Showing 114001 words to 117000 words out of 145917 words
karkarwa yana nuna Mamanmu da yatsa yana Fadin"ke kika kasheta..Kika rabata da Duniya Batare da ta miki komai ba. ?
Meyasa kikayi haka..?
Meyasa kika kashe ran da bata taba Sauya matsayin ki aranta ba .?
Balaraba Bazaki taba gamawa da duniya Lafiya ba..!
Kawai sai kuka jikinsa ya fara rawa yana neman Faduwa Jafar ya mike da gudu shi da Nasir suka taroshi ya Fada Jikinsu yana kuka jikinsa na rawa yana karkarwa yake fadin"Ita ta rabani da Hadiza..Ya Allah ka wulakantata..!.
Sai kuka gabadaya sai kowa yaji ya kara Raunana.
Jadwa da Jaleela suka ruga wajen Abba suka rikesa suna kuka sai ga Jamila itama da Jawahir,har da Jawaad na wurin yana kuka duk da ba Duka yake Fahimta ba ya Fahimci kan Rasuwar Yaya ce.
Ganin haka yasa Amina ta kalli ya Dannallan cikin rauninta tace"Ina so naje wajen Aba!.
Bai musa ba ya Saketa Lokaci Daya ya mike ya taimaka mata ta mike ya karisa da ita gaban yan"uwanta dukkansu suka Dago suna kallonta Aba yana Kuka Kukansa na Fitowa yace"Ki yafemin Amina..ki yafemin..!
Kawai sai Amina ta zube kan kafafun Aba ta wani saki kuka,kukan da kowa yaji sai da jikinsa ya kara yin sanyi Su Jamila suka Fada kan Aba suma suna kuka mai tsuma zuciya Danmallam na gefe yana jin kukan Amina har Cikin Ransa da Ruhinsa ammh ba yarda ya iya Bai isa ya hanata kuka ba..!
Su Zulfa suna ganin su ya Jawaheer wajen Aba ammh kunya da Bakimciki sun saka sun kasa karisawa garesa suna Zaune sai sharban kuka suke kada Hamida ma taji Labari..
Anty Amarya ta runtse ido sai ga Hawaye lokaci Daya Tana Fadin"Tun Lokacin da naji labarin wannan auran Hankalina ya tashi..Saboda bai kamata wata tazo ta sha gaban Sakina ba..Duk da duk kokarina Burina bai Cika ba,Sakina ta samu Ciki sau hudu tana barinsa..Auran Amina ya razanani ni da Sakina razanan da bamu yi shi Lokacin auransa da Sarood ba Saboda ita na saka mallam ya maidata Hoto..An yi ma Umar Sihirin da bazai iya Zama namiji awajenta ba..Awajen Sakina ne kadai zai amsa sunansa Namiji..!
Danmallam ya kalleta Tsam kafin ya juya ya kalli Mallam shima shi yake kallo.
Danmallam kansa ya maida kasa bayan sun Hada ido da Aliyu da mamakin abunda ke faruwa yasa ko motsi ya kasa Anty Amarya ta Cigaba da Fadin"Yadda Mallam ya shammacemu ne yafi batamin rai..Sannan ina Tunanin da Sanin Sa"idu komai ya faru..shiyasa na yi alkawarin shima sai ya Kurbi kwatancin bakimcikin daya kunsamin na Kira Dayyaba muka yi mgana..Nace mata ya kamata Yaya TA,MUTU..ita kuma tace Tabbas ya Dace ta Mutum..Ko domin ta Rama Bakin cikin da Sa"idu ya Dade yana kunsamata aranar na Kira mallam na Fadamai komai,Adaran kuma ya Turo ma yaya Hayakin Daya Turketa ya Sarke mata Numfashi...Numfashin Da yayi Sanadiyar mutuwarta..!
Anty Amarya ta karishe Fada Cikin gunjin kuka ita da Mamanmu gabadaya Falon aka Dauki Salati sai kuka Mamata na Sharan hawaye tana Fadin"Wannan wani irin mugunta ne..?
