Showing 84001 words to 87000 words out of 145917 words
mata mgana..Gidan ba wanda ya tashi..!
Da haka ya nufi Bedroom dinsu shi kanshi ai kayan barci ne masu taushi ajikinsa Aliyu ya bisa da kallo har ya bace ma ganinsa Umar ya kallah yana kara nazari da Tunanin me suka zo yi gidan Aisha..?
Shi dai yasan ko gidajen su Jafar a kirga zuwan Umar ko Nazir kila sau Daya ya taba Taka Lagos in bai manta ba bama shi kadai ba ko su isu isu matan Mallam bai yarda su rika Bin gidajen juna ba sai da kwakkwaran Dalili ballatana shi namiji kuma in bata ma da Lafiya ne ya tabbata sai dai Cikin su Hajiya za su zo bashi ba Gabadaya mamaki ya kamasa daya kasa mgana shi kuma Umar kansa ya Jinginar jikin kujera Idanuwansa a Lumshe fatansa da Burinsa yaga Amina yaga cikisa Dake Jikinta Da yanzu yakai wata shida.
Usman Cikin blanket ya Samu Aisha ta nade tana barci yaye blanket din yayi yana kiranta.
Sweety..!
Dakyar ta Bude ido cikin Barci Tana Fadin'"Darling ka barni nayi barci don Allah..!
Kafarta ya matsa yana Fadin"Baki fa mukayi..!
Bude ido tayi da Sauri tana Fadin"Baki kuma..?
Da sassafan nan..?
Mikewa yayi yana Fadin"masu muhimmaci ne kuma ba Safe bane wajen 12pm fa yanzu rana tayi!
Mikewa tayi tana mamakin wasu irin baki ne haka sai ta saka aranta yan"uwan Darling ne ammh Daga barayinta bata tsammani haka ba.
Dogon Hijabinta ta Zurma na sallarta ne kan kayan barcinta Doguwar riga ta Sako Silafas dinta na yawo Cikin Gida ta fito shi kuma yana Biye da ita a baya har Cikin Falon.
Wadanda ta gani ne yasa ta Tsaya Cak tana kallon Usman baki Bude Dariya yayi mata ya koma ya zauna yana Fadin"Suprise..!
Saboda murna sai ta kasa zama Cikin wani yanayi a muryanta tace"Ya Danmallam .!
Ya Aliyu..!
Tafada Cikin farimciki suka kalleta gabadayansu suna mata Mirmishi ai da gudu ta nufi Danmallan ta Rumgumesa daga Zaune saurin Kwacewa yayi yana Fadin"Miye haka kanar wata yarinya..?
Tana yar Dariya tace"Allah ya Danmallam nayi murnan ganinku ne ko Jiya mun yi mgana da Hajiya bata fadamin zaka zo ba..!
Kai Tsaye Danmallam yace"Ban tabbatar da tafiyar ba nima..!
Kasa ta koma ta zauna tana gaishe da Aliyu ya amsa cikin Fara"a sannan ta gaida Danmallan ya amsa mata ta Tambayi sakina da Sarood yace"Duk suna Lafiya sarood da ita muka zo Tana gumel..!
Aisha tace"Allah Sarki..Sannun ku da zuwa gaskiya ammin zuwan bazata kuma Harda Darling aka hada baki ko..?
Tafada tana Hararansa da Sauri Aliyu yace"Kada ki ga Laifinsa ba ruwansa ko ni da ya Daukoni Tundaga Dutse bai Fadamin gidan nan zamu zo ba..Ga mai Laifi nan yayanki..!
Yafada yana Hararansa da bai masan yanayi ba,Aisha zatayi mgana kenan sai ga Saude da Faranti Cike da kayan ruwa da Lemo Aisha ta karba tana Fadin"Bari nazo Kitchen din Saude yayyina ne suka zo..!
