Showing 84001 words to 87000 words out of 98809 words

Chapter 29 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

shi ma Dee ya lura da hakan dan haka sai ya mata sallama ya tafi.


Saifullahi kuwa bangaran sa ya wuce da Emjay, ya na shiga tsakar gida ya ci karo da kwanukan wanke wanke fal tsakar gida, daga gani an san kwanukan tun na jiya ne, kudaje ke bi gashi warin ruwan wanke da ke aje cikin kayan wanke wanke ne ke tashi. Dama ya kwaso bakin cikin Amatullah da Dee Yusuf. Jikin sa har rawa ya ke tsabagen bacin rai,


"Aisha! Aisha! Aisha!"


Ya shiga kwalla mata kira da ƙarfi har sai da Emjay ya tashi daga bacci ya sa masa kuka. Amatullah da ta biyo sahun ɗan ta da sauri ta nufi bangaran Saifullahi jin kukan Emjay, shigar ta yayi daidai da fitowar Aysuh sanye cikin rigar bacci, wanda hakan ke tabbatar ma sa har lokacin ba ta bar gadon ta ba, bare a yi maganar yin niyar wanka da gyaran gida, bare uwa uba girki.


Wani irin kallon tsana karara ta ke yiwa Saifullahi da Amatullah, yayinda Amatullah ke kokarin karbar Emjay. hannu bisa kugu Ayush ta ce


"Malam lafiya? Wannan wani irin wulakanci ne za ka shigo min da tsohuwar matar ka gida ka na kwalla min kira haka kamar sakarai?"


Bakin ciki da kunyar yanda Aysuh ke masa magana gaban Amatullah babu da'a bare tarbiya, ya ce


"Aisha ni ki ke yiwa magana haka?"
Amatullah da ta samu ta karbe ɗan ta gaba ta yi ta bar su nan tsaye Saifullahi na mai kumfar baki, ta na jiyo Aysuh na faɗin


"An maka din! Akan wani dalili za ka kawo min tsohuwar matar ka gida? Ka kawo ta ne ta ga yanda ka ke kuntata min?"


A fusace ya ce
"Waya ya damu da ke da har zai kawo wata gurin ki? Why? Me ya sa ki ka cika lalaci ne? Why are you so dirty? God ban taba ganin kazamar mace kamar ki ba Aisha! Ace tun safe rigar bacci ne jikin ki? Kalli tsakar gidan ki kaca kaca! Wanke wanke fal guri! Kin mike kafa ki na ta baccin asara!"


Yatsune ta yi, cikin halin ko in kula ta ce
"Gidan da ka dauko ni ko tsinke ba na daukewa, diyar hutu ce ni ka sani sarai ka san in da ka ɗauko ni! Ni ba baiwa ba ce bare yar aiki! Nan su Naja'atu suna shigowa suna taya ni aiki kai da Hajiya ku ka haɗa baki ku ka hana su, saboda haka idan ya maka ciwo kai ma kana da hannu ka gyara! In kuwa ba ka iyawa sai ka yiwa Hajiya magana ta zo ta gyara ma....."


"Shut up!!! Mahaifiyar tawa ce za ta zo ta gyara mi ki gida? Ashe ba ki da mutunci Aisha?"


Ya katse ta cikin tsawa. Kallon sa ta ke a wulakance ta ce


"Wallahi na yi da na sanin auren ka Saifullahi, dan haka a yau da za ka sauwake min ba ƙaramin farin ciki zanyi ba....."


"Na sauwake mi ki? Haka ki ce?"
Ta na murguda baki ta juya da niyar komawa daki, wani irin wari ne ya buso su sanadiyar iskar da ta kado ruwan waken da ke wajan wanke wanke, Saifullahi yayi saurin ja da baya yana mai toshe hanci, ita kanta Ayush sai da ta rufe hancin ta, murya kasa kasa ta ce


"Hmmmm Hajiya ta yi hamma!"


Hakan ya sa Saifullahi harzuka dan kuwa ya so ya ji abun da ta ce
"Ke! Me ki ka ce? Me ki ka ce Aisha?"
Daki ta shige ba tare da ta amsa masa ba, cikin masifa da bambami kamar wanda ya zautu Saifullahi ke faɗin
"Da mana ki maimaita! Ashe ke maraya kunyar karya ce! Ki maimaita mana! Da yau na tattaka ki, sakarya wacce ba ta san darajar iyayen ta ba!"


