Showing 78001 words to 81000 words out of 98809 words
Chapter 27 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
yana komawa wajen tawagarsa da ke duba Baban Sasa.
Baba Anas na sauri don zuwa ya bincika ko zai samu ya bangaje mutum. A tare su ka ba juna hakuri nan su ka shaidi juna.
"Baba ina kwana, da fatan lafiya na ganka a asibiti da safen nan" Yace fuska a sake.
"Kai dai bari ɗan nan, Baba ne ake bukatar jini 0- ne, shine zan duba ko za a samu, ina ne ma blood bank ɗin" yace cikin ruɗu.
"Subhanallah, Nima ai 0- din ne muje baba a yi min gwaji in lafiya lau sai a ɗibi nawa, Nima na zo wajen supervisor na ne" yace yana mai kamo hannun Baba Anas ganin yanda duk ya rude.
An ci sa'a jinin Dee lafiya lau ya ke, haka kuma ya na da ishasshe dan har leda uku aka samu daga wajen shi. Godiya mara adadi Baba Zubairu da Baba Anas su ka ta yi masa, da shi aka zauna har aka shiga da Baban Sasa aiki.
Awanni aka dauka ana yiwa Baban Sasa aiki, har Allah ya ba su iko su kammala masa aikin aka fito da shi rai a hannun Allah. Yanayin da aka fito da shi ba su Baba Anas ba, shi kan shi Dee sai da ya sha jinin jikin sa, dan kuwa hatta su likitocin da su ka masa aiki ba su da tabbacin ko zai tashi.
Daki na musammam aka kwantar da shi, Baba Zubairu ne mai dauriyar kai kawo, shi kuwa Baba Anas tun ganin yanda aka fito da Baban Sasa bakin shi toshe da abin bada taimakon numfashi ya ke fidda kwalla.
Sai da aka kwantar da Baban Sasa, Dee Yusuf ya mu su sallama tare da alkawarin zai dawo jiki sanyaye ya tafi.
Ranar daga Baba Zubairu har Baba Anas babu wanda ya runtsa, haka ma Baba Salihu tuni ya ɗauko hanya, in da Baba Muhamuda shi ma ya karaso tare da Baba Hamza da Baba Idiris.
Har dare yayi Baban Sasa bai farfado ba nan aka shiga muhawarar wanda zai kwana da shi, dan kowannan su gani ya ke idan har ya tafi kafin ya isa gida za a kira a ce Baban Sasa ya cika. Daga karshe su ka yanke hukuncin barin Baba Idris, su kuma sauran su ka kama hanyar gida.
Isar su kofar gida nan su ka taradda Saifullahi zaune, abin duniya ne ya isheshi tun bayar faduwar Baban Sasa wanda ya ke gani kamar shi ne sila, gashi kunya da tsoro ya sa kasa tunkarar asibitin. Ganin su ya tashi da saura ya na faɗin
"Sannun ku da zuwa Baba, ya jikin Baban Sasa?"
Babu mahalukin da ya amsa masa, Baba Anas kuwa ko kallon in da ya ke be yi ba, su ka shige gida su ka bar shi nan tsaye.
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Ba zan iya jure fushin iyaye ba! Allah ya tashi kafadar tsohon nan ko Allah ya sa ku yafe min"
Cewar Saifullahi yayinda ya koma in da yake zaune da ya zauna zuciyarsa cike da da na sanin biyewa Aysuh da yayi.
Cikin gida kuwa, idan aka ɗauke Ayush kowa cikin zulumi ya ke musammam Amatullah wacce ta wuni ta na kiran wayar Baba Anas domin jin yaya jikin Baban Sasa. Gidan tsit kamar gidan makoki, jin motsin shigowar su ya sanya kowa fito ana tambayar
"lafiya? Ya Baban Sasa ya ji da jiki?"
"Babu sarki sai Allah, ku yi addua idan na tafiya ne Allah ya ba shi saukin tafiya, ya sa ya cika da imani, idan kuma mai tashi ne Allah ya saukaka masa ciwo, dan kuwa dai Baba na cikin wani hali!"
