Showing 135001 words to 138000 words out of 145917 words

Chapter 46 - TAFITA ZAKKA BOOK 2 COMPLETE.txt

04 Nov 2024

83949

Hadiza kuma ita tayi Yajin jego,zuwa yammah duk sun gama gyara ma Amina gidanta Yakaka ta Dawo ita tayi ma ma Amina wankan yammah ko kafin mangariba duk sun watse sun koma gidan Baba Mallam har su Hanne Amina da Farko Har da sa Rigiman ita ma sai taje Yakaka tace da Danyen Jegon ne zata fara yawo Dole ta Hakura ta koma tana ta Faman gunguni.
Achan gidan ya Danmallam kuwa Ana Idar da Sallar Isha"i mallam ya Hada Taron daya ce za"ayi Sannan har da su ya Nazeem da Uzairu sun iso aranar dukkansu mallam ya kira su yace yana som ganinsu gabadayansu suna Falon mallam illah banda Amina da ya Akila da bata samu zuwa ba sai ya Jadwa.
Ammh harda su ya Danmallan suna wajen,Aliyu dai sun tafi dazu da yammh shi da Aliya,Sai su ya Jafar da ya Nasir ya Nazir shima bashi wajen Tunda bai samu zuwa ba sai Aba sai Jawaad har Anty Hadiza da su mamata mallam yace su shigo Tunda Tunatarwa ne ya kamata suna wajen..
Nasir ne ya Bude taron da addu"an sannan Mallam ya fara jawabinsa da Farko Yayi musu wa"azin riko da Zumuncu da yadda zasu Hada kansu waje Daya su zama Dangi Daya kamar yadda yake fata sannan ya gangaro kan wa"azi kan shirka da azaban da Allah yayi tanadinsa domin masu Hadashi da wasu,Tunda ya fara mgana suka Fahimci inda ya Dosa sai jikin kowa yayi sanyi bai fito ya Fada musu Sakin daya shiga Tsakaninsa da Uwani da Marliya ba ballatana ta Bangaran Aba yadai gyara Zama ne ya Fara karanta musu muhimmancin Uwa ga ya"yanta sannan da irin yadda Annabi ya Fadi Darajan uwa.
Mallam ya kallesu Daya bayan Daya kafin ya Cigaba da Fadin"Ita uwa tana Daraja da kima..Annabi ya ambaci abi uwa sau uku kafin yace abi uba kunga ko ta haka kadai ya isa kusan Tasirin uwa..Sannan duk lalacewar Uwa uwace..Domin ta Dauki Ciki na Tsawon Wata Tara ta sha wahala kafin ta Haifi abunda ke Cikinta ga azaban Radadin Naguda wanda aka Fadama cewa acikin Azaban mutuwa ne aka Dibosa kadan..Kuma dukkanku kusan mutuwa tana zafi da azaba Saboda Alokacin da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam zai bar Duniya Sai da ya ce Lalle mutuwa tana da zafi tana azaba da magagi Annabi ma kenan wanda ya kasance Shugaba ne na Hallitun Duniya ya Dandana azaban mutuwa ballata mu bayi da kowa kowan ba..?
To acikin wannan azabar ne aka Dandana ma uwa wajen Haihuwa bayan ta haihu kuma ta fara Wahalan shayarwa da Reno walwalun duniya akanta suka kare taki ci taki sha Duk domin ta inganta rayuwarka Sannan ta Jajirce wajen tarbiya bata barci Saboda ganin ta inganta Rayuwarka komai lalace uwa komai nata kan ya"yanta ne,kuma komai zata aikata mai kyau ko mara kyau ne to bazata Fara Duba kanta ba sai ta Duba ya"yanta ku Saki ranku ku Bude zuciyarku..Ku sani Cewa Uwa ta wuce wasa komai ta Zama awannan Duniyan bai kamata ta Fuskanci Tsagwamma da Kyama awajen ya"yan data Haifa bq ..Ko kuwa kowa zai gujesu bai kamata ku ya"yansu ku juya musu baya. !


Mallam ya Karishe Fada yana nazarinsu ganin yadda Gabadaya Jikinsu yayi sanyi ne yasa ya Cigaba da Fadin"Komai kuka samu anan Duniya baku isa ku biya kwayan Zarra na wahalan da iyayanku sukayi akan ku ba..Sannan kada ku manta Kisaar da wani cikin Sahabai yace ya Dauki mahaifiyarsa a saman kafadansa yayi dawafi da ita shin ko ya Biyata wahalansa da tayi akansa..?.
