Showing 60001 words to 63000 words out of 145917 words
ne Dazu Mallan bai Saki ba har yanzu..!
Awannan Daran yadda Amina taga Rana haka taga Dare domin barci ko barawo bai Saceta ba ga kuncin zuciya ga Zazzabi Cikin Dare kaf Abunda ke Cikinta sai da ta amayar dashi kafin Safe Jikinta yayi zafi sai rawan sanyi take da Haduwar Hakora sallar asuba ma Dakyar ta iya yi tana neman Faduwa Hanne ta jira sai da Hajiya ta Dawo daga Shashen mallam ta Fada mata cewa tayi su sauya ma Amina Hijabi bari ta Fadama mallam ya ma Idi mgana yakai su asibiti.
Mallam na jin jikin Amina yayi zafi Hankalinsa ya tashi ya Kira Idi a waya yace yazo ya kai Hajiya asibiti ba Dadewa sai gashi Lokacin Hajiya har ta Shirya Amina ko Tafiya bata iya yi Saboda yadda Jikinta yayi zafi Hanne da Hamida suka riketa har Bakin mota ta shiga Suka Bita da fatan samun Sauki Cike da Tsausayi mallam ma Sai da ya Tsausayamata ganin yadda ta koma Cikin kwana Daya yace su Hajiya su yi gaba komai kenan ta Kirasa.
Kafin su tafi sai da Hajiya tace su Hanne su shirya su tafi makaranta Harda da Jawaad suka amsa mata da Toh suna masu Tsausayin Amina.
Suka koma Shashen Hajiya suka yi wanka suka karya suka yi shirin tafiya makaranta Harda Jawaad sai da suka fito ne suka ga Aba suka gaisa sai Lokacin ya rike Jaawad yana Fadin ya yi musu yaji shi da balaraba ko Mallam na wajen yace to yaga su Hamida sun dawo ina zai zauna in da ba kowa abunda mallam bai sani ba in Aba baya ga Jawaad bane yanzu mancewa ma yake yi dashi.
Hamida ta shiga gidansu ta gaida mamanmu ta sameta cikin kwalliya kamar wata yarinya ita abun ma sai ya bata mamaki sama sama suka gaisa ta shiga Dakinsu ta Dauki littafinta na Biology data manta Dashi bata ma samu Fadama Mamanmu Amina bata da lafiya ba Shidai Mallam ya sanar ma da Aba sai dai ba gida ya koma ba gidan gona ya wuce Shiyasa Mamanmu bata ji ba Sannan a matan mallam ba wacce ta Bude shashenta ma ballatana tasan abunda ke faruwa..!
General Hospital tace Idi ya kai su suna zuwa ta Kira Nasir a waya ta Fadamai yace bai riga ya shigo asibitin ba ammh gashi nan kan Hanya ba Dadewa sai gashi ya iso ya Iske har Hajiya ta yanki kati suna bin layi Tunda gidan mallam bai Dauki wani Family Doctor ba ba ruwansa da wannan,Duk da ba bangaran yara bane A sanshi a asibitin shi ya karbi katin su Hajiya ya shiga wajen Likita yamai bayani ganin Dr.Isa ne abokinsa ne yamai bayanin Hajiyarsu ne ta kawo kanwarsu ba Lafiya jin haka yace su shigo kawai.
Dole sai Nasir ne ya rike Amina Saboda tana mikewa jiri ya kwasheta ta kusa fadi Allah yasa yana kusa ya Tareta Hajiya bazata iya ba ita kadai
Ganin yadda suka shigo da ita a rirrike yasa Dr Isa yace su shimfidar da ita kan gadon dayake ganin marasa Lafiya nan Nasir ya Dorata shi kanshi ya ji Tsausayin Amina jikinta kamar wuta Saboda Zafin Zazzabi.
Likitan yazo ya Duba bayan ya cire mata Hijabin jikinta ya taba Temprature din jikinta ya gwale mata ido ya kuma Duba Tafin hannunta bayan ya kalleta na tsawon mintina goma kai ya girgiza kafin ya Dawo ya Zauna ya kalli hajiya da Nasir yana Fadin"Zamu dibi jininta za ayi Test..sannan akwai yunwa tare da ita zan kara mata drip da allurai wanda zasu taimaka mata ta Dawo Cikin hayyacinta..!
Ba musu Hajiya tace"Ayi abunda ya kamata likita in ma gado zaka bamu ba Damuwa..!