Ta amsa cikin Fara"a tana gaishesu suka amsa mata sannan ta fice Daga Falon taja Center Table din Dake Falon ta Dora musu akai tana Fadin"Ku fara da wannan yaya..bari a sama muku abun karyawa..!
Aliyu na Dauka goran ruwa yace"Tab ai mu nan sai da na Rana..ni kinsan ban cika irin wannan abun na bature ba..Sai dai shehi kila shima bai karya ba ya fito..!
Sai yanzu ya Hararesa Yana dan kallon Usman da hankalinsa baya kansu yana kaa wayar hannunsa ya karkata daidai saitin kunnensa yace"Kaima kenan Dake da mata Daya kayi karin ka agida ballatana ni Dake da Daya biyu uku..!
Ya Fada yana Kirgasu da Hannu Aliyu na Dariya yace"Ba shakka..!
Usman ya mike yana isa kusa da Aisha a hankali yace"Kefa ba waJen ki suka zo ba.Wajem Amina nefa ammh kin Tsaya kina ta kallonsu..!
Kanta ta Dafe ta juya tana Fadin"Murna ce ta sa na Rude Darling..!
Mirmushi yayi mata sai bai bita ba yace ma su Aliyu bari yazo ya tafi ya basu wuri kada ya Takura musu.
Amina na Dakin yakaka kwance akan gado tana barci yakaka kuma na Saman Darduma ta daidaici gabas tana Ta lazimi tun bayan data gama Sallar walha ko Hijabin jikinta bata Cire ba ammh sai faman gyangyadi take yi.
Aisha ta shigo Dakin da Sallama yakaka ta amsa cikin Fara"a tana Fadin"Aisha kin tashi..?
Gaban yakaka ta Durkusa tana amsa mata Lokaci Daya da gaisuwa Ta amsa tana Tambayan Tashin Usman tace mata Lafiya Amina ta kalla data yi kwanciyar gefe saboda Cikin jikinta tace"Yakaka ita wannan bata tashi bane..?
Yakaka tace"Tun dai da ta koma bayan Sallar asuba bata tashi ba..Kinsan ta da barci kuma kila Cikin mganin da likitan ya bata akwai na barci ne inaga..duk da dama tun jiya naganta tana tura baki tana kunkuni bansan me aka mata ba.
Aisha tace"To ina ga...,Yakaka ai Takwaranki jidalinta tashi yake yi ko ba"a mata komai ba..
Yakaka tace"A"a yafi dai tashi in an Tabamu..!
Ya Aisha tayi Yar dariya kafin tace"To ai tashi zatayi yanzu yakaka mijinta ne yazo..!
Yakaka ta zaro ido Lokaci Daya tana Fadin"Wani mijin nata..,?
Ya Aisha ta mike tana Fadin"Ya Danmallam mana yakaka..!
Yakaka sai ta mike tana Fadin"Allahu akbar kice bakin Madina garin manzon Allah Sallahu alaihi waasallam..Zuwa haka ba sanarwa..?
Ko daman kin san da zuwansa..?
Aisha tace"Bai fadamin ba yakaka..!
Yakaka na gyara Hijabin tace"Ahto bari na fita mu gaisa ki tasheta in ta Tsaya wannan kunkunin nata kice na tafi kwace mijin sai ya cike ta Hudu dani ya Rufe kofa..!
Ya Aisha na Dariya tace"To yakaka .!
Ta fice tana Fadin"Tadata ta taso ai barcin ya isa haka..!
Ta fice abunta ita kuma ya Aisha ta dan Daki gefen katifa tana kiran sunan Amina sai chan ta jita ta dan Dago kai Cikin barci ta Bude idonta ya Aisha tace"Dilla ki tashi barcin ya isa haka..!
Amina zata sake juyawa Aisha ta Make mata hannu tana Fadin"Ya Danmallam ne fa yazo Amina..!
Da sauri ta dan mike zaune tana Fadin"Da gaske..?
Ya Aisha ta mike tana fadin"Ko nace ya shigo ne..?