Cewar Baba Zubairu wanda har lokacin shi ne ke da karfin halin magana. Abin ku da mata nan gida ya kaure da salati har da masu kuka. Sai da Baba Anas ya tsawatar mu su sannan kowa ya shiga hayyacin sa.
Ayush da ke jiyo komai daga bangaranta ran ta ne yayi fari tas, Alhamdulillah tsoho zai mutu ta bar zaman gidan gandu, ta na mai adduar Allah ya sa ya tafi kenan.
Jiki sanyaye Amatullah ta koma ɗakin in da ta dauro alwala ta shiga nafilfilu domin nemawa Baban Sasa sauki, ko da kuwa na tafiya ne. Dan kowa ya fidda rai Baban Sasa bai taba jinya da ta kai wannan tsanani ba.
Ranar kowa kwanan zulumi yayi, cikin daren Mahaifin Amatullah Baba Salihu shi ma ya iso. Hatta Ayush da ke farin cikin rashin lafiyar Baba Sasa ba ta ji dadin daren nan ba, dan kuwa Saifullahi juya mata baya yayi a karan farko tun da ya auro ta.
Da asubar fari su Baba Anas har Baba Salihu su ka dunguma asibiti, Nan ma su ka tadda Baban Sasa bai farfado ba, haka aka sake wani wunin zulumi da fargaba. Da la'asar Dee Yusuf ya koma duba Baban Sasa, Nan ya tadda duka baffanin Amatullah. Bayan ya gaishe su, su Baba Muhamuda, Baba Hamza, Baba Idris su ka amsa da kyar cike da kyama. Baba Anas ne ya ce
"Ya ka nan zo zauna kusa da ni ɗana, abin da ka mana Allah ya ma ka, wannan yaron da ku ke gani shi yayi mana abinda duk cikin mu idan ban da Salihu da Muhamuda babu wanda zai iya ko da kuwa muna da niyya, wannan da kuke gani shi ya ba da jini har leda uku, wanda aka karawa Baba, duk da kuwa ya san kyamar shi da mu ke yi ........"
"Yanzu jinin arne aka sanyawa Baba? Haba mana shi ya sa gashi har yanzu bai motsaba ba shi ba raye ba shi ba a mace ba! Kwa bari a ɗura masa jinin mushe fisabilillahi!"
Cewar Baba Hamza ya na mai kumfar baki. Shi kuwa Dee idan har maganar ta ba shi haushi sam bai nuna a fuska ba, dan kuwa ya san za a yi hakan.
" Baba ina ga babu ruwan bambancin addini a wajen ceton rai, nayi imani da littafi mai tsarki babu haka a cikin addinin ku, saboda Ubangijina na bashi, ina fatan Allah ya bashi lafiya"
Dee ya faɗi cikin sanyin murya, kalaman sa be sanya sun ji sanyi a zukatansu ban na bakin ciki da takaicin jinin Arne ke gudana a jikin mahaifin su.
"Sannan Baba in ma a blood bank a ka siyo, ana bambance jinin musulmi da Christian ne, sai naga aka yi rashin sa'a kila na mara addini kwata kwata zaku siya"
Dee ya sake faɗi ganin yanda suke gimtse fuska, ya tashi tare da faɗin
"Na bar ku lafiya, ubangiji ya tashe shi lafiya"
Ya juya ya tafi abin shi.
[4/18, 9:49 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA TALATIN DA ƊAYA
Gaba ɗayansu bin sa su ka yi da kallo har ya fice, nan ne Baba zubairu ya ɗan muskuta ya ce
"Nifa ban ga laifin yaron nan ba, na tabbata da ace shi mu ka gani a wannan hali ba zamu taɓa waiwayensa ba balle mu taimaka masa, bayan mu ne addininmu ya koyar da mu kyautatawa" yace yana mai kallon ƙanensa zuciyarsa cike da Nadama.
"Gaskiya ne, don wallahi ba ruwan bambancin addini a kyautata mu'amala ko sauke hakkin makotaka. Yanda ya wajaba a kan musulmi haka ya wajaba akan wanda ba musulmi ba, sannan a ko ina cin fuska haramun ne" Baba Anas ya ce yana mai goyon bayan Baba Zubairu.
