Showing 93001 words to 96000 words out of 145917 words

Chapter 32 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83950

sai a fara kirga kwanaki Daga kwanaki sai a fara kirga satittika Daga Satittika sai a fara kirga wattani to kamar haka ne tunda gashi har su Hanne sun kamallah duka jarabawarsu ta kamallah babban Sakandiri suna gida sai jiran sakamako sai dai basu Daina zuwa islamiya da Hadda ba Daga Umarnin Baba mallam.
Har zuwa wannan Lokacin Daga ban garan Hajiya ba"a wani bayanin inda takai Amina ba,Sai dai irin Anty Amarya da mamanmu da sauran masu Tunani irin su suna Daukan Amina tana maiduguri sannan ganin Dadewa da akayi ba labarin takamammen inda Aminar take sai suke Tunanin auranta da Danmallan ne ya Lalace Hajiya ke son gyarashi.
Ita dai ta koma gefe tayi bakam bata taba nuna tasan wani abu ba, yanzu in an isheta da Tambaya sai tace bata sani ba,Har Abida data isheta haka ta Fadamata har kuma ya Aisha ta kira sun yi mgana ammh bata taba ce mata Amina na wajenta ba ta riga ta rike alkawarin Hajiya da gargadin datake mata akoda yaushe kan Boye Cikin Amina da zamanta a wajenta.
Anty Amarya ita da Uwani ake takun saka yayinda mamanmu ta koma gefe ta Zama yar kallo domin bata da wata matsala,In Anty Amarya ta Kirata sai ta mata Dadin baki da mganganun nasara ta rufe bakinta sai sun gama mgna ta rika mata Dariya Haj.uwani kuwa Amarya bata gabanta domin tana kallonta karamar alhaki ne badai Nazeem din na tare da Sa"idun ba har an sakarmai komai ba..?
Maji mgani an tura uwar Amarya Biko ita har ta hango kanta a matsayin data Dade tana Hango kanta Tunda Dadewa.


*****


Achan Abuja kuwa a bangaran Amina cikinta na cikin na wata Takwas kenan ta kara kiba sannan komai na Jikinta ya fashe hancinta bakinta komai ya kara girma sannan sai da cikin yakusa wattanin Haihuwansa sannan yayi wani irin girma Allah yasa tana da Tsaho ai da ya shanyeta,Tana cigaba da zuwa awo da ganin Likita In usman baya nan ita da ya Aisha take zuwa ko Zuwansu na karshen nan an tabbatar musu da Abunda ke Cikin Amina yana cikin koshin Lafiya.
Amina in ta kalli kanta a madubi sai ta fashe da kuka wai duk ta sauya kamar ba ita ba watarana Yakaka tayi ta mata Nasiha ranar da yan Fada ke kusata ta mata fada ko kuma tayi mata bakam kamar bata jita ba.
Kishin Amina akan mijinta ba irin na Sauran mata bane nata na Dabam ne akwai Tsabar jidali da neman rigima atare da ita koda yaushe suna waya da Danmallam domin yaji lafiyanta inda ta gane koma wani abu ne mamanmu ta mata ya fara rabuwa da ita ko tace ya rabu da ita gabadaya saboda ta gama amfani da duka mganin da ya Danmallan ya kawo mata Ta daina jin zafin zuciya da kunci sannan ta rage Taurin kai da Kafiya ammh fa bata rage rashin Tsoronta ba Sannan bakinta bai mutu ba Jidali kuma ta gama Fahimtar Halintarta ne sannan kuma Hali ai zanenn Dutse ne..
Ita yanzu ban da su Hanne da Haamida da Hajiya da mallam to sai Aba duk ba mgana take yi dashi ba yana ranta tana kuma bada sakon gaisuwa duk sanda sukayi mgana da Hajiya tace tana gayamai,Mamammu kuma ko Sau daya bata taba cema Hajiya a gaiisheta ba abun na bama Hajiya mamaki sai dai bata ma Aminar mgana ba Sauran yan"uwanta kuma duk da bata waya da kowa acikinsu suna ranta tana tunawa dasu Lokaci bayan Lokaci watarana in bakincikin ya isheta sai ta Zauna ta rika Tunano Rayuwarta Tun daga farko har zuwa yadda yau ta kasance da ita sai ta hau kuka sai tayi ya isheta take yin shuru ta koma tana Sauke Numfashi
Watarana in ta tuna da Aminu sai tace ko yana ina yanzu..?