Amina ta Tura baki batayi mgana ba Ya Aisha tace"Suna falo suna gaisawa da yakaka ki Sauya kaya ki sako Hijabinki ki fito ku gaisa..!
Daganan ta fice Daga Dakin Amina ta Bita da Harara tana kunkuni tace"Ba"aza afiton ba sai yau ne ma zai zo wajena tunda ya dawo ya manta dani ya samu guzumayen matansa ko kirana bayayi..!
Ashe Fushinta datake yi kenan tun jiya Saboda sau daya suka yi mgana Daya Dawo.
Aisha na fita falo ta iske yakaka sai Hira suke sha da Aliyu Har da ya Danmallam da bai mgana Dariya kawai tayi yakakace fa balle ai yasanta Saboda in suna waya da Amima yana jin mganarta sannan sun taba gaisawa sau biyu da ita kuma ai Hajiya ta Fadamai akwai kakar Usman agidan tun kafin ta kawo Aminar.
Tana ganin Aisha tace"To ina takwaran tawa.?
Na ganki ke kadai..?
Aisha tace"To nidai na tasheta na Fadamata ban sanin mata ba..!.
Yakaka tace"Kajimin shegentaka ace maka ga mijinki ya taso daga wata uwa Duniya domin ka sai ka Tsaya Sakarci..?
Ahtto ni dai dan madina tunda Takwaran tawa tana ja maka aji gani sai ka Rufe kofa dani mu Daga garin manzo sai dai taji asalansa..!
Dariya Aliyu yayi tsohuwar farat Daya ta shiga ransa sai da yana ta mamakin waye wannan da Aliyu yazo gani..?.
Saboda shi bai taba sanin Amina bata nan ba..
Danmallam ne yace ma yakaka"Shikenan baaba..Sai mu tafi Dake ai ni naga Amaryata.
Ta washe baki tana Fadin"ah to in ita bata so..Ai ni ina son abuna..Daman ita naso na raka garin na manzo Tunda na mata fashin Mijin ai shikenan kowa yayi ta kansa..!
Har Aisha sai da ta Dara yakaka ta mike tana kallon Aisha kafin tayi mgana sai ga Amina ta shigo Falon da Karamar sallamanta tana Tura baki Sanye take da Dogon wando plazo Sai Dogom Hijabin Dake jikinta duk hannun Data sanya mbai iya kare Cikinta Daya bayyana ba sannan tayi Kiba har ta Fuskarta ta Cicciko Idanuwanta duk girmansu sun shige Ciki.
Yakaka na ganinta ta koma ta zauna tana Fadin"ki zauna kina wani Tafiyar wahainiya ni dai na riga na yi fashin Dan Madina abuna..!
Amina ko kanta bata Dago ba har ta kariso falon Aliyu Sai kallonta yake yi ya Bude baki yafi a kirga yana Rufewa saboda mamaki Danmallam kuma Hannayensa Sarke saman kirjinsa yana kare ma Amina kallon Tundaga sama har kasa yana mamakin girmanta yarinyar daya barta marabanta da kwaila kadan ne itace ta koma wata Big mama..?
Ko"ina ya cika haka?
Cikinta kawai yake kallo duk nacinsa taki yarda su hada ido shi ko Aliyu ba mamakin ganin Amina bane ya Razana shi ba illah Cikin Dake jikinta ne ya fi bashi mamaki ya kalli Umar yafi sau goma ya kasa mgana shi kuma sai ya basar dashi bai shirya mgana dashi ba yanzu.
Amina kuwa kanta na kasa ta nemi kasan Cafet ta zauna Dakyar yakaka na fadin"kada ki takura kanki kowa yasan Lalurace hau kujera ki zauna mana..!
Ko kallon yakaka batayi ba tayi zamanta Saman cafet kanta na kasa Ya Aisha sai kallon Amina take yi tana Hararanta ganin yadda ta hade rai Yakaka ta saki baki tana kallonta kafin tace"Yau naga Tsiya Indo..?
