Showing 30001 words to 33000 words out of 98809 words
Chapter 11 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
akan abin da bacci ya ɗauke shi yana mai alfaharin aikatawa.
Shirun baban Sasa ne ya sanya Saif ɗaga ido ya kalle shi, sai a lokacin ya dawo cikin hankalinsa ya tuna gaban wanda ya ke, ya tuna duk wani shirin sa ba zai yi tasiri ba matukar bai goge abin da ya aikata ba.
"April Fool!!!" ya samu kansa da faɗi yana mai kirkiro murmushi da kuma rungumar Baban Sasa da ya zauna kamar mutum-mutumin da aka danka.
"Baba Nagode da wannan kyauta, cikin bacci na ji su Shahid na maganar baka ji farin cikin da na shiga ba, amma na ce bari in dan ɗanaka duk da dannen kirji yaci in maka" ya faɗi yana mai rike hannun baban Sasa kamar wanda ke tsantsan farin ciki. Shi dai baban Sasa zaune yake yana mai cike da waswasi don in ba ƙarya idanunsa ke masa ba toh tabbas Saifullah a haukace ya shigo ɗakin babu wani zancen wanawa.
"Ka san halin da na shiga da tace min wani Danliti ta ke so, Nagode Allah mai kyauta mai ƙari, na gode Baban Sasa ina mai farin cikin kasancewa tsatsonka. Na maka alkawari zan riƙe maka Amatullah fiye da yanda kake tsammani" ya faɗi cikin farin ciki tsantsa wanda gaba ɗaya na abin da zuciyar sa ta raɗa masa ne akan zai iya aikatawa ga Amatullah.
Baban Sasa bai iya cewa komi ba don kaɗuwar da yayi tun farko, shafa kan Saifullah ya shiga yi yana murmushi da addu'ar Allah ya kauda idon makiya da shaiɗanu a auren su.
[2/10, 9:28 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA GOMA SHA UKU
Ɗago kai Saifullah yayi ya ga me Baban Sasa ya ke yi ya dai ji yana shafa masa kamar mai neman tubarrukin maraya.
"Watau Baban Sasa in a ce kowa zai dace da fitowa daga tsatson mutum irin ka ai ba sauran tashin hankali" ya faɗi bayan sun haɗa idanu.
Dariya Baban Sasa yayi yana mai jin wani sanyi na ratsa shi don ya kasa gaskata abin da kunnuwar sa su ka jiye masa.
"Nagode da biyayyarku gareni Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya" Baban Sasa ya ce yana mai murmushin farin ciki, Aameen yayi nauyin fita daga bakin Saifullah, sai yaƙe yake yi don shi bai son a tsawaita addu'ar ma balle a dace da yinsa a bakin ƴan Aameen.
"Bari na shiga wajen amaryar in tabbatar da dagaske na kada kai" yace yana mai miƙewa.
"Ja'iri ai ni ɗin nan nine masoyinta na asali kai sai manaji" baban Sasa yace shima cikin dariya.
Ficewa Saifullah yayi don ya gaji da ɓoye halin yake ciki, neman inda zai zuba su yake yi. Bai ɓata lokaci ba ya wuce ɗakin mahaifiyar sa ba tare da ya ankara da mahaifinsa da ke zaune a ƙarƙashin bishiya ba tare yake da Baba Salihu suna tattauna abubuwa da su ka jiɓinci danginsu.
Haka su ka ɗaga kai su ka kalle shi, kallo ɗaya za ka masa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. Shiru Baba Salihu yayi yana mai addu'a a cikin ransa yayin da Baba Anas ya tashi kamar wanda aka tsikare shi ya bi bayan Saifullah.
***
Zaune ya iske Hajiya tayi tagumi da hannunta duka biyu, tun bayan fitar mijinta ta rasa ina za ta sa ranta taji sanyi, shike nan mafarkin da tayi ba mai tsawo bane balle ta sa ran tabbatuwarsa. Ba za ta ce ga lokacin da Madina ta fita daga gidan ba.