Bata da masaniya sai dai tana mai Fatan Duk inda yake yana cikin koshin Lafiya duk yanzu bata san Dalili ba,bata jinsa aranta ko Domin tayi aure har da ciki ne..?
Ammh ai da Farko ai tana jinsa aranta ammh yanzu sam sai da ta tuna dashi tausayinsa ya kamata.
Danmallam kuma yana madina ne ammh Babu abuda Bai gani na Jidalin Amina bata barinsa yayi sukuni baya Kiranta in yana gida sai dai in ya fita Wajen aiki ita kuma Amina sai ta Fahimci hakan sai ta hada mai Tsiyarta bata kiransa sai ta Daidaici goman Dare a nan Nageria ko sha Daya sai ta kirasa shi kuma baya iya Share Kiran Amina data zama wata bangaransa a yanzu ammh baya yarda ya dauki waya gaban Sakina ko Sarood saboda komai na Bukatar sirri sannan akwai Tambayan da Sarood tatabamai bayan sun dawo wai ina Amina..?
Ko sun Rabu ne..?
Ya dade yana mamakin tambayarta Daya turketa sai ta fadamai wanda ya Fadamata saboda ba Tunaninta bane yadda yaga tayi ne yasa yasan Tsara mata akayi kuma ba kowa bace face Sakina abakinta ne Sarood zata ji wannan mganar bai ce ma Sarood komai ba ya bar mganar shiyasa yake kafa kafa bai taba bada Kofar da zasu Fahimci wani abu ba.
Ko a wayarsa Da NOOR yayi mata Saving din Lambarta hankalinsu kuma bai taba kaiwa wajen ba Saboda ma Tsaro yasa duk inda Zashi wayarsa na Hannunsa ko tana Jikinsa
Daya ga Kiranta yake kashewa sai ya ce bari yazo ko ya shiga Dakinsa ko ya fita waje in kuma yana Ciikin gari ya tafi masallaci sai ya sallami Amina da Rigimarta wanda shi da kukan nan nata in da zata mai kudi tsab sai ya siyesu da ya huta basu taba waya sun gama Amina bata tadamai hankali ba haka kurum sai ta kirasa ta sakamai kuka shi kuma Hankalinsa ya tshi bayason yaga Mace na kuka macen ma Amina fa duk yadda baisan Hayaniya yanzu sun kulla abota da ita Saboda Amina..
Ko dan wuni yayi bai kirata ba Daya Kira zata sakamai kuka tace ya manta da ita tana cikin wani Hali shi yana chan yana jin Dadinsa haka zai zauna yayi ta lallashinta har sai ta Sauko watarana ma in ta ji iskancinta bata Daga kiransa sai dai in ya gaji ya Kira Wayar Aisha suyi mgana sai an Lallabeta sannan take Daukan wayansa ta bakin yakaka tace duk ta rikita bawan Allah ita ya Aisha har mamaki take yadda Amina take juyaa Danmallam kamar waina a Tanda da Iskancinta iri iri.
Wani Lokacin fa sai da tashi cikin Dare ta Dokamai kira bata Tunanin wani Hali yake ciki yana tare da matansa ne ko basa tare..?
Ita kawai in ta kasa barci sai itama tace bazai yi ba,ai D'ansa ne ya hanata barcin shiyasa yawancin yanzu a Falo yake karihe barcinsa saboda da Zarar yaga Kiranta sai ya lallaba ya fita Falo in ya gama Lallashin nata bai komawa ciki sai yayi kwanciyarsa anan wani Lokacin ma barci ke Daukansa bai sani ba Tun Sakina bata saka Ido ba har ta Fara Tuhumansa ammh bata taba kamasa yana waya da Amina ba.
Ai shi ya kara ma saka mata suna Aminene jidali Aminene rigima duka taci sunanta domin ba wanda baya gani.
