Showing 27001 words to 30000 words out of 98809 words

Chapter 10 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

agogo ka ga lokaci kuwa? Sha biyu ya wuce fa, gidan mutane za ka je mu su da wannan daren?"
Cewar Mummy ta cike da fara'a. Shi ma ɗin dariya ya ke, har ran sa da zai samu dama babu abinda zai hana shi zuwa gun Amatullah domin yi mata wannan kyakkyawan albishir ɗin. A zahiri kuwa cewa yayi
"Toh da asuba kuwa zan je, ana buɗe kofar gidan su Amatullah za su ganni bakin kofa domin ta san cewa I mean business, I love her Mummy"


"I know right, I hope she loves you too son, Allah ya mu ku albarka ka ji dan albarka?"


"Ameeen, you're best, thank you"


Da wannan su ka yi sallama. Ciwon rashin masoyin ta ne ya tashi, Nan ta zauna ta na mai zubda hawaye domin kuwa mahaifin Dee ya so ta, soyayyar da har yau ba ta sami irin shi ba, ya tararraye ya ta kuma ya kare hakkin ta, ya kance da ita yana yi mata hakan ne domin cika hakkokin ubangiji, haka addinin shi ya koyar. Ina ma ace mutuwa ba ta raba su ba.


Dee kuwa yanda ya ga rana haka ya ga dare dan kuwa ya nemi bacci ya rasa, Allah Allah ya ke Allah ya wayi gari ya ga Amatullah. Haka ita ma Amatullah wacce tun rabuwar ta da mahaifin ta ta shiga yanayi mai wuyar fasaltuwa, ta nemi bacci ta rasa akan dalilin da ita kan ta ba ta sani ba. Kawai dai gaban ta na faduwa da wani tashin hankali da tsinci kan ta ciki, haka har aka fara kiraye kirayen Sallar asuba sannan bacci ya fara sace ta.


***


A cikin masallaci bayan an idar da sallar asubahi, Baban Sasa wanda tunda su Baba Anas su ka ga ya fito sallar asuba su ka san ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, ya matsa kusa da liman ya ce da shi
"Allah gafarta Malam akwai auren da mu ke so a daura a yau, tsakanin jikoki na biyu, dan wajan Anas da diyar Salihu....kai Ina Saifullahin ma ya ke?"
Ya tambaya ya na mai wage wage.


"Ina ga fa yau be sami damar fitowa ba ko kuma masallacin bayan layi da ya fara zuwa ya je"


Baba Anas ne ya bashi amsa, shi kuwa Baba Salihu da ya san halin da ƴar sa ke ciki na game da auren Saifullahi ne ya sa jikin sa yin sanyi dan kuwa dai be yi tunanin Baba Sasa da gaske ya ke zai daura auren a yau ba sai yanzu da ya ga zahiri.
"Ah toh madallah, ai sai a ɗaura me za a jira in dai akwai waliyai, shedu da sadaki?"
Cewar liman yana mai baza babbar riga. Ba tare da ya damu da rashin Saifullahi a wajan ba sai ga Baban Sasa ya fito da kudi daga aljihun rigar sa, ka na ya mika ma Baba Zubairu ya ce
"Amshi nan Zubairu, kudi ne dubu hamsin sadakin dan ka ne, kai na umurta ka zama wakilin Saifullah, Ni kuma ni zan kasance waliyi ga Amatullah, kai yaro yaka nan shiga gida, ɗaki na za ka ga alawa da goro maza kwaso su nan...."


Da saurin yaron da aka aika ya tashi ya fita, nan aka fara shirin daurin aure, inda Baba Anas da Baba Salihu su ka zama yan kallo.


*****
Tun kafin a idar da sallar asuba Dee ya shiga wanka. Ana idarwa shi ma din yana fitowa daga wanka a gurguje ya shirya cikin shadda brown dinkin jamfa. Alkawarin doka sammako zuwa gidan su Amatullah din da ya dauka na gaske ne. Domin kuwa yau da shi za a bude gidan.
Kasancewar Hamza baya nan tun jiya da ya fita be dawowa ba, yaci sa'ar fita ba tare da ya sha tambayoyi ba, yanda ya sha hula da turare kai ka ce ango haka ya shiga motar sa cike da nishadi ya nufi gidan su Amatullah.