Yana Rubutu saman wata Takarda yace"A"a mama Ba gado bane zamu dai mu riketa na awa daya ko biyu zuwa uku mu saka mata Drip muyi mata allurai kafin Lokacin Sakamakon gwajin mu ya fito..!
Wata Nurse ya kira tazo yace ta Dibi Jinin Amina aka kai lap yana son abun da Sauri ne Amina duk Tsoron Alluranta bataji ba yau ko Ihun batayi ba tana gama Diba ta fice shikuma Nasir Likita ya bashi Takardan Daya Rubuta allurai da Driip yaje phamarcy cikin asibiti ya siyo ya kawo mai nan da nan ya saka Handgold ya Hada allura biyu ya yi mata ta Jijiya Biyun kuma tana Cikin Drip din Amina ahalin Datake ciki kuka ma Har ta gaji da yi ashe sai kana da ma natsuwa kake jin zafin wani abu ita ko Zafin Alluran ma yau bata ji ba..
Kamar almara ba Dadewa Amina sai barci ganin haka yasa Nasir ya tafi bangaransa inda yake aiki yace in da wani abu Hajiya ta Kirasa waje ta fita Tana jira domin Dr.Isa ya cigaba da ganin mara sa Lafiya kamar yadda aka saba..!
Hajiya na babban Falo zaune tana jira sai ga Kiran mallam ta Dauka sukayi mgana tace mai Amina na ciki ta samu barci yace su dan jira na wani Lokaci Da haka sukayi sallama Idi bai koma ba yana nan yana jiransu.
Awa Biyu da wani abu Hajiya ta kwashe Tana jira sannan wata Nurse tazo ta Kirata zuwa Office din Likita koda ta shiga har lokacin Amina barci take ammh Ruwan ya kare har an cire mata.
Kujera yanuna ma Hajiya yace ta zauna, ta Zauna tana Sauraransa wata Farar Takarda Doguwa ya mika mata Hajiya ta karba Tana Fadin"Likita wannan Takardan fa..?
Fadamin abunda ke faruwa kune yaran zamani yan Boko..!
Mirmishi yayi kafin yace"Amina Sa"idu yarki ce Hajiya ko..?
Hajiya ta Dagamai kai da Sauri kafin ya Cigaba da Fadin"Tana da aure ne..?
Hajiya taji gabanta ya fadi sai ta basar kafim tace"Eh likita..!
Ina fatan ba wata matsala ko..?
Da Sauri yace"Babu Mama..Takardan Dake hannunki Sakaamakon gwajin da muka ma Amina ne..Sakamako ya nuna mana tana Dauke da Ciki kimanin Wata Hudu da kwana goma..!
Hajiya sai taji kamar bata ji da kyau ba ta Zari ido kafin tace"bangane ba..Likita wani irin ciki..,?
Dr Isa yace"Ciki dai na Haihuwa mama .!
Hajiya taji jikinta ya Saki Cikin mamaki ta juya ta kalli Amina Dake Sharan barci kafin ta kalli Likitan tana Fadin"yanzu nan Likita Amina ciki gareta har na Tsawon wata Hudu da wani abu bamu taba ganin alamu ba..?
Dariya Dr.Isa yayi kafin yace"hakan yana Faruwa sosai Mama...naga shekarar ta 17 ajikin katinta ko..?
Hajiya ta gyada kai tana mamakin ikon Allah acikin ranta.
Likita ya Cigaba da fadin"ba abun mamaki bane in baku gane ba..Tana da karancin shekaru sannan Cikin nata irinsa ne Hausawaa ke cema Kurman ciki bai cika bayyana kansa yana karami ba sai ya kusa fitowa Duniya..Sannan in kun lura Cikin yabi Jikinta ne ya kuma yazo Lokacin ta na age din kuruciyarta ne sannan tana da Tsawo sai ya shanye shi ajikinta inbamu masana abun ba, ba lalle ku iya gane tana da ciki ba..!
Hajiya ta jinjina kai kafin tace"Ko fa Laulayi batayi ba Likita sai dai ta rika cin abinci sosai..da yawan barci..!
Dr ya gyada kai kafin yace"Ba lalle sai tayi ba ai kowani Ciki da nasa Salon mama..Ita nata nacin abinci ne da yawan barci kila ko zatayi Laulayin sai nan gaba kadan..!
Hajiya ta sake jinjina kai kafin tace"Sai jiya tayi ma amai sau Daya..!
Dariya wannan karon yayi kafin yace"Normal ne..Mama kila ma Daga yanzu Lokaci bayan Lokaci in taci abund bai karbi Cikin ba Zata iya yin amansa.!
