Showing 9001 words to 12000 words out of 98809 words
Chapter 4 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
gaban hijabinta a jike da hawaye ba saboda ita kanta ba ta san iya lokacin da ta ɗauka tana zubar kwalla ba. Mamaki, Farin ciki, Nadama su ne su ka cika ƙirjinta. Ba komi ya bata mamaki ba sai kalaman Dee Yusuf don su ne abu na ƙarshe da ta yi tsammanin ji daga bakinsa. Kalaman sun sanya ta farin ciki don tun bayan kalaman Saifullah ta sadakar babu namijin da ke mata kallon mace mai daraja, don har ta danganta rashin samun mashinshini da kasancewarta bagidajiya.
Ta Yi Nadama ba ko kaɗan ba don ba tare da ta san waye Dee Yusuf ba ta alakanta shi da mutum mara kamun kai, tambaɗaɗɗe kawai don ya taɓa ta.
'Kuma ai yana rungume mata' wata sashi na zuciyarta ce ta nemi kare ta. Amma hakan bai hana nadama cika zuciyarta ba.
Da wannan yanayi ukun ta haɗe kayanta ta kama hanyar hostel, kalaman Saifullah yayin da ya ke kiranta bagidajiya, baƙauyiya cikin murya mai cike da ƙyama su ka dinga dawo mata a kwanya yayin da take tafiya, bakinciki na gaf da mamaye mata zuciya ta jiyo muryar Dee Yusuf daga can ƙasan zuciyarta yana faɗin.
'Hijabi ko suturta jiki abu ne mai muhimmanci ga addini, abu mai daraja shi ake suturtawa, fitar da tsaraici shi ne kauyenci da gidadanci Mama nah, hijabin ki abun sha'awa ne ga duk wanda ya san darajar diya mace'
Wannan ya bata ƙwarin guiwar ƙarasawa ɗaki cikin farin ciki, tasbihi take tana mai gode ma Allah da ya jefo mata Dee Yusuf cikin rayuwa. Tana shiga ɗaki ta yi wani murmushi tare da faɗin
"Saifullah ba zan auri malamin Allo ba, amma za ka raina kanka in ka ga mijin bagidajiya, Mark my words, today 28th April 2009" Dariya ta yi bayan ta ankara ga kanta take magana ba wai Saifullah ba. Nan ta shiga yi ma kanta dariya tare da jin takaicin kanta.
'Ta ya ma na fara wannan tunanin?' ta tambayi kanta a zuciya tana mai jan tsaki, take sai ta sake kwashewa da dariya tana fadin
"Oh! Su Amatullah, watau daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi" kan gado ta kwanta hannayen biyu ta sa ta rufe fuskar ta cike da kunya da yanayi na jin dadi yayinda ta ke yiwa kan ta dariya
[1/13, 10:29 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA BIYAR
Haka ta ƙarasa yininta cikin matsanancin farin ciki, wanda ya kasa ɓoyuwa ga Zulaikha da ta shigo ɗakin daga baya.
"mutumiyas me muka samu ne" ta tambayeta bayan sun zauna cin abinci. Kallon ta Amatullah ta yi cikin murmushi ba tare da cewa komi ba, sai da ta cinye ɗanwaken ta, ta sha ruwa sannan ta kalli Zulaikha tace
"Ɗazu kin ishe ni me ke damu na, yanzu kuma kina me muka samu, ɗazu ina cikin yanayin tuna mutuwa yanzu kuma tunawa nayi da ɗimbin rahmomin ubangiji da ya tanadar ma duk macen da ta kiyaye dokokin Allah tun daga shiga, mu'amala da ibadunta sai na ga in Allah ya yarda mun shallake" ta karanto mata yayin da zancen Dee ke mata echo a zuciya.
"Ubangiji Allah ya sa mu dace, ciwon Baban Sasa ya sa ki tunawa da mutuwa, Amatullah ciwo ba mutuwa bane, sannan sau da dama jinya kan zama Rahama ga bawa. Insha Allah zai ji sauki" Zulaikha tace cikin sigar rarrashi, faɗin haka ya sanya wasu zafafan hawaye gangarowa daga idon Amatullah, ba don komi ba ambaton Baban Sasa ya sanya gaba ɗaya Amatullah ta tsinci kanta cikin yankewar kauna daga samun wani miji bayan Saifullah da ya ke kallon ta a matsayin kazanta.