****
An ɗaura aure an shafa fatiha in da Amatullah ta tabbata matar Saifullahi. Cikin wanda su ka shaida ɗaurin auren, In aka dauke Mahaifan ma'auratan biyu wato Baba Anas da Baba Salihu babu wanda abin bai masa dadi ba, musamman Baban Sasa wanda zama yayi dirshen cikin masallacin ya na raba alewa da goro cike da jin dadi. Lokacin da Dee ya sami isowa gari yayi haske, haka kuma yayi mamakin ganin kofar gidan su Amatullah a bude. Ya na mai tunanin kila sammako su ke yi wajen buɗe gidan ya sami gefe ya faka, sannan ya fito ya tsaya kofar gidan ya na shawarar kiran Amatullah ko kuwa dai ya jira gari ya daɗa wayewa. Ganin fitowar Baban Sasa daga masallaci hannun sa rike da sauran alawa da goran da ya rage, tare da su Baba Anas sun nufo gidan yayinda jama'a wanda su ka shaida auren da kuma wanda su ka ji labari daga baya ya sanya Dee ɗan ja da baya ya koma jikin motar shi. Kamar yanda ya kula da su haka suma su ka lura da shi, musammam Baba Anas wanda ko cikin bacci zai gane shi, shi kuwa Mahaifin Amatullah kallon sa ya ke ya na mai mamakin kamannin sa da marigayi wato Mahaifin Dee Yusuf Haɗeja.
Ko da su ka isa kofar gidan sai Baban Sasa ya tsaya yana mai tsurawa Dee ido, ganin haka suma kawun nan nata tsayawa su ka yi, su ma din Idanun su kan Dee din ya ke. Cike da fargaba Dee ya ƙarasa gaban su har kasa ya durkusa cikin girmamawa ya shiga gaishe su.


"Yaro daga ina? "


Baban Sasa ya tambaya. Cike da jin nauyi Dee ya ce
"Dama na zo ne...."


Sai kuma yayi shiru, ya kasa magana.
"Ka zo me?"


Baban Sasa ya sake tambaya. Jin shirun yayi yawa Dee ya kasa magana Baba Anas ya ce
"Shi ne wanda ya zo neman Amatullah jiya"


"Auho kai ne Dee Yusuf din da na ke ji gurin jikata?"


Jin Baban Sasa ya kira sunan sa ya sanya Dee jin dadi har cikin ran sa, wato har iyaye da kakannin Amatullah sun san da zaman shi. Ya na mai murmushi ya ce
"Eh ni ne Dee Yusuf"


"Kai ne kirista da ke kokarin hurewa jikata kunne, ka ke kokarin ruguza tarbiyar da mu ka bata ta hanyar sauya mata addini da dabi'a ko? "


Tambayar Baban Sasa ba karamin tayar da hankali Dee ya yi ba, in da ya dago kai da sauri ya na mai fadin
"Wa'iyazubillah!!! Afuwan Baba, amma dai ina ga an sami rashin fahimta ne, ko kusa ban taba tunanin aiwata haka ba, na zo ne a yau domin shaidawa Amatullah zan karbi addinin musulunci, ta kuma shige min gaba domin shaidawa iyayen ta, ina mai neman izinin turo iyaye na neman auren ta......."


"Kai tafi can rufewa mutane baki!!!"
Cewar Baban Sasa cikin tsawa da tsangwama, yayinda Baba Salihu ya runtse idanun sa cike da tausayin Dee da ya rufe shi. Baban Sasa be gushe ba ya cigaba da fadin


"Ku ji fa dan Allah yana kirista shekara da shekaru kawai an wayi gari wai ya zo wajan mu karbar musulunci da ke ka mayar da mu shashashe irin ka! Mu za ka zo ka yaudara? Toh ka ruke tubar ka ka kai can ba dai gare mu ba! Ahir din ka! Jika ta dai na aurar da ita ga jika na musulmi dan musulmai!!"