"Yanzu Fisabilillahi kin yi abin da duk wata uwa yaci tayi kenan? Kalli lokacin da Amatullah ta nuna ba ta so kina ganin in uwarta ba ta mara mata baya ba za ta iya furtawa ne? Ku kenan Ɗanku banza ko? Ni wallahi sakin ta zanyi ku neme ni ku rasa" ya ce yana mai sakin kuka kamar wani ƙaramin yaro.
Har cikin ranta take jin kukansa tsanar Amatullah na ƙara mamaye zuciyarta. Ko Baba Anas da ke tsaye bakin ƙofa ya ji kukan Saifullah har cikin ransa har ya fara tunanin bai yi ma ɗansa adalci ba. Yana shirin shiga ɗakin ya ji hajiya ta ɗora da faɗin
"kul! Sakin Amatullah daidai yake da nawa sakin" tace cikin muryar lallashi da son tare kuka.
"What!!! Hajiya me kike faɗi ne" Saifullah ya faɗi a firgice.
"Eh haka mahaifinka ya ce, yanzu maganar da ake sai dai muyi mata gashin ƙuma, kar ka kuskura ka nuna baka son auren, mu bi ta da kisar mummuke" tace kai tsaye, hakan ya sanya Baba Anas yaye labule.
"Kin san Allah sadiya, daidai da kuka na tabbatar Amatullah ta yi a gidan aurenta sai kin yi mafiyinsa. Ba zan hana ku ba fa, duk abin da kuka shirya ku aiwatar ni kuma zan tabbatar da na aiwatar da mafiyinsa gareki" ya ce daga bakin ƙofa ya juya ya fice daga ɗakin.
Shiru duk su kayi babu abin da ake ji a falon se shesshekar kukan hajiya wanda maimakon ya sanyaya zuciyarta ƙara rura wutan ƙiyayyar Amatullah da mahaifiyarta kawai yayi..
Sun zauna fiye da mintuna goma sha biyar kafin Saifullah ya samu ƙarfin tashi ya bar ɗakin sakamakon kiran Sallah da aka yi.
Jiki a sanyaye ya bi jam'i ya koma ɗakin sa, duk wani notin tunaninsa ya kwance akan mafita kafin can da kyar ya tuna da ai dama kiran gaggawa aka yo masa ya dawo, kuma kullum hanyar da aka hau ta nan ake sauka.
Ji yayi kamar ya jawo lokaci zuwa tsakankanin magariba da isha'i da iyayensa kan zauna.
***
Tuki ya ke kamar wanda ya ke shirin rasa ransa da gangan, zagi kuwa ya sha ba adadi a haka har Allah ya isar da shi gidan da su ke zaune. Nan ma fitowa daga motar ne ya gagare shi, kansa ya kifa bisa sitiyari ya na mai zubda hawaye. Karar da wayar shi ta ke bai sa ya ɗago ba balle ya duba ya ga wanda ke kiransa har wayar ta katse, aka kara kira karo na biyu, ta sake katsewa. Sai a karo na uku ya dago a fusace da niyar kashe wayar gabada ɗaya. Ko da ya ga number da ke kiran sa tuni ya daga ya na mai faɗin
"Mummy......."
"David na shiga uku David, dama nima na mutu na huta, na ƙara rasa miji! Philemonis dead, my husband is dead!! life is never fair to me!!!!"
Mummy ce ta katse shi cikin ihu da kururruwa wanda hakan ba karamin gigita shi ta yi, cikin tashin hankali ya furta
"Mummy calm down and talk to me, mai ya samu Dady?"
"He is dead, Philemon is dead!"
"Jesussssss"
Cewar Dee yayin da maganar Mummy ya daki kunnan shi a karo na biyu. Kuka da kururruwa jama'a da ya ke ji ya na tashi shi ya daɗa gasgata abin da zuciyar shi ke kokarin karyatawa.
"But why? How? When?"
Tambayar da ya jero mata kenan. kuka ne ya ci karfin ta har ta kasa buɗe baki ta bashi amsa. Tausayin ta ya lullube shi, ya na kukan rashin Amatullah, ashe shi ba rashi yayi ba, Mahaifiyar shi ita ce ta yi rashi babba.
"It's ok Mummy, ki yi hakuri gani nan zuwa"
Ya aje wayar cikin zafin nama ya shiga ciki. Cikin kankanin lokaci ya shirya tsaf, kamar goma daidai ya hau titin da zai sada shi da birnin tarayya.