Hakuri Zulaikha ta cigaba da bata, tana faɗi mata kissoshi da jinyoyi su ka zama Rahama ga bawa, ciki har da kissan Annabin Allah Annabi Ayyuba Alaihis salam, wanda ciwo ya ci shi ya ci shi ya zama babu abin da yake faɗi sai RABBI INNIE MASSANIYAD-DURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEEN kuma Allah ya amsa masa ya bashi lafiya kamar ba wanda ya yi jinya ba.
Kalaman Zulaikha sun yi tasiri wajen tuna mata da girman Allah, da kuma kasancewarsa maji rokon bawansa.
***
Washe gari sun tashi kamar kullum, shirin zuwa ɗaukan darasi su kayi sanye da hijabansu, Amatullah ta fita cike da buri da addu'ar ɗaura ido akan Dee Yusuf, har sun shirya fita ta tuna da karin maganar hausawa na 'idan kana da kyau ka ƙara da wanka' nan ta ɗauki kwalli ta sanya ta ɗan shafa hoda kaɗan, ganin kallon da yan ɗakin ke mata ya sanya ta fadin
"Fuskar ce naga duk naso, kar a ce ina shafa mangyaɗa" nan suka sanya dariya suna tsokanar ta.
"Wallahi an ci amanar kyau, yanzu wai haka kike kyakkyawa amma kike sakaci" Salma Ateeku ta ce, nan su ka sa dariya.
"Anty Sophie Wai haka" tace tana kallon kawar salma da suke zaune tare Safiyyah Jibril amma anty Sophie su ke ce mata.
"Sosai Amatullah, kin yi kyau sosai, ga lip balm can ki sanya, you look so cute and take away" Anty Sophie tace cikin jinjinawa. Da haka suka fice zuwa aji, sun kammala na farko suna zaune zaman jiran wanda za su shiga ƙarfe goma sha biyu ne Maman Jafar ta ja su zuwa community market tana son duba ma Jafar dinta drawing book. Tafe suke suna hira kamar ko yaushe, tun daga nesa ta hango shi tare da yan mata biyu daga ganin shigarsu za ka ce arna ne ko kuma marasa kishin jikin su, ta gefen sa kuma wani namiji zaune cikin shigan English wears, zaune suke gefen Faculty of engineering irin zaman nan nane da juna, akan idonta ɗaya ta saka hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro kudi saboda sanye yake da kaftani da wando har ma da hula kalan sararin samaniya.
Ba ta san me ya tokare mata a kirji ba, hakan ba ta san sanda hawaye su ka gangaro mata ba, hannu ta sa ta share, Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa yana ɗaga ido sai ga ta gaban shi, sun hada idanu. Kauda da fuska tayi ta cigaba da magana duk da kirjinta bai fasa mata nauyi ba, da haka su ka isa Com market.
A ɓangaren Dee Yusuf kuwa bai taɓa zaton ganinta a wannan lokacin ba duk da dai ba wai ya ɗauki ganin shi cikin course mate din shi da ta yi ba a matsayin laifi, sai dai yanda ta ga daya daga cikin su na zarar kudi daga aljihun shi ta karfi da ya ji ne da kuma yanayin da ya ga fuskar Amatullah ne bai ma sa dadi ba.
Yunkurin tashi yayi don bin ta nan wayar sa ta ɗauki kuka, ganin mahaifiyarsa ce ya sanya shi ɗauka cikin ladabi.
Gaisheta yayi tare da tambayar lafiyan Ahlin gidansu.
" Gawar Baffanka Haruna na hanya, tun da karatun bai yi zafi ba ka kamo hanya don kar ka rasa janaza" tace cikin sigar Alhini, tunawa da mutuwar Baffan nasa yayan mahaifinsa ya sa shi sanyin jiki.
"Mummy ya wajen su mimi toh, bana son na tuna mutuwar nan fa" yace cikin dauriya, mimi autan mai rasuwa ce da kowa ya shaida shaƙuwarsu.
