Showing 138001 words to 141000 words out of 145917 words

Chapter 47 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83948

da Tarkadunta sannan yaran su kara Wayau shi ya Lallashi Danmallam da bai da tacewa Hajiya ai tagama dashi.
Ya samu Amina yana mata magiyan taje tace ma Hajiya ita zata Bisa su tafi Amina tace bazata iya ba sai yayi Fushi batare da sanin kowa ba ya Nema ma kansa Visa shi da Sakina Sai ana Saura kwana Biyu Tafiyarsu yaje ya Daukota Sakina sai da tayi kuka har ta cire rai da auranta da Umar ganin san da suka zo ko fuska bai Sakin mata baHakama yan"uwanta nata jin Dadi,Gidan mallam ya fara kaita Hajiya da mallam suka Taru suka mata Nasiha mallam kanshi yaji Dadi yadda Umar ya zama mai Afuwa
Sai alokacin yake shaida musu jibi zasu koma Madina shi da ita Hajiya tasan don Turama Amina Haushi yayi sai bata nuna mai ba kuma bai Fadama Amina zai koma ba Dauke mata kafa yayi ana gobe Tafiyar yazo yaga yaransa ita tana barci sai da Safe Yakaka ke Fadamata,Bata san ya tafi ba Sai da sukayi waya da ya Aisha take Fadamata Ya Danmallam ya tafi da Sakina itama Hajiya ke Fadamata Ranar Amina wuni tayi kuka Yakaka na lallashinra abun fa da Ciwo aiko bai Fadamata komai ba ya Fadamata Zai Dawo da Sakina ammh Duk Sai dai Taji Daga sama itama sai ta Zuciya ta Cigaba da kula da kanta da ya"yanta.
An biya mata Jarabawar ta a Unity dinsu da an fara zata fara zuwa sannan Huce Takaicin abunda Danmallam yayi musu Hajiya ta saka Baki mallam ya barta sukaje Abuja suka kwana Biyu ita da Yakaka dagachan har da ya Aisha suka Dumguma sai Zaria wajen Hamida suka kwana Daya gidanta suka kwana Gidan ya Zulfa suna ta murna da ina suka saka da yan"uwansu sun je har kaduna gidan Abida sun je kano gidan ya Jidda Lagos ne da parthercourt yayi nisa basu je ba Amina ta taka yola Wajen Hanne sai gata agidan Aminu Taga Nenne Dangi kuwa sai zuwa ganin Aminan Aminu ake yi yara kam sun sha Dauka shi kanshi Aminun ya kasa sukunu ya siyo wannan ya siyo wanchan,Amina sai yi ma Hanne Tsiya take ganin ta da Ciki.
Kwanansu Biyu suka Dawo Gida suka Sauke Gajiya..
Danmallam bai nemeta ba itama kishi da Haushin Abunda yayi mata ta yi biris dashi,Shi ma Yayi zuciya ransa ya baci da abunda tayi mai sannan kuma bayan ya tafi bata nemesa ba abakin Mallam yaji Tafiye Tafiyen da Amina tayi ko izininsa ba"a nema bai Taba Jin Haushi in Hajiya ta yanke Hukunci kan matansa ba sai kan Amina ya Lura tafi son Ma Amina da kowa komai take so shi take yi..
Amina Taurin kanta bai barta ba,Tana nan dashi shiyasa ta nuna ma Danmallam kalanta Har Yakaka taji Haushinsa Sai dai tayi ta lallashin Amima kada ta Damu sai ya Nemesu.
Ana cikin haka suka fara WAEC ta Dinka sabbin kayan makaranta ta fara zuwa Ranar datake da paper yakaka take barin ma yaran Agidan mallam in ta Dawo sai ta biyo sai yammah su koma gida Domin yakaka bazata iya Ronon yaran ita kadai ba gasu sun fara girma da kiba suna samun kulawa sosai..
Tana kokarin ya kice Takaicin Danmallan aranta taurin kanta yasa bata ko nemesa ba shima yaki nementa Amina tasan yaushe zai nemeta yanan chan wajen Guzumanyen matansa ita kuma tana nan tana mai renon ya"ya..!
Zai gane shayi ruwa ne da Aminene yake zencen..!