Hajiya ta Damke Takardan Hannunta tana Fadin"Nagode likita yaushe Zamu tafi gida..?
Yace"Yanzu da zarar ta farka..alluran barci nayi mata yanzu zata saketa..!
Suna ma cikin mganar Amina ta Farka tana Kokarin tashi Hajiya ta karisa gabanta ta mata sannu Dr Isa ya taso ya kara Dubata ya tambayeta me take ji tace ba komai jikinta ya rage Zafi Zazzabin ya Sauka mganganuna ya Rubuta mata ya Sallamesu sai ga Amina na takawa da Kafarta har wajen mota sai alokacin hajya ta kare mata kallo Taga Cikin da Likita yace yabi Jikin Amina Allah mai iko Annabi mai Dumbin Daraja.
Basu tafi ba sai da ta Kira Nasir yazo haraban asibitin ya same su koda ya Tambayi Hajiya me likita yace sai taki Fadamai ta dai basa Takardan mganin daya bata shi kuma yace ta Jira yaje ya siyo ba Dadewa sai gashi ya Dawo da Ledan mai Tambarin General Hospital Gumel.
Shi Nasir bai wani tsaya duba takardan mganin ba shiyasa bai Fahimci ko na menene ba.
Daganan sukayi sallama bayan ya leka Motar yayi ma Amina Sannu ta amsa tana Dagamai kai.
Har suka kai gida Hajiya ta kasa gasgasta abunda taji Aranta kawai sai ta shiga wani Tunani Tsakanin miji da mata sai Allah bata Zargin Amina har ga Allah sai dai kuma likita yace Cikin Jikinta wata Hudu da kwana goma sannan in ta Lissafa dai dai Danmallan shima nada wajen wata hudu da sati Biyu in bai fi ba da komawa Madina,kenan kafin ya tafi ne in ma wani abun ne ya shiga Tsakaninsa da Amina Allah mai iko sai abun ya bata mamaki matuka.
Sanda suka Dawo Mallam bai fita ba ammh yana Sauri zai je Fadar Sarki ana nemansa shiyasa bai Tsaya ma sun yi mgana da Hajiya ba ganin Amina Taji Sauki har gata ma tana Tafiya da kanta kuma cikin ikon Allah har suka kai Shashen Hajiya basu hadu da kowa ba.
Suna shiga Hajiya bata Zauna ba ta Hado ma Amina tea mai kauri ta matsa mata tasha ta bata mgungunanta duk yawancin na karin Jini ne sai na Vitamin C da polic acid na masu Ciki sai kuma panadol sai da ta sha ta natsu Fatan ta kada tayi Amai sai kuma Allah yasa batayin ba.
Hajiya ta rakata Dakin su Hanne ta kwantar da ita kan gado sannan ta Zauna gefenta tana kiran sunanta Aminaa na kokarim mikewa Zaune Hajiya tace ta koma ta kwanta.
Hajiya ta kalleta Cikin ido kafin tace"Mama kinsan me Likita yace yana Damunki..?
Amina ta girgixa kai kanta a kasa Hajiya ta gyara Zama kafin tace"Yace Kina CIKI har na Tsawon wata Hudu da kwana goma..!
Dam!!!
Gaban Amina ya fadi ta kalli Hajiya da Kumburarrun Idanuwanta ta maimaita Cikin mamaki "Ciki ...?
Hajiya ta gyada mata ai sai acikin Ran Amina tayi wata Hamdala ta yi kabbara ta sake yin wata kabbara domin mganar mamanmu take Tunawa da tace bazata Haihu da Ya Danmallam ba sai Sakina sannan kuma auran haka zai kare ba Fa'ida Ashe ashe basu sani ba Allah ya Riga yayi ikonsa..!
Ganin kamar bata wani Razana Sosai bane yasa Hajiya tace"ko kin san da shi ne Amina baki Fadamin ba..?
Amina na sharan Hawayen data rasa ko na Dadi ne ko na Murnan Karshen mamanmu da Anty Amarya yazo ne. Bata sani ba cikin kukan tace"Wlh bansani ba Hajiya bansani ba..!
Hajiya ta Dafa hannun Amina Kafin tace"Basai kin Rantse ba nima da naga Jiya naga yau ban gane ba sai ke yarinya karama Mamah..?
Yi shurunki..!
Hajiya ta fada tana Faman share ma Amina Hawaye Tsausayinta na kamata.
Hajiya ta Dakata tana Fadin"Tambayarki zan yi Tsakaninki ga Allah Mamah..kada kiji nauyi na ina so na gasgata wani abu ne..