"Sun je tarbo shi, ya aka iya abin da ake jira kullum" ta fadi tana mai kara nanata masa mahimmancin zuwansa janaza.
Anan yayi sallama da abokansa tare da fada masu zai wuce Kano ya kwana washegari ya wuce garin su Don halarta makoki da janaiza.
Ko da su ka juyo don komawa in da za su yi darasi. Su ka iske babu Dee Yusuf a wajen, nan Amatullah ta kara cika da takaici don a lokacin ta tabbatar da cewa shi ɗin ba wai ya dauke ta yanda take tunani bane.
Tun daga ranar take sa ran ganinsa tare da sa ma ranta duk suka haɗu sai ta masa tambayar dalilinsa na rashin bin dokokin ubangiji, sai ta tambaye shi me yasa ba zai dinga rungumar garwashin wuta ba akan ya dinga rungumar matan da ba muharramansa ba?
Kamar ya san abin da ke ranta ya ɓace ɓat, tun tana ƙirga kwanaki har aka yi sati ɗaya ba ta ganshi ba, haka ta cigaba da zuwa ɗaukan darasi tare da yin muraji'ar darussan kar ya cunkushe mata, hakan kuma bai hana mata tunanin Dee Yusuf ba da son jin dalilin da ya sa ta dena jin sa.
***
Bayan Sallar isha'i, dakin su Amatullah cike da yan kallon series wanda Zulaikha ta saba tara mu sa, tun Amatullah na kokawa ta ce ana hana ta karatu, har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido.
Kwance ta ke bisa daddumar sallah. Ta idar da sallar isha'i kenan ta yi kwance ta na sana'ar ta ta da ta zaman mata jiki kwana kin nan, wato tunanin Dee Yusuf na dalilin bacewar sa da kuma muhawarar da zuciyar ta ke tafkawa na kiran shi dan ta ji lafiya tunda dai Allah ya sa ya rubuta ma ta numbar shi a dan littafin ta. Cikin gargadi zuciyar ta ke ayya na mata
" Toh ke Amatullah ina ruwan ki da shi da har za ki addabi kan ki da tunanin shi? Har ki na tunanin kiran shi don zub da aji?"
Wani bangaran zuciyar ta kuma ta ji an furta
"Menene zubda aji dan ka kula me kula ka? Ai mai kaunar ka ya fi mai kin ka ko yaya ne. Ina laifi idan kin kira kin ji ko lafiya? Idan kuma wani mummnan abu ne ya same shi fa? Irin haka ne sai dai kawai ka ji an wayi gari babu mutum, mutum ya mutu....."
Firgit ta yi ta tashi tsaye jin batun mutuwa, da saurin ta ta nufi jakar ta, littafin nan ta dauka tare da zare wayar ta daga jikin chaji, su Zulaikha na tambayar lafiya? Ina za ta je kuma? Amma ina nuni kawai ta yi mu su da hannu alamar tana zuwa, ta fice. Waje mara hanayi ta samu daga waje, hannu na rawa ta kwafi numbar cikin wayar ta. Sai da ta gama kwafewa tas sai kuma ta kasa danna kira. Da kyar ta sami karfin gwiwar dannawa amma kafin ya fara ringing ta yi sauri ta katse. Ta na mai dafe kirji saboda tsabagen faɗuwa da ta ji gaban ta na yi ta dan takaita kusan mintin ta biyar cikin wannan hali, sannan ta kara kiran numbar cikin ikon Allah sai gashi ya fara ringing. Jin wayar ta kusa katsewa ba tare da an daga ba ya sa ta sakin ajiyar zuciya, hakan yayi daidai da daukar wayar yayinda ta jin muryar shi ya daki dodan kunan ta ya na mai fadin
"Hello?"
Maimakon ta amsa, sai tsuntar kan ta tayi ta na mai runtsa idanu.
"Hello? Who is that please? Wanene?"
"Amatullah"
Ta fada cikin rada yayinda ta ci saukar numfashin sa daga dayan bangaran na alamun ajiyar zuciya.
"Amatullah....."
Ya sake maimaitawa.
"Kin dauki tsahon lokaci kafin ki kira ni ba, har na fara fidda rai Mama nah...."
