinga sakamai albarka kafin suyi sallama tace Zata kirasa in sun yi mgana da mallam zuwa gobe take son ta kai Amina Abujar bazata ba ta Lokaci ba.
Bayan ta gama mgana da Danmallam Nazir ta kira suka gaisa shima abunda tace ma Danmallam tacemai shima sai yaji wani iri Hajiya kamar tana barin Wasiya suna gama waya ya Kira Danmmallam a chan madina yana Tambayansa ko sun yi waya da Hajiya yace eh sai yake tambayansa ko ta yimai nasiha da rokom ya Dage da addu"a yace eh sai nazir ya fara Tambayansa ko Hajiya bata da lafiya ne ya Tabbatar mai da lafiyanta kalau sun Dade suna tattaunawa kafin su rabu kan Shi Nazir din ranar Lahadi zai zo yaga Hajiya ya koma saboda Hajiya is d Best mother in d word.
Bashi ba ko Hidiya na Fadin bata ga Uwa kamar Hajiya ba mai kirki mai kawaici sai ta kirata sau goma su gaisa bata kira dan data Haifa ba Tunda suke da Hajiya sai dai ta Bisu da addu"a bata taba Saka ido kan samun su ba bata taba tambayansu wani abu ba sai dai su Dauka su bata ta amsa tana godiya tana saka albarka ita da Mallam samun a iyaye is a Bleesing basu taba Dogara ga abun hannun ya"yansu ba sai dai su bisu da saka albarka da addu"an nasara.


Hajiya kuma suna gama mgana da Nazir ta shiga wanka Saboda tana sauri suka Fita asibiti bata Tsaya yi ba tana fitowa taga wayarta na Haske tana Dubawa taga Mallan ke kiranta ta Dauka sukayi mgana yace mata ya Dawo tace mai gatanan zuwa Daman shi take jira,Mai ta shafa ta shirya Cikin wani sabon less din da Mijin Aisha ya Dinkamata suka aiko mata dashi har da mallam ma sun dinkamai shadda ganin Dattakon Mijin Aisha da kuma sanyin Aishan yasa ta Zabi ta kai mata Amina ta Zauna awajenta tasan zata kula da ita sannan kuma ba wanda zai san tana wajenta indai ba ita Hajiyan ta Fadama wani abu ita kuma tayi alkwarin bama Amina da abunda ke Cikin kariya da ikon Allah..!
Kitchen din Shashenta ta shiga ta Dora ma Maallam Ruwwn Tea dinsa Datake dafamai na Sassaken mganungun Musulunci mganin sanyi ne sai da ya tafasa ta Juyemai a Fulas Ta Dauka da kofi saman wani katon Faranti ta fita zuwa Kitchen din Tsakar gida suka gaisa da su Lami taga Doya suka soya sai Miyar albasa da sukayi ta Diban ma mallam din ta Nufi Shashenta ahanya ta Hadu da Anty Amarya ta Dawo daga wajen mallam din Fuska kozai kozai kamar wacce tatashi Daga jinya sama sama Hajiyar ta Tsaya suka gaisa ta wuce Anty Amarya ita kanta sai da ta Bita da kallon mamaki ganin yanayin Hajiya na yau din da bata taba gani ba ,ko Sakina bata tambaya ba akwanakin nan kuwa ko bata shiga ba in suka Hadu sai ta tambayi Jikin Sakinar sai ta Danganta hakan da abunda ya Faru Jiya Uwani ai tatashi Wasa da ita yanzu ma mallam taje kara bama Hakuri har ya Sallameta bata samu wani kyakyawan kallo Daga garesa ba.
Ta bi shawaran Dayyaba ta kira mallaminsu ta gayamai yayi mata mganin Uwa sannan ta sanar dashi ya Dakatar da Barin Cikin da Sakina take yi yace zai kirata nan da kwana uku ta Saurareshi,so take kafin Lokacin ta Samu mallam ya kalleta da kallon yafiya da kauna sai abun da yazo mata da Sauki ammh kalli fa mallam ko son ganinta bayayi ai Uwani ta gama Cutar da ita..!


Hajiya koda ta shiga Falon mallam yana zaune yana nazarin Wani Littafin labarci ya amsa mata sallamanta ta shigo ta ijiye farantim Hannunta ta Zauna gefensa suka gaisa
Ya tambayeta jikinn Amina tace da Sauki ya karya Tukunnah sai suyi mgana Littafin hannunsa ya ijinye ya Sauka kasa ya Tankwashe kafa ta Zubamai ya fara ci Hajiya na gefe tana kara Nazarin shawaran data yanke tana fatan Allah yasa mallam ya yarda da Tsarinta kada ya matsa sai yaji Dalili duk da awajensa ya"yansa suka Dauko Rashin son jim abunda ba"a so su ji ba
Suma haka suke basu da yawan Tafiya ballatana Bin kwakkwafi.
Sai da ya gama sannan ta tattara komai ta matsar gefe ita ko yunwar bata ji Cikinta ya Cushe da yanayin Data ke Ciki shima mallam din kallonta yake yi Cikin wani yanayi yace"Zainabu Fuskarki ta bayyana Damuwa..?
Me yake Faruwa ne..?
Hajiya ta Sauke Numfashi kafin ta mike tana fadin"Mganace dani mallam mu shiga ciki..!
Yayi mamakin jin tace su shiga Ciki bai mata musu ba ya tashi yabi bayanta zuwa Cikin kuryan Dakinsa abunda ya basa mamaki suna shiga ta Sakayo kofa shidai yana binta da kallo ta Dawo ta Zauna agabansa asaman Katuwar Dardumar Dake Dakin.
Cikin ajiyar rai tace"Mallam Munje asibiti likita ya Dibi Jinin Amina an aunata kuma yaga Ciki wanda yakai kimamin Wata Hudu da kwana goma ajikinta..!
Mallam sai yayi mata kyar yana kallonta na tsawon Lokaci kafin kawai ya saki kabbara..!
"Allahu akbar..!
"Allahu akbar..!
"Allahu akbar..!
Sai da ya maimaita sau uku sannan Cikin Tsantsan Farinciki yace"Kin gani ko Hajiya..?
Allah shi kadai yasan Lamarin Daya Boye kam Mamana da Umaru ...Kai wannan labarin Farinciki ne Hajiya Masha Allah ina mamar tawa fata Dai Likitan yace ba wata matsala ko..?
Hajiya tace"Ba wata matsala..!
Mallam na jinjina kai Cikin Farinciki yace"madallah..Allah ya inganta Allah ya Bata lafiya ya zaunar dashi Allah yasa ta Sauke lafiya..!
Hajiya ta amsa da Ameen Mallam yaga yanayin ta wani a sanyaye yasa yace"Hajiya naga bakya murna ne..?
Ko da wata matsala ne..?
Sannan ya kamata a Fadama mijinta..!
Hajiya tace"Na fadamai..!
Cikin mamaki yace"kin fadamai fa kikace..!?
Ta gyada kanta kafin tace"Eh mallam..Kuma na rokesa bayan ni da kai da shi ko Sa"idu bazai ji labarin Cikin nan na Amina ba mallam..!
Mallam ya kalleta yana fadin"Bangane ba.?
Hajiya ta gyara Zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login