*Godiyata ta musamman ga iyayena guda biyu da sune silar tsayuwa kan kafafuna da nayi ayau din nan Alhaji Umar Muhammad mailoki da Malama Hadiza Muhammad Ba"are,Baba, mama ina matukar godiya da jajircewan ku akaina Ina godiya da Goyon bayanku ina godiya ga Allah da kuka kasance iyaye nagari a wajenmu Allah ya saka muku da Alheri ya muku Tukwaici da gidan Aljannah Firdausi Ameen Ina matukar son ku Babanmu da Hajiya mama tamu Allah ya kara muku nisan kwana da kwanciyar Hankali Ababen Alhafarinmu..*










*Janafty**TFZB2031*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*




Shifa Namiji duk inda yake sai ya nuna kansa barin ma in yana da mace fiye da Daya,Sannan su fa abunda muke kallonsa abun kunya a wajensu Daidai ne kuma mai kyau ne sannan in zaki shekara kina kyautatamusu Rana Daya in kika karkace sai ya manta baya ya Dora miki laifin duk Duniya akanki sannan ba kasafai suke Fahintarmu yadda Ubangiji Ya bamu ikon mu fahimcesu ba.
To kamar haka ya faru Tsakanin Danmallan da Amina ko yaya ne so yake ya nuna mata ba ita kadai garesa ba in bata bishi ba ai ya tafi da Sakina Sannan yayi hakane domin ya kure Hakurinta yana ganin kamar in ya tafin zata nemesa ta basaa hakuri sai kuma yaga akasin haka ya fahimci Tana da Taurin kai da kafiya domin shima Daurayewa yake da bai nemeta ba shi adole sai ta nemesa ta basa Hakuri sannan su sai su daidaita ammh Ina Sai ya Fahimci Amina tayi nisan da batajin kira.
Wajen watansa Biyu da Tafiya ko Flashing bai taba mata ba, itama haka Sai dai ya Kira Hajiya ko mallam yaji Lafiyansu wani Lokacin ma suna gidan in Amina ta tafi Jarabawarta koda wasa bai bari kowa ya Fahimci akwai baraka Tsakaninsa da Amina ba ballatana ita data share batunsa Sai dai Yakaka Datake zaune da ita ta Fahimci Tsakanin ma"aurata basa mgana Dole wani abu na faruwa.
Amina sun gama WEAC dinsu Cikin Nasara suna jiran Ta gaba lokaci Daya tana kula da ya"yanta sai kuma alokacin Danmallam ya gaji da Jiran Amina ta Kirasa su sansanta shi ya Sauke Girman ya Kirata taki Dauka Har sai da ya jera mata wajen sati yana Kiranta Tana gani bata taba Dauka ba sai abun ya kara bashi mamaki gashi dai anan hankalinsa yana kwance ne saboda Sakina tayi Laushi Sosai kamar ba ita ba,ga Sarood Daman bata da Hayaniya Cikinta ya shiga watansa na bakwai kusan duka ayyukan Sakina ta Dauketa mata ita ke yi tace Sarood din ta Huta duk yadda yake jin Haushin Sakina Sai da ya Tsausayamata da aka cire mata Mahaifa,duk son ta Haihu Allah ya nuna mata nasa ikon Da Farko bai Sakar mata ba sai daga bayaa shima din ba Sosai ba kadahan kadahan dai kada ya shiga Hakkinta sannan ya Duba Nasihan mallam da Hajiya ammh Daidai da rana Daya bai taba mantawa da Amina ba yana Madina ne ammh gabadaya ransa da Tunaninsa na Nageria wajen Amina da ya"yansa yaso ya jure sai ya kasa ammh Sai gashi yana kiranta bata Daga wayarsa.
Daya Dameta sai ta Fara Dagawa ammh yayi sallaman Duniyan nan tayi mai bakan sai da yayi ta jin kananun kukan su Aba na yara tun yana ganin Lamarin nata wasa har ya Fahimci abun nata yayi nisa,Ita kuwa yadda Danmallan ya kunsa mata Bakinciki ya raina mata wayau ne ta Dauki alkwarin sai ya gane bai da wayau sai yasan ya wulakantata Shiyasa ko da yazo yana kiranta Daga baya bata Taba bashi Dama ba Tayi alkwarin sai ta rama Fiye da yadda yayi mata sannan ta koyamai Darasin da har Abada bazai kara gigin mai da ita mara amfani a wajensa ba !