"Amma kuma aka ce kada mu riƙe su aminai" Baba hamza ya ce a ɗan hasale..
"Eh an ce kada ka rike su aminai don za su cutar da kai amma ba a ce kada ka rike su da amana ba, kun manta zamanin Annabi SAW sau da yawa kafirai na zuwa da niyyar kashe shugaban halitta amma su ɓige da musulunta ba su kaɗai ba har mutan garin su, duk saboda kyakkyawan mu'amala da musulunci ya koyar da ayi ga kowa ciki har da wanda ba musulmi ba." Baba Anas ya ce kai tsaye.
" Ni dai babu wani kame kame da za ku min, kun ci amanar Babanmu, kun sani sarai yanda yake ƙyamarsu don su ɗin najasa ne, da kuke maganar na siya ba a sanin ko nawaye me yasa kullu. Muke addu'a muke faɗin RABBANA LAA TU'AKHIZNA INNA SINA AU AKHƊA'ANA toh shi Ubangiji ai mai Rahma ne, ba zai kama mu da laifi ba amma kuma yanzu fa? Haba! Haba!! " faɗin Baba Hamza ransa a ɓace.
" Kunga matsalar Bahaushe kenan, shi a duniya gani yake babu wanda ya kai shi zama kusa da Allah, haka kuka dinga tada jijiyar wuya lokacin da ɗan wajen madina ya auro Gara, a bakin bahaushe za ka ji yana kaskantar da wani jinsi in dai ba yarensa ɗaya ba da kiransa ƙabila.
Shi bahaushe shi dai wanda bai cikata farillansa ba amma a duniya ba wanda yake nuna wa Yatsa sai wanda ba musulmi ba, shi ne zai kalli malamin addini ya kira shi da tubabbe matukar daga baya ya musulunta.
Da haka manzo SAW yayi da ya tara manyan sahabbai da yake da su? don dukkansu tubabbu ne a fassaran bahaushe." Baba Salihu ya faɗi kai tsaye.
" Shine ai nagani, gashi kiri kiri wanda kuka zaɓa akan arnen yana shirin kashe muku mahaifi. Na gwammace a ce Arnen can ne ɗa na in dai zai tuba ya musulunta akan wancan sakaran" Baba Anas ya sake fadi cikin takaici.
"Ko me zaku ce muna dai jin ku ne kawai don ba zai wanke cewa baku kyauta ma babanmu ba kunci amanarsa ba ko kaɗan ba, Jinin Arne fa ke gudana a jikin Baba, mutumin da yayi rayuwar sa kaf cikin musulunci" Baba Mahmuda da tun farko bai maganta ba ya ce yana mai tsananin jin takaici.
Tun da suka fara magana Baban Sasa ya dawo hayyacin sa, idanunsa a rufe sai yake jin zantuttukan su kaf a kunnensa inda yake ji kamar mafarki yake yi, so yake ya fahimci me su ke faɗi amma ya gagara, idanun sa sun masa nauyi dan haka ya kasa bude so, bubu abin da ke motsi jikin sa face yan yatsun hannun sa. Baba Idris wanda tun da aka fara magana bai tamka mu su ba, shi ne ya lura da halin da ya ke ciki. Cikin hanzari ya tashi ya na fad'in
"Ina ga fa Baba ya motsa, yi maza kira likita! Baba Muhammadu ne ya fita cikin sauri sauri gudu gudu, in da gaba ɗayan su suka zagaye shi suna masu faɗin
"Sannu Baba! Allah ya tashi kafadar ka"
***
Faɗin Damuwar da Amatullah ta shiga ba zai misaltu ba, don gaba ɗaya kanta ta ba laifi don gani take damuwar rashin komenta ne ya kwantar da Baban Sasa.
Addu'a kam ta yi sosai akan ya samu lafiya.
Zaune take tana tunanin zuwa shika Amma wa zai kai ta? Lokaci take kallo tare da tsimayen kiran sallan la'asar domin ta ba da farali. Ɗumi ta ji ya fito mata wanda ta dan razana tare da gyara zama yayin da taji fitowarsa a karo na biyu.
