Showing 123001 words to 126000 words out of 145917 words
Sarood daman Yar Fara,"a ce koda yaushe Fuskarta a Sake ne.
Ita abunda ma ya bata mamaki yadda Aliya matar Aliyu ke ta faman mata Sannu in ta ganta alhalin a baya ko mganar arziki bata taba Hadasu ba Amina bata amsa mata ita bata son munafunci wato taga ta bare ma Kawarta Sakina shine zata zo ta mata Bariki aiko gidan ta taras itama sai ta basar da ita kamar ma bata ganta ba.
Bayan an fito dasu Daga shashen mallan har yan gusai maza da basu koma ba sun yi nasu nasihan yan bazanga dai sun koma har ta da kawun Hajiya sun Dauki Hanyar Bauchi tunda sun yi mai wahalar an Daura auran Sa"idu da Hadiza kamar yadda mallam ya nema..!
An riga an gama saka kayan gara da Sauran kayan da baza"a rasa ba a motcin da za"a tafi da Amaren su kawai ake jira Hajiya ta ga Hamida da Sa"adatu bai kamata su tafi basu yi sallama da iyayensu mata ba
Yasa ta Damka Sa"adatun Hannun Sadiya tace ta kaita wajen marliya suyi sallama itama Hamida ta Damkata Hannun Zulfa tace suyi Sauri kada Mallam ya sani. Kowa mamakin Kirkin Hajiya da zuciyarta ake yi ganin ko a Fuskata bata nuna Wata alama ba.
Haka kuwa akayi Sadiya takai Sa"adatu shashen Anty Amarya da ko kaunar barayin yanzu basa yi tana Ciki kwance daga kuka sai kuka cikin kwana Daya ta fara sauya kamanni Tana ganinsu ta mike jikinta na rawa Zata rumgume su suka matsa baya.
Ya Sadiya ta kalleta Cikin wani yanayi kafin tace'Ba wata mgana ya kawomu ba. sa"adatu zata tafi gidan mijinta..gatan nan in kinga dama ki bata Shawaran daya dace in kuma kin ga Dama ki Dorata kan hanyar da kike kai ayau..!
Da haka ta Saki Hannun Sa"adatu ta Juya tana Sharan kwallah ta Fice Daga Shashen gabadaya Anty Amarya taji gwiwanta yayi sanyi ta Duke gaban Sa"adatu tana Fadin"Sa"adatu don Allah kada ki gujemin kamar yadda Sauran yan"uwanki suka gujeni..!
Sa"adatu ta girgiza kai sai Hawaye Cikin kuka tace"Abunda kika aikata abun kunya ne da abun Tir..Ina Fatan kada Rayuwarki ta Shafi namu Rayuwar..Ko Sau daya baki Tuna kina Damu ba..?
Sai yanzu ne da Kika Fara Girban abunda kika Shuka zaki ce kada na gujeki..?
Nagodema Allah da zan yi nisa da Rayuwarki gabadaya sannan kuma Insha Allahu zan zauna da mijina da Danginsa Lafiya zan masa Biyayya har karshen Nunfashina..!
Daga haka ta juya tana kuka Anty Amarya ta Tashi Tana kiran sunanta bata juyo ba tana shirin Barin Falon tace"Wani Hali Sakina take ciki..?
Cikin Dakushewar Murya Sa"adatu ta Tsaya Cak kamar bazatayi mgana ba Sannan tace"Saboda abunda kika aikata ta kara rasa Cikin jikinta..Sannan su Anty A"i sun Dauketa ita da sauran yayinta sun maidata asibitin Dutse Dazu da Safe..!
Da haka ta fice ta bar Anty Amarya da Gunjin kuka Duniya ta juya mata baya alokacin da batayi zato ba ballatana Tsammani ba..!