Yakaka Tasan basa mgana da Mijinta ammh bata taba mata mgana ba Sai Ranar Aba na wajenta mallan ne ke wajen Amina tana basa Nono,ta kawo mata shi kenan ta iske waya gefen Amina ta saka ta speaker Muryan Danmallan Tar yana mgana sai magiyan kiran sunan Amina yake yi tayi kamar bata ji ba, Hankalinta ma na kan bama Mallam Nono kamar yana Kiran Dutse..!
Fadi yake yi "Noor don Allah ba don Halina ba kiyi mgana..!
Amina haba Amina..Haba Amina da Allah fa nake hadaki..Nasan kina jina..!
Kiyi mgana saiki fadamin Laifina i Promise you zan baki Hakuri..!
Kinji Amaryata..!
Amina tayi wani Dariyan rainin Hankali har sai da yaji aranta tace su Amarya an ji jiki ai baka san ni Amarya bace sau na nuna maka matsayina..!
Yakaka na bakin kofa baki ta saki Tana Bin Amina da kallo Har Danmallam ya gaji da magiya ya Datse kiran Sannan ta kariso Dakin koda Amina ta ganta bata Damu da taji ko bata ji ba yadda ta yi nisan nan Mallam ko Hajiya ne kadai zasu saukar da ita Su kuma tana da Tabbacin ya Danmallam bazai bari su sani ba..!
Mallam ta karba ta miko mata Aba Amina ta karbeshi tana bata rai tace"Ni wlh na fara gajiya yaran nan duk sun gama tsotseni na fara yamushewa..!.
Tafada tana wani Tura mai Nonon a baki ruwan nonon ya kawo yaran ya Shake ya fara Tari Yakaka tayi Saurin Ijiye mallam Kan gadon Amina ta karbesa ta Daga sa sama tana shafa Bayansa Cikin Lallashi Lokaci Daya Tana Hararan Amina data kauda kanta Gefe kamar bata ganta ba..!
Cikin Ikon Allah aka samu yayi barci ta Lallaba ta kwantar dashi gefen Dan"uwansa sannan ta Dawo kan Amina tana Fadin"Ashe zama na Dake bamai amfani bane Amina..?.
Ina ga gwara nayi tafiyata sai ki zauna ki yi yadda kika ga Dama..!
Yakaka ta fada Cikin bacin rai ta Juya da Niyyar Tafiya Amina ta mike ta Riko Hannunta tana Fadin"Haba yakaka me kuma ya faru..?
Yakaka ta juyo tana Hararanta tace"tambaya ta ma kike me ya faru ko..?
Ai kina Sane Mijinki ya kiraki kin Dauka kina ji yana mgana kin yi banza Dashi Sannan kina bama yaro nan Nono kina mai mugunta kina so ki kashe ya"yanki ne..?
Kada ma kiyi Tunanin domin kun samu matsala da Babansu kike jin Haushin su yaro ina ruwansa..?
Sannan ki Sani yaki dan zamba ne Amina kuma abunda Hakuri bai baka ba Wlh Tsiya bazai taba baka shi ba. !
Kawai sai Amina ta saka kuka ta sanya Tafukan Hannayenta ta rufe Fuskarta dashi tana wani irin kuka mai cin rai Kukan Daya Dade yana Damunta aranta sannan Hade yake da Kishi da Takaicin D'a Namiji.
Yakaka sai Tsausayinta ya kamata ta Jawota jikinta ta rumgumeta tana Buga bayanta alamun Lallashi.
Amina sai ta Bude muryanta tana kuka sosai har da Shessheka.
Yakaka na Dafa bayanta Lokaci Daya Tana Fadin"Kidaina kuka Amina. bari kada yaranki su tashi su ga kina kuka. !
Gefen gado ta zaunar da ita tana Share mata Hawaye Amina ta Dago Tana kallon yakaka Lokaci Daya tace"Yakaka meye laifina da ya Danmallam zai min wannan wulakancin..?
Yakaka tace"Me ya faru ne..?
Amina tace"Kan mganar komawarmu Madina tare ne Lokacin da zai koma ai kinsan dani zai tafi Daga baya sai Hajiya ta hana tace sai nayi jarabawa Sannan yara sun yi kwari ko..?
Yakaka tace"Eh anyi hakan..!
Amina na sharan kwallah ta Cigaba da Fadin"To shine fa yazo ya sameni wai sai naje na samu Hajiya nace ni zan Bisa..Ina aka taba yin hakan yakaka..?
Tsakanina ga Allah fa Hajiya matsayin uwa take gareni tana da kimar da zata yanke Hukunci kan abunda ya Shafeni nayi shuru da Bakina Saboda bazata taba aikata abunda zai zama Cuta gareni ba..!