****
A daddafe Saifullahi ya iya hakurin jiran ayi sallan magariba. Bai ko tsaya azkar ba ya tashi ya je wajen zaman iyayensa ya zauna yana jiran su. Ɗaya bayan ɗaya su ke fitowa nan yake gaida su, amsawa su ke suna mai masa fatan alkhairi a aurensa.
Bai ji dadin fitowar mahaifinsa ba amma sai ya ji sanyi ganin baban Sasa ya fito
"Fitinannen tsoho dole ka yi ƙarfin fitowa sallah tun da ka gama haɗa fitina" ya samu kansa da fadin haka a zuciyar sa duk da murmushi ke kwance a fuskar sa.
"Baban Sasa gara da ka fito dama ina shirin shigowa in same ka ne, wannan makaranta tamu yan bakin ciki ne, sun min kiran gaggawa" yace yana yamutsa fuska kamar wanda aka shiga hakkinsa da gaske.
"Subhanallah! Yaushe ake bukatar ganin ku" Baban Sasa ya faɗi ba tare da ya samu shakku a maganar saifu ba.
"Wai nan da Laraba fa Baban Sasa, ka ga ba samun jirgi zan yi ba gara na kama hanya zuwa Lagos gobe na fara rage zango, domin fara Shirin tafiya, idan na ci sa'a nan da kwana biyu ma zan iya samin jirgi" ya fadi yana mai sinne kai.
"Amma da matarka za ka wuce ko? Ko jiƙa jibge kake tunanin mu ka yi?" Baba Anas ya ce yana ƙara yamutsa fuska cikin takaicin hali irin na ɗansa.
"Anas!!!" Baba Zubairu da Baban Sasa su ka faɗi a tare cikin sigar tsawatarwa.
"Saifullahi zango nawa ya rage maka a Rasha" Baba Zubairu ya faɗi yana kallon Saif.
"Zangon Ƙarshe nake zan haɗa masters ɗina, inshaAllah nan da wata uku na kammala da yardan Allah" yace cike da ladabi, kallon sa Baba Anas yake kamar ya kwaɗe shi.
"Toh madalla, abu ya kawo gangara, tun da buri na ya cika ka je, in ka dawo nan da wata uku sai matarka ta tare inshaAllah" fadin Baban Sasa yana mai mikewa don shiga gida.
"Amma Baba sai ku ta biye masa" Baba Anas ya ce don ba haka ya so ba. Ko ta kansa Baban Sasa bai yi ba illa ya wuce abin sa ya tafi don ya shiga cikin gida Saifullahi na bin bayan sa yana mai cika shi da daɗin baki.
"Ni Anas na rasa irin ka, wai me Mairo ta baka ne? Kwatakwata in dai abin da ya shafe ta ne ko yaranta idonka rufewa yake yi. Ina laifi yaron nan bai nuna rashin so ba amma ita yar gwal din ƙaton arne ta kawo don ta aura. Wallahi ka yi ma kanka faɗa" Baba Zubairu ya ce cikin fushi. Nan duk su ka shiga faɗin albarkacin bakin su akan bakin halin Amatullah da mahaifiyar ta duk da cewa su kansu ma su faɗin sun san ƙarya su ke shirgawa.
***
A bakin mahaifin ta Amatullah ta ji batun tafiyar Saifullahi wanda hakan ba karamin kwantar mata da hankali ya yi ba, domin kuwa idan akwai abin da ta ke fargaba ya bi bayan ranar tarewar ta gidan Saifullahi.
Washagari da safe Saifullahi yayi harama duk da kuwa jirgin sa na zuwa Lagos na yamma ne, gani ya ke zaman jiran lokacin tafiya tsautsayi ne. Sanye ya ke cikin kananan kaya, shuɗin riga mara hannu da shudin wandon jeans yayi kyau kamar bakin bature. Bayan ya sallami Hajiya har zai fice daga gidan ya hangi ɓangaran su Amatullah, Gwaggo ce ta ratsa zuciyar sa, ya tuna alkhairin ta gare shi kuma ya san tabbas idan ya je yiwa Baban Sasa sallama sai ya tambaye shi ko ya shiga wajan amaryar ta sa ta dole, dan haka ya yanke hukuncin shiga ba dan komai ba ko dan darajar Gwaggo.