Amina fa sai Addu"a jira take su gaisheta kenan..?
Amina sai alokacin ta Dago kanta karaf suka Hada ido da ya Danmallam Daya gama kafeta da ido tun shigowarta ya kasa dauke ganinsa akanta yana ta mamakin girmanta sannan yana Tunanin yadda yaganta da Cikin nan bai taba Hasaso hakan nan kusa ba akanta ba sai gashi Allah ya nuna nashi Ikon.
Saurin Dauke kanta tayi Saboda wani Dum dataji da yanayin kallon nasa sai da taji dan Cikinta ya koma gefe daya Ta Cikin Hijabin ta dora hannunta kan cikinta tana jin wani kaunar abunda ke Cikinta na kara shiganta Tun ranar da sukaje Scan aka hasko mata abunda ke Cikinta wani soyayyarsa ta ratsa kirjinta taji duk duniya bata da wanda take so kamarsa abun ya bata sha"awa dan mutum acikinta yana Rayuwa..
Bata kara kallonsu ba cikin shakewar murya tace"sannun ku da zuwa..!
Aliyu ne ya amsa yana kallonta Cikin Shanye mamakin sa yace"Yauwa Amina ko..?
Amina ta dago ta kallesa kafin ta maida kanta kasa ta gyada mai kai Cikin mirmishi yace"Allah Sarki ashe kina nan..?
Ya nauyin jiki kuma..?
Sai ta kasa mgana Yakakace ke fadin"Ai ta Dade anan watan ta biyu ko Aisha..?
Ya Aisha tace"Eh ta dan jima..!
Aliyu ya jinjina kai yana kallon Amina yace"Allah ya rabasu lafiya..!
Yakaka da Aisha suka amsa mai da Ameen ya Danmallan dai bai ce komai ba,Sai kallon Amina yake yi kasa kasa.
Aisha tana Lura dashi sai ta isa wajen Amina tana fadin"Amina taso na ganki mana..!
Tafada tana taimaka mata ta mike Tsaye yakaka ta kalleta tana Fadin"Ahto gwara ki jata ki Fadamata gaskiya ko zataji..Koda yake ta makara na riga na kwace mijin Dani zai koma garin Manzo..!
Aliyu na Dariya yace"Kwarai baba. !
Hararanta Amina tayi tana Tura baki Yakaka tace"Ni miye nawa..?
Ga wanda zaki tura ma bakin nan..!.
Tafada tana nuna Danmallam da suka Hada ido da Amina ta Tura mai bakin sannan tabi bayan Aisha Mirmishi ya subucemai tuna Kirarinta Aminene ce fa..badai ta mutum ba sai ta Allah .!
Yakaka ta bita da kallo tana rike baki tace"Mun shige su ta ko turamai bakin Ali kana dai gani ko..?
Dariya yayi yana Fadin"Kyalesu yakaka chan tsakaninsu ne mu ba ruwanmu..!.
Yafada yana kallon Umar Dayaki yarda su hada ido.
Inda su Amina suka shiga ya kurama Ido Yakaka da Aliyu suka cigaba da Hirarsu tana ta mai Hirar zuwanta Saudiya ne na farko yana shan Dariya shiko Danmallam gabadaya hankalinsa na kan Amina shi yasan Laifinsa tun kafin ta fada.
Suna shiga Dakin ya Aisha ta ja ta tsaya tana Hararan Amina..
Amina ta nemi gefen gado ta Zauna tana Fadin."To wai ni me nayi ne..?
Ya Aisha tace"Bansani ba..Kada kiban Haushi na make ki wlh..!
Amina ta tura baki batace komai ba ya Aisha ta zauna gefenta tana Fadin"Haka ake gaida mutane .?
Shi fa ya Dannallam ko gaishesa baki yi ba ballatana ya Aliyu..!
Amina tace"To ba nace musu sannu da zuwa ba.!
Ta fada tana Hura Hanci Aisha tace"Ai sannu da zuwa ba gaisuwa bace malama. !
