Showing 117001 words to 120000 words out of 145917 words
tsana da Bakikciki yake Binta dashi da tir da ita bisa yadda ta Aikata wannan abun kunya.
Juyawa yayi kamar sauran zai fita Ta saka Hannu ta rike kafarsa ya juyo ya Fizge Kafarsa ya fice da Sauri yana Sharan kwallah Haj.Uwa ta Dora hannu akanta tana Fadin"Na shiga uku na Lalace..!
Kaico na..Kai co na..!
Wajen Nazifa ta nufa itama kawai sai ta kauda kanta tana kuka Haj.Uwani ta riko hannunta tana fadin"kema gujemin zaki yi nazifa..!
Kada ku manta ni mahaifiyarku ce..!
Duk abunda nayi yau saboda ku ..!
Bata gama mgana ba Nazifa ta kwace Hannunta tana kuka Cikin kukan take Fadin"Ki daina kokarin dora mana Girman zunuban ki..Kin sakamu jin kunya Mommy..Nayi nadamar kasancewarki mahaifiyarmu ayau..Kin cucemu kin bar mana Tabon da har abada bazamu taba mantawa ba..!
Tana gama fadin haka ta mike da gudu itama tabi bayan yan"uwanta tana gunjin kuka suka bar Hajiya tana wani irin kuka,kukan nadama da nasani mara amfani.
Ita da Anty Amarya da Mamammu wanda ko Tsausayi basu bama kowa afalon ba.
Baba mallam sai da ya Dauke kwallah a kwarmin idanuwansa kafin yayi gyaran murya yana fadin"Duk Sboda Dukiya ce yasa kuka kai kan ku ga Halaka..?
Shirka acikin gidana da zuru"ata..!
Allah ya tsaremana imaninmu..!
Bayaso ya cigaba da mgana Rauninsa ya bayyana yasa ya Dakata,irin su Goggo Husai ne da su yakaka suka iya amsa da Ameen ko Hajiya kanta na kasa tana sharan hawaye.
Mallam ya cigaba da fadin"Kun Saka ido kan Dukiyar da baku san Wahalar da Sa"idu ya sha wajen tarata ba..Rana iska damina yana Tsaye da Amana kan Dukiyata..Dai dai da Rana Daya bai taba gazawa ba..Sai yau rana Daya komai Dayake faruwa saboda ita ce..?
Daman an ce Dukiya da mata sune abun shagala anan duniya..to bari in sanar daku abunda baku sani ba ko nace wasu basu sani ba..Gabadaya Dukiyata Rabinta mallakin Sa"idu ne..Rabi ne nawa shekaru kusan uku da suka gabata ribar da muke samu da nashi aciki..Na saka Lauyoyi sun yi Rubutu ko yau na Fadi na mutu Rabin Dukiyata na Sa'idu ne ya Chanchanta ya kuma Dace domin yafi wahala da ita Fiye dani dana mallaketa..!
Ya karishe mganar cikin wani yanayi,Sai kallo ya koma wajen Baba mallam,Kar Baba Sa"idu da Ya"yansa su ji labari cikin mamakin jin kalaman Baba mallam..
Baba Sa"idu dake jikin Jafar ya Dago Cikin Rauni yana Fadin"Baba mallam ammh...!
Hannu kawai ya Daga masa yana Fadin"Basai kace komai ba..Wannan ba mgana bace..Tuni an tabbatar dashi Tuntuni takardun komai yana nan a Rubuce..Sa"idu kai D'a na ne..Har yau gobe kana nan a matsayin Babba yaro na..Kafin na same su kai na Fara samu har gaban Abada bazan manta da karamcin Mahaifinka gareni ba..Kafin na Fara sanin kowa Ku na fara sani kai da Hajiya..Dole ku zama wani jigo nawa abunda baku sani bane ba boka ko mallam ba..nan Duniya ba wacce zata kai matsayim Hajiya a wajena..Hajiya ta zauna dani Tun ina amsa sunana Yunusa ban tara komai ba kuma ban da komai ban isa komai ba,ban kai ko'ina ba sannan ba wanda ya sanni..Itace ta wahala dani ta Zauna dani tun ina malamin zaure ta jure yawon gari gari da nake yi domin Da"awa sannan ta jure abubuwa da yawa akaina,Itace ta Fahimceni Fiye da kowa acikin ku..Sannan duk abunda na kawo mata Zata karbesa hannun Biyu bazata taba korafi ba,dukkan ku da na aure ku Hajiya bata taba Daga Bakinta akan hakan ba..Ban taba kawo mgana ta tsallaketa ba yadda ta Daukeni Allah ne kadai ya sani..Bayan ita sai Sa"idu Shima yazo ya wahala dani, wahalan da ko ya"yana basu yi dani ba..Har gaban Abada Hajiya da Sa"idu matsayin su bazai sauya a wajena ba..!
