Showing 75001 words to 78000 words out of 98809 words
Chapter 26 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
su ka fice daga gidan, ba su tsaya ko ina ba sai cikin GRA inda ya kama musu ɗaki.
Sosai su ka mori darensu, don duk wani salo Ayush ta yi kwas a kai kuma ta ba shi. Hakan bai sa ya gamsu ba, asali ma tuna masa yayi da kwanakin sa da Amatullah, kenan da gaske suturta jiki na ƙara taimaka wajen bambance zuma da suga ko kuma dai dan sun dan saba dan wasanni tun kafin su kai ga auren.
Duk wannan tunanin bai hana masa yi mata alkawura ba tare da bata duk wani yanci da take so a rayuwarsu.
"Kaga ita Ayush matar so ce ita Amatullah sai ka rike ta don samun cikon natsuwa da kamala" ya tuna hirar abokin sa bayan an sanya ranar sa da Ayush.
Tabbas ga shi ya zahir, duk da ita ɗin ma shine farkon ta, amma tazarar da ke tsakanin Amatullah da Ayush mai faɗi ce.
Ayush kuma neman yanda za ta sami damar hadiyar kwayoyin da Sameera ta siyo mata ta ke yi, bata shirya bacci ba sai da ta haɗiyi kwayoyin don gudun ɗaukan ciki, a tsarin ta ba ta ga za ta iya ɗaukan ciki kafin shekara uku bayan aurensu ba, bare yanzu da take zaune gidan gandu.
A haka dai suka kwashi kwana bakwai ɗinsu sannan su ka koma gida, babu wanda ya ce da shi kanzil kamar yadda babu wanda ya ma sallama kafin ya tafi.
***
Babu abin da ya fara ɗaga hankalin Ayush bayan dawowarsu sama da tashin ta da yayi ƙarfe bakwai ta je ta gaida iyayensa.
Kallonsa ta yi sheƙeƙe tace
"Honey pie, ba zan yi bacci ba Fisabilillah, wani irin in je in gaida mutan gida, ni fa bana son fara abin da ba, zan ɗore ba, ha'an" tace tana harararsa kamar ta yi kuka.
"A'a fa babe, kinga duk wannan na ɗan lokaci ne kafin mu tafi gidan mu, sai mun so zuwa za su ganmu, ki yi haƙuri daga kin dawo shike nan" yace yana rungumar ta.
"Ɗakin Hajiyarka kawai zan shiga, wancan tsohon ma bana auren da shi don shi bakin cikin kasancewarmu tare yake" tace tana mai faɗin iya gasikyar ta, shi kuma ya dinga wangale baki yana tunanin wasan jika da kaka ta ke da Baban Sasa.
"Shike nan mu je kin ji" yace yana mai miƙo mata gyale ta yafa akan kayan jikinta wainda su ke ƙanana masu bayyana sura.
"Au ba zan iya fita haka ba, ni dai Allah zaka haramta min zuwa gaisuwan nan, what is wrong with my dressing for goodness sake" tace cikin tsiwa.
"A'a muje, ba komi, naga amarya ce ai"
"Amarya baka ci sadakinka bane" tace tana watsa masa harara. Tunawa da garar da ya kwasa da yanda ya san kowace rijiya da yanda take amsar guga.
"Babe oooo muje muyi mu dawo kiji" ya ce yana miƙewa, haka suke tsallake mutane tana gaida su a tsaitsaye har ta isa ɗakin hajiya.
Kujera ta samu ta zauna, sannan ta gaida Hajiya tana mai ƙare ma ɗakin kallo tana tsine ma soyayya a zuciyar ta,
'in ban da soyayya wai nan ne za a kira ɗakin uwar mijina' tace cikin ranta.
"Ai na sha bacci za ku yi, hayaniyar biki ai sai da hutu" hajiya ta faɗi cikin murmushi, kallon Ayush take tana ƙara gode ma Allah da ta bata surukar da tafi ta kowa.
"A'a ai muna neman Albarka ne" tace a yatsine.
"Allah ya muku albarka" Hajiya ta caɓe cikin sauri.