Ajiye littafin 'Ina Darajar take?' da take karantawa tayi ta shiga bayi don gane ma idanunta. Abin da bata zata bane ta gani, wani irin yanayi ta shiga don gaba ɗaya ba za ta ce murna kaɗai ta ke ba.
Gyara kanta tayi ta isa ga mama da ke ɗaki tana hutawa tace
"Mama abin ya zo, na kusa fita idda" tace cikin farin ciki.
Kabbara mama tayi tana mai gode ma Allah sannan ta ce
"Kiyi shiru da bakinki, ba za su ji ba sai kin yi wankan na ukunki, kai Alhamdulillah Alhamdulillah" mama tace cikin farin ciki.
****
Ayush kuwa tunda garin Allah ya waye take cika ta na batsewa musammam da ta ji Baban Sasa ya farfaɗo daga bakin su Naja'atu. Gaishe da Hajiya da ta ke zuwa kowacce safiya ma yau ki ta yi.
Hajiya da ta ji ta shiru, tunanin ko lafiya ya sanya ta shiga bangaran Aysuh din. A falo ta tarar da ita, sanye da wando wanda ko gwiwa bai kai mata ba, da riga damammiya mara hannu.
Ta yi dai dai bisa doguwar kujera, ƙafa ɗaya kan ɗaya, yayinda ta ke cin gashesshiyar kaza ta na korawa da lemo mai tambarin five alive.
Yanayin shigar Ayush ya sanya Hajiya tsayawa bakin kofa ta ɗan yi Jim, ganin Ayush ba ta da niyar tashi ta rufe jikin ta bare ma ta nuna ta san da zuwan Hajiya, Hajiya ta ɗaure ta karasa cikin falon da fara'ar ta ta ce
"Assalamu Alaikum, Aisha sannu"
Sai da ta kora kazar bakinta da lemo, sannan ta amsa da
"Yauwa Hajiya barka da maraice fa, da fatan dai lafiya ko? Dan dai yau ko fita ban yi ba inan dakina bare ku ce na fito mu ku cikin tsiraici!"
Jikin Hajiya yayi sanya kamar wacce aka zubawa ruwan sanyi, ta ce
"Haba yar nan, kar ki ce haka ai gyara kayan ka ba zai zamto sauke mu raba ba, rannan da ki ka ga na tanka shi ma ai da dalili, yanzu na ji ki shiru ne ba ki zo an gaisa ba ya sa na biyo sahun ki na ji ko lafiya"
"Lafiya lau na ke, gudun kar na fito ku ce na fito mu ku zindir ya sa na yi zama na ɗaki, gidan ubana ba a takura min ba, ban ga dalilin da zai sa a takura min a nan ba, ehe!"
Ba ta damu da yanayin da Hajiya ta shiga ba, ta kara kora lemun ta, sannan ta ƙara da
"To Hajiya ma fisabilillahi ɗan ki ya ajiye ni a gida kamar bukka sam babu ventilation kuma you guys are still expecting me to dress like the local woman you're?"
"Iyye? me ki ka ce? Na ji kina turanci kin san ba ji na ke ba"
"Aw haka fa, yi hakuri hajjaju ashe ba boko, dama cewa na yi tunda ɗan ki ya aje ni gida irin wannan dole na ke shigan shan iska, na saba da AC gidan uba na"
Kai Hajiya ta girgiza, sannan ta ce
"Eh da gaskiyar ki, mun takura ki zaman gidan nan tun da ba ki saba ba, amma kar ki damu komai zai wuce, za ki koma na ku gidan daga ke sai mijin ki"
Hajiya ta faɗa ta na mai kallan kazar da Ayush ta ke ci. Ganin in da idanun ta ke kallo ta ce
"Ragowar kazar da Saifullahi ya saba siyo min ne duk dare, na ga kamar ran ki ya biya, za ki iya ɗauka Hajiya"
Ran Hajiya ba ƙaramin motsawa yayi ba, dan kuwa rabon da alkhairi ya shiga tsakanin ta da Saifullahi tun sanda ya ke auren Amatullah, lokacin su kazar nan babu laifi ya kan kawo mata, yau gashi sai dai ta gani ɗakin matar shi, har ta na mata tayin wulakanci. Hajiya na mai kokarin ɓoye bacin ran ta tace
"Ah ah madallah, na gode, idan yayi niya shi Saifullahi zai kawo min tawa ai"
"Eh toh nan fa ɗaya , kun fi kusa ai ɗa da mahaifiya, na gode Hajiya, Allah ya huta gajiya"
Jiki sanyaye Hajiya ta ce
"Ameen"
Har ta juya za ta fita ta kara dawowa ta ce
"Baban Sasa ya farfaɗo, sai ki shirya da anjima kaɗan in za a je duba shi a tafi da ke ko?"