Amina ta tura baki tana fadin"Ni ba ruwana dashi sai fa yau yazo alhalin yafi kwana hudu da zuwa kuma kuma ma sau daya ya kirani tunda yazo wato yana chan wajen guzumayen matansa ni kuma yamin ciki ya barni da Wahala..!
Sai hawaye Ya Aisha ta saki baki tana kallon Amina Dariya na cinta tana auna Dimarar da za"ayi in zama waje Daya ya tabbata Tsakanin Amina da su Sakina akwai kallo.
Ya Aisha data Fahimci kishi Amina ke yi bata sani ba yasa Cikin sigar lallashi tace"To ai gashi yazo yanzu ko..?
In ma zaki nuna bacin ranki bata haka Zaki nuna ba kamata yayi yanzu ki tashi kiyi wanka ki sauya kaya ki gyara Jikin ki kina tashin kamshi,Sai in dan ya shigo kuka gaisa sai ya ce ya kike..? Ko ya bby na..?
Sai kice ai baka so kasan ya nake ba Tunda kazo su Anty na sun sa ka manta dani..!
Irin haka dai cikin shagwaba..!
Amina ta kalleta Sheke sheke kafin tace"Tab uban wa zai ce musu Anty..?
Allah ya Tsareni ni ko abaya ban ce mata Anty ba ballatana yanzu da muka Hada miji kowa yayi ta kansa .!
Ya Aisha na danne Dariyanta tace"To naji Kiyi hakuri ki tashi kiyi wanka ni yanzu Kitchen zani na sama musu abunda zasu ci ni da Saude kin karya ko..?
Tana kunkuni tace"nasha kunin da Saude ta Damama yakaka..!
Ya Aisha ta mike tana Fadin"To yi wanka in mun gama sai Saude tayi miki wainar Fulawanki..!
Da haka ta fice bayan ta kara Lallaba Aminar ganin kishin Ya Danmallam take yi bata sani ba..
Falon ta koma yakaka dai da Aliyu sai hira suke sha,Danmallam kuma na Zaune yayi shuru,Tace bari ta shiga Kitchen suka amsa mata sai da ta leka Usman ta iskesa yana waya sai ta fice ta shiga Kitchen domin taya Saude wasu ayyuka,sun saba tun agida basu taso da son jiki ba.
Amina tana Fushi tana kunkuni tatashi tayi wanka tazo ta Shafa Lotion din da Ya Aisha ta siya mata ta Dauko Cikin Dogayen rigunan da Aisha ta siya mata mai kalan baki da Zanen ja ajiki.
Ta saka Rigar kenan ta juya saman gado ta Dauko bakin Dankwalin Rigar sai ta dan taka Rigar ta kasa ta dan Zame tayi baya zata fadi har ta Sadakar ta sha kasa taji ta ta Fada Hannun mutum tana Bude ido suka Hada ido da ya Danmallam har Gemunsa na taba Fuskarta.
Kallon kallon sukama juna kowa da abunda yake sakawa gajiya yayi da Zaman falo yakaka da Aliyu na Hiransu ya tashi ya shigo Dakin da Amina ta shiga tun dazu Aliyu ya Bisa da kallon mamaki Yakaka dai batama Lura dashi ba Ta tsinke da Hira abunta.
Amina ta lumshe ido jin kallon nasa har Cikin kanta Saurin tashi tayi ya taimaka mata ta tsaya sosai yana Fadin"Ki kula fa Aminene..!
Da mugun mamaki ta kallesa tana Tunanin ina yasan ana ce mata Aminene..?
Gira ya Daga mata yana Sakin mata Mirmishinsa na koda yaushe Daga sama har kasa yake kallonta yana kara more kallonta Har da jingina jikin Madubin Dakin yana dunkule hannayensa saman kirjinsa yana binta da kallo da dukkan zuciyarsa.