Yakaka tace"Kwarai Amina..Daga ke har Danmallam din Hajiya ta isa ta Zartar da komai akan abunda ya Shafe ku batare da kun Daga ido kun kalleta ba..!
Amina na kuka tace"To shine fa Dalili Saboda nace mai ni bazan iya zuwa nayi ma Hajiya musu ba..Hajiya tamkar uwa take gareni tamin abunda ko Uwata Data Haifeni sai haka Tayaya zata ce ga abunda ya kamata kuma na bata kunya..?
Na fadamai bazan iya ba shima yayi hakuri nan da wata Biyar komai ya Daidaita sai in na koma chan ba Jeka ka Dawo shine yayi fushi Yakaka ya tafi ya Dauko Sakina fa ya tafi da ita yakaka Wlh kin ji rantsuwan musulmai bansan ya tafi ba ko sallama bai mim ba ballata nasan da Sakina zai koma in ya gayamin zan Hanasa ne ai matarsa ce Tare na gansu..Ammh sai yaki Darajani ya saka Kafa ya tafi ya manta Dani Ko waya bai tabamin ba sai acikin kwanakin nan duk wani abun na yaran nan ko kayan abinci sai dai su ya Jafar su kawo ni bai taba mgana Dani ba..Sai yanzu ya san Dani..?.
Yakaka ina Laifina domin naki Sauraransa don Allah..!
Amina ta karishe Fada Cikin kuka Yakaka ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya Umaru bai kyauta ba..Nima da Hajiya ta Fadamin da Sakina ya tafi sai da naji ba Dadi to ganin baki min mganar ba yasa nima ban miki ba..!
Amina na jan majina tace"Yakaka ki Duba mganar nan ina Laifina aciki..?
Yakaka tace"Baki da Laifi Amina ai Hajiya tana gaba da Umar bama ke ba..Sannan abunda babba ya Hango ai yaro ko Rimi ya hau bai isa ya Hango ba.Sannan ta yaro kyau take bata Karko..kiyi hakuri Ki kara Hakuri ke Macece sannan shi Mijinki ne kuma Shugabaanki ne kina kasan shine biyayya ya zama Dole gareki Ki yi Hakuri ki Sauraresa kiji ko dame yazo..!
Amina ta mike cikin Wata murya tace"Yakaka kiyi hakuri bawai bazan Saurari mganarki bane..A"a naji mganarki sai dai nayi Rantsuwan bazan Taba sauraransa ta waya ba..In ya matsu ya tako yazo ya Sameni in yana so na Sauraresa ammh matukar yana Chan wajen wadanan matan nasa bazan taba Sauraransa ba..Ya zauna dasu Tunda su ya Zaba..Zai gane muna mata ya tara..ga inda suke nan suke bata mawa su nuna an musu ba Daidai na rantse ga Allah Sai na nuna mai ni ba abanza nake ba Sannan nafi karfin yamin wannan wulakanci yaci banza. !
Ta karishe Fada tana Huci Yakaka tayi Dariya kafin tace"Na tabbatar miki da zai zo..mu ai ba"a isa a wulakantamu ba..Na goyi bayan ki nuna mai kema kina da Muhimmanci..!
Yakaka ta bama Amina goyon baya Sai dai ta mata Fada tabi komai a Sannu sannan ta Sasaauta.
Ana cikin wannan Tsukin Ya Ikram ta Haihu Amina sai taji Dadi tunda basu Fara Neco ba Da ita akayi suna ya Zulahait ne kadai tazo sai ya Fatima Sauran duk basu samu zuwa ba,Kuma har alokacin Danmallam bai Daina Kiran Amina tana banza Dashi ba Shi kuna yaki Hakura ita kuma Taurin kanta bazai barta ta Saurareshi ba..
Suna waya dasu Hanne har Hamida yanzu tana da ciki sannan bata Taba Fada musu ga abunda ke faruwa ba tadai Samar dasu sai ta gama Jarabawa zata bi ya Danmallan madina sai Tsiya suke mata wai wa ya ga Amina a madina ita kuma tace sai ma sun ga ta Saje da Larabawa..!