Annabi ya shaida masa cewa ko Kwayan Zarra bai biyata ba kun ga kenan Allah ne kadai yasan Alherin Uwa ga abunta ta Haifa..Da wannan Tunasar da nayi muku nake Fatan zaku Hankalrta..Uwani da Marliya da Balaraba sun aikata Laifi mai muni ammh kuma ga wajen Ubangiji abu ne mai Sauki in suka Rokesa zai iya yafe musu sannan muma mu sani afuwa da yafiya abu ne mai kyau tunda muma muna kuskure sannan Allah Gafurin Rahimun ne yana yi mana Gafara a duk sanda muka aikata Laifi yana mana afuwa koda Laifin mu yakai Cikin Duniyar nan ne to meyasa mu bazamu yi musu afuwa ba .?
Sai mu barsu su ji da Laifinsu Tsakaninsu da Ubangijinsu,Sannan ku sani aibata su ko gayamusu mummunar kalma bai Dace ba..Ku Sausauuta kalamanku kan iyayanku Domin Fadin mummuna mgana akansu Tamkar ja da hukuncin Allah ne Tunda shi ya Kaddari komai Daya Faru..Daga karshe ina Umartanku Gobe kuje ku Duba iyayanku mata sannan ku Musu kalamai mai Dadi Daga karshe ku yi afuwa ga laifikansu ko Wani Nauyin Zai ragu daga garesu..!


Gabadaya Falon baka jin komai sai Shesshekan kukan su ya Zulaihat Hamida ma sai kuka take jikinta Duk yayi sanyi,Saboda tasan ta aikata kuskure ta yi ta yabama mamanmu manganganu Allah ta Tuba dukkansu haka Suke fada aransu sannan Jikinsu Duk yayi sanyi da Nasihan mallam bayan nan ma Hajiya ta Dora da nata kafin su tashi sai da suka Tabbatar ma da mallan cewa komai ya wuce sannan zasu bi Umarninsa..
Haka taron nan ya tashi kowa jiki ba Dadi alamu nasihan mallam ta Shigi Kowa sannan Hatta Aba yaji Nauyin Zuciyarsa ta Ragu yana Tunanin zai iya yafe ma Mamammu har ya Jafar ma yaji aransa ya yafe mata shi da su ya Jawahir aransu sukaji sun yafe ma Mamanmu tun balle ma da su mamata ke Labarin Halin da mamanmu ke Ciki nan da suka ji Tsausayinta bayan sun Furta sun yafe mata.
Washegari Mota guda sukayi su ya Zulaihat zuwa Gusai har da Ya Jawahir da ya Jalela sukace zasu ce sai ya Sadiya da Jidda da Sa"adatu suka Dauki Hanyar Dutse sai Ya Nazeem da Nazifa da ya Uzairu sai Umaima suka Dauki Hanyar Tsafe sun yi waya da Shamsu zai samesu achan..!
Dukkansu Halin da suka iske iyayan nasu ya Raunana ta su sun kara Tsorata da Duniya Mamanmu nata yafi muni Tana kwance Cikin kashi da Ftsari bata iya mgana abinci ma ko ambata rabi ke shiga Cikinta ba baki ba Ido haka su ya Zeenatu ke kuka kamar ransu zai fita har ta su ya Jawahir sun koka Mamanmu sai dai taji muryansu bata gani sai kuka tana Faman mika hannunta mai Lafiya.
Allah Sarki ya Zeenatu da ya Zulfa da ya Jawahir suka Zage suka gyara mamanmu suka Sauya mata kaya ya Jaleela ta bada shawaran su kaita asibitin Basu ji Haushin kowa ba Ganin yadda aka banzarta da mamanmu ka shuka alheri ma ya ka kare ballatana ka shuka Sharrin
General Hospital Gusai suka kaita Liktoci nata Fadan an bari Jikinta ya Saki agida Dayake akwai kudi nan da nan aka karbeta aka shiga da ita aka Fara bata Taimakon gaggawa su kuma suna gefe suna ta Faman sharan kwallah
Zuwa yammah ta Dan fara Dawowa Hayyacinta sai dai anan asibitin zasu riketa zasu rika yi mata gashin kashi sannan sun saka mata abun Fitsari ta kasanta sannan da Drip wanda zai taimaka ya Dawo mata da Ruwan jikinta Daya zaganye a kwance aranar dai basu samu daman Dawowa ba Sai washegari da Mamammu ta dan Fara mgana kadan kadan tana kuka tana Rokonsu gafara suka Rumgumeta suna kuka suna Fadin sun yafe mata Jaleela ce da Jawahir suka Dawo Gumel aranar saboda washegari zasu tafi zulfa da Zahra suna chan sai Hamida sai washegari zata koma Zulaihat ma Dagachan ta koma Jigawa sun bar ya Zahra data tambayi Mijinta zatayi sati wajen mamanmu Alla barshi ya Zulaihat zata Dawo ta karbeta sai ita ta koma gida.