'Allah ka min katangar karfe da ganin bakar fuskar yarinyar nan!'
Addua'ar da ya ke yi kenan yayin da ya nufi bangaran su Amatullah. Da sallaman shi da shigar shi falon lokaci daya ya yi su, tsayawa yayi baki bude tamkar wani soko sanadiyar abinda idanun sa yayi tozali da shi, Amatullah ce kwance a bisa kan doguwar kujera, irin wannan kwanciyar na rigingine. Bai san sanda ya bi ta da kallo tunda daga dogayen yatsun kafarta, har zuwa dogon wuyar ta, zuwa kanta da ke daure da kallabi ba, Yayinda bugun zuciyar sa ta karo cikin kaduwa da ganin baiwar ubangiji. Sanye ta ke cikin koran materials riga da siket, da ke Amatullah mashaAllah akwai diri, kayan ya zauna jikin ta ya yi mata cif cif. Littafin husnul muslim ne kife a kirjin ta, hawayen da ke gangarowa daga idanun ta da yake a lumshe ne ke nuna alamun ba bacci ta ke yi ba. A hankali ya furta
"Hasbiyallahu wani'imal wakil"
Hakan yayi daidai da fitowar Gwaggo daga dakin ta, ganin yanda Saifullahi ya shagala ya na kallon Amatullah wacce daga ganin alama ba ta san da shigowar shi ba, da niyyar Amatullah ta farga ta furta
"Ah ah Saifullahi shirin tafiyar kenan!"
Jin haka a zabure Amatullah ta bude Idanun ta su ka yi ido hudu da Saifullahi wanda yayi tsaye bakin kofa. A rikice ta tashi da sauri ta nufi dakin ta, Saifullahi kuwa ganin Gwggo bai sa ya fasa bin ta da idanu ba har ta shige daki.
"Saifullahi ka na ji na kuwa?"
Gwaggo ta sake magana a karo na biyu ta na mai duban Saifullahi wanda sai a sannan ya lura da fitowar Gwaggo, cike da jin kunya ya durkusa har kasa, yana mai sosa kyeya ya furta
"Iyye? Na'am Gwaggo barka da asuba, ai ban ga fitowar ki ba ne"
Gwaggo na murmushi ta ce
"Eh gaskiya dai ba ka gani ba, cewa na yi shirin tafiyan kenan"
"Eh Gwaggo, dama sallama na zo na mi ki, sai Allah ya dawo da ni"
Ya bata amsa a takaice domin kuwa Allah Allah ya ke ya fita daga gidan tsabagen kunyar da ya rufe shi. Kamar wanda ya ke kan ƙaya yayiwa Gwaggo sallama a gaggauce ya fito. Haka ma Baban Sasa, sallamar a tsatsaye aka yi ta domin kuwa sam ba ya cikin hankalin sa.
Cikin ikon Allah ya samu motar da zata kai shi Kaduna tun kafin ya isa tasha saboda fitowar direbobi masu lodin Kaduna Abuja.
Gidan baya ya shiga a cikin Sharon ɗin da ya samu. Wayar sa ƙirar Sony Ericson ya ɗauko yana karanta abu a yana gizo duk don ya cire tunani a ransa amma ina, maimakon ya ga rubutu, surar Amatullah kawai ya ke gani a fuskar wayar sa.
Yana jin ana faɗin mata masu mazauna da dukiyar fillo bai taɓa haɗuwa da wanda nata su ka zauna daidai da jikinta ba.
Lumshe ido yayi maimakon ya bar gani sai hango ta yayi kamar ta nufi shi cikin murmushi.
"Yaa Rabbi" ya samu kansa da neman agajin Ubangiji.
[2/15, 3:53 PM] +234 814 945 8522: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA GOMA SHA HUƊU
Amatullah da tun bayan fitar Saifullah gaban ta ke faɗi, ta san tsayuwar da yayi kallon nan na kaskanci ya ke mata. Ta ji haushin ganin ta da yayi a haka. Kirjinta ne ya mata nauyi duk da ba ta son tuno halin da Dee zai kasance abin ya gagara.