"Aameen" Ayush ta faɗi cikin miƙewa. Shi ma a mike su ka fice duk yanda Hajiya taso ta ɗan keɓe da shi.
Haka rayuwar su ke tafiya kullum safe zata gaida Hajiya ta koma ɗakinta, abinci kuwa in bata soya dankali ba zata girka musu taliya ko farar shinkafa da wake su ci da mai da yaji.
Tun yana ganin hakan a matsayin amarci ne har dai ya lura da gaba ɗaya cikin sa baya samun lafiyayyen abinci kamar da.
***
Zaman Ayush a gidan bai tsinana ma kowa komi ba ciki har da hajiya, don cin abin hannun Ayush wahala ne, daban ta sa ƙannen sa Najaatu da Aisha su dinga zuwa suna mata gyaran gida da wanke wanke, hakan bai sa ta musu ihsani ba.
Tun ranar da su ka dawo gidan ta ke raba idanu domin ganin Amatullah ko dan Saifullahi, amma babu su babu alamar su, har ta gaji ta tambayi Najaatu, in da take shaida mata ai tun satin biki ta ji Gwaggo ta ce ta koma makaranta saboda jarabawa. Hakan sam bai mata dadi ba, amma ta ce ba komai ta na nan tana jiran ta.
Shigar da take musu a cikin gida kuwa babu ruwanta da wa zai gani, kwatakwata ɗan kwali bai dame ta ba haka za ta dinga tsallake matan gidan da sannu in zata shiga ɗakin hajiya.
Abu ɗaya ne bata wasa da shi watau maganin ta, ko da wasa ba ta yarda ta yi tsallake ba don ba ta ga wajen haihuwa a gidan ba.
Yau ma kamar kullum sanye take da doguwar riga mara hannu, tayi sabon kitso da lallai wanda ya kwanta a kan farar fatanta. Tuwo yace mata yana jin ci kuma ita har ga Allah ba ta iya ba, Najaatu take son kira ta tayata ta shiga wajensu tana tsallake su Hajiya da sauran matan gidan suna hidimar su, ganin ba sa wajen sai ta wuce soro in da ta ga su Baba Anas, Baba Idiris, Baba Zubairu da Baban Sasa zaune bisa tabarma.
"Sannun ku"
Abin da ta furta kenan, kafin ta gifta su ta leka waje.
"Wacece wannan kuma" Baban Sasa yace bayan sun amsa mata sannu da tace.
"inaga baƙuwa matar saif tayi" Baba Idris yace yana mai basarwa.
Dawowar da ta yi tare da Najaatu ya basu damar gane ta. Cikin jinjina kai Baba Idiris ya ce
"Wannan fa Aisha ce matar Saifullahi"
Baban Sasa na mai kame baki ya ce
"Wai matar Saifullahi ce ta zo ta tsallake mu da wannan shiga haka?"
"Toh ai in dai wannan yarinyar ce kaɗan ku ka gani, wani shigar idan ta yi sai dai a kau da kai tsabagen munin shigar"
Cewar Baba Zubairu cikin al'ajabi, ya kara da "tashin hankalina yanzu shi ne Kar Allah ya sa yaran gidan nan su dauki dabi'a irin na ta"
"Ah ah, 'ya'yan mu masu tarbiya ne, Allah ya tsare mu da ganin dabi'a irin wannan a zuri'ar mu, ina Anas surukar ka ce, ina fatan za ka yiwa tufka hanci!"
Cewar Baban Sasa cikin jaddadawa. Kai Baba Anas ya gyada kawai, ya san dai in har hawan jini ya kama shi toh ko shakka babu Saifullahi shi ne sila. Baban Sasa be gushe ba ya kara da
"Ai ni daga ganin dangin yarinyar nan na san Saifullahi ya saki rashe ya kama ganye, mu ka bashi diyar mu diyar mutunci ya watsa mana kasa a Ido, ai ga irin ta nan, ga irin wacce ya je ya kwaso"
Ya karasa maganar ya na fitar da kwalla. Takaici ne ya dada rufe Baba Anas, in da ya tashi ya shige ciki.
