Showing 72001 words to 75000 words out of 98809 words
Chapter 25 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
wanda Saifullahi be yi ba, Amma ta ki. Ranar haka su ka rabu kowa babu dadi.
****
Tun bayan tafiyar Saifullahi ta shiga tsaka mai wuya, gashi ba ta san jama'ar gidan su san halin da ta ke ciki dan tabbas su ka sani aure tsakanin ta da Saifullahi ba mai yiyuwa ba ne. Da zaman gidan ya ishe ta mayafi ta saka in da ta neme izini gurin mahaifiyar ta, ta figi motar ta kirar honda, ba ta zame ko ina ba sai gidan su kawar ta Sameera da ke hotoro GRA.
Ba ta boyewa Sameera ko mai ba dan kuwa abokin kuka ba a boye masa mutuwa. Jiki sanyaye Sameera ta ce
"Ayush kin san duk wannan abin na su ba dan komai ba ne sai dan su hana auren nan na ku, kuma gashi kin sa burin su zai cika!"
Ayush na share kwalla ta ce
"Ya ki ko so na yi Sameera? Kin fa san muddin aka ji wannan maganar a gida ba za su bari a yi auren nan ba!"
"Idan har ki ka tsaya tsayin daka walllahi dole su hakura, Saifullahi na san ki fa Ayush! Maza da idan su ka ce an aura mu su cousin shikenan tsakanin ku, Amma shi ya rike alkawari har ya saki matar shi saboda ke? Ai ke ma kin san dole akwai consequences ai, bai kamata ki juya masa baya ba Ayush"
Cewar Sameera. Shiru Ayush ta yi cikin nazari kafin ta ce
"Yanzu haka zan zauna na haihu gidan gandu?"
Sameera na girgiza kai ta ce
"Kash wa ya ce mi ki zuwa za ki yi ki haihu? Ai idan kin ga kin haihu da Saifullahi to kun tashi daga gidan nan Ayush, inaaaa ko ni ba zan yarda ki haihu ba, emergency contraceptives pills za ki sha, within 72 hours za ki sha idan wani abu ya faru tsakanin ku you know, amma ya fi aiki idan ki ka sha immediately after sex, shi ne zai lalata kwaiyoyin sinadarin haihuwa da su ka shiga cikin, ya hana su developing zuwa kwayoyin halitta"
Cikin farin ciki Ayush ta ce
"Dadi na da ke Sameera sanin duniya wallahi! Ai shikenan zan bi shawarar ki, zan faɗa ma sa na hakura zan yi zaman shekara ɗaya family house din na su, Amma fa ki samo min pills din nan, kin ga dai sati shida ya rage"
"Kar ki ji komai mata a gidan Saifullahi, kuma wallahi kar ki saurara mu su in dai ki ka shiga family house ɗin nan, yanda su ka mi ki rama, musammam wannan tsohuwar matar ta shi da ya ke kira bagidajiya!"
Su ka yi shewa su ka tafa. Nan Sameera ta cigaba da kimtsa mata yanda za ta yi gidan auren ta. Ita kuwa Ayush ta na mai maraba da gangar shaidan ɗin da Sameera ke buga mata.
Daren ranar ta shaidawa Saifullahi amincewar ta na zama gidan su. Duk da yayi mamakin yanda ta canza ra'ayi cikin kankanin lokaci amma ya kasa tambayar ta dalili. Soyayyar su suka cigaba cikin jin dadi.
****
Da yardar Allah da kuma taimakon kula da Amatullah ke samu wajan Mama jikin ta yayi kyau sosai. Har aka gama mid semester break ba ta iya daga waya ta kira Mimi ba sai dai Mimi ta kira ta, wai a nata kar ta kira Mimi ta na tare da Dee Yusuf. Duk yanda ta so ta yaki zuciyar ta akan wani abu mai kama da kishi da ke taso mata duk sanda tunanin dangantar da ke tsakanin Dee da Mimi ya zo mata.
Fatan ta dai Allah ya sa ba abin da take tunani ba ne, saboda tazarar da ke tsakanin ta da Dee Yusuf bai hana ta kishin sa ba. Amatullah ba ta sami damar komawa makaranta ba satin da aka koma saboda yanda Mama ta dage lalle sai ta zauna a gida ta murmure, dan haka Mimi ce ke mata attendance da assignment har satin nan ya kare.
Dangane da Saifullahi kuwa ta yi kokarin cire shi daga zuciyar ta duk da dai hakan ya ci tura saboda Emjay. Zaman taka tsantsan take yi a gidan gudun kar Allah ya hada ta da shi, ko yara sun bi da Emjayi ta bangaran Hajiya sai ta koro su, haka kuma ba ta fasa yaɗawa Amatullah da Gwaggo habaici ba musammam da ta ga auren Saifullahi ya taho gangaganga, komai na tafiya yanda ta ke so.