Ita kuma ganin yadda yake kallonta yasa ta Tura mai Baki ta juyamai baya tana kokarin Daukan Dankwalinta ta Rufe Kitson kalaban da ya Aisha ta mata.
Kawai sai jinsa tayi a bayanta gemunsa na taba wuyanta saboda ya fita Tsawo ita tana iya kirjinsa ne Dankwalin ya karba ya rankwafa yana mata rada"Ya kika juya..?
Kada kimin rowan ganin Yadda Cikina ya sa kika tashi daga kwaila kika koma Big mama .!
Batasan Sadda ta sakarmai Dankwalin ba ga kunya sannan ga fushi sai ta ki juyowa tana Tura baki hannunsa duka Biyu ya sa ya juyo da ita yana kallonta Runtse ido tayi taki Budewa.
Dariya ta basa sai ya ja karan Hancinta yana fadin"Duk fushin ne yasa ko kallona ma an kasa yi..?
Kara Turo bakin tayi sai ji tayi ya Sakar mata Kiss a saman bakin da Sauri ta Bude manyan idanuwanta ta ware akansa cikin mamaki gira ya Daga mata yana kallonta itama shi take kallo ya kara fari sannan yayi kiba Yana sanye da Shadda fara dinkin Tazarce da hula sai tashin Sayayyan kamshin Turaransa yake yi mai Dadin Shaka wanda Amina taji yana mata Dadi har Hancinta take Budewa tana kara shaka..
Gemunsa take kallo ganin ya kara Tsawo sai dai yana sheki yaji gyara sosai ya shagala da kallonta yaji ta jamai gemu da Sauri ya kalleta yana Waro ido tura baki tayi lokaci Daya ta kara Juya baya.,Mirmishi yayi kafin ya taka zuwa Gabanta yana kaallonta kokarin kara juyawa take yi ya rikota Cikin mararaicewar da baisan ya iya ba yace"Haba MEENA..a daure a fadamin Laifina mana..?
Meenar da yace ne yasa ta Kallesa Cikin wani yayi a baya Aminu kadai ke kiranta da wannan sunan a kuma Lokacin sai taji yafi kowa iya Kiranta da haka sai dai yau sai taji Duk Duniya sunan a bakin mai Daraja wato Danmallam yafi dadi
Lumshe ido tayi sannan ta Bude tana kallonsa hannunta Daya ya rike Dayan kuma ya Dafa Cikinta yana Fadin"Ko saboda Abunda ke Cikin ki Amina .!
Baki ta kara Turawa kafin tace"Ba kai bane..Sai yau kazo ganina..!
Sai ido ya kawo ruwa da Sauri yace"Am sory kiyi hakuri kinsan gajiyan hanya..Sannan kinsan Dole sai na natsa na samu natsuwa ko .?
Amina ta Hura hanci tana Fadin"kuma ai baka kara kirana ba Tun ranar da kace zaka kirani. !
Sai hawaye sharr suka zubo baisan Lokacin Daya jawota jikinsa ba ya Rungumeta har Cikinta na Dukansa bai Damu ba kam ya rumgumeta yana jin wata natsuwa da salama abun mamaki itama hannayenta tasa ta Zagayo bayansa ta rikesa kanta ta baje saman kirjinsa domin sai taji kamar ta samu kafadan data Dade tana nema domin tayi kuka ta kauda kuncin zuciyarta yau ba yaya aduniya ita kadai ce zata kwanta ajikinta tayi kuka son ranta to sai Mijinta Datake ganin bata da kamarsa sannan yasan abunda ke faruwa yasa ta barke mai da kukan da yayi wata Biyu yana cinta acikin ranta,Lallashinta yake yi da sigar Shafa bayanta zuwa kanta yana dan jijjigata,ammh kamar ana bude mata famfo haka ta saki kukan nata riri riri sai ya rude hankalinsa ya tashi daman tun Fil"azal shi bamai son kuka bane ballatana Hayaniya,Sannan kukan ma irin na Amina duk sai yaji ya