Ganin yanda ya shigo a fusace ya sa Hajiya bin bayan shi. Cikin ɗaki ya kwance mata kwandan takaicin da ya kwaso, ya kuma umarce ta da ta je ta yiwa surukar ta magana, ba sa shigar mutanen banza a gida, idan ba haka ba shi da kan sa zai mata magana kuma ba zai mata ta dadi ba. Ya na magana ya fice fuu, jiki sanyaye Hajiya ta nufi bangaran Ayush.
A falo ta tadda ta, kwance bisa kujera. Ganin Hajiya bai sa ta tashi zaune ba, daga kwance ta ke duban ta, ta ce
"Hajiya lafiya mu ke ko?"
Cikin kame kame ta ce
"Eh kwarai yar nan, lafiya lau, dama na zo ne da yar wata magana"
Jin haka ta tashi zaune, ta ce
"Bisimillah zauna mana Hajiya, na mi ki laifi ne?"
Hajiya ma ta zauna, ta na mai girgiza kai ta ce
"Ah ah ko kadan, dama yar shawara ce"
"Uhum?"
Cewar Aysuh ta na mata irin kallon nan na hadarin kaji, Hajiya ba ta kula ba ta cigaba da faɗin
"Kinga a matsayi na uwar mijin ki, na ke son jan hankalinki akan shigar da kike yi, tabbas babu haramci a ciki saboda a gidan mijinki kika yi, amma ki sani fitowa a haka ya saɓa ma addini da al'ada. Don Allah ki ɗan dinga yafa mayafi kinji, Allah ya muku albarka " ta fadi cikin sakin fuska.
Takaici da bakin ciki ya sanya Ayush kasa cewa komai har Hajiya ta mata sallama ba tare da ta amsa ba ta fice, ta na fita ta kora Najaatu cikin zage-zage ta sa ma ƙofar sashinta makulli.
Saifullah da ya shiga Abuja ya dawo gaf da magariba, yunwa ce sosai yake ji ga gajiya yana zuwa ya iske gidan a garkame. Komawa ɗakin hajiya yayi ya tambaye su ko Ayush ta fita ne nan Najaatu ta fadi masa abin da ya faru.
"Amma Hajiya ya za ki biyewa Baba fisabilillahi ku ɓatawa yarinyar nan haka daga tarewar ta! Haba Hajiya!"
Kafin Hajiya ta kai ga bashi amsa ya tashi cikin sassarfa ya isa ga ƙofar tasu, magiya yake da ban hakuri akan ta buɗe masa ita kuma faɗi take
"Ba zaman kulle na zo yi ba, babu wani ɗan bura uba da zai sa nayi kulle" hakuri dai Saifullah yake bata inda mutane ke tsallake su tare da ganin halin da ya ke ciki.
Yana kan bada hakurin ne Amatullah ta wuce shi tana mai waya, ga Emjay yayi ɓulɓul da shi rike a hannun ta. Shagala yayi yana mai mamakin dama a sashin Baba Hamza suke? Dama gidan nan take ko zuwa tayi? Idan idanunsa bai masa ƙarya ba kyau tayi ba ko kaɗan ba, surarta ya ƙara fitowa tayi shar da ita.
"Haba Don Allah ki buɗe ki ji hukuncin da zan yanke Amatullah... " ya ce hankalin sa na ga Amatullah da ta ɓace ma ganin sa.
Babu shiri Ayush ta buɗe haɗe da jawo shi cikin ɗakin da rufewa.
[4/15, 10:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA TALATIN
Jawo shi ciki da aka yi ne ya ankarar da shi abin da ya faɗi. Nan ya sanya dariya cikin borin kunya haɗe da faɗin
"Haba Babe, kawai ki zauna kina sa mutane na min gani gani" yace mai rungumarta.
"Wallahi ka sake ambaton sunan nan a gidan nan wallahi a bakin aurenmu" tace cikin ƙara haɗe rai.
"ki gafarce ni Babe, wallahi sai da na faɗi ma Hajiya ina ruwansu da ke, ina ce dai ni kike aure" yace yana mai ƙara manne ta da jikin sa.