In ta fara kuka tana Fadin wai Cikinta ya Dunkule waje Daya ta kasa barci sai mamaki ya kamasa daman ai Dole Zata Fuskanci haka tunda Wani Hallita ne ke Rayuwa acikinta wani Lokacin sai ta faramai kukan duk tayi muni ta xama katuwa kamar ba ita ba Shi dai ai nashi ban Hakuri ne da lallashi Ranar datake jin yan arziki kuma ayi ta mai Shagwaban an yi kewarsa to sai ayi soyayya ranar kuma da yan tsiyan suke kusa sai a wuni ana Rigima ko kuma ta rika mai kananun kuka ya tafi chan ya manta da ita saboda yana da matansa achan shidai baki yake bata yana kawo mata Uzurinsa sannan take hakura kadan shidai fa yaga Jidalin Amina ganin idonsa ba Labari baa.
Dayake bata da matsalan kudi a waya Ya Usman na saka mata haka ma ya Aisha sannan ko kudin da ya Danmallam ya barta mata bata taba komai aciki ba sannan su ya Aisha bata karbi kudin ba tace Aminar ta ijiye a Hannunta tunda bata Bukatar
Komai na Bukatar Rayuwa babu abunda ya Aisha da ya usman suka Rageta dashi.
Mganar siyayyan Kayan Haihuwan kuwa Hajiya ya kira sa suka Tattauna yace zai turo mata kudi cikin satin da sukayi mgana Jafar ya kawo mata kudi 100k daga ya Danmallam,ita kuma bata taba komai ba sai ta nuna ma mallam shi kuma sai yace ta bari ya kara wani abu akai sannan yayi mganar Hada lefen da Umar bai samu hada mata ba mai zai hana a Hada ayi mata gabadaya..?
Sai Hajiya taga haka ya chachanta sai tace mallan din ya Kira Umar din suyi mgana haka akayi shi ya kirashi yamai tuni kuma ba domin ya Tunaamai ba sam ya manta yace zai Turo wasu kudin a kara dasu ammh zai siyan mata wasu kayan anan,Duk da bai da wani kudi a Hannunsa sosai bai Fadama mallam ba ammh shi mallam din ya Fahimci haka saboda Biyayyah Umaru garesa yasa kawai yayi ma Aba mgana aka fitar da kudi Dubu Dari hudu ya damkama hajiya yace a Hadama Amina lefe gangariya da kayan Haihuwa Bakin Hajiya yaki Rufuwa Amina ta fita Tsara Sai dai Danmallam yaji mganar kudin da mallam ya bada abakin Hajiya mamaki yasa ya kasa mgana Daya Kira mallam zai yi mgana sai ya hanasa albarka kawai ya sakamai tare da Fatan Cigaba da aminci a Rayuwarsa..
Danmallan kamar yayi kukan karamcin mallam agaresa wani kaunar mahaifinsa yana kara shiga ransa mallam kuma yasan tun bayan da Umaru ya tsaya da Kafafunsa bai Taba karban wani abu Daga garesu ba Sai ma shine da alherinsa baya yankewa koda dayake wani kasar Sannan yanzu Iyalai sun mai yawa ga Zama inda kasarsa ba akwai kashe kudi Sosai shiyasa yayi mai wannan karamcin domin ya nuna mai jin Dadin yadda ya amshi Umarninsa da Mutumci na auran Amina kuma ya riketa Bisa gaskiya da Amana.
Hajiya ita kanta taji Dadin hakan Sannan ai Dannallam ya chachanci komai a wajensu saboda Biyayyarsa,batare da Sanin kowa ba ta Kira Aisha sukayi mgana ta kuma Tura mata kudin duka 500k din tace a siya duka abunda ya kamata Hade da kayan Haihuwa ita kanta Aishar tayi mamakin uban kudin sai dai Tasan Amina ta Chanchanci dukkan gata yadda Hajiya da mallam ke sonta.
Duk ta Online tayi duka Siyayyan Tundaga kan akwatina da Sauran kayan Size din Amina kadai ta karba Duka har na bbys din ta Online ta siya so take sai ta gama Hada komai a kawo mata tunda anan Abujan matan mai saida kayan take Direba kadai zata bama Sako ya karbo mata.
Ko Amina bata san da kayan ba sai da aka kawo kuma na Jarirai kadai ta nuna mata ita da Yakaka Lefen kuma Damam Hajiya tace kada ta nuna ma kowa,Amina ita bata ma wani Damu ba Damuwarta ta Haihu Lafiya saboda ta fara Tsoron yadda ake fadin Haihuwa take Yakaka tayi ta saka albarka tana fadin basu da Tsara ita da takwaranta.