Achan Tsafe ma abun ba Dadi Haj.Uwani ciwo ya kusa cinyeta ta rame ta lalace kamar ba ita ba su ya Nazeem suma sunyi kuka Halin da suka iske mahaifiyarsu aciki suma basu ji Hauahin kowa ba domin Gaskiyan mallam ne a wannan gabar sai su ya"yanta suma sun yi kokarin kaita asibiti aka Fada musu ko sun je baza"a ga komai ba Yayanta ne yayi musu kwantance wani mai mganin gargajiya anan kauyen Tsafe nan suka kaita ya Dubata yace babu abunda zai mata Ciwonta kaikayi ne ya koma kanta Sai dai Kawai ya bata wani mganin da Zata rika sha kirjinta ya kwanta mata da Tarin dake Sarketa haka suka Dawo da ita gida suka tasata suna faman kuka tana Hawaye tana Nishi wajen rokonsu gafara suka riketa suna Fadin sun yafe mata Nazeem shi yaje yazo da Likita ya Dubata yayi mata alluran barci Saboda ta samu barci sai abakin kakarsu suka san Mallam ya Saketa to damam ai sun san haka zai faru sai dai sun jinjina ma mallam ba Tozarci Cikin Lamarinsa Mutum ne mai Dattako..!
Ganin yaranta sun Sauko sun nemeta yasa suma yan"uwanta suka Sauko Daman Hannunka bazai taba Rubewa ka yanke ka yarba Dole itace Dolensu,Nazeem da Uzairu kwana Biyu sukayi suka koma bayan sun bar ma Nazifi kudi sosai Dayake Nazeem ya Fara aiki Shamsu kuma Sai ranar da zasu tafi ya iso nan suka barsa,Umaima dai gata nan ne dai sai ahankali Ita kanta aljanun su taba kwakwalwarta yau lafiya gobe Hauka ne Nazifa ce aka bari tana kula da Hajiyan Uwanin wanda har taji Sauki Data ga ya"yanta sannan Danginta sun mata afuwa..!
Chan Dutse ma abun yayi muni Domin sun je sun iske Anty Amarya ta Fita Daga cikin Hayyacinta Domin Tsorata take yi acikin barcinta sai ta rika ganin Yaya tana fito mata Tun abun na karami har ya Girmama bata iya barci Sai abun ya taba kanta gabadaya ta Birkice yan"uwanta sun taimaka mata sun kaita asibiti Shashen mahaukata ana Dubata To Cikin wannan Halin suka isketa ta Rame ta lalace duk ta Firgice kamar ba Marliya yar kwalisa ba alokacin Duka yan"uwanta sun koma Tsausayinta harta Sakina da Anty A"i sun koma suna Tsausaya mata ganin Halin data koma ko da Rana ne ana Zaune sai ta mike tana Firgita da Ihu su ya Jidda suma sun koka matuka haka suka Rumgumeta suna kuka Tsausayin Mahaifiyarsu ya kamasu Nadama suka kamasu na yarda suka ki nemanta na tsawon Lokaci.
Sukaji aransu sun yafe mata har Abada anan suka Hadu da Sakina da ta Dawo nan da zama sai sabon kuka Tana Faman fada musu ta gaji da kiran Danmallam bai Dauka ba ta turamai sako ba adadi bai mata Reply ba in ya Saketa ne ya Fadamata sakina duk ta Rame gwanin ban Tsausayi..
Nan Sa"adatu ke fadamata daga wajen sunan Amina suke yara sun ci sunan Aba da Mallam sannan Sarood ma Cikinta har ya fito Sakina sai kuka Nadama da tsoron Rayuwa na kara shiganta har hotunan yaran ta gani Aliya ta Turo mata ita yanzu ta gama ganin rayuwa wani kishi baya gabanta ta sanu ta san makomarta kawai irin yadda Anty Amarya ta koma ya isa mai Hankali ishara..!
Sa"adatu ce ta fara komawa gombe Daga baya kuma ya Jidda,Ya Sadiya na nan Dutse ita tunda sunzo ne ita da Mijinta Tana Cigaba da kula da Anty Amarya..!