"Ba kowa ya ja wannan abin ba na tabbata sai tsohon nan da ya kamata a ce ya rasu tuni amma ya tsaya cin zamanin wasu" tace cikin takaici, duniya babu wanda take tsana cikin birgewa dama da Baban Sasa. Tun farkon labarinsa da ta fara ji a duniya na yanda ya ke kawo mata cikas ne a rayuwa, ta san kuma ta ganshi da ta je kiran Najaatu.
"Barni da shi zan same shi, inshaAllah nan da ƙanƙanin lokaci za mu bar musu zariar gaba ɗaya" yace duk da ya ji haushin kalamanta ga Baban Sasa amma sulhun da ya ke so daga ita yafi komi.
"Allah ya amince Honeypie, zan kira Anty Rukayya akan issue din allocation na estate ɗin don mu samu" tace cikin farin ciki. Satin da ya gabata su ka ji labarin gidajen da ake rarrabawa ma'aikata gwamnatin tarayya don a rage masu matsalar samun gida a Abuja.
***
Amatullah kuwa hutun karshen zango ta dawo, sun yi jarrabawa cikin sauki da fatan samun nasara.
Ko da ta dawo Sasan Mama su ka sauka, cikin murna ta tarbe su, nan ta cika musu ciki da abinci.
Emjay da yake wata shida a duniya yayi ɓulɓul da shi, fuskar sa sak na Saifullah haske kawai zai nuna masa.
Mama wasa ta shiga yi da shi tana hurga shi sama tana caɓewa.
"Ya karatun Amatullah, dafatan megidan nan nawa baya hana ki" Mama tace tana mai cigaba da wasa da Emjay.
"Alhamdulillah! Ai mama Baaba tana mana kokari" Amatullah ta ce tana mai nufin yar aikin da mama ta haɗa ta da ita, duk da ba kwana take da su a samarun ba amma ko da za ayi takwas ta isa gidan.
Sai yamma can ta fito don zuwa gaida Baban Sasa. Ta fito kenan za ta wuce ta ci karo da Saifullah yana buga ƙofa cikin magiya. Dariya sosai tayi a ranta, tana ganin yanda ya bi ta da kallo, maƙe dariyarta tayi har sai da ta tabbatar da ta ɓace ma ganin sa.
Nan ta zauna a kan dakali, ta dinga tuntsira dariya. "Emjay ka ga abin da na gani kuwa, ka taya ni dariya mana" tace ma Emjay shi ma kamar ya ji abin da ta faɗi nan ya shiga wangale baki yana dariya shima. Sai da su ka yi mai isarsu sannan ta tashi ta nufi wajen Baban Sasa.
Sosai yayi farin cikin ganinta duk da in ya tuna cewa ba ta gidan Saifullah sai ya ji babu daɗi a ransa.
"Oh jikan yara wannan ƙiba haka se ka karya min mata" yace yana mai amsar Emjay.
"Aikuwa Baba gashi se muni yake, ai kwalelenka matanmu ba sa sonka" Baba Zubairu ya ce, su baba Anas ya taya shi.
Ita dai Amatullah banda murmushi babu abin da take yi, son iyayenta na ratsa, ita a halin yanzu ba ta da lokacin jin haushin kowa, lokacin da take ɓatawa wajen son kanta da neman cigabanta ma ya mata kaɗan.
" Amatullah!!!" Baban Sasa yace wanda ya dawo da hankalin su wajen shi.
"Ki dubi yaron nan ki tausaya masa ki koma ɗakin ki Amatullah, Don Allah ba don ni ba" yace cikin sigar roko.
Jin zancen tayi kamar saukar aradu amma ta ɗaure ta ce.
"Wallahi Baban Sasa saki uku ya min, da tuni na koma" tace tana mai danne hawayen da ke neman fitowa.
"Shi fa yace saki ɗaya ne, kaddara ukun ya miki a take zamanin Annabi SAW, da khalifancin ABUBAKAR RA zuwa Farkon Umar RA duk saki uku a lokaci ɗaya ana kirga shi a matsayin ɗaya ne, dalili yasa Umar RA ya maida shi uku, maluma na ganin ana iya ɗaukan hukuncin farko" yace yana mai ƙara narkar da fuska.