Sun Fara Neco dinsu cikin Nasara wani Lokacin da Yakaka suke zuwa makarantar in suna kuka takan fito ta basu Nono malaman makaranta su kansu mamaki suke Amina ce ta zama uwa ta kuma natsu kamar ba ita ba Tsakaninta da kowa sai gaisuwan mutuntawa Kamar ba itace a ka sha Gwagwamarya da ita ba Daman Haka Rayuwa ta gada
Danmallam kuma Amina na Neman ta Hauka tashi ko barci ba yayi yasa ya nemi Tahowa sai dai bai sami Dama ba Sai karshen wata Yasa sai ya bari karshen wata in yazo sai su yi ta kare shi da Amina yarinya karama zata chazamai kai da Rigimanta Shi yana ganin Rigiman mata ammh na Amina na musamman ne ita kadai take Fushi Dashi yaji ya Damu yanzu hakama Duk ya kasa sukuni har su Sakina sun Fahimci wani abu na Damunsa ya Dade da Samin Amina nada Jidali Sai dai baisan haka take da Taurinkai ba sai yanzu da ta nuna mai Sai yaji yana raina ta ashe ta wuce nan sannan kuma yana raina matsayinta aransa sai yanzu yasan Amina ta fita zakka ko acikin zuciyarsa komai in da tayi Birgesa take yi.
Bai yi shawara da kowa ba ya nemi Visa suma su Sakinan sai ana gobe zai Tashi ya Sanar dasu zai je Nageria Duk da bai Fada musu ba susan wajen Amina zai je basu ji Haushi ba Matarsa ce sannam kuma uwar ya"yansa.!
Washegari yabi Mota zuwa Jidda Sannan Daganan jirgin Dare yabi zuwa Abuja,washegari suka sauka Filin Jirgin Nnamadi azikiwe Dake Abuja da yammah sallah kadai ya Tsaya yayi ya hau Motar Haya zuwa Gumel batare da ya kira kowa ba. !motar bata gudu sosai basu isa Gumel ba sai Dare misalin Karfe Tara a masallacin Anguwan ya Tsaya yayi Mangariba da Isha"i sannan ya nufi Gidan Amina get din na Rufe Daman bai Dauki megadi ba ta cikin gida ake Rufewa..wayar Amina ya Kira Duk da yasan bazata Dauka ba Haka ya Dinga jera mata Kira bata Dauka ba.
Sai ya Hakura ya koma yana Faman Buga get din Amina na Dakinta kwance ita da ya"yanta har sun gama Hira da yakaka ta nufi Dakinta ita kuma tazo tayi wanka yaran daman yakaka ta musu na yammah ta Gaji yau English sukayi tun Safe sai yammah suka Dawo Har yaran sun gaji suna shan Nono sukaji Ruwan zafi suka fara Barci itama barcin Take ji Tana Fitowa wanka tayi salla ta Saka Rigar Barci masu Taushi Riga da wando ta saka Hula ta kwanta wayar ma na chan gefen gadon kuma tana Silent ne shiyasa ma bata ji ba Sannan har buga gidan bata jiba sai Yakaka ce Data fito Daukan ruwa a Kitchen taji kamar ana Buga gida.
Sai ta Tsaya ta kara Saurarawa taji Dai da Gaske ne har zata leka Amina sai kuma ta fasa jikinta ya fara rawa tana Tunanin waye ne da Daddaran nan..?
Sai tayi tunanin ko su Jafaru ne..?
Yasa ta Dauki Tocila ta fita har Haraban gidan dayake an Dauke wuta tana fitowa taji buga get din anan ne yasa ta karisa jikin kofar tana Fadin waye..?
Danmallan Dayaji muryan yakaka sai Hankalinsa ya kwanta Cikin Muryansa mai Sanyi yace"Ni ne Yakaka..!itama ta gane Muryansa Cikin mamaki tace"Danmallan..?
Yana mirmishi yace"Nine yakaka..!
Da Hanzari ta Cire sakatan kofar get din sai gashi ya bayyana a gabanta Har ya shigo tana cikin mamaki ita ta koma ta kara kulle kofar get din ta Juyi Tana Fadin"Danmallam zuwa ba Sanarwa haka.?
Danmallam ya shafa kanshi bai ce komai ba yana Sanye da yadi mai Santsi riga da wando kansa ba Hula sai Sumar kansa data Fara Tahowa yana gaba tana Binsa a baya har Cikin Falon gidan sannan suka gaisa yaga gidan da Duhu Lokaci Daya yace"Yakaka Sun Dauke wuta ne..?
Yakaka tace"Da yammah nan suka Dauke ammh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login