Abangaran mamanmu kuwa Ita take ganin Abunda ta aikata Domin ko yan"uwanta sun ce badai zuru"arsu ba Ta nemi wani Ahalin sukan sun yafe ta,Tayi kuka kamar ranta zai fita Tana gani suna Hada kaya sun ce ana wucewa da Amare zasu kama Hanya Tazama kamar wata mujiya acikin mutane ya"yanta kaf sun juya mata baya bama ta su Jafar wadanan tasan Da wuya su iya yafe mata.
Ita kadai agidan dukkansu suna gidan Hajiya tana cikin Dakinta tana gunjin kuka,Sai ga su Hamida har aranta taji Dadi ta mike da Sauri zata rumgumesu Hamida ta tureta sai da ta Fadi Cikin Bakinciki ta nuna ta da yatsa tana Fadin"kul kar ma ki fara..Na Fada miki ban sanki ba baki sanni ba..!
Zulfa ta kasa mgana sai kuka Daga karshe ma sai ta fice Daga Dakin Mamanmu na kwance in da ta Fadi tana wani irin kuka take fadin"Hamida ni fa mahaifiyarku ce..?
Ko Duniya zasu juyamin baya na Dauka kuna tare dani..?
Hamida tayi wani Dariya kafin tace"Wlh nayi Nadaman dana fito Daga Cikin ki..Nayi nadamar kiran ki da sunan uwata da nayi..Yadda kika Cutar damu kika bar mana Bakin Fenti kema Bazaki taba Gamawa da Duniya Lafiya ba..!
Sannan ga wani karin albishir Aba Yayu din nan tare da auran mu mallam ya Kara Daura masa aure..Da Diyar kanwar Hajiya kin ga kenan tundaga nan kin fara ganin karshenki..!
Mamanmu ta Zaro Ido gabanta ya Fadi cikin rawar baki tace"Au...Reee..?
Hamida ta gyada mata kai Ta cigaba da Fadin"Kuma na tabbatar da cewa ke ba matar Aba bace yanzu..Gwara tun wuri ki neni inda zaki..Ni dai zan tafi gidan mijina ina Fatan kada Laifin ki ya Shafi rayuwarmu kije Duniya ce..Da Sannu zaki girbi abunda kika Shuka..!
Ta juya tana sharan kwallah zata Fice Mamanmu ta riko kafafunta tana Kuka tana Fadin"Hamida kada ki tafi ki barni ina zan je..?
Kuma ai Sa"idu bai ce ya sakeni ba ko..?
Hamida na kuka da kuma Dariyan Bakinciki tace"lalle Balaraba kin raina ma kanki wayau ba kuma ki da kunya. ! Duk abunda kika aikata kina Tunanin kina da wani Sauran kima ne..?
Kima kara gaba tun kafin kifara wulakanta..!
Daganan ta Fizge kafarta ta fice tana kuka,a haraban gidan ta hadu da Zulfa suka rumgume suna kuka jin su shuru yasa Ya zulaihat ta Biyo bayansu ganin suna kuka itama sai ta Fara kai mamanmu ta lalata rayuwar ya"yanta.
Hakanan suka fito suna kuka Daman duk an fito ana kofar gidan baba mallan ganin Tafiyar Amaran duk yadda Amina taso kada ta fito sai da ya Abida taje ta Taho da ita domin Hanne da Hamida sun ki shiga mota sai kuka suke yi Ganin Amina yasa suka kara rudewa Amina taso ta Daure ammh ta kasa itama sai kuka Aminu kansa kawai ya kauda har da su Nenne a yan Lallashi,
Hajiya bata wajen tana cikin gidan su goggo Yagana da su Hajiya Nasara sai yan gusai dake wurin ya Danmallam ma na falon mallam ya Shamsu yaje ya Kirasa yazo ganin yadda suke kuka shima sai da ya tabasa ba kunya ya Riko Amina ajikinsa ya Rumgumeta yana lallashinta ita kuma jinsa ajikinta yasa ta kamkamesa tana kuka Da haka aka samu suka shiga Mota Sa"adatu tuni har sun mika Hajiya da kanta ta sakata a Mota Allah Sarki Hajiya mai rama Sharri da Alheri
Su ya Abida suna ta gulmar ya Danmallan ganin ya nufi Cikin gida rumgume da Amina suna Fadin abaya ya Dammallan ko mgana da matarsa bai iya yi gaban mutane sai gashi yau har da su rumgumewa gaban mutane..!