Mimi kuma tun ranar da auren Amatullah ya mutu sanadiyar Dee Yusuf ta ke addabar shi da maganar Amatullah. Tun ya na share ta har ya mata alkawarin ta same shi office ɗin sa bayan ta gama lecture zai fada mata abin da ta ke son ji.
Ana gama lecture din ta yiwa Amatullah waya, in da take shaida mata suna da test gobe in za ta iya ta samu ta shigo.
Bayan sun gama waya ta wuce department din su Dee. Cikin office din na sa ta tarar da shi, sanye ya ke cikin farin yadi dinkin jamfa ya masa kyau na kwaran gaske. Ganin Mimi ta shigo sanye cikin hijabi da ya tsaya mata iya gwiwa ya na murmushi ya ce
"Zama da madaukin kanwa, so Amatullah ce ta koya mi ki sa hijabi haka Mimi?"
Ita ma din murmushi ta ke in da ta zauna kujerar da ke kallan ta sa tare da faɗin
"Ban son sharri fa Dee, dama tun kafin na san Amatullah din ta ka na ke ɗan sa hijabi na"
"Amatullah dina? Kin ba ni ita ne?"
Cewar Dee ya na mai sosa kyeya
"Do you still love her? Do you have feelings for her?"
Kai ya girgiza, ya bata amsa
"It doesn't matter how I feel about her Mimi, she can never be mine....."
"But y? Ba dai saboda ta yi aure ba ne? Ai ya sake ta! I'm sure dan ta taɓa aure ba zai zama dalilin da za ka guje ta ba"
Cewar Mimi cikin nuna rashin fahimtar Dee Yusuf. Kallon ta ya ke kafin daga bisa ya ce
"Mimi ba za ki gane ba"
"Try me"
"Owk, iyayen ta ba za su taɓa bani auren ta ba, ba sa san tsatson da na fito daga ciki"
"But Dee ai ya wuce, da ne, y not try your luck again? I mean everything has changed..."
"Nope, not everything Mimi, expecially my background Mimi....wanda bai so ka da kwana ba ba zai so ka da wuni ba"
Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Mimi ta ce
"Idan ita kuma ta na son ka fa?"
Kafaɗa Dee ya daga ya sauke, sannan ya ce
"I love her too, babu yanda zan yi Mimi"
Cike da farin ciki ta ce
"Akwai yanda za ka yi, ka ga yanzu ta na idda ne ko me suke kiran waiting period ɗinsu, last time da ta ke min bayani ta ce min until then ba za ta iya kula kowa ba, so you have enough time, ka shirya yanda za ka sace zuciyar ta da na iyayen ta, Amatullah ta sha wahala a rayuwar ta na aure, in ba haka ba you will end up with me, you know I love you right?"
Dariya mai fitar da sauti ya ke yi jin furucin Mimi na karshe, ya daɗe da sanin Mimi ta na son shi, amma hukuncin addinin christain na hana auren cousin ne yayi tazara a tsakanin su, har ita da kan ta ta yi wa kanta gata ta yi watsi da wannan lamarin, abin mamaki sai gashi yau ita ce ke kokarin daidai ta shi da Amatullah. Cike da fara'a ya ce
"Allah ya baki miji wanda ba zai ga laifin ki ba Mama na, yanda ki ka ce din shi zan yi, I don't want to end up with beautiful Mimi, ba zan iya faɗa da samari ba"
"Kaii Dee!"
Dukan su dariya su ke cike da jin dadi su ka cigaba da hira.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, duk wani shirye shirye da ke gaban Saifullahi ya yi kokarin saukewa, ya gyara in da Baban Sasa ya umurce shi da tarewa, wanda hakan sai da ya kai shi ga cin bashin banki don ya gyara ginin da zata ji dadin zama.
Ranar da za a kai lefe ya kama ranar asabar, Amatullah ta yi rashin sa'a ta na gida, ta so fita ta bar mu su gidan amma Gwaggo ta hana. Guɗa da habaici babu wanda Amatullah ba ta ji ba daga dangin Hajiya. Gwaggo da Amatullah na zaune a falo sai gashi an fara shigo da akwatuna ana ajewa gaban ta, da ta tambaya daga ina, kanwar Hajiya ta ce
"Abin arziki Hajiya ta ce a kawo ki gani, kayan lefan Saifullahi ne, Allah yayi"
Ta karasa maganar ta ba mai rangwaɗa guɗa. Kallon Amatullah Gwaggo ta shiga yi, wanda idanun ta sun ɗan ciko da kwalla tsabagen takaicin zaman da Gwaggo ta sa ta yi a gidan. Daki ta tashi ta shige ta tarar da Emjay na shan baccin sa, ita ma ɗin kusa da shi ta kwanta, hannun ta bisa jikin sa yayinda ta shiga karanto adduoin samun kwanciyar hankali.