"Saboda mai ya sa!"
Cewar Aysuh ta na mai aje lemon hannun ta kasa, ta kara da
"Miji na bai ce na je ba, duk sanda na sami lokaci zan je dan Allah Hajiya kar ku matsa min! Ai da ya na so na je ai da ya faɗa min ko?"
"Eh gaskiyar ki yar nan, Allah ya sa mu dace"
Hajiya ta ce yayinda ta juya da sauri ta bar dakin zuciyar ta na tafasa, ba dan Aysuh Amarya ba ce, kuma ta na shakkar zuri'ar da ta fito da yau sai ta sanya Saifullahi ya saba mata! Tunanin da Hajiya ta ke yi kenan, har ta kusa buge Amatullah ba ta sani ba.
Amatullah sanye cikin hijab din ta har kasa, ruwan kwai dan kyau har sheki ta ke, dauke da Emjay. Fuskar ta cike da fara'a ta ce
"Afuwan Hajiya ban gan ki ba ne"
Takaicin yanda Amatullah ta yi bulbul ta yi kyau, wanda kallo ɗaya za ka manta ka tabbatar da kwanciyar hankalin da ke tattare da ita, ba ƙaramin baƙin ciki ya karawa zuciyar Hajiya ba.
Amatullah ta kara da
"Barka da maraice, ina wuni?"
"Lafiya lau"
Amatullah ta wuce abin ta, da yake dama fita za ta yi, za ta je asibiti duba Baban Sasa. Ta bar Hajiya da bakin ciki fal zuciya.
Da fitowar ta, da tsayuwar motar Saifullahi lokaci guda ne. Tun kafin ya fito daga motar ya kura mata idanu, gani yayi ta zame masa sabuwa gal, dan ko sanda ta ke buduwar ba ta taɓa masa kyau da kwarjinin da ta masa a yau ba, abin mamakin shi ne ba wai ta yi ado ba ne, wannan hijabin nan dai da ya tsana shi ne sanye jikin ta.
Fitowa yayi ya tsaya jikin motar, ganin ta nufo in da ya ke bugun zuciyar sa ya karu, bai taɓa tunanin ganin Amatullah zai sanya shi cikin mawuyacin yanayi da shiga ba. Ya sakankace gun shi ta nufo, in da murmushi ya bayya fuskar sa, wani daɗi ne ya mamaye zuciyar sa. Amma da Amatullah ta zo dab da shi sai ya ga ko kallon sa ba ta yi ba bare ma ta nuna da wani ɗan adam nan tsaye, wucewar ta tayi ta, in da ya bi ta da kallo tamkar sa ƙara'i.
'ashe Amatullah za ta iya ganin sa ta ki gaida shi?'
Tambayar da yayiwa kan sa kenan cikin zuciya, a zahiri kuma bin ta yayi da sauri ya na kiran sunan ta
"Amatullah! Amatullah! Amatullah!"
Amatullah ta tsaya, juyowa ta yi fuska ɗaure ta na duban Saifullahi fuskar ta ɗauke da alamun tamabaya. Saifullahi na duban ta kamar zai haɗiye ta ya ce
"Haba Amatullah, yau ina ɗa'a da tarbiyar na ki? Ko babu komai ai ni yayan ki ne ko Amatullah? Ya kamata ana gaisawa"
Ta na mai ɗan sakin fuska ta ce
"Ban san kai na wuto ba ai, na dai san akwai wani tsaye jikin mota. Da fatan ka na lafiya"
Amsar da