Mallam yaji Dadi da yaran suka kirasa sukace sun je sun Duba iyayan nasu ya Dinga saka musu albarka sanna yaji ba Dadi da labarin halin da suka samu su Marliya abun dai sai Addu"an da Fatan gamawa da Duniya Lafiya..!
Hajiya ma dataji Hankalinta sai ya tashi ta tambayi Izini Mallam bai hanata ba ya barta ita da Hajiya Nasara da Anty Hadiza suka tafi Gusai suka Duba Mamanmu a asibiti haka ta rike Hajiya tana kuka,Hajiya na Faman share mata hawaye tana Fadin ta Yafe mata har ta Hajiya Nasara Sai da Jikinta yayi sanyi,Sun iske Zulaihat na asibitin ita ke kula da ita,Basu jima ba suka gaisheta da kayan Dubiyansu Daganan suka Dawo Washegari kuma Tsafe sukaje suka Duba Hajiya Uwani..Hajiya Babba sai da tayi mata kuka tana kuka tana rokonta gafara ta yafe mata da ita da ya"yanta Hajiya tace bakomai Nazifa ta nan bata tafi ba,Sannan Umaima na nan jiki Sai ahankali kawai..
Basu jima ba sallah kawai sukayi suka juya Dagan suka je Dutse suka Duba Amarya Halin da suka ganta sai Allah Amarya hauka Tuburan sun isketa sai da aka Rirriketa,Sadiya ke nan tare da ita da Sakina Hajiya sai da ta Tausaya ma Sakina duk ta Bushe ta gaida Hajiya sai Sharan kwallah take Sai ta bama Hajiya Tsausayi har tayi alkawarin yima Danmallan mgana in suka koma..!
Koda suka koma Jikinta Duk a Sanyaye bata samu yima Danmallam mganar ba sun dai yi da Mallan shima ya jinjina ya kada kai yayi musu Fatan Dacewa mganar Sakina kuma yace tana Hannun mijinta abunda ya yanke shine Daidai.
Amina kuma ana chan ana ta Jego Yakaka sai da Allah ya sakamata ita ke kula da Amina da yaranta sun koma asibiti an yi ma yaran Shayi na pampers har sun warke,Yaran sun yi Kiba sun yi Bulbul Saboda Amina Nononta mai kyau ne sannan Danmallan kullum sai yazo ya Dubasu Safe da yammah kwana ne yake yi Wajen Sarood Amina bata dai nuna Damuwarta ne ammh fa abun na cin Ranta,Don ma Yakaka na mata Fada sannan ta Dage da kokarin gyara Amina kamar yadda tayi alkawari hakama Anty Hadiza ba"a barta abaya ba Tana kokarin gyara Diyar tata.
Hajiya na Shirin samun Danmallam da mganar Sakina sai gashi yazo yana mata mganar Sarood zata koma Madina sun koma makaranta shi zai jira in Amina ta gama wankan jego su tafi Tare Hajiya batace komai ba tace Allah ya Tsare daganan ne tamai mganar Sakina sai ya nuna mata Sakon Datake Turamai na ban hakuri
Harda mganar cire mata mahaifa da akayi Hajiya jikinta ya karayin sanyi da Rayuwar nan ta kalli Danmallam cikin wani yanayi tace"Kayi hakuri Danmallam in har baka saketa ba kaje ka Daukota ka maidata gida..Na tabbata ta ga Ishara ga abubuwan da suka faru. !
Danmallam yace"Ban saketa ba Hajiya..Sai dai ina tsoron na Sake Dawo da ita ta batamin zama na..Ta Rikitamin gidana Hajiya. !
Hajiya tace"Bazatayi haka ba..Insha Allahu..!
Kai ya kada kafin yace"Shikenan insha Allahu in na gama chukun Chukun Tafiyar Sarood zan je na Taho da ita .!
Hajiya tace"Allah ya bada iko..Sannan ina so in kun sun samu Lokaci kai da su Nasir da Jafaru kuje ku Duba su Uwani da Marliya suna cikin wani Hali.
Bai yi gaddama ba ya amsa mata Domin sunyi mganar dasu Jafar zasu je su Dubasu ciwo ya kore komai ko don Darajan zaman tare da kuma ya"yan da suka Haifa.