Acikin satin da Aisha ta gama Hada kayan Hajiya tazo ta Duba Amina ta kuma ga kayan wannan karon ma banda Mallam ba wanda yasan da zuwanta Amina taji dadin ganinta ta makaleta har da Hawayenta Hajiya mamaki ganin yadda Amina ta koma sai ya kamata ta fara Tunanin anya Mutum Daya ne acikin Amina ganin yadda girman cikinta ya wuce misali Har Aisha sai da ta ma mgana batace komai Sai Dariya datayi Hajiya bata kwana ba kamar wanchan zuwa Idi ya koma da ita bayan tayi ta ma Yakaka Godiyar irin kulawar datake bama Amina ta kawo mata kyautan Turaman Zani guda Biyu da Turaruka Yakaka nata godiya Hajiya ta tafi bayan ta sanar da Aisha ta bar duka kayan a Hannunta In Lokacin isan su gumel yayi zata mata mgana..!
Batare da kowa ya sani ba Danmallam ya yi ma Aliyu mgana ya neman masa gida anan gumel,yana so zai siya wannan karon bai nemi Jafar ba ballatana Nasir ko Aba ko Hajiya da mallam basu sani ba Aliyu kuma bai Fadamawa kowa ba an samu gida flat mai kyau da Tsari an gama ginasa kenan wanda aka bama kyautar kuma yace zai saida ne,An yi Ciniki Miliyan shida Tunda gidan bai da wani girma Bedroom biyu sai falo sai kitchen sai Haraban gidan karami shigar mota Biyu,To bayan ya fadama Danmallam kudin sai da akayi kwana uku ya Turomai kudin Saboda sai da ya Saida wani Share dinsa na harkan Saida gold da suke yi da wani Abokinsa Balarabe ne Riyad yake zaune Tare sukayi karatu shi sai ya koma kasuwanci,to shi yayi ta ma Danmallam Sha"awar fara kasuwanci har dai ya yarda ya saka Hannun Jarinsa suna dan yi tare to Kuma ba Laifi yana samun Alheri saboda Tasowar Hidimar Dake gabansa ya sa ya Karbi duka share dinsa Daga Hannun Abokinsa nasa.
Ya turo ma Aliyu kudin gidan sauran kuma ya rike a Hannunsa,Daman yana Tunanin siya ma Amina gida Saboda wanchan bazai Dauke su ba gata Zata Haihu tana Bukatar wajen da Zata zauna ita da abunda ta Haifa daman yana Tunanin yadda zai yi abubuwa sun mai yawa sai ga Tallafin mallam Daya Dauke mai hidimar Hala ma Amina lefe sai shi kuma yace bara ya wanke masu Hajiya zuciya da wannan gidan duk da daman akwai Sharadin siyan ma Amina Gida Tsakaninsa da su Hajiyan.
Gidan yana nan a anguwan Babura ne Dake garin Gumel makullan gida da Duka Takardun suna Hannun Aliyu ne tunda Shi yayi komai Yaso Umar ya Fadama mallam sai yace zai Sanar dasu sai Lokaci yayi yasan Tabbas Hajiya bazata bar Amina ta Haihu a Abuja ba gida zata Dawo da ita to yana so in ta haihu bazata zauna gidan Baba Sa"idu ko gidan mallam ba Insha Allahu sai dai ta Zauna agidanta.


Ana cikin hakane Mallam ya tara Su Hajiya duka matansa ya sanar dasu Cikin watan nan manema auran su Hanne da Hamida da Sa"adatu zasu zo su gana dasu basu yi wani mamaki ba Daman ai su san tunda sukayi jarabawa a SS2 susan mallam bazai zuba musu ido ba aurar dasu zai yi Anty Amarya ce kadai ta nuna Damuwarta ta kalli Mallan tana Fadin"Mallam nawa duka duka yaran nan suke..?
Shiyasa naso da ka bari sai wannan shekarar su zana jarabawar tasu kamar yadda duka yaran gidan nan suke yi..!
Mallam yace"To ai nasu tsarin ne yazo ahaka sun gama zaman me zasu yi..?
Kuma daman tun kafin haka suna da mgana akansu ai bazan zuba musu ido suna zaune haka ba sannan da kike mganar yara su hannatun ne yara..?
Ko basu kai sha takwas ba nasan sun kusa ko Hajiya..?