Baba Anas ne ya zo wucewa, jin muryar Saifullahi ya na bambami ya sa ya ɗan tsaya, ya lekoshi tare sa faɗin


"Saifullahi a na yin hakuri, zama da mata ai sai da hakuri, amafanin dace da kamular mace kenan ai Saifu"


Yana maganar ya wuce abin shi ba tare da ya jira amsar shi ba, dama shi ma Saifullahi da ya san magana ya faɗa masa bai da niyar amsa masa. Ciki ya shiga ya nemi su Naja'atu ya ce su zo su gyara masa gidan dan ko ruwan gidan ba zai iya hadiya ba muddin ba gyarawa aka yi ba.


*****
Washagari a makaranta tun safe Amatullah da Mimi su ke fafutukan lectures, duk da tun safe jikin Emjay ya ki dadi, kuka ya ke mata na babu gyara babu dalili gashi ya ki shan nono. Sai da ta goya shi yayi bacci sannan ta samu sauki. Kusan minti ishirin yayi ya na bacci, suna gaban notice board suna kwafar timetable da aka canza kawai ta ji ya na mimmike mata a baya.


Cikin damuwa ta ce da Mimi
"Mimi kin ga yanda Emjay ya ke mimmike min a baya, ina ga yaran nan be da lafiya dan Allah kama min shi na kwanto shi"


Mimi ta amsa da "toh" yayinda Amatullah ta sauko da Emjay da tuni ya gama mimmikewa kamar mai shirin suma. Ganin haka Amatullah ta


"Na shiga uku me ke damun yaron nan haka!"
Mutanan da ke kusa da su duka hankalin su ya koma kan Emjay, nan aka zagaye su in da aka basu shawarar kai shi asibiti da gaggawa. Dan ajin su Amatullah ne ya karbi Emjay, ya wuce gama Mimi da Amatullah na biye da shi. Allah ya so nan cikin department ya aje motar shi, ko da su ka shiga motar Mimi ta karbi Emjay dan kuwa Amatullah jikin ta har rawa ya ke tsabagen tashin hankali, ba tare da bata lokaci ba su ka wuce asibiti.


Yanda Emjay yayi wata mika tare da sauke numfashi ya sanya Mimi ta san rai yayi halin sa, amma ta kasa faɗawa Amatullah. A haka su ka isa asibiti. Haka shi ma ɗan ajin na su da ya dauki Emjay bayan da su ka isa, ya ji ya kara nauyi ga idanun sa sun kafe ya san Emjay kam ya kare, kallan Mimi yayi in da ta gyada masa kai. Haka jiki babu sanyi su ka shige asibitin, Amatullah da ba san halin da ake ciki ba tuni ta yi gaba da saurin ta.


Suna isa emergency tun kafin Doctor ya taba shi ya ce da su
"Ku yi hakuri, yaran nan ai ya cika....."


Cak Amatullah ta tsaya ta na kallon Doctor, kafin daga bisani ta mayar da kallon ta ga gawar Emjay da ke kwance gaban su, a hankali kamar mai rada ta ce


" Ko taba shi ba ka yi ba ka ce ya cika? Haka ku ke aikin asibitin? Bai cika ba Doctor, duba ka gani ai suma yayi fa, dan Allah ka tayar da shi......"


"I'm sorry Madam"


Ganin yanda Amatullah ta dauki gawar Emjay ta na mai rungume shi a kirjin ta, ya na kallan Mimi ya kara da


"ina ga zai fi kyau ku tafi da su gida, she is in shock".