Shiru Amatullah ta kasa magana, ji ta yi kamar an daure bakin ta. Be gushe ba ya kara da
"Kin ji ni shiru ko? Tafiya na yi an mana mutuwa ne na tafi jana'iza gida amma gobe zan dawo tunda kin kira ni"
"Allah sarki waye ya rasu?"
Ta tambaya a takaice.
"Baffan mu ne"
"Allah ya ma sa rahama"
"Ameeen Mamanah, thank you very much for the prayer"
"You're welcome"
Ta kara amsa ma sa a taikace. Sai kuma ta yi shiru. Cikin zolaya ya furta
" Shin akwai abun da ya kamata ki fada min"
Cikin tsarguwa kardai ya dago jirgin ta na tunanin shi da ya mamaye zuciyar ta ta furta
"Eeeeh? Na'am? Dama CHEM 132 na kasa ganewa....."
"Are you sure shi kaɗai ne?"
Ya katseta cikin zolaya. Ta na wasa da yatsun kafar ta, cikin jin kunya ta ce
" Shi kaɗai ne"
"Toh Mamanah Allah ya kai mu gobe da na dawo zan kira ki sai mu sami lokaci da wajen bita ko?"
Maimakon ta amsa masa sai ta tsinci kanta ta na gyada kai alamar "eh" sanan ta kara da
"Na gode sai da safe, Allah ya kawo ka lafiya...."
"Ameeen ameen"
Cewar Dee Yusuf, ta na shirin katse wayar ta ji ya furta
"Amatullah"
Har cikin zuciyar ta taji kiran, a hankali ta furta
"Na'am"
"I've missed you so much"
Kasa bashi amsa ta yi, fuskar ɗauke da murmushi ta katse wayar. Hannu biyu ta sa ta rufe fuskar ta.
[1/15, 11:38 PM] Khadija Sidi Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA SHIDA
***
Kusan mintuna talatin ta yi nan zaune ta na ta sakar zuci, kafin daga bisani ta koma ɗakin zuciyar ta cike da farin ciki.
Washegari kamar yadda ya ma ta alkawari ya na dawowa ya mata waya domin shaida mata ya dawo. Babu damar zuwa library, ɗaya daga cikin ajin su Amatullah su ka zaɓa in da su ka yi za su hadu bayan la'asar.
Amatullah ta so gayyatar Zulaikha zuwa karatun amma ta nuna mata ita ba ta da bukata, babu laifi ta na gane course din. Ranar wuni tayi tana duba lokaci. Tana idar da sallar la'asar duk da marar ta na mata ciwo alamar ta kusa fara al'adar ta, hakan bai hana ta fara shiri ba. Atamfa ta sa fara Mai adon koran ganye. Dinkin ya zauna a jikin ta ya mata cicif da ke Amatullah irin matan nan ne da Allah ya ma sura mai kyau. Wata kawar Zulaikha da ta shigo dakin wacce tun da Amatullah ta sanya atamfar ta ke bin ta da kallo ta kasa daurewa ta ce
"mashaAllah wannan jiki na ki Amatullah, gashi kullum ki na cikin hijabi abin ki dan kuwa da mazan makarantar nan zasu gan ki babu wannan hijabi ai da an sami matsala"
Kafin Amatullah ta bata amsa Zulaikha ta ce
"Da hijabin ma makaleta su ke, ba ki ga yanda Dee....."
"Zulaikha!"
Amatullah ta katseta cikin gargadi. Kafada Zulaikha ta daga ta sauke tare da fadin
"Toh baki na kanin kafata"
"Ya dai fi mi ki sauki, kun ga tafiya ta ni"
Hijabin ta ta zura, ta na jiyo kawar Zulaikha na tambayar wani Dee ta ke nufi, cikin ran ta ta ce kwa dai ji da shi. Tun daga nesa ya hango ta tafe. Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin jamfa, tsaye gaban ajin da su ka yi za su hadu, jingi ne jikin bango kafafun sa harde, hannun sa biyu cikin aljihun sa. ya kura ma ta ido tamkar karo na farko da ya fara ganin ta kenan. Komai game da Amatullah birge shi ya ke. Kamannin ta, kamalar ta, tafiyar ta, muryar ta........