Hajiya na gefensa tace"Ai sun ma Shiga a watan musulunci mallam..Su kansu sauran yan"uwan nasu suna Sha takwas wasu sha tara ake aurar dasu nake ga..!
Mallam yace"Ahto .Nidai na fada muku ku sanar da yaran ku su fara Shiri Insha Allahu bikin kuma zai kai karshen watan gobe ne bazan Dauki Lokaci ba..Su kuma su Akilu na yi ma Wani abokina Dake Jami"ar ABU mgana zai tuntubamin in sun samu gurbin karatu chan zan tura su tare. !
Hajiya ta amsa da Allah ya bada Sa"a ya kuma yi albarka Hajiya ita da Hajiya Nasara Hajiya uwa dai duk yadda takai ga Boye Damuwarta Sai ta bayyana Mallam nata aurar da duka ya"yansa ya manta da Umaima ne .?
Bai taba mganarta ba ya Jingineta gefe ba boko ba islamiya sannan ba mganar aure Tunda ta ke ganin ta kusa Cika Burinta sai kuma Umaiman yanzu ne damuwarta.
Ita ke da mallam yau yasa su Hajiya suka fice suka barta sai da suka shiga Ciki bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya ta kallesa tana Fadin"Mallam naji kayi mganar auran su Hanne ne..?
Ban ji ka saka Umaima aciki ba..?
Na zata wannam karon zaka Hada da ita ne..?
Sai da ya Zauna gefen gado ya dora kafafunsa saman gadon sannan ya Fuskaceta yana fadin"Umaima da bata da Lafiya Uwani..?.
Kuma ma ba wanda ya kaawo min mganarta ne har yau shiyasa kikajini shuru da ita..Sannan ni fata na ta samu Lafiya sai komai ya Biyo baya. !
Sai hajiya Uwani ta saka kuka tana Fadin"Haba mallam domin Allah ya Daura mata wannan Laluran sai kace bazatayi aure ba .!
Ai sai ita ma ka hadata da mijin daya Dace da ita kamar yadda kake ma Sauran ya"yanka har da ma wanda ba Naka ba. !
Ta karishe Fada tana kuka kallonta kawai yake yi yana Nazarin mganarta Mimirshi yayi kafin yace"Uwani..Kinsan Kalmar wlh Rantsuwa ce..?
Ta daga kanta ya Cigaba da Fadin"To wlh tallahi ban taba Tallata ya"yana ba ko ya"yan Sa"idu ba Duk Cikin yaran da na aurar dasu zuwa akayi aka sameni mganar ana son aure Cikin iyalaina abu Daya nake yi shine ni nake Zaban wacce ta Dace sai nace na bama wane na bama wane kaza..Sau Daya tak na taba Aikata haka kuma shine na karshe da yardan Allah mganar Umaima kuma ni bazan zama mara adalci ba kamar Zalunci ne na aurar da ita da wannan laluran batare da sanin wanda zai aureta ba Saboda haka in Bukatar hakan ya taso Lalle to sai an Bude komai a Fili in wanda yazo neman auran yaji ya gani Shikenan Uwani nima zan so ganin na gama Sauke Nauyin aurar da duka ya"yan Matan da Allah ya bani..!
Daga haka bai kara mgana ba sai ma mganinsa na Ciwon kafa Daya Dauka yana Shafa ma kafarsa tasa.
haj.Uwani tayi jagale tana kallonsa kafin ta Cigaba da matsan kwallarta Hujjan mallam ai ba Hujja bace in ya bata da ita yadda ake ganin girmansa ai bazata wulakanta ba ammh Saboda An ga gazawarta ne kowace mata za"a gama kwashe ya"yanta ita kuma ko Oho.
Ranar haka suka kwana kowa da Abunda yake sakawa aranta,Da Safe data koma Shashenta ta Kira Batula ta Sanar da ita komai tana Fadin"Batula Hankalina ya fara tashi..kannen bayan Umaima mallam aurar dasu zai yi tana Zaune. !
Batula tace"Mafita kawai ki shiryo kizo Tsafe mu tafi Niger wajen mama..Bazamu bari aga gazawarmu b...!
Da wannan shawarar Haj.Uwani ta Zauna adaran ta tambayi mallam zuwa Tsafe bai hanata ba yace Allah ya tsare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login