Shi kan shi dan ajin na su ya tausayawa Amatullah, bare Mimi da Emjay ya zame mata tamkar dan cikin ta. Dan ajin na su ne ya ce zai kai su gida, amma har lokacin Mimi ta kasa tabuka komai, bare uwar gayya Amatullah da ta rungumi gawar dan ta tana mai raba idanu. Mimi na share hawaye ta ce da Amatullah


"Amatullah"
Karo na farko da ta Kira sunan ta kenan, maimakon ta amsa mata, kawai sai ta zuba mata idanu. Mimi ta ce


"Tashi mu tafi gida"


"Mimi bai mutu ba, Emjay bai mutu ba, dana bai mutu ba, ku kai ni wani asibitin wannan ba su san abun da su ke ba"


Hawaye ne me zuba daga idanun Mimi, ta ma kasa magana sai kawai ta ruko Amatullah ta na kuka. Da kyar dan ajin na su ya shawo kan Mimi, ta taimaka su ka samu Amatullah ta shiga mota. Mimi ce ke nuna masa hanyar zuwa gidan dan kuwa tun da Amatullah ta shige gidan baya dauke da gawar Emjay, ba su kara jin ko tarin ta ba, idanu ta tsurawa gawar har su ka isa gida.


A kofar gida ta tarar da Saifullahi, daga ganin alama fita zai yi. Ganin shi Amatullah tun kafin su faka mota Amatullah ta bude murfin motar, dan haka dole dan ajin na su ya tsaya nan tsakiyar hanya, da sauri ta fito gun Saifullahi ta nufa ta na mai nuna masa gawar Emjay ta ke faɗin


"Ya Saifullahi ka ga wannan Doctor din sam be san abin da ya ke yi ba, ya kalli tsabar idona ya ce min Emjay ya cika!"


Kallan ta ya ke tamkar ba hausa ta ke masa ba yayinda yayi kokarin karbar Emjay daga hannun ta amma ta hana shi. Cike da alamar tambaya ya ke duban Mimi da ta biyo bayan Amatullah.


"Me ke faruwa ne? Me ya same shi?
Saifullahi ya shiga jerowa Mimi tambaya. Cikin sanyin murya ta ce


"Sai dai ku yi hakuri, Emjay ya koma ga Allah"


Wani irin razana Saifullahi yayi ya na mai kokarin duba gawar Emjay. Amatullah kuwa cikin gargadi ta ce da Mimi
"Ina ganin mutuncin ki Mimi, kar da ki sake cewa dana ya koma ga Allah! Emjay na nan tare da ni!"


***
Ba da sadaka sai mai tsananin rabo, sai Allah na baiwa wanda ya so zuciyar ba da sadaka.
Azumi ya gabato, muna ta hidimar haɗa kayan abinci da kayan sallah. Su kuma marayu marasa galiho fa?
A dalilin haka gidauniyar Nisaau Ahlil Jannah Charity Foundation wacce aka assasa ta don cigaban marayu ta ke rabon abinci da kayan sallah ga marayu a cikin shirin ta na Ramadan sabil.
Idan zamu sanya kaɗan din da Allah ya hore mana zai haɗu da na wasu ya wadatar wajen ciyar da marayu.


Ku zo mu ba Allah rance, mu samu ladan kula da marayu mu kuma samu ladan ciyar da mai azumi.


Zuba a
0334993079 (Naira)
0334993093 (Dollars)
Nisaau Ahlil Jannah cha. Fdn
Gtbank


Don ƙarin bayani kira su
08157284164
Ko whatsapp
08025968968


Jazakumullahu khairan
[4/21, 10:23 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA UKU


Kasa zama sallahn yayi, shigewa cikin gidan yayi kamar mai shirin tashi sama. Koke-koken mata ya ke ji zuciyar sa na ƙara tsinkewa. Haka ya lallaɓa ya shiga sasansa ya zauna a kujerar falo. Ba komi ke masa yawo a idanu ba sai yanda da hannunsa ya cusa ɗansa a cikin rami, sannan yana kallo aka maida ƙasa aka rufe shi.


Tiryan Tiryan komi ya dinga dawo masa kamar mai bita, tun daga kai ta asibiti don a cire cikin, zuwa haihuwar da tayi bai dire a ko ina ba sai inda ya sheganta ɗansa.


"Yaa Rabbi ka yafe min, Emjay ka yafe min" ya ce yana mai dafa kansa.


"Ai da bin sa ka yi ƙarshen soyayya" Ayush da tun shigowar sa take kallonsa tace tare da jan tsaki. Sai a sannan ya ɗaga ido ya kalle ta haɗe da kula da zaman ta a wajen.


"Ayush Muhammad Jamoh yaro na ya rasu" ya ce mata cikin sigar neman ɗauki, kallonsa take cikin yanayin rainin wayau, ba ta san sanda ta kece da dariyar rainin wayau ba haɗe da ɗiban dambun naman da take ci tare da kai shi baki.