Dakin su Nazeem ya shiga da ita yana ta lallashinta Sai da ya dan mata jan ido ne ta Daina kuka ta koma ta Lafe a Kirjinsa tana kuka sai da ya tabbatar da ta daina kuka sannan ya fito da ita da kansa ya rakata har kofar shashen Hajiya sannan ya Dawo..sallama sukayi da Aliyu zasu wuce shida Aliya,Hajiya ta rkota har haraban gidan ta mata godiya bayan ta bata kayan Biki haka su Aliyu suka Dauki Hanya ba tare da sun kara tada mganar abunda ya Faru Jiya ba
Sun dai yi mganar Amina yau za"a rakata Sabon gidanta Aliyu na mai Tsiyar yau ango yake shi kuma yana jin Dadi ita kuwa Aliya duk jikinta yayi sanyi ta kara tsorata da Duniya.
Ana tafiya da amare yan gusai sukayi Harama Zafira dai tun kafin tafiyar su Hanne ita da mamata sukabi yan Daurin aure suka koma.
Ba yadda Hajiya batayi su bari su raka Amina Gidanta ba sukace bakomai in ta Haihu zasu dawo suna gabadaya ransu babu Dadi kaf dinsu suka juya aranar gidan Aba bako Tsinke sai Mamanmu ita kadai da Halinta kaf su ya Jadwa sun koma Shashen Hajiya Babba.
Hajiya uwani kuwa abakin Umaima sukaji bata agidan itama taje shashen taga ba kowa Ya Nazifa ke ta kula da kanwar nata ya uzairu ya koma inda yake Service ana gama Daurin aure Ko Tsayawa bai yi ba,Nazeem kuma nan da Sati Daya zai tafi Lagos ya Fara aiki sun yi mgana da Nazifa zata roki Mallan ya bata Umaima tatafi da ita Domin suna da Tabbacin zamam Mahaifiyarsu agidan mallam yazo karshe Duk da sai Dare ne mallam yazo da Labarin rasuwar Batula shima wani Cikin yayyin su Batula ya kirasa yake fadamai sai Lokacin ma kowa yasan bata agidan.
Ba wanda ma ya Damu ana ta Hada Hadar raka Amina Sabon gidanta Hajiya ta kasa zama su ya Abida sun tafi tun Mangariba suna gyara gidan suna Share kura da saka labulanya sannan Hajiya tasa Hadiza Amarya Aba ta dan ma Amina gyaran jiki Dayake Sana"arta ce sannan tazo da kayayyanki Tunda tayi ma su Hanne yan"uwanta sai tsiya suke mata suna cewa zata gyara yarta ita kuma tana jin kunya ba Zato ba Tsammani taji auran nan Daga sama har ta fara kuka Hajiya tace kul dinta ta Godema Allah Sa"idu mutun ne har da Rabi,Tun bayan Rasuwar mijinta bata kara marmarin aure ba, ta koma makaranta Tayi NCE sannan ta ke kuma Hadawa da Sana"ar gyaran jiki.
Sannan ita bazata ce ga Aba ba, Saboda ganinsa da tayi ba wani mai yawa bane ammh ai suna nan jiya abubuwan nan suka Faru marasa Dadi Hajiya ta mata fada tare da Rokonta ta rike auranta Hannu Bibbiyu.