Jin maganar ya ke tana shigar sa kamar kibiya tsabagen ciwo, hawayen da shi kan sa bai san da zubar su ba ke gangarowa daga idanun sa yayinda ya dukar da kan sa kasa.
[2/8, 12:21 AM] +234 803 579 6693: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA GOMA SHA BIYU


Baba Anas wanda shi kan shi maganar Baban Sasa ya masa tsauri girgiza kai ya shiga yi, Jan hannun Baban Sasa cikin dabara tare da faɗin


"Baba ai ina ga zai fi kyau ka ɗan shiga ciki ka huta, ka jima a waje"
Cikin cijewa yayin da Baba Anas ke jan sa be fasa faɗin
"Ai to ka bari Anas na yi masa wankin babban riga, ɗan tselan uwa, ta Allah ba taka ba, jika ta dai na maka katangar karfe da ita....."
"Baba faɗa ba naka bane tun da TAZARAR da ke tsaƙaninsu ya ƙara ƙarfafa" Baba Anas ya ce yana jan Baban Sasa zuwa cikin gida.
Su Baba Zubairu ma baya su ka rufawa Baban Sasa, mahaifin Amatullah ne kaɗai ya rage tsaye gaban Dee wanda ya sunkuyar da kai kamar an ajiye dutse.


Cikin sassanyar murya Baba Salihu ya
"Ban san da wani ido zan kalle ka ba, ban san da wani baki zan baka hakuri ba, ni mahaifin Amatullah na so ka da ɗiyata, ko ba don komai ba ko don kuskuren da na aikata dangane da Mahaifiyar ka a baya....."
Yanda yaga Dee ya ɗago kanshi a karo na farko su ka haɗa idanu, da yanda ya ga idanun sa sun kaɗa sun yi jajur ya sanya Baba Salihu shanye maganar sa, kana daga bisani ya furta
"Allahu akbar Allah ya jikan Yusuf da rahama, babu shakka kai jinin sa ne, ina mai fatan za ka yafe mana a karo na biyu Yusuf"
Yana gama faɗin haka shima ciki ya shige cike da danasani, dan kuwa da ya taimakawa Mahaifiyar Dee da ya girma cikin musulunci.
Allah kaɗai ya san tsahon mintocin da yayi nan tsugunne, har sai da jama'a su ka fara taruwa suna tambayar lafiya? Sannan ya tashi da kyar ya na mai goge hawayen da suka rufe fuskar shi. Har ya karasa ga motar shi kafin ya juya ya kalli kofar gidan su Amatullah, gani ya ke kamar za ta fito ta ce duk ba gaske ba ne, ganin babu ita babu alamar ta ya sanya shi buɗe motar, ya shiga ya zauna, Amma kunna motar ya gagare shi


"Amatullah shikenan yanzu na rasa ki?"


Cewar Dee ya na mai kifa kan sa bisa sitiyari yayin da maganganun Baban Sasa ke masa yawo cikin kwakwalwar kan sa.


"Amatullah..... Amatullah........."