Saboda kwallafa rai har mafarki ta yi ya zama gawurtaccen pastor hakan ya sanya ta tashi da nannauyyar ƙirji.
Tun da ta yi sallah ta yi azkar ɗinta na safe ta ke karanta addu'ar da ake lokacin ƙunci da damuwa, can dai ta Hau kan kujera ta miƙe baya. Rashin jin dadin kwanciya da hijabi ya sa ta cire ashe za ta yi mummunar gamo ne.
Sai da ta tabbatar da ya fice da daɗewa ta sanyo hijabinta don zuwa gaida iyayenta a cikin gida.
"kuma in kin shiga ɗakin hajiya ka da kiyi gaggawan fitowa, yanzu banda Kasancewar ta matar babanki uwar mijinki ce, saura kije kina soliɓiyanci" ta tsinkayi mahaifiyarta na faɗi yayin da za ta bar ɗakin.
Haka kuwa aka yi, sai da ta gaida sauran ta shiga ɗakin hajiya. Sai da ta zauna a ƙasa sannan ta gaida ta cike da ladabi. Hango hawayen Saifullah da hajiya tayi ne ya sa ta kauda ido gefe ba tare da amsawa ba. Sai da ta yi zaman mintoci sannan ta Mike don gaida Baban Sasa.
A nan ta iske wasu daga cikin Baffaninta ta gaida su kafin ta isa kusa da baban Sasa kamar za ta shige jikinsa.
"Jiya ban ganki ba, nace har kin fara kewan na ainihin ne" yace cikin sigar tsokana.
Sinne kai ta yi tana dariya sannan tace
"Ai zan dinga ganin fuskarka kullum a tashi fuskar in maka addu'a da ka zaɓa min baƙin bature, nagartacce tsatson Muhammadu Jamoh" ta ce tana kwantar da kanta a jikinsa.
"Ki yi hakuri kinji. Ke kin san shi ma, hajiya Sahura ba ta san ni ba sai bayan ta tare, hajiya Talatu na haka, kadarko ce kawai mu ka yi soyayya kan aure.
Kinga a tsawon zaman mu da su ban taɓa ganin halittu mafi soyuwa a gare ni sama da su ba. Ki zama nagartacciyar mata soyayya zai zo daga baya. Ki yi hakuri ki yafe min... "
" shisssssssssssshhhhhh!!! " tace tana rufe bakin sa.
" Babu abin da ka min sai gata da kauna. Ka tabbatar min da duk cikin zuri'a ni ce ta ƙasan heart" ta ce tana dariya, shi ɗin ma dariya yayi.
***
Tun isar sa Abuja jiya da azahar ya ke rarrashin Mahaifiyar shi, mijin na ta ya mutu ne irin wannan mutuwar fuji'a, babu ciwo aka wayi gari babu shi Allah ya ma sa cikawa. Alhinin mutuwar da kuma shirye shiryen bikin birne mamacin bai bashi daman zama yayi tunanin Amatullah ba, duk da kuwa zafin rashin na ta ya zame masa tamkar gyambo cikin zuciyar sa.
A safiyar aka shirya mamacin tsaf cikin riga da wando suits, kwance cikin akwati da ya sha ado da furanni iri iri. Akalla motoci uku ne su ka jeru wajan rakiyar mamacin, in da Dee ke tuka motar da ke dauke da Mamacin, hanyar Yola su ka dauka in da za a yi bikin birne mamacin.
****
Igiyar auren Saifullahi bai hana Amatullah tunanin Dee ba, wanda hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali ya ke ba, ta na matar aure ta na tunanin wani namiji daban, har ta na duba wayar ta ko za ta ga sako ko kira daga gare shi ya shigo. Ganin hankalin ta na shirin gushewa ya sanya ta ɗauro al'wala, sanye da hijabi ta kalli gabas, da kyar ta iya idar da raka'a biyu. Tun tana addua a hankali har kuka ya ci ƙarfin ta ta fara addua a bayyane, tana cewa
"Ya Allah ka rufa min asiri, ya Allah kar ka kamani da laifin soyayyar da na ke yi wa wanin mijina, ya Allah ka yaye min wannan masifar