Shin Kafin tafiyar Danmallam wani abu ya shiga Tsakaninku ne..?
Ai sai Amina taji kamar kasa ta Bude ta Shige sai ta juya baya ta Dunkule kanta tana mai jin kunyar Hajiya abunda ya faru Tskaninta da Danmallam yana Dawo mata kamar a jikin magiji.
Hajiya ta Daga hannu tayi kabbara Tare da Hamdala ta mike tsaye ta Fice Tana Mai Farinciki wanda ya kasa Boyuwa a saman Fuskarta.
Tana fita Direct Dakinta ta shiga waya ta Dauka ta Kira Danmallam bakinta kamar Gonar auduga saboda Murna
Yana gida bai fita ba yaga Kiran Hajiya sai da gabansa ya fadi suna Falo Tare da Sarood ne ya barta ya shiga Cikin Bedroom dinsu,kafin ya Katse kiran yabi bayan kiran Hajiya Tana Dauka ko amsa sallamarsa batayi ba tace"Danmallam kana jina..?
Cikin Wani yanayi yace"Ina jin ki Hajiya..!
Ta cigaba da Fadin"Tambayarka zan yi kuma ina so ka fadamin gaskiya..!
Zama yayi gefen gado yana fadin ina jinki Hajiya..!
Hajiya tace"Wani abu na auratayya ya Shiga Tsakaninka da Amina ne kafin tafiyarka.?
Ina kasa ta Tsage Danmallan ya shige ya kasa mgana gabadaya sai jikinsa ya Fara rawa kamar yana gaban Hajiya,Ya kasa mgana ma kamar ya kashe wayar haka yake ji meya kawo wannan mganar..?
Badai wani abu ne kuma ya faru ba..?
Jin yayi shuru yasa Hajiya tace"Amsar ka tana da muhimmanci Danmallam..!
Muryansa a shake yace"Ehhh..!
Hajiya tace"Allahu akbar Sarkin gagara Misali..UMAR ka godema Allah..Amina nada ciki har na Tsawon wata Hudu da kwana goma cikin ka Umaru..!
Haka yaji Hajiya tace kafin ta katse kiran sai ya fara Tunanin kodai bai ji Daidai bane..?
Wata Aminar ke da Ciki..?
Kwakwalwarsa ta Fara Hasko masa Amina ita ce ke Dauke da Cikinsa kuma ya Tabbata Hajiya bazata Kirasa tamai wasa ba..!
Allahu akbar ya furta sau uku ashe Ashe Daman wannan kwan Hallitar yasa tafiyarsa bata yuyu ba aranar Allah ya Kaddara mahaifan Amina Zata Dauki wannan hallitar shiyasa tafiyarsa bata samu ba sai da ya Dawo gida sannan cikin abunda bai Tsammani ba ya tara da Amina ashe ashe ya saka mata kwan haihuwa ashe ashe ya zama Daya da ita baisani ba..!
Wannan shine ake kira Zanen kaddaran..?
zakaran da Allah ya Nufa da Cara ki ana muzuru ana shaho sai yayi.
Yau Cikin Farinciki suka tashi shi da Sarood na warkensa gabadaya jiya ya tabbata namiji ga Sarood ya maida ita mace shiyasa bai fita ba ya Zauna yana kula da ita Allah yayi gaskiya Qur"ani waraka ne bai san Sadda ya Durkushe a saman cafet din Dake Bedroom din ba ya Daidai ci gabas yayi Sujudul shukur Muryansa cikin Zaki da gardi yake fadin.
"Alhamdulillah..Alhamdulillah..Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban Halittun duniya Annabi muhammadu Sallalahu alaihi wasallam.."
*Janafty**TFZB2015*
*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*
Hajiya na fita Daga Dakin Amina ta Dago kanta sai da ta tabbatar da Hajya ta shige Dakinta sannan ta Mike Zaune kan gadon ta yaye rigar kikinta Cikinta Daya fara tasowa kadan take kallo sai da ta kuramai ido sannan ta Fahimci ba"a sama yake ba yana kasan maranta ne dan tasawar da yayi ashe ashe ba Timbi bane kamar yadda suke Tunani ita dasu Hanne Ciki ne na Haihuwa..?
Ita yau Amina ke da Ciki zata Haihu..? Yau ina yaya take..? Bata raye saboda haka bazata ga wannan ranar ba..?