Amatullah kuwa tana cikin tilawa saƙon ɗaurin aurenta ya isa kunnuwanta, ba ta yanke da karatun ba cigaba ta yi tana mai godiya ga Allah ba don tana son auren ba amma don ta san aure wata dama ce da Allah ya ke ba wanda ya so, ba wayon mutum ba dabararsa ke sanya ya yi aure a duniya ba, sannan matukar lokacin mutum yayi to babu shakka za a ɗaura ga kuma mijin da Allah ya riga ya tsara.
Shigowar Mahaifinta ne ya sanya ta kasa kunne Jin ya na magana da Gwaggo, ya na mai rokan Allah kariya daga dukkan sharri a gidan auren Amatullah.
"Mairo na so a ce yaron nan ya iso kafin a ɗaura auren nan, wallahi sai dai a yi duk abin da za ayi shi zan ba Amatullah."
Amatullah ta tsinkayo mahaifinta na faɗi, ajiye Qur'anin tayi don jin wani yaro babanta ke magana akai.
"Wa kenan baban Hafiz?" ta tambaya a sanyaye don za ta iya rantsuwa ta dade ba ta ga mijinta cikin tashin hankalin nan ba.
"Wancan da Amatullah ke so" ya faɗi kai tsaye.
"Wanda Hajiya tace bamaguje ne?" ta ce a ɗan firgice.
"Ahlil kitaab ne, ya zo da shahadar sa a zuci so kawai yake a sanya masa a laɓɓansa amma ya zo an riga da an ɗaura auren Amatullah." Amatullah tana jiyo tausayi da buri a cikin muryar mahaifinta.
'Dee Yusuf ya zo don ya musulunta' ta faɗi a cikin zuciyarta tana mai jin wasu zafafen hawaye suna gangarowa kuncinta.
" Baban Hafiz mu kaddara hakan ne Alkhairi, ka manta duk wani abin dai auku a rubuce yake, Allah da kansa ya faɗi a zancensa mafi gaskiya LIKULLI AJALIN KITAAB" tace muryarta a sanyaye, Amatullah ba ta iya jin sauran zantuttukan iyayenta ba ta tashi ta jiki na rawa ta fice waje, jama'ar gidan na amarya amarya amma ina hankalin ta yayi waje domin kuwa ba ta da buri da ya wuce kanin Dee Yusuf ko da kuwa shine gani na karshe da za ta ma sa a rayuwar ta.
Sai da ta ganin motar ya dauke ma ta, sannan ta juya a hankali kamar wacce kwai ya fashewa ta shige gida. Dakin ta ta koma tana mai kuka kamar ranta zai fita, shike nan Tazarar da ke tsakanin su ya tabbata, shike nan za ta rayu da wanda ya fi kowa ganin ta a matsayin kaskantaciyar halitta. Tunanin da su ka dinga tunzura kokenta kenan. Fadi ta ke
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Ni Amatullah na rasa masoyi!!!"
***


Baban Sasa kuwa ɗakinsa Baba Anas ya wuce da shi, nan ɗin ma baki ya dinga bashi yana mai koɗa haɗin da yayi wanda hakan ya zama ruwan da ya dinga wanke zuciyar Baban Sasa da ganin Dee yusuf ya sanya shi cunkushewa kamar tuƙuƙin hayaƙi.


"Anas a ce Arne har ya ga fuskar da zai ce yana son ta, shi yasa na tsani bokon ƴa mace" Baban Sasa ya nisa ya faɗi, sai da baba Anas ya ɗauki wasu yan daƙiƙai kafin ya ce
"Ka san Arne da tsaurin ido, dama an ce su kan janye yayanmu cikin hilla da kyautatawa. Amma ni ban shakkar Amatullah ko da na daƙiƙa ne, Allah ya albarkaci Auren nan nasu, Baba ba zan iya kwatanta farin cikin da nake ciki ba. Allah ya saka da Alkhairi" murmushi Baban Sasa ya yi cike da farin ciki da alfahari da abin da ya yi.
Nan Baba Anas ya zauna su baba Zubairu su ka shigo su ka dasa hira, ba su suka bar ɗakin ba sai da baban Sasa ya fara gyangyaɗi bayan ya sha maganinsa na safe.
Ba su yi mamakin ganin yanda mata su ka cika gidan ba saboda mafi akasarin su na yan tsakankanin Amaru ne.