Danmallam ba yi gigin Fadama Amina zai Dawo da Sakina ba asatin aka sama ma Sarood Visa ya kawota sukayi sallama da Amina yana zaune yana kallon Amina da mamakin yadda yaji labarci na Fita abakinta Kanar wacce ta zauna a madina bai Taba Sanin ta iya ba ballatana yayi Zaton tana ji..
Ta bama Sarood Atamfa da Su Turare da Sabulai Saboda ta mata kokari Sannan ta Dauki su Aba da suka yi Wayau ta Rumgumesu har Yakaka sai Yabon Sarood take yi,Haka ta Rumgume Amina suka rabu kan sai sun zo tunda Danmallan yace tare zasu Taho da Amina ita Aminar bata ma san mganar ba.
Daganan gidan mallan ya kaita tayi musu sallama Hajiya ta bata Turaren Wuta tace ta kaima Mami Sara.
Washegari ya kaita kano Jirgin yammah Tabi zuwa Jidda dare yayi mai ya kwana a Hotel da Safe ya Dawo.
Lokacin Amina saura kwana Uku tagama wanka Danmallan nata musu Shirin komawa Madina Hajiya tayi mai bakam sai da Amina tayi arba"in yayi mganar Tafiya Hajiya tace sai ta Zaga yan"uwanta ransa ya baci sai dai bai nuna ba gashi yana son kebewa da matarsa an hanasa da gangan Yakaka ke Tsare waje in ya shigo bata so basu gama gyara ba ya bata musu saboda ta Lura ita kanta Aminar Ja'ira ce..!
Kwana Biyu da arba"in dinta suka fara yawo ta fara zuwa Hadeja wajen goggo Jumai ta kai musu Yaran ta gani ta saka albarka suka kwana Daya ita da Yakaka Idi yakai su bayan sun Dawo Washegari suka tafi gusau wajen kwanansu Hudu,Har asibiti taje ta Duba Mamanmu Halin Data ganta sai da taji ta manta da komai ta yafe mata Ya Jamela ta rakata Mamanmu na Hawaye Amina ta Dora mata su Aba Ajikinta haka take son tayi mgana ba hali Hannunta mai Lafiya ta saka ta Dafa kansu tana hawaye ya Zeenatu suka samu a wajenta tana kula da ita raba raba suke da junansu.
Amina ta yawata Dangin Aba kusfa kusfa Har kwana sai da tayi agidansu Zafira,suka sha Hira Yakaka kuma ta Shige Cikin Dangi kamar yar gida Ta zama yar gidan baba mallam yanzu.
Ranar da suka Dawo gidan mallam suka kwana washegari suka tafi Dutse Gabadayansu har ya Danmallam da Su Ya jafar da Hajiya ta koma suka Duba Anty Amarya data koma bata mgana sai kuka duk ta Firgice wani Lokacin in abun ya tashi sai an Daureta Amina da su ya Jafar sun kara jin Tsoron Duniya Sadiya ta nan tare da ita Sannan sunga Sakina Amina tayi mamaki Sakina har da karban su Aba duk ta rame sai Amina taji ta bata Tsausayi basu Dade ba Daga Dutse Tsafe suka wuce chan din ma sai ahankali Hajiya uwani dai ba wani Cigaba tayi ta rokonsu Danmallan da Amina Gafara Allah yasa ita da Bakinma sai dai Ciwo duk yaci Jikinta Nazifa ta koma sai Yan"uwan Hajiya uwani ke kula da ita itama har Su Aba aka Doramata kan jikinta tana kallonsu tana Kuka.
Da zasu Dawo suka Dauko Umaima suka Dawo da ita,Umarnin mallam ne
Washegari kuma su ya Danmallam suka je gusai suka Duba mamanmu Suma kansu jikinsu yayi sanyi Tana kuka ba baki tana mika musu Hannu Tana neman gafara sukace sun yafe mata Duniya da Lahira sun bama Zeenatu kudade kafin su kamo Hanyar gida suna Hirar yadda Allah ke nuna ishara da izina tun a Duniya.


Amina taso taje gidajen yan"uwanta Mata Mallam ya hana yace ta shirya tabi mijinta alokacin Sai Hajiya ta hana tace sai dai yaje ya Dawo ,sai ya tafi da ita Lokacinn yaran sun kara wayau bazai Daukesu tana Danyen Jego ya Hau jirgi da ita.
Sannan kuma zatayi Jarabawaarta ta Fita alkawari tayi kuma sai ta cika.
Mallam sai yama kasa mgana Daga baya yaso ya nuna ma Hajiya bata isa ba sai dai data mai bayani sai ya gane gwara Amina tatafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login