Gaskiya Balaraaba bazaki gama da Duniya Lafiya ba sai kin lalace..!
Hajiya kanta sai da ta Durkusa kan gwiwiyonta cikin rauni tace"Wani irin Rudin Duniya yake diban ku da har kukayi Tunanin Kashe ran da bata muku komai ba..?
Kai Haabunallahi wa"inamal wakeel..!
Hajiya take fada sai ga Hawaye ganin yadda Hajiya ke kuka ga Aba nayi da su Amina sai kusan kowa ma ya fashe da kukan banda Mallam da Mazan dake da sauran kwarin zuciya.
Ammh yau kam Jafar shima kukan yake rerawa Hawaye wani na korar wani.
Anty Amarya bata yi shuru ba ta cigaba da fadin"Mun so auran Amina da Umar ya kare a lalace ne Ganin An Dibi Lokaci basu tare ba sai muka Saki jiki..Sai kuma kwatsam Hajiya ta taso da mganar tarewar Amina Data rugazamin Shirina ni da Dayyaba ba yadda bamu yi ba kada hakan ta Faru ammh ina Bakin Alkalami ya riga ya Bushe Allah ya Rubuta kaddara zama Tsakanin Amina da Umar..Bayan ta tare na saka mallam ya kara mata rashin kunya da Fitsara saboda Umar ya gaji ya sakota sai kuma yazo ya bar garin ta kare abunta kan Sakina..Alokacin hankalina ya karkata kan yadda Umar zai zo ya tafi da ita Madina har kiranye na saka an yi mai ammh ba Nasara hankalina ya kara tashi Lokacin da Sakina ta samu Ciki ta karayin barinsa alokacin ne na gane bayan ni acikin matan mallam ma akwai wata mai Buri irin nawa..Saboda mallaminmu ya tabbatar min da ita ke lalata duk cikin da Sakina take samu..!.
Anty Amarya kawai ake kallo wacce ta Runtse ido ta cigaba da Fadin"Dana Fahimci ko wacece naso nayi fito na fito da ita Sai dai ina sai ta nuna min In an shirye nake ita atafe ta kwana..Daga karshe sai ta nemi ta lalatamin Duka Shirina ta lankwasa komai ya koma kaina..awannan gabar na rasa madafa.sai da naga Umar ya Danu sannan su Hajiya ma haka sai Hankalina ya kwanta..Ban taba kawo ma kaina wani abu zai ya faruwa ba nan gaba ko da Hajiya ta Dauke Amina nayi Tunanin maiduguri ta kaita sannan Daga baya sai mukayi Tunanin ba auran ne sannan Balaraba kuma hankalinta ya karkata kan Sa"idu da ya koma sai abunda tace mai ni kuma ma samu Natsuwa tunda Umar yazo ya tafi da Sakina sannan Sarood bamu da damuwa akanta Sakina tajata ajiki da farko da sai da ta riga ta mata illah taja baya da ita..Sannan Mallam ya tabbatarmin dacewa sai dai ta gaji da zama dashi araba auran sannan ita kanta Aminar banmu taba Zaton wani abu zai shiga Tsakaninta da Umar har ta samu Ciki ba Shiyasa muka bar wannan Gibin bamu Cike ba..Na rantse har ga Allah Sakina bata da Laifi nice idona ya rufe da Cikar burina ammh ita bata san komai ba,sai soyayyar Mijinta da kaunarsa komai ta aikata ni ce Sila..Ni ce silar duk abunda ya faru..Don Allah ku yafemim..!
Sai kuka har da Shasaheka Falon yayi shuru sai tashin koke koke Mallam kansa na kasa yana ta Salati kansa ya Daure acikin gidansa acikin zuru"arsa Shirka ya samu wajen zama bai taba Sani ba..?