Farin cikin da ke tattare da muryar Baba Anas yayin da yayi sallama a ɗakin matarsa ƙadai ya isa ya fassara tarin farin cikin da yake ciki.
"Wai ni kam Alhaji Anas wannan farin ciki duk akan samun kwancen surika ne" Madina ta tambaya tana wani yamutsa fuska.
"aikuwa ke ma kya faɗi a ce mutum Sam bai san abin da ya kamata ba" Hajiya ta amshe tana ƙarasawa da ƙaramin tsaki.
"Ohhh toh ni ban fahimci in da kuka sa gaba ba, ke madina abin kunya ne ma a ji zancen nan daga bakinki, in ita sadiya karere ce a gidan nan ke kuma fa? Nono ɗaya kuka sha fa da mahaifin yarinyar nan" yace yana gimtse fuska.
"Toh ni dai ban ga mai Mairo ta tsinana a gidan nan ba in banda raba tsakaninmu da iyayenmu, sannan shi Salihun da kake magana sai naga ɗan uba ne a gareka, har wani cancanta yayi ka sayar da farin cikin ɗanka akan tashi ɗiyar, wacce Allah kaɗai ya san abin da ta shuka a jami'a" Madina ta faɗi cike da bakin ciki da takaicin yayanta, shirun da yayi ya sanya su tunanin cin galaba akan tunaninsa, na hajiya ta ɗaura
" ai in za a ci kwaɗo ai gara a ci me mai. Shi yayan nasu ma ya riga ya shirya da wata tun a can Turan. Yar babban gida wacce ko ba komi mun san ba hayen boko ta yi ba" tace, cike da alfahari don tun jiya ta kwana da mafarkin suruka yar baban gida da za ta zama silar komawar ta haji ba ma sau ɗaya ba duk shekara.
Shiru yayi yana kallon sa suna magana wanda duk akan kushe Amatullah ne da mahaifiyarta da kuma ƙawata masa zaɓin Saifullah.
"Madina ki zama shaida, Duk abin da ya sami auren Amatullah kwatankwacin sa ne akan Sadiya. In kun ga dama ku sanya shi ya yaƙice auren" yace bayan ya gaji da jin kalamansu, bai jira sun farfaɗo daga kaɗuwar da su ka yi ba ya sa kai ya fice daga ɗakin.




***


"Wai ko yau baban Sasa ya rasu zai rasu da cikar burinsa, aure da subahi sai kace ana neman kai" maganar da ya daki kunnen Saifullah kenan ya yi saurin tashi daga kwance ya zauna don tabbas in ba ƙarya kunnensa ke masa ba muryar Shahid ne Dan wajen baba Mahmouda.
"Kai dai bari, ai Saifullah yayi mugun dace, ina ma ni ne aka ma wannan alkawarin, kana ji murya kamar ana busa sarewa, wani abin ma hmmmn ba a ko magana wallahi Amatullah ne ake kira da wife material" abokin hirar Shahid ya faɗi wanda muryar sa ta faɗi ma Saifullah Yasir ne ɗan Baba Zubairu.
"Yaya Yasir bari anty Amina ta jiyo ka, kasan kishin ta babu part 2" Shahid ya faɗi cike da shaƙiyanci. Saifullah bai ji amsar da Yasir din ya bada ba saboda yawo da kalamansu na fari ke yi a kwakwalwarsa. Bai san lokacin da ya miƙe ya ja jikinsa zuwa ɗakin Baban Sasa ba, yana isa ya iske shi yana bacci bai tuna da halin da yake ciki na ciwo da tsufa ba ya fara magana yana jijjiga shi.
"Why Baban Sasa, me yasa za ka min haka, ka aura min wanda duk duniya na tsana, bagidajiya, baƙauyiya wacce ba ta san kanta ba, why Baban Sasa" yace yana kuka shaɓe-shaɓe kamar ransa zai fita.
Kamar a mafarki Baban Sasa ya ji kalaman nan, a hankali ya bude idonu ya ke kallan Saifullahi.
"Baba ko mace an hana a mata auren dole balle ni namiji, auren dolen ma ga bagidajiya irin Amatullah" ya sake faɗi yana girgiza kanshi alamun shi kanshi bai yarda ba. Kallo mai cike da firgici Baban Sasa ke masa, shi bai taɓa tunanin Saifullahi baya so ba duk kuwa da a lokacin ya dinga taro duk abubuwan da su ka gudana. Take tausayin Amatullah ya cika shi, yana mai tuna tsantsan soyayyar da ya gani a idanun Dee Yusuf yana mai jin haushin abin da ya aikata masa.
"Bagidajiya ce bana sonta, aurenta abin kunya ne a gare ni Baba, ka taimaka min" saifu ya faɗi yayin da ya hango ta cikin hijabinta da safa a ƙafa da hannu.
Faɗin irin mamakin da Baban Sasa ya shiga ba zai misaltu ba, zufa yake yi yana kallon jikan da yake masa kallon gudaliya wajen kauna, wanda duk inda ya zauna zai ba da shedar irin biyayyar Saifullah gare shi amma shi ne zaune yana masa ɗibar albarka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login