"A'a fa Baba, zance mafi inganci Shine a yi amfani da hukuncin sayyidina Umar RA. Annabi da kansa ya ce ALAIKUM BI SUNNATIE WA SUNNATU KHULAFA'UR RASHIDUN ka ga hadisi ne ingantacce da ya wajabta amfani da hukuncin su a fage na addini" Baba Anas ya tare shi, hakan ya saukar ma Amatullah natsuwa.
"Kuma Babanmu wallahi yaron nan bai yi hankali ba, ka daina damuwa da lamarinsa, lusari ne ba ko ƙarami ba" Baba Anas ya ƙara faɗi ganin baban Sasa bai gamsu da shi ba.
"Shine dalilin da ya sa nake son komensu, ka ga za ta gyara shi, da wuya amma da nasara a gaba" Baban Sasa yace a maraice.
"Zata koma Baba, ka bar komi a hannuna inshaAllah" Baba Hamza yayi karaf ya faɗi yana mai musu signal da ido.
A nan gaɓan Saifullah da Ayush su ka shigo wanda Ayush ta tabbatar da ta in gizo shi da su zo yayi magana da Baban Sasa akan a fita rayuwarsu.
Babu bambanci a shigarta ta ɗazu su ka shigo da Sallama. Kallo ɗaya su ka yi ma juna ita da Amatullah su ka shaidi juna. Ta san dai za ta nuna ma Amatullah fari da tsawo amma diri da tsananin kyau ko kaɗan ba za ta kamo Amatullah ba.
Sanye take da atamfarta riga da skirt da hijabinta da ya shiga da kayanta amma sheƙi da Amatullah ke yi ya ɗan rikitata don natural glow ne da ta fara koyon sirrinsa daga mimi.
Ɗaukan Emjay tayi ta fice tana ma iyayen sallama su kuma suna masu bin ta da Albarka, kafin duk su gimtse fuska.
"Baban Sasa Ƙaran Hajiya na kawo" yace yana mai yamutsa fuska ganin yanda iyayensa su ka yi fuskar shanu.
"Toh me hajiyar tayi?" ya ce yana ƙara haɗe rai.
"Ta fita idon iyali na, ko a musulunci an yarda ai mace ta yi shiga irin shigar da mijinta ke so, Baba ni ke auren Ayush ba kowa ba, haka nake son ganinta don haka ka ja masu kunne" yace yana mai kumburewa.
"Tohhh Madalla da tabbatacce mara kishi, shi ne ka..." Baban Sasa bai ƙarasa ba saboda sarƙewa da maganar ta yi amma bai fasa nuna Saifullah da Yatsa ba, nan take ya faɗi a wajen sumamme.
Ruwa suka ɗauko su ka watsa masa amma ko motsi bai yi ba, duba shi su ka yi nan su ka ga maɗiga na bugawa, ɗaga idon da Baba Anas yayi ya ga su saif tsaye a firgice ya ce
"Saifullah Allah..." bai karasa ba dalilin rufe bakin sa da baba Zubairu ya yi.
"Fice mana da gani Saifullah" Baba Idris ya faɗi cikin tsawa nan su ka fice sum sum shi da Ayush, ita tana addu'a Allah ya sa Baban Sasa ya margaya a huta shi kuma tsoro da Dana sani ne ke cike da kirjinsa.
***
Asibitin Koyarwa ta Shika su ka nufa da shi, addu'a su ke kada ya rasa ranshi. Sashin gaggawa da hatsari su ka yi da shi inda take aka mika shi sashin masu fama da ciwon ƙoda bayan an duba an gano jininsa ne ya hau da kuma kodarsa guda ɗaya ta lalace, dole a cire ta in ba haka ba ciwon zai iya taba dayar kodan.
A asibitin su ka kwana don likitoci a kansa su ka kwana, kafin su ka samu ya farfado amma nan aka nemi jini saboda saboda za a shiga da shi aiki.
"Sai dai a siya duk mu nan da muke nan babu mai kalar jininsa, Salihu ne da mahmuda su ke da shi amma duk mu positive gare mu" Baba Zubairu ya ce ma likitan cikin damuwa.
"Yaa salam, samun jini 0 negative yanzu aiki ne, amma kuje bankin jini ko za a dace" yace