Bai sani ba sai da Hajiya da Danmallan suka zo suka same shi da mganganu wadanda ya kasa gasgasta su ya rude ya shiga Dimuwa Sannan alokacin ya kasa gasgasta mganarsu ammh yaji Daga Bakin da bazai mai karya ba Hajiya da Umaru...sannan Amina bazata taba fadin Wani abu kan Balaraba ba indai ba Gaskiya bane..ita kanta Hajiya ta shiga Rudani sanda Danmallan yake sanar da ita abunda Amina ta Fadamai sai dai bata ji ita kadai ba,ta tarasa suka isa gaban mallam ya sanar dasu abunda Amina ta Fadamai alokacin zuciyar Mallam ta raunana matuka tundaga wannan Lokacin baya barci Damuwa da bakincikin irin wannan abunda yake faruwa acikin iyalansa bai kara barinsa ya runtsa Dakyau sannan tun alokacin jikinsa yayi sanyi da bai Taba yi ba.
Danmallam ma ya girgiza da jin wannan al"amarin ballatana mallam..?
Hajiya kuwa duk ta san wani abu sai da labarin Balaraba ya girgizata.
Dukkansu shuru sukayi da mganar Suna jiran wannan ranar da dukkan sirrin Boye zai fito Fili.!
Baba Mallam ya Dago kansa Rawaninsa ya jike da Zufa duk da Sanyin A.C dake cikin Falon Cikin son ya kara Tattabarwa yace"Wacece ita wacce take Lalata Cikin da Sakina ta samu..?
Muna so mu santa sannan mu ganta..Allah ne ya nufemu da Sanin Ainihin Fuskokin wadanda muke Zaune dasu..!
Yafada cikin raunin murya raunin da ko Hajiya bata sam mallam dashi ba.
Anty Amarya zatayi mgana kenan sukaji muryan Hajiya Uwani Daga Bakin kofar Falon na Fadin.
"Gani nan..!
Sai kowa ya juya yana kallonta Baki Sake Nazeem da Uzairu suka kalli juna suna mai Nuna Tsanatsanin mamaki.
Baba mallan yana kallom Haj.Uwani har ta kariso Falon Idanuwanta sum kode saboda kuka ta Zube gaban mallam Tafashe da kuka Lokaci Daya tana Fadin"Nasan ko ban fallasa kaina ba kasan Abunda nake boyewa..!
Don Girman Allah Mallam ka yafemin..Ni ce nayi ma Umar kuruciya shi da Nazir suka kasa zama kusa dakai sannan ni na mai da Nasir mara amfani a wajenka..Ni nake Hana Cikin Sakina Zama mallam duka nice na aikata hakan..!
Ta karishe fada Cikin kuka Baba mallam yayi wani mirmishi Takaici kafin yace"Kema saboda ki same ni dani da Dukiyata ko..?
Haj.Uwani kanta na kasa tace"Mallam kayi hakuri..Idona ya rufe..Burina naga ya"yana ne gaba akomai..Hajiya tasha gabana a wajenka..Sai nayi Tunanin in ya"yanta suka sha gaban ya"yana na gama yawo..Shiyasa na nemi Cikar Burina ido rufe..Ina da wata Bokanya Da muke cema Mama a Niger take ita take min aiki..Sannan ita ta bankadomin sirrukan Marliya da Balaraba,ita ta bani mgani na saka ma Sakina a tea tasha ita da Sarood har da Amina ma na bata..Ammh sai gashi na ganta da Ciki wanda Mama ta tabbatar min da cewa ko sun samu Ciki sai ya zube..!
Ta karishe fada tana gunjin kuka ai Kowa a Falon sai ya kasa motsi ashe abun bai kare ba..?
Hajiya Cikin Zubar Hawaye ta kalli Uwani Tana fadim"Saboda mene..?
Meyasa kika zabi ki kashe rai Uwani..?.kinsan girman Laifinki kuwa a wajen Allah..?