Gwaggo kuwa biye mu su ta yi, aka bude kaya da ita, ta na mai sanya albarka ba tare da ta kula da habaicin da ake yada mu su ba, dan kuwa ta san kawo kayan bagaran ta ma da biyu aka yi.
*****
Ana saura sati ɗaya biki, yana shirin tarewa a Kano saboda bukukuwan da za su yi mahaifin sa ya kira shi.
"Ango ka sha miya, amma na ga ka manta da wajibi kana ta ɓarin kudi a wanda ke shirin zama wajibi" yace cikin sakin fuska. Zai iya rantsewa tun bayan sakin Amatullah bai ga fuskar mahaifinsa a sake ba, sai ranar. Kallon sa yake cikin rashin sani.
"Yarinyar nan Amatullah ka manta tana cikin idda ne, ko ka manta har yanzu cinta da shan ta yana wuyanka, bana ko zancen Babana don kace ba naka bane, amma kam yanzu ka ciro kuɗi ka bani na abincin Amatullah, kuma bana son harkan ƙaranta" mahaifinsa ya faɗi cikin dakewa.
Gaba ɗaya kan Saifullah ya kwance, ita da ake maganar akanta tun daren nan bai sake ɗaura ido akanta ba, ba zai iya tantance tana gidan ko bata ba, ya san ya kan shiga ɗakin iyayenta ya gaida su amma ko Emjay bai sake kuskuren gani ba.
Aljihunsa babu komi sai kudin da ya je ya canzo bandir ɗin yan hamsin hamsin, kallon mahaifin sa yayi yana mai sunkiyar da kai ya ce
"Baba da za a min haƙuri na gama wannan hidiman zan bada" yace cikin muryar neman ɗauki.
"A'a fa Saifullah, ba zamu yi haka da kai ba, duk wata dubu hamsin zaka bata har ta gama idda, yanzu dai bani nan in ga" yace yana miƙa hannu.
Gaba ɗaya kudin Aljihunsa dubu hamsin da biyar ne, su kaɗai su ka rage masa gaban sa da bayansa.
"Baba..."
"A'a fa engineer, miƙo kawai ga kuɗi nan ina hange a aljihunka"
Cikin sanyin jiki Saifullah ya ciro sabbin kuɗin da ya yi niyyar zuwa yayi liƙi da su, ji yake kamar ya ɗaura hannu a kai ya dinga kuka don gaba ɗaya Baba Anas ya shiryi tona masa asiri.
"Madalla, Allah sa a watse taro lafiya" Baba Anas ya fadi tare da jingina sosai a kujerar da yake zaune, zuciyarsa ƙal da farin ciki.
Ya san ya katse masa da Hajiyarsa wani yanki na jin daɗi, sarai ɗazu ya ke jin tana faɗi cikin fariya Saifullah ya je ya canzo kuɗi, da yanda za ayi liƙi kada dangin Ayush su raina su.
Dariya Baba Anas yayi, yana jin ko a haka ya barsu ya rage wani sashi na takaicin su da yake ji.
A ranar Baba Anas ya damkawa Amatullah kudin, in da ta ce dan Allah ya taya ta neman izinin Gwaggo ta koma makaranta tun da exam za su fara, yanayin taro na biki ba zai bari ta sami nutsuwan karatu ba. Hakan kuwa aka yi, da sa bakin Baba Anas ta hade dan kayan ta da na Emjay cikin farin ciki ta yiwa Mimi magana.
Gidan dalibai da Mimi ke zaune ta koma, dake gida ne irin na dalibai 'ya'yan manya, gidan yayi kyau ba laifi. Nan Mimi ta bata ɗaki ɗaya, ta na murna lalle Dee zai yi alfahari da ita.
***
Washe gari yan danki su ka iso, motocin ɗaukan kaya biyu su ka zo da shi cike da kaya, duk da iyayenta sun rage yawan kayan a dalilin faɗin Saifu na zamanta gidan Jamoh. Ta kofar kuyanbana su ka shigo tare da tahowa kamar za su fita gari su ka shigo ta ƙofar kona.
"Kai cikin kuttu za ta zauna dama" faɗin ƙanwar mahaifin Ayush da ta san kan zaria sosai. Yanayin da ta faɗi cike da takaici ne da jin alamun kaskanci ga zuriar su.
Shiru matan wajen su ka yi suna mai kallon yanayin anguwar, gidajen gandu ne mafi akasari sai sabbin gine-gine ɗaiɗaiku. Gaba ɗaya bakunan su kamar an ɗinke duk da dama ba wai zuga su ka yi ba, kannen mahaifinta ne guda uku tare da yar mahaifiyarta da kannen mahaifiyarta biyu.
Hajiya Haske kuwa da ta san ƙanin mijinta mai kuɗi da gadon kuɗi ya so Ayush amma na nace ma Saifullah bata san lokacin da ta ja tsaki ba sa'ilin da motar ta tsaya a kofar gidan Jamoh.
Gini ne na da amma da gani