"Wai dama kana da ɗa ne? Ina ce tuni ka yar da kwallon mangwaro" tace masa cikin tuna masa Kalamansa gareta lokacin da ya faɗi mata ya saki Amatullah.


"Aisha!!!"


yace cikin daka mata tsawa, ita kuma tattara kwanon dambunta tayi, ƙara kallonsa tayi ta saki dariya kafin ta shige ɗaki ta rufo ƙofa har da saka makulli.


Ɗumin da yaji na sauka a fuskar sa ne ya sanya shi sharewa, sai a lokacin ya tabbatar da kuka fa yake, kuka akan mutuwar yaron da ya ce ba nashi bane.


***
Dee Yusuf na idar da sallah ya kauce zuwa gefen Baban Sasa saboda sallah da su baba Anas ke yi.


Azkar ɗin da annabi ya koyar na bayan sallan farali yayi, cikin natsuwa wanda hakan ya zama masa jiki tun bayan da aka koyar da shi.


Fara'a sosai Baban Sasa yake yi yana mai jin ƙauna Dee na ƙaruwa a zuciyarsa, Godiya ya shiga yi ma Allah da ya sa hakan ya tabbata.


A kan idonsa Dee ya yi Raka'a biyun da zai cika na sallah, mamaki sosai ya cika Baban Sasa ganin sallah yayi a natse cikin kwarewa.


"Dan Yusuf jika na" Baban Sasa ya ce yana mai shafo shi cike da ƙauna.


"A'a fa, ka ji min tsoho, ni dai jini na kawai zaka bani" yace cikin shaƙiyanci.


"Ja'iri!!!" Baban Sasa yace yana mai kai masa duka.


A wannan gaɓan su ka idar da sallah, baba Zubairu tsam ya tashi ya nufi Dee ya miƙa masa hannu.


"Allah ya ƙara ma rayuwa Albarka, mene sunan" yace masa bayan sun yi musabaha.


"Dawood!" Dee ya amsa cikin farin ciki.

"Dauda dai ko?"


Baban Sasa ne ya tambaya. Dee na girgiza kai ya ce
"Ah ah fa tsohon nan kar ka ɓata min suna, Dawooda ne, haka sunan ya zo cikin alqur'ani, inda Allah ya jero sunayen annabawa 25 acikin suratul An'am, haka kuma suratul Saba'i inda Allah yayi magana akan falalar da ya bawa annabi Dawood, haka suratul Namli in da Allah yayi magana akan ilimin da ya bawa annabi Dawood, haka kuma suratul Saad inda Allah yayi maganar Khalifancin da ya bawa annabi Dawood a doran ƙasa, haka da sauran wajajen ma"


"Ummmmm" "ummmm"


Abin da ke fita daga bakin su kenan jin yanda Dee ke musu bayani cikin nutsuwa da tsari. Dee ya kare da


"A cikin Bible kuma sunan a David ya zo....."


"Allahu akbar! Allah shi ne mafi girma! Allah ya sa mu cika da imanin mu! Allah ya maka baiwa yaro, ka gode masa!"
Cewar Baba Anas cikin sauki da kaunar Dee.


"Bamu labari ma" Baban Sasa ya ce yana mai riƙe masa hannu cike da ƙauna.


Dariya Baba Anas da Baba zubairu su ka yi, yayin da Baba Mahmuda ke yaƙe, Baba Idris da Baba Hamza kuwa zama su ka yi don jin ƙarshen ƙarya.


"Bayan zuwa na gidan nan, na taradda auren Amatullah, lokacin gaba ɗaya na amince da babu addinin gaskiya sama da musulunci.


Zuciyata ba ta karye ba, amma ina barin gidan nan na samu saƙon rasuwan uban riƙo na mijin mahaifiyata, haka na isa gida na tsaya mata a lokacin da ta fi bukatata sannan aka yi makoki da ni.


Bayan kammala karatu na, duk lokacin ina cikin waswasi tsakanin amsar addinin musulunci ko kuma maida hankali wajen gyara rayuwata ta duniya. Na koma gida a wannan halin, ban ɓoye ma mahaifiyata komi ba game da halin da nake ciki.