Haj.Uwani na kuka wurjajan tace"Saboda Mama ta fadamin maallam na Matukar son Umar Sannan ya"yansa da zai haifa sune masu soyuwa a wajensa shiyasa na hana matansa su Haihu shi Nazir bai da wani Tasiri ne shiyasa ban Damu dashi ba..Dalilina kenan na daya sa na Tura Nazeem ya rabu da Sa'idu a kan Harkokin dukiyar mallam Burina shine Nazeem da uzairu su zama kan gaba aduka Dukyarka ni kuma na zama nice gaba da Hajiya tunda ya"yana ne akan komai..Wlh sharrin shedan ne ku yafemin don girman Allah sai yau nayi nadama na Fahimci Zakaran da Allah ya nufa da Cara ko ana muzuri ko ana Shaho sai yayi..!
Kuka take kamar ranta zai fita Mallam ya Datse Hakoransa waje Daya Cikin Bakiimciki,Sai ga Hawaye sharr na zubar ma mallam hawayen Tsausayin kansa da Bakincikin yadda iyalansa suka Gurbace suka gurbatamai zuru"a.
Hajiya ce ta share Hawayenta tana Fadin"Allah ki kayi ma Laifi shi zaki roka uwani..Allah ya gani ban Taba Zama Daya daga Cikin ku da wata manufa ba Shiyasa Allah ya nuna muku iyakarku..Kun ga dai ku baku isa kuyi abunda Allah bai yi ba ko..?
Amina tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe ina Mganin da kikace kin bata..?
Sannan ita kanta Saratun Ciki gareta yakai Wata Hudu ni nace kada a fallasa mganar Cikin ina mganin da kikace kin bata itama..?
Sannan ke marliya ina Sihirin da kikayi ma Danmaallam..?
Kin Fahimci in Allah yace kun yafakun bawa bai isa ba. !
Sai kallo ya koma kan Sarood da mamaki Sakina kuma cikin ta taji yana Juya mata saboda Tsabar Tashin Hankali.
Hajiya ta cigaba da Fadin"Daga karshe nagodema Allah da komai naku ya kare a kanku..sannan ina kara Fada muku ni ban Dogara da boka ko mallam ba..Ni Allah na rike shiyasa na Gagarara har yau har gobe..Kuje Allah zai muku sakamakon abunda kuka aikata Hakkin Rayukan da kuka kashe kuka gurbata bazai taba barin ku ba..!.
Hajiya ta fada tana juya baya Lokaci Daya tana sharan Hawaye..
Nazeem na kuka uzairu da shamsu nayi ganin yadda iyayen nasu ke kuka suna neman gafara.
Nazifa har muryanta na Dishewa.
Hajiya Nasara sai kuka take yi tana Fadin"Wlh ban taba sakama kaina Bakinciki ba..Da zuciya Daya har ga Allah nake zaune da kowa..!
Kawai sai ta saka kuka Mamanmu da Anty Amarya da Haj.Uwani Duke suna kuka neman gafaran ya"yansu da Su mallam ammh ba wanda ya kallesu yan gusai kuwa haka suke aibata Mamanmu suna kirarin bazata gama da Duniya Lafiya ba.
Tashi tayi tana kuka tana Rangaji ta isa gaban su Amina ta Duka tana kuka tana Fadin"Don Allah Sa"idu kai da ya"yan Yaya ku yafemin..Sharrin Shedan ne nasan na cutar daku..ammh ku yafemin ku yafemin ko domin Darajan su Hamida..!
Tafada tana kokarin rike Kafafun Aba yayi Saurin janye kafarsa ya juya baya yana Fadin"Bazan taba yafe miki ba Balaraba..Insha Allahu sai kin girbi Abunda kika shuka..!
Sai Hawaye Mamanmu ta Dukar da kanta tana Kuka tana kokarin rike Amina fadi take"Amina nafi cutar dake don Allah ki yafemin..!