"Salamun'alaikum"
Muryarta ce ta katse masa tunanin da ya ke, fuskarsa cike da murmushi ya furta
"Wa'alaikum salam Mama nah, na yi kewar wannan muryar Mama nah"
Murmusawa ta yi cike da kunya ta ce
"Ka dawo lafiya? Ya hakuri kuma?"
Baki bude ya ke kallon ta har sai da ta tsargu, ta ce
"Lafiya me ya faru?"
"Murmushi? Ni kike ma murmushi Amatullah? Ahhh my ancestors will be proud of me o!!! I've made it in life!"
Dariya Amatullah ta ke sosai ta ma kasa bashi amsa. Dee Yusuf ya kara da
"Alhamdulillah Mama nah, hakuri mun gode Allah. Ina san dariyar ki, dan Allah kar ki dena"
Ganin dai idan ta biye shi nan za su tsaya ya ta sakin baki ta daga littafin da take dauke da shi tare da furta
"Our tutorial Sir?"
Ya na mai murmushi ya nuna mata hanyar shiga anjin ya na mai furta
"Yes Ma'am, Lady first"
Cikin jin kunya ta wuce gaba, ya na biye da ita su ka shiga ajin. Mutane kalilan su ka tadda ciki, hakan ya ba su damar yin karatun cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Dee Yusuf ya iya koyarwa kwarai da gaske tamkar dama sana'ar shi kenan. Wajan awanni biyu ya dauka ya na koyar da ita har sai da aka kira magariba ya ce da ita.
"Toh Mama nah ya kamata mu tsaya anan ko? Kin ga lokacin sallah yayi"
Kai ta gyada masa alamar "eh" cikin ranta kuwa cewa ta yi ka dai je ka yi sallah, ni kam Allah ya kawo min sauki yanzu yanzun nan. Har kofar hostel ya rakata, ya tsaya su yi sallama Amatullah ta ce
"Kar na sa ka yi missing sallah, na gode gwarai"
Yana murmushi ya ke duba agogo, kana ya ce
"Ina fatan dai kin gane?"
Kai gyada alamar "eh" sannan ta kara da
"Sai Allah ya kai mu gobe?"
"Toh Mama nah, sai anjima"
Sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta shige hostel zuciyar ta cike da annashuwa, da a ce Dee Yusuf ne Malamin su ai da ba haka ba.
***
Bayan sati biyu, zaune su ke a ajin da yan Agric Education ke ɗaukan darasi a can sashin horar da malamai (Faculty of Education), Jakanta ne su ka sanya marabi tsakaninsu, bayanin Bond yake mata yadda ba a taɓa mata ba, fahimtarsa take cikin haddacewa. Kallonsa ta yi tare da fadin
"me ya sa ka zaɓi anatomy maimakon chemistry? Ban taɓa ganin wanda koyar da chemistry ya ma kyau ba sama da kai"
Murmushi ya bi ta da shi, sanyin muryarta na ratsa shi.
"Ni kuwa menene sirrin muryar nan taki, zan so jin sa yana mai rera waƙa" yace yana basar da tambayar da ta yi masa.
"Ayya mana Yusuf, maimakon ka so jin ayoyin Allah da muryar" dariya yayi cikin basarwa ya ce
"Kuma fa, yauwa dama akwai abin da nake so na fada miki" ya ƙarasa cikin tattaro duk wani natsuwa na shi, nan gabanta ya shiga faɗi cikin sauri, bata shirya ma jin maganar ba duk da ya daɗe yana cewa za su yi, kullum ya ce sai ta kawo dalilin fasawa yau ba ta san me za ta ce masa ba.
"Uhmm ina jin ka" tace masa, duk da ta san zancen bai wuce na tona asirin zuciyarsa wanda ƙwayar idanunsa sun daɗe da tonawa.
"Amatology 10CU"aka ce daidai san da ya ɓude baki da niyyar magana.
Hamza ne ya bayyana gaban su, sanye cikin riga mara hannu da wando wanda be kai har kasa ba. Amatullah ya tsurawa idanu, idan ya san da Zaman Dee Yusuf be nuna alama ba. Cikin kokarin boye rashin jin dadin ganin sa Dee ya ce
" Amatullah meet