To me zatace..? Sai Fatan Allah ya Zaunar dasu Lafiya sannan bata da matsala macece mai wayewa da sanin Duniya.,Yanzu kawun su Hajiya yace bazata koma ba nan da Sati daya zata Tare wajen Hajiya zata zauna abunda kuma ba"a rasa ba Hajiya da Mallam sun Dauke komai akan abunda ya shafi Sa"idu jikinsu har rawa yake yi Tabbacin kaunace daga Allah.
Shiyasa ko kafin ta gama yima Amina Dilkar da tayi mata sun Fara Sabawa Daman ita tana da Sakewa a manganunta Amina ta Fahimci Aba yayi Dacen mata suma kuma sun yi Dacen wata uwar
Har su ya jadwa sun shaida haka yadda ta gyare Amina ta sakata tayi wankan Turare Kora su ya Abida tayi waje suna ta mata Shakiyanci Hajiya tace ta korasu waje tayi aikinta Tana yi tana hada ma Amina da yan Shawarwarin rike miji ta bata wata Zuma ta sha saboda cikin jikinta tace bazata sha wani mgani ba sai ta Haihu Tun Amina najin kunya har ta fahimci ita Anty Hadiza ba ruwanta sai itama ta saki jiki tana Sauraranta.
Koda karfe takwas na Dare tayi Amina ta shirya Cikin Wata atamfa riga da Zani an Nadeta cikin Lafayan da Ya Aisha ta siya mata har kwalliya sai da Anty Hadiza mata aka fesheta da Turaren Humra masu kamshi Domin Hajiya tace da wuri za"a tafi kai Amina bata son Dare yayi.
Sai alokacin Sarood tasan Amina ce Amaryan Umar ya Aisha ta gayamata Cikin Larabci sai kallon Amina take yi da mamaki sannan ga Ciki ajikinta Ahalin Umar bai taba mata Zencen ba sannan ta Fahimci Sakina wani abu ya faru da ita duk da batajin Hausa ammh koken koken da akayi tayi jiya bana Lafiya bane..
Kamar wanchan karon an kai Amina Falon mallam ya saka mata albarka Daganan Idi ya Dauki Hajiya da Amina sai Yakaka da Haj Nasara..Sauran su ya Aisha kuma suka Bi sauran motocin su ya Nasir har da ya Nazeem ya Kai mutane a Motar makarantar su Amina.
Su ya zulahait suna baya baya Hajiya tace bai kamata ba su wuce su raka kanwarsu dole suka shige suma anayi dasu.
Sune har Babura inda gidan Amina yake Kowa yaje yaga gida sai santi da son barka su ya Abida sun gyare ko"ina sai tashin kamshi Sannan ga wutar nepa haske ya gauraye gidan akwatinta Daya Ya Aisha ta Daukomata Sauran kayan sai gobe Hajiya tace zata za"a kawo mata..
Hajiya da kanta ta shiga da Amina gidanta bayan tace tayi addu"a har kan gadon auranta sannan ta Dafa kanta ta Saka mata albarka
Matan kuma suna ta Zagayen gidan suna Santi Su jidda har da Sadiya duk sun zo ganin gida harta Sarood tazo aranta kawai ta Sadakar Umar na son Amaryan nan tasa tundaga abubuwan ma da suka Faru.
Su ya Zulaihat suna sharan kwallah suna saka albarka Da wuri Hajiya tace suyi Haraman tafiya haka Amina ta rumgume yan"uwanta tana kuka bata bambamce su ba Har ta su ya Zulaihat Saboda su Daya suka Dauki juna aka suka Taru suna faman lallashinta sai da tayi shuru sannan suka fara Shirin Tafiya Tun dazu su hanne suka kira amare dukkansu sun isa gidajensu Lafiya sai fatan Allah ya bada Zaman Lafiya.