Amina bata yi sanya ba ta mike da katon Cikinta ta saka Hannu ta Dago mamanmu Tsaye kowa mamaki ya kamasa Ammh basu gama mamakin ba Amina ta Cire Hannunta ta Zabga ma Mamanmu mari kafin ta taso ta kara mata a Hannun hagu kafin ta kara tasowa ta kara mata
Sai da ta Durkushe kasa,su Hamida sai kuka ba bakin mgana ba kuma wanda ya Hana Amina.
Cikin hucin kuka da Hawaye ta nuna mamanmu tana Fadin"Marin farko na kashe mana uwa da kika yi ne..!
Mari kuma na Biyu na yadda kika Lalata rayuwata ce..!
Mari na uku kuma na Aba ne..Na yadda kika Raunana masa zuciya..Tsakaninmu Dake BALARABA allah ya isa..Bazamu taba yafe miki ba..!
Amina tana Fada tana kuka sai kuma ta fara kokarin Sulalewa Numfashinta na Sarkewa kafin su ya jafar su farga Ya Danmallam yayi saurin isa gareta ta Fada Jikinsa jijjigata ya fara yi lokaci Daya yana Kiran sunanta.
Noor..!
Nooor...!
Sama sama ta jisa kafin ta Bude ido ta fara ganin fuskarsa Cikin Fitan Hayyaci tace"Hubby...!
Da Sauri yace"Na"am Noor..ki tashi kada ki tafi ki barni na shiga uku..Ina zaki tafi baki tsaya kin taramin zuru"a Daga Tsatsonki ba..?
Tana kuka ta wani kamkamesa Ta fashe da kuka yau Dannallam ba kunya Hajiya bana Mallam da sauran mutanen Dake Falon ya kamkame Amina kamar zai maidata Ciki yana jinsa kamar yana yawo a gajimare kukanta na Dafa mai rai kamar ya Dawo da abunda take ji akansa bayanta yake shafawa a Hankali alamun Lallashi.
Kallo sai ya koma kansu Hajiiya ta saki Mirmishi haka ma Mallam da su Ya Aisha Goggo Husai tace"Ajiyan Allah..Gaskiya ne Amina ta FITA ZAKKA acikin gidansu sannan ko azuciyan Mijinta ta fita zakka..!
Tafada tana sharan kwallah Aba ma kallonsu yake yi yana jin bakincikinsa na dan raguwa,lokaci Daya yana kallon Mamanmu da wani kallo kallon kin gani..?
Baki da yarda zaki yi Alkwarin Allah ne ya cika..!
Sakina kuma sai taji kamar wani abu na Bin katafunta tana shafa kasanta tadago da hannunta taga Jini..Sai ta Zaro ido..tana kokarin mikewa jiri ya kwasheta ta zube kasa sumammiya..!
Allah ya riga ya Rubuta har ta koma gq Allah bazata taba haihuwa ba..
Shi bawa bai isa ya kankare wannan kaddaran ba..!
Cikin ya sake zubewa kamar yadda Sauran ma aka rasasu..!
*Janafty**TFZB2027*
*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Su sadiya suka ruga da gudu wajen Sakina data fadi sumammiya jini na malala ajikinta,A"i kanwar Anty Amarya ta riketa lokacin Da ta ga jinin dake malala ta kasan Sikat din Dake jikin Sakina sai ta fashe da kuka.
Ita kuka Sadiya kuka Jidda kuka Sa"adatu kuka,Anty Amarya ta taso hankalinta a tashe tana kuka zata rike Sakina,Anty A"i ta Daga mata Hannu Cikin kuka take fadin"Marliya kada ki kuskura ki taba Sakina..Kije Abunda kika aikata kawai ya isheki ko Alhakin Sakina ya isheki..!
Daga haka tace ma Sadiya ta kamata Sakina suje asibiti da ita da yan"uwansu dake Dutse duk suna falon komai ya Faru Anty Amarya tana ji tana gani suka fice da Sakina Daga falon haka ma su Jidda suka Fice suka barta ko gizau Sa"adatu ne kamar zata tsaya sai kuma ta juya tabi bayansu tana kuka Anty Amarya nan ta Sulale tana gunjin kuka.