Duk Kokarin mai kokari bai isa ya Ture abunda Allah ya kafa ba..Shiyasa duk kan sharrin ku ya koma kanku..Allah ya gani ban taba cutar daku ba..Ammh tunda kuka Zabi ku cutar damu bazamu ce komai ba..Sai dai zamu bar ku da Allah mai Fitowar rana da Faduwar ta,Kamar yadda ya Fallasaku yau..Sannu sannu zaku amshi Sakamakon a Hannunku..!
Ya karishe Fada yana kauda kai Daga kallon Anty Amarya da mamammu Dake kuka kamar ransu zai fita.
Gogggo Husai tace"Hakkin rai bazai barsu ba mallam..!
Mallam yace"Tsakanin su da Allah ne wannan Husai..Basu isa su kashe rai ba..Saboda basu ke Kashewa su raya ba..Duka na Allah ne..Allah daman ya Rubuta Lokacin Hadiza yayi..Ko ba Sanadi zata rasu a wannan ranar..Allah ya rubuta Hakan Wa"adinta ya kare..Ammh sune Sanadin hakan
Cutar da sukayi ma Sa"idu da ya"yansa kadai aka bar Balaraba da Marliya sai ya hanasu zaman Lafiya a Duniya..!
Goggo Husai tace"Allah ya isarmu..Allah ya sakama Sa"idu..!
Take fada tana kuka Yakaka na gefe tana jinjina kai mamaki duk ya cikata wannan aikin duk agidan malami kamar Mallam yunus..!
Tsoron Allah ya kara kamata da tsoron rayuwa. !
Amina ko na jikin Danmallam tana Shesshekan kuka shi kuma yana ta lallashinta su ya jadwa na gaban Aba suna ta gunjin kuka.
Mamannu ganin Aba ya juya baya su Jadwa ma sun juya mata baya suna kuka sai ta rarrafa wajen Zulfa kafin ta kariso ta mike ta isa gaban Aba ta Zauna tana kuka Daya bayan Daya suka koma wajen Aba da yan"uwansu suka zauna suna kuka suna Binta da kallon kyama..hamida ce ta mike tana wani irin kuka kallon Mamanmu take Idanuwanta sun juye.
Mamammu ta rarrafa gabanta ta rike Kafafunta tana fadin"Hamida kema kada ki gujeni..Wlh sharrin shedan ne da Sharrin so..!
Hamida ta yi wani mirmishi kafin ta Saki Dariya kamar mahaukaciya.
Cikin Dariyan take kallon mamammu cikin wata murya tace"Tunda kike aikata wannan Muguntar naki baki Tunawa damu ya"yan ki ba..?
Baki Taba Tunanin watarana abunda kika aikata zai taba mu ba..?
BALARABA KO NACE DAYYABA..ki sani Duk abunda kika aikata kanki zai Dawo..Ba yaya kika kashe ba kanki kika kashe ba Amina kika lalata ma Rayuwa ba ya"yanki kika lalata ma Rayuwa Kika gurbatamu kika Wulakantamu..Duk abunda kika aikata tare damu ya"yanki zamu girbeshi..!
Ta karishe fada cikin Kuka lokaci Daya da dariya kamar wata Mahaukaciya kowa sai ya koma kallonta cikin mamaki da Tunanin me ya Sameta .!?
Mamanmu ta fara kokarin mikewa ta Rumgume Hamida cikin Fitan Hayyaci ta tureta Sai ta fadi kasa cikin muryan kuka tace"Kada ki kara tabani..baki sanni ba..Ban sanki ba..Tsakaninmu Dake sai Allah ya isa..Bazamu taba yafe miki ba kin cutar damu kin Cutar da kanki.Da izinin Lahi sai kin lalace sai Allah ya wulakantaki..Sai Allah ya Dai'daita Rayuwarki sai Allah ya tsarwatsaki BALARABA..!
ta karishe fada cikin wani yanayin da sai da ta bama kowa Tsausayi Amina ta Baro Jikin Danmallan Tsausayin Hamida ya kamata kafin ta karisa wajenta Hanne ta isa ta rumgumeta tana kuka tana fadin"Hamida ki daina Fadin haka don Allah ki daina. !
Hamida na gunjin kuka take fadin"Ya zan yi Hanne..?
Ina jin zuciyata kamar zata fashe..Kamar zan yi hauka.!