Kafin karfe Tara na Dare duk sun watse an maida su gida sai Amina kadai aka bari tsoro ta fara ji gashi ba megadi bai riga ya Daukesa ba Sai misalin karfe goma na Saura na Dare Taji shigowar mota Daman ta kasa Zaman ciki tana Falon ta kasa Zama waje Daya duk Haduwar gidan tsoro bai barta ta wani Dubasa Dakyau ba
Danmallam na shigowa falon da Amina ya fara cin karo Daman yasan Za"a rina Amina ce fa sarkin Tsoro rike da ledan kaza da madara ta fadamai ta rumgumesa tana mai kukan shagwaba ya barta ita kadai tana jij tsoro.
Yana shafa bayanta da Hannu Daya Lokaci Daya yana shakan kamshin Turarenta yace"Shii..Ba shikenan ba gani na shigo ba..Ni dai yau ataimaka kada kukan nan naki ya hanani Shagali..!
Tana jinsa sai ta kara kamkamesa Shima yana rike da ita har suka zauna Saman Kujera ya Dora ta ita da Cikin Saman jikinsa bayan ya Sauke Lodojin Kasan Cafet harshensa ya sa yana Lashe mata hawayenta Lokaci Daya yana Fadin"Noor nidai kimin kudin wannan kukan naki na siyesa na kwana Biyar..Lokacin na gama Shagalina sai ki dawo da kukanki..!
Yafada cikin Shagwaba yana kwaikwayon muryanta Dariya ta saka ta Fara Dukansa da Hannunta a kirji Tana fadin"Hubby..La..la..!
Dariya shima yake ya rumgumeta yana Shafa Cikin jikinta Lokaci Daya yana Fadin"Eh Noor..Kinsan ai nayi kokari ko..?
Kiyi hakuri yau kam bazan iya Hakuri ba..!
Yana fada yana Shafa wuyanta Lokaci Daya yana shakan kamshin Turarenta dake jikinta Sama sama taji yana Fadin"Noor..!
Chan kasan makoshi tace"Uhmm!
Cikin wata kasalalliyar murya yace"Ya sunan wannan Turaran..?
Itama cikin wani yanayi yace"Bansani ba..Anyy Hadiza ta sakamin..!
Kai Tsaye yace"Wacece haka..?
Kanta na nutsewa saman kirjinsa tace"Amaryan Aba..!
Yar dariya yayi ya kamkameta yana Fadin"Ina yinta sosai..kamar tasan ina bala"in son kamshi..Barin ma irin wannan..!
Daganan bai Tsaya ba ya shiga wata Duniya Har Lafayan shi ya warware yana Shagalinta itama saita Dafe shi Tana taimaka mai domin bata juya ma wannan al"amarin baya ba.
Ganin zai shiga wani duniyar yasa ya Sarara mata duk tayi laushi yasa bai Takura mata ba,ya je kitchen da kansa ya Samo Filet da kofi yazo ya juye Zabbin Daya Siyo yana Fadin"Na Biya bashi kazan amarci..!
Tana daga kwance tace"Biyan bashi kazan amarci Amarya da Tsohon Ciki..!
Dariya ya Fashe da Shi yana Fadin"Ke bana son jidali..Kinsan dai Cikin maza sai an tona za"a samu mai kokarina ko..?
Tana Dariya tace"Sosai ma Hubby..!
Mirmishi yake mata yana jinsa cikin wani yanayi.
Shi ya taimaka mata ta tashi zaune haka ya tasata yana bata abaki itama tana bashi Sun kusa cinyewa ta kalli Kazan tana Fadin"Kazan amarci ai kanka ka siyo mawa ko..?
Yana Dariya yace"Naki ne..Na zata kin sam min ne fa..!
Cinya ta Dauko ta Turamai abaki Tana Fadin"Ai tunda kaci kazar amarcin Amarya sai ka famshe mata..!
Cikin Farinciki yace"Da gaske Noor..!?