Ganin yadda gabadaya Falon ba wanda yabi ta kan abunda ya faru,Har ta dashi Danmallan din kuwa yana rike da Amina bai Saketa ba ballatana Hajiya da mallam da wannan yanayin bai gama Sakin su ba..
Bakajin komai ba sai tashin koken koken su ya Zulahait kamar ransu zai fita,da kukan Mamanmu da na Hajiya Uwa,haka suke kuka kamar ransu zai fita.
Nazeem ne ya fara mikewa Idanuwansa sun kala sun yi jajir Saboda yanayin dayake ciki Cikin wani yanayi ya kalli Uzairu da ya kasa tashi Har da kwallah shi sai da ya Zubar jin abunda Mahaifiyarsu ta aikata.
Cikin Kaushi yace"Uzairu tashi mu tafi..Zaman mu bai da amfani a nan wajen...in muka ci gaba da zama anan wurin zuciyata zata iya bugawa..!
Uzairu na jin haka ya mike yana Bin Hajiya Uwa da wani kallo kallon Tsana da Bakinciki kafin ya juya zai bi bayan Nazeem daya fara tafiya zai bar Falon da Sauri Hajiya uwa ta kira sunayensu suka tsaya batare da sun juyo ba.
Haj.Uwa ta rarrafa zuwa inda suke Tsaye Cikin kuka take fadin"Meyasa zaku juyamin baya. ?
Kada ku manta duk abunda na aikata Saboda ku ne..Wlh duk abunda na aikata Saboda ku ne..!
Kuyi hakuri ku yafemin Don Allah..!
Sai kuka har tana Dukewa saboda kuka,Nazeem ne ya juyo a fusace yana Fadin"kada ki kara jingina Zunuban ki da sunanmu..Tunda nake dake ban taba Fada miki ina son zama a Karkashin Baba mallam ba..Ko Uzairu ma nasan ba Ra"ayinsa bane Meyasa kafin ki fada wannan Halin baki zauna Damu kin tambayi Ra"ayin mu ba..?
Me kika nema kika rasa..?
Me Hajiya ta rage ki dashi ita da ya"yanta..?
Me Baba mallam ya rage ki dashi..?
Wlh Tallahi ban taba jin kunyar Hajiya da mallam ba sai yau mugin Halinki yasa na kasa Hada ido da yan"uwana..!
Ya karishe fada yana Sharan hawaye Uzairu ma haka cikin Hawaye yace"Mommy meyasa kika Zabi wannan Rayuwar..?
Baki taba Tunanin Sharri dan aike bane..?.inda ka aikasa nan ko min Daren Dadewa zai dawo maka..?
Wlh ko Kaffara bazan yi ba Shiyasa kanwar mu Umaima take cikin wannan Jarabawar saboda irin abubuwan da kika aikata ne ta ke Fuskata..!mommy kun Cutar damu Kin sakamu jin kunyar Mallam da Sauran yan"uwanmu..Nasan Ya Nazeem bai Fada miki ya samu aiki da wani kamfani a Lagos ba,Sannan ni kuma ,masters dina zan koma bamu da burin komai sai muyi karatu mu nemi na kanmu Muma watarana mu taimakama iyayanmu da abunda muka Tara na Halaliyarmu..!
Ya karishe fada Kamar zai Saki gunjin kuka kawai sai ya juya ya fice Nazeem ya mara mai baya Haj.Uwa ta bisu da Kuran sunanyensu ko waiwayo ba wanda yayi..nan ta durkushe tana wani irin kuka mai sosa rai Shamsu na Zaune ya mike shima cikin wani yanayi yazo gabanta ya tsaya sai ji kawai tayi ya Kira sunanta da Sauri ta Dago sai dai ganin kallonta Dayake Binta dashi yasa jikinta yayi sanyi.
Kallon