Mamanmu ta rabata da yaya Har gaban Abada mamanmu bazata ga Daidai a Rayuwarta ba Tana hawaye tana shafa Cikinta Daga jiya zuwa yau wanu Tsanar mamanmu ne ke yawo acikin ranta Tsanar da ko Anty Amarya bata yi ma irnsa ba Domin ta Cutar da Rayuwarta tundaga matakin Haihuwa har zuwa jiya da asirinta ya Tonu Shafan Cikinta take yi ta ke taji wani kaunarsa na mamaye aranta Dariya tayi acikin Ranta tana Hango Amina da y'a tab lalle za"a ga uwa anan wajen Sun so su hana ta Tarewa auran ma ba da son ransu bane sai dai In dan Rana ta fito tafin Hannu bai isa ya kareta ba Allah yace kuma ya isar da Cewarsa Hawayenta ta share wani kunci na Shiga aranta Tana Dafe da Cikinta tace"Allah ya kare min duk abunda ke Cikina..Allah ba ikona bane ko Dubarata ba ne da ka bani wannan kyautar ajikina kuma ka karesa batare da kowa yasan dashi ba Ya Allah ina Rokinka da kariyarka ka cigaba karesa har ya fito Duniya domin Fitowarsa Duniya ko bayyansa Shine Zai Taimakamin wajen Tona ma mugaye azzalumai asiri mara sa Tsoron Allah Kamar yadda suka ce na Ratso aikin su batare da sun sani ba nayi alkwarin Dawowa Amina Sa"idu gusai dina mai Biyayya da ladabi Mai Tsayawa ga Kafafunta nayi alkwarim Daga yau bazan kara kuka Domin na gaza ba sai domin imanin ka ya Allah ka Tsareni da Tsarewarka kabani Kwarin gwiwan da zan bankada Azzalumai dani suke zencen mu zuba mu gani shege kafasa Aminene nike kirarina badai ta mutum ba sai ta Allah..!
Ta karishe fada Lokaci Daya wani karfin gwiwa na shiganta Tsoro yana barin ranta son Cikinta da son ta Rainesa ya fito Duniya ya Zauna aranta Abu Daya take son gani Tozartan Mamanmu da Sauran masu mugayen zuciya irin su Anty Amarya da Haj.Uwani yau gata da ciki in sun isa su hana Allah ya ikonsa ashe karyan Boka da mallam suke tunda suka kasa bankado musu wannan sirin Shashashan banza azzalumai Da Yardan Allah karshen ku yazo ku Fara Kirga Lokacin da zaku wulakanta.
Hajiya ta rasa ina zata saka kanta Saboda Farinciki,Ta kasa zama ta kasa Tsayuwa waje daya ta Daga Hannunwanta duka biyu sama tanayima Allah kirari domin wannan shi ake kira tsammanin Abunda baka yi Tsammani ba.
Hajiya ta rasa da wa zata ra ba wannan Farinciki na ganin Amina Dauke da cikin Danmallam ta Dade batayi farimciki irin na yau ba gashi mallam baya nan balle ta ruga ta Fadamai suyi wannan murnan tare yaya kuma bata Raye balle ta Ruga ta Fadamata Amina zata zama uwa nan bada Dadewa ba Amina zata koma yadda take so sai Bata a duniya lokacin da hakan ta faru sai dai tana Fatan Ta cikin samu salama acikin kabarinta har Abada.
Haj.Uwani ta Fado mata arai itace tafi Kusa da ita in wani abu ya sameta bayan mallam da Sa"idu itace ta ukun Datake sani yasa ta kwashi Sauri zuwa Shashen nata bakinta kamar zai tsage Saboda murna.
Koda ta shiga Falon ba kowa tsit tana Tunanin kila tana ciki ne yasa ta yi sallama sai dai ba"a amsa mata ba ta Bude baki zata sake wata sallama ne Taji Muryan Haj Uwani cikin shewa da Dariya tana Fadin"Batula naso kina wajen nan kiga idanuwan marliya gaban mallam da Hajiya..?
Kinga yadda ta muzanta ba halin ta Fadi wata mgana na riga na gama Daureta da Jijuyoyin jikinta..sai uban kuka take yi mallam kuwa yayi mata Fata Fata Hajiya har da yar Nasihan kan Marliya ta Daina bin malamai wlh Batula naso kiga yadda marliya ta koma abun Tsausayi..!
Shuru na wani Lokaci ya biyo baya Hajiya bata Fahimci kan zencen ba ganin kamar tana waya da Yar"uwanta Batula yasa Ta juya da niyyar Barin Falon AllaH barshi ta Dawo an juma ko in