Muryan Amina taji a bayanta tana Fadin"Ki rika maimaita innalillahi wa"inna ilaihirraju"un acikin ranki zaki samu Sauki..!
Hamida ta saki Hanne ta karisa gaban Amina tana Fadin"Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un Amina da wane ido zan kalle ki ina jin kunyarki..?
Take Fada tana kama kanta sai tayi suu kamar zata fadi Amina da Hanne sukayi saurin tarota ta fada jikinsu haka suka kankame juna su uku suna ta kuka kamar ransu zai fita.
Kowa afalon sai da ya Tsausayamusu suna yi su ya zulaihat nayi bamai lallashin wani.
Mallam ne ya mike yana kallon Hajiya yace"ki Rarrashi yaran nan Hajiya..kukan ya isa haka..Allah ya Tsaremu..!
Ta amsa da Ameen Idanuwanta sun kada kafin tace"Cikin wannan halin da suke ciki za"ayi Daurin auran..?
Mallam ya gyada kai yana Fadin"Insha Allahu ba fashi..!
Ba wanda ya kara mgana Baba mallam yana gyara Rawaninsa yace"Sa"idu tashi muje shashena..Tashi ga Kafafunka da izinin Lahi bazasu taba ganin gazawarka ba..Allah ya Dauke Hadiza ni kuma nayi alkawarin Zan aura maka wacce ta fi Hadiza komai da komai kamar yadda na aura maka ita da farko..!
Aba ya mike da taimakon Jafar yana kokarin Daidaita yanayin sa yace"Nagode mallam..Allah ya kara Nisan kwana..!
Kawai sai yaji kamar yasaka kuka Baba mallam ya kariso ya rumgumesa yana Buga bayansa Kafin ya Dagosa yana faman share masa hawaye yakuma ja Hannunsa suka fice Daga Falom aka Bisu da kallon Tsausayi da kauna.
Su ya jafar ma suka mimmike da su Aliyu jiki duk a sanyaye Ya Danmallan ne ya isa wajen su Hanne yana Fadin"Noor ki bar wannan kukan kinga fa bake kadai bane..Sake su..Ku saki juna hakanan..!
Jin muryansa yasa suka saki juna suna kuka Sai suka basa Tsausayi sai ya fara rike hannun Amina sannan ya rike na Hanne da Hamida ya jasu har gaban Hajiya yana fadin"Hajiya ki yi abunda kika saba..!
Don Allah kice subar kuka in suka bari Noor zata bari itama..!
Hajiya tayi mirmishi ta Karbi Hannun Amina kafin ta karbi nasu hanne Hajiya Nasara tataso ta karbesu tana Fadin"kada ka damu Danmallam bazasu kara kuka ba Insha Allahu..!
Ya kalleta kansa na kasa kafin ya juya yabi bayan su Nasir da suka fice tun dazu.
Aka bisa da kallo sha"awa irin su Anty Amarya kuma sai kunci da Nadama mara amfani.
Hajiya ta tasa su Amina Cikin Dakinta ta Kira Yakaka dasu Aisha tace su lallashe ita kuma ta koma Falo tace a kwashe kayan Amina akai Dakinsu Hanne..
Yan gusai kuma suka koma gidan Aba suma da su ya zulahait domin Hamida ce kadai tare da su Amina Su ya jadwa ma suna Shashen Hajiya suna faman kuka su kuma sai suka koma gida suka Hada kai suna ta kuka ya Zulfa da ya Zeenatu da ya Zulaihat sai yaya Zahra bamai lallashinsu su kansu yan gusai sai Tofin Allah tsine suke yi ma Mamanmu.
Kamar wasu marasa galisu haka akayi banza dasu Haj.Uwani ta fara rarrafawa ta Fice cikin kunya da kuka sai Anty Amarya da ta fita tana kuka sai Mamanmu kallo arziki ba wanda ya kara yi musu har suka shige shashensu Daga Anty Amarya har Haj.Uwani Datse shashensu sukayi suna ta kuka ita Anty Amarya ba yan"uwanta duk suna asibiti wajen Sakina da tayi bari ita kuma Hajiya uwani Daga ita sai Umaima dake kwance batasan meke faruwa ba su Nazifa bata san ina sukayi ba,Bata Tunanin ma zasu nemeta nan kusa.
Mamanmu kuma fakaitan idon mutane tayi ta shige Dakinta chan kurya tana kuka saboda yawanci bakin suna Dakin yaya ne yaran kuma suna Dakin su Amina kowacce tana Ciki tana Dirzan kukan nadama da nasani da kuma rashin madafa Daga mallam har Aba basu ce musu komai ba ballatana su san ina matsayinsu.!