Yafada yana rike hannunta kunya ya kamata ta Dukar da kanta kawai sai ya Saketa ya Cika mata Kofi da madara ya bata tasha shima ya Cika ya sha bai Tsaya ma wasa ba ya Dauketa ita da Cikin sai Bedroom din su acikin Tiolet ya Sauketa yace su yi alwala shi ya taimaka mata tayi alwalan sannan shima yayi nashi suka Fito shi ya jasu Sallah raka"a Hudu sannan sukayi ma auransu da Zuru"arsu Addu"a.
Jikin ya Danmallam har rawa yake yi shi ya Raba Amina da kayan jikinta duka bayan shima ya raba nasa da Jikinsa ya kamkameta suna Sharing din Body Cantact sannan suna jin Bugun zuciyar juna
Cikin hankali ya fara Sarrafata Amina bata bari kunya ya Cutar da ita ba ta tallafesa tana taimakamai sai da Tafiya ta mika ne ta fara mai kukan shagwaba shi kuma ya mika bazai iya komawa baya ba sai kawai ya Tallafeta Sosai yadda Cikin jikinta bazai basa matsala ba
Cikin karyewan Sauti yace"Noor..Ahankali fa zan yi..Kadan kadan..!
Yake fada mata yana tusa kansa a wuyanta Amina tace"Hubby..Shi..Da Zafiiii...!
Fadi kawai yake"Noor a hankali zan yi na rantse miki da Allah..!
Daga gani baya cikin Hayyacinsa ba wani Zafi Amina take ji ba,kawai Kukan Shagwaba take jin Dadin mai Duk sai ya karamai karfin gwiwa.
Ya Dauki Lokaci mai Tsawo tare da Amina lokacin da bai taba Samu ba Shudewar Mintina Talatin da biyar sannan dukkansu suka samu natsuwa da juna haka ya kamkameta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Noor..!
Yadda kika farantamin Allah ya farantamiki..!
Tana kwance saman kirjinsa yace"Ameen Ameem Hubby..Ana Behabbak..
Yana kamkame da ita yace"Ana bihabbeki Khatheran..!
Haka suka kwana cikin Farinciki da Asuba bayan sunyi sallah suka koma Amina tayi Dauriya sosai wajen mijinta shima yasani yana ta saka mata albarka.
Sai wajen goma sukayi wanka suka Sauya kaya Hajiya ta aiko Idi Direba da abinci da akwatun Amina Duka suka kwasa zuwa Cikin gida.
Wuni sukayi suna cin amarcinsu Amina tabara kala kala take masa yana Biye mata Da rana ma Daga gidan mallam aka aiko musu da abinci da Daddare ma haka.
Har sai da akayi kwana Biyu sannan ya Fita ya yi musu Cafane shi ke taya Amina Girki abunda bai taba yima Sakina ko Sarood ba..Bai taba Zaton Amina ta iya abubuwa haka ba bangaran Girki da bangaran kwanciya da miji ta kwancemai kai har mamaki ma take bashi wlh ga Ciki ammh bata taba nuna mai Raki ba.
Saka albarka kuwa ta shashi har ta gode Allah Shiyasa take nuna juriyanta akan komai ganin yadda yake Lalacewa akanta.
Su Hanne sun kirata da wayoyinsu da Hamida suka fara waya sai daga Baya Aminun ya siya ma Hanne waya tana Yola ita da Nenne suna zamansu Lafiya sai Hankalin Amina ya kwanta.
Bangaran gidan mallam kuwa Baki na nesa da na kusa sun koma gidajensu Dakin Hajiya Daga Anty Hadiza sai Yakaka da tace sai Amina ta Haihu zata koma.
Bangaran Aba kuwa baya kwana agidansa gidan gona yake kwana Jawaad kuma yana wajen Hajiya Mamanmu kuma ita kadai agida kamar mayya tayi kukan har ta gaji Ta rame ta lalace sannan ga Fama da Mutuwar jiki da kasala