A bisa umurnin ta na isa Haɗeja, ban sha wuya ba wajen gane gidanmu, kamanni na da mahaifi na ya sa ba su gardama kasancewa na tsatsonsu ba. Sun min tarbo na musamman ba tare da sun damu da sanin addini na ba, sun yi farin ciki ainun sannan na ƙara da musu albishir din son amsar musulunci.


Sai da nayi wata ɗaya a Haɗeja sannan na kai ma mahaifiyata ziyara a lokacin na iya izifi huɗu daga tabara zuwa nasi.
Ko da mu ka tashi zuwa bautar ƙasa na yi yanda za a tura ni jihar Jigawa daga nan na nemi hanyar yi a Haɗeja, a nan na yi amfani da shekara ɗayan nan na nemi ilimin addini sosai, nayi fiqhu na yi tauhidi ga Hadisai duk na nemi ilimin su.
Muna kammalawa na samu gurbin aiki a ABU saboda fita da sakamako mai lamba ɗaya da nayi, sannan na cigaba da masters dina, bayan dawowan ne na fara zuwa ɗaukan karatu wajen Ustaz Yunus inda nake haddan Ƙurani, yanzu Allah cikin ikonsa na haɗa izifi Arba'in, daga Nasi zuwa Tauba"


Ko da ya kai ƙarshe hawaye sosai Baban Sasa yake, imani na ƙara ratsa shi, ya san cewa akwai wainda aka haifa a cikin musulunci da basu samu ilimi mai zurfi da Dee ya samu ba.


Ko a zaria da yake matattaran ilimin addini, inda duk in da ka zaga ina ka fito islamiyya ina zaka majalisi ne akwai da yawa da suke da shekarun Dee kuma ba su samu gatan ilimin ba. Kenan ba ruwan sanda ka shiga addini da yanda za ka riƙe shi.


"Dawooda Ɗan Yusuf, Na maka murna, lallai kai din mai tsananin rabo ne, Ubangiji Allah ya baka dukkan alkhairi duniya da lahira"


Baban Sasa ya faɗi zuciyarsa cike da Nadamar abin da ya aikata a baya. Nan dai Su baba Anas su ka haɗu suna masa fatan alkhairi.


Sai wajen ƙarfe biyar da Rabi ya nemi Mimi ta fito su ka tafi.
A hanya ya ke tambayar ta halin da Amatullah ke ciki, ta amsa


"Sai ka tausaya mata Dee, she is in pain, wallahi ta na ganin rayuwa"


"She will be fine in Sha Allah, I will give her the best I can when we unite"


Baki washe jin maganar Dee Mimi ta ce


"Yessssssss! That's the spirit!"


Dariya yayi, cikin ran sa ya na mamakin yanda Allah ya haɗa jinin Mimi da Amatullah.


*****
Dee bai sau damar yiwa Amatullah gaisuwa ba sai da aka yi uku. Daga soro ta fito sanye cikin hijabi. Muryar ta dashe saboda murar da ya kama ta. Ya na mai tsura mata idanu ya ce


"Amatullah, ki yi hakuri, Allah zai musanya mi ki da alkhairin sa, Allah na sane da ke"


Kai ta gyada masa ala'amar "eh" sannan ta kara da


"Ina wuni?"


"Lafiya lau Alhamdulillah, ya hakuri?"
Cewar shi cike da tausayawa.


"Alhamdulillah"


"Allah ya masa rahama, ya sa mai ceto ne"


"Allahumma Aameen"


Shiru ne ya biyo baya, daga bisani ya mata sallama ta koma ciki shi kuma ya koma wajan Baban Sasa. Duk wannan hidimar da ake yi akan idanun Saifullahi, idan akwai wanda ya tsana duk faɗin duniyar nan ya bi bayan Dee Yusuf.


Nan ya kara shan alwashin tsananta tazara tsakanin Dee da Amatullah ta hanyar tunkarar Baban Sasa da maganar komen Amatullah, da zarar An yi bakwai din rasuwar Emjay.


****
Ranar da aka yi bakwai da daddare Saifullahi ya sami Baban Sasa, Nan ya kalallame shi har ya na fitar da kwalla ya ke faɗin


"Baban Sasa ka rufa min asiri ka mayar da aure na da Amatullah,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login