Su Amina kuwa Dakyar suka Daina kuka suka koma ajiyar zuciya.Yakaka tayi ta kokarin Lallashinsu.
Sannan su kansu ya Jadwa sai da Hajiya tayi ta musu nasiha suka Saurara sannan Hidiya matar Nazir da Aliya matar Aliyu na tare dasu ita duk ta tsorata tasan tana da Zafin kishi ammh bata san Bin malamai ba..su matan su ya Jafar ma suna nan tare dasu Sarood Hajiya Nasara ta kaita Shashenta Hayaniya ya saka mata Ciwon kai,su fatima na Tare da ita suma duk jikinsu yayi sanyi sun kara Godema Allah Daya tsare imanin Mahaifiyarsu domin ba wayau bane kuma ba Dubaransu bane.
Su ya Danmallam kuma suna Shashen mallam,shi da Jafar da Nasir sai Nazir,Aliya su shamsu dai suna Dakim su Nazeem sun kulle kansu Nazifa dai Ta koma Shashen Hajiya Nasara bayan sun gama kukan nasu.
Su kansu zaman jugun jugum duk Dauriyan mallam Lamarin ya tabasa shi da Aba sai dai yayi kokarin nuna komai ba komai ba sabida Aba da su ya Danmallam.
Mganar Daurin auran gobe suka Tattauna Daganan ya Sallamesu dukkansu ba wanda yayi kokarin komawa gidansa duka nan suka kwana Har Aba da su ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir a falon mallam kamar kwanan zaune ma sukayi su ya Nasir ne da Jafar suka kwana Dakin samarin gidan su Akilu da suma Jikinsu duk yayi sanyi har garin Allah ya waye ba wanda ya saka wani abu acikinsa ko su kansu matan sai da Hajuya tayi ta Fada ne suka sha Tea har su Amina.
Mazan kuma da Safe kowanne ya koma gidansa Ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir gidansa suka tafi suka natsa kafin Lokacin Daurin aure kowa kagani ba walwala.
Ammh Danmalam bai tafi ba sai da ya leka Amina ya tabbatar da ta daina kuka sannan tana Lafiya.
Chan gidan Aba ma haka aka tashi Goggo Husai ne tazo ta zauna dasu Zeenatu tana nuna musu suyi hakuri Laifin Balaraba bazai shafesu ba su yi Hakuri Bikin kanwarsu ake yi to da hakane suka samu suka karya da Safe har suka Dan saki jiki Mamanmu kuma bana wanda ya san tana gidan ballatana abi ta kanta ta kwana kuka ta kasa fitowa ta zama mujiya yau gashi Bikin data cima burina ne ake yinsa ta zama kamar mujiya Cikin mutane.
Haka ma bangaran Anty Amarya ita Kadai kamar mayya ta gaji da kiran wayoyin su Jidda sun ki Daga kiranta Har ta A"i taki Daukan wayanta ballatana taji wani Hali sakina ke ciki ta rasa ina zata saka kanta taji Dadi har Sabeeha bata nan sun tafi da ita.
Hajiya Uwani kuma kafin Safe har ta Rame saboda tashin Hankali sannan tayi ta kiran Batula bata samu ba tana so ta Sanar da ita komai fa ya Tsaya.
Alokacin Datake kiranta ita ta kama Hanyar Minna domin taje ta aiwatar da gudurin Uwani bata sani ba,Ajalinta ne yake kiranta.
Domin sun fita Tsafe ba Dadewa suka samu Mummunan Hatsari da yayi Sanadiyar rasa rayuwakan mutum Hudu Dake motar har da Batula aciki..!
Sai da Hajiya ta saka baki sannan su Ya Aisha suka Tafi da su Amina gidan su ya Jafar saboda su Shirya Sa"adatu kuma Mallan ya kira Jidda yace Sa"adatu ta Dawo gida ko batasan yau za"a Daura mata aure bane..?
Ba Dadewa suka Dawo ita da Sadiya fuska duk ta Kode saboda kuka gidan su ya Jafar suka wuce tunda chan zasu shirya kafin Daurin auran.
Anan ne su ya Aisha ke jin Labarin Sakina cikinta ya zube sannan tana chan ana mata karin jini bata san inda kanta yake ba.
Sadiya ke maida musu zencen tana kuka su ya Abida na Faman bata baki Amina kuma na tare da su Hanne ita yanzu tama Daina kukan Hamida ce sai Ahankali ita da Hanne suna ta faman bata Baki ammh Taki sakin jikinta gashi ana Daura aure za'a tafi Dasu mallam yace bamai Daga wannan auran.
Baba Mallam da Aba tun safe suka fita ba wanda yasan inda suka je sun dai yi mgana da Hajiya kafin su fita Sannan har yan bazanga da bakin gusai suka iso maza basu dawo ba sai wajen 12,da rabi na rana suka Dawo Shima Baki akayi daga maiduguri wani kawun su Hajiya sai D'ansa guda Daya wanda ko Hajiya bata san da zuwansu ba.
Ashe Labarin abunda mamanmu ta aika yaje kunnen su kawu Salisu matan sun kirasu sun Fada musu komai,Kawu Salisu sai Fada yake yi yanaCema Aba ya saki Balaraba taje duniyace Mallam ne ma ke basa bakin kan mganar Aba dai bai ce koma ba ai ko bai ce balaraba ta bar mai gida ba in Tana da kunya basai ma ta jira yace ba zata san inda Dare yayi mata.
Zuwa Lokacin Yan Daurin aure sun fara Zuwa Mutanen Yola ne suka fara zuwa da Mata guda biyu suka zo aka kai su Shashen Hajiya sai yan Zaria suma sun Iso da mace Daya.
Na gombe ne karshen isowa su kan maza ne kadai suka iso banda mace ko Daya.
Amaran nachan gidan ya Jafar an samu sun yi wanka sun saka wani Less din da Mallam ya Dinka musu mai Fari da Golden sai Hijabansu mai ruwan kasa Itama Amina ta shirya Cikin leshinta mai Tsada da ya Aisha ta Dinka mata iri daya da ita har da Yakaka sai dai ita Bubu tayi saboda Cikin jikinta kowa ka gani ba walwala ido Duk ya kumbura.
Su ya Zulaihat sun zo da Safe suka Hade dasu Hamida da Amina suna ta kuka dasu ya Jadwa suna ta basu Hakuri su kuma suna cema musu ba Laifinsu bane sai da ya Aisha tace zata Kira Hajiya sannan suka sarara.
Misalin karfe Daya da wani abu na Rana Kofar gidan mallam ya Cika ba matsaka Tsinke su ya Danmallam sai Lokacin suka iso Cikin shigarsu ta alfarma haka ma su Ya Jafar mallam ma da Sabuwar shadda da rawani haka ma Aba kowa dai yayi kokarin Boye abunda ke ransa har da su Nazeem kuwa.
Alokacin kuma Hajiya Uwani ta san da abunda ya faru da yar"uwarta Batula sai ta rude kuka kamar zata Haukace bata tsaya neman kowa ba ta Hada kayanta Ko Umaima bata Tsaya bi ta kanta ba,ta ma bar Shashen nata tana Shashen Hajiya ta shiga Cikin yan Biki ita kadai ce batasan me ya faru ba mutane sun yi yawa yasa har ta fito ta tari abun hawa ta hau zuwa Tasha ba wanda ya lura da ita ammh Nazeem ya ganta sai dai bai nuna ya ganta ba yana Tunanin abunda ya Dace da ita kenan ya Dauka ta neman ma kanta mafita ne kafin mallam ya koreta.
Anty Amarya kuma tana Shashenta ko kare bata kara gani ba,kaf Danginta suna asibiti wajen sakina su jidda kuma suna Tare da Sa"adatu domin cire mata Damuwar dake damunta duk da suma karfin Hali ne Mamanmu kuwa Sai da ta raina kanta Har Daki yan Gusai suka Bita suka mata tsofin Allah Tsine shiyasa ta kasa Fitowa Tayi kuka har ta bama uku Lada yan"uwanta sun Tsine mata kamar me sun ce ana Gama Biki yau gobe zasu koma sannan sun ga karfin Halinta Data iya Takowa gidan Sa"idu..
Ita kuma tana Tunanin ina Zata..?
Bata da inda zataje a karbeta Ta riga tayi ma rayuwarta mummunan Tabon da har Abada bazai goge ba.
Karfe Biyu aka Dauran auran su Hanne,Na Aba aka fara Daurawa da Hadiza Babbar Diyar kanwar Hajiya Yagana Datayi aure mijinta ya rasu bata kuma taba Haihuwa ba..!
Hadizan ma da ita aka zo Biki Suma kansu basu sani ba sai da aka Daura shi ya kawo kawun Hajiya Tun Daran Jiya mallam ya kirasa yamai bayani Tun Safe kuma suka Biyo Jirgi Daman a Bauchi yake da zama shi da iyalansa. !
Daurin auran daya bama kowa mamaki Hajiya kam Bakinta yaki rufuwa Mallam a koda yaushe Tunaninsa mai kyau ne
Daga nasa sai na Hamida sai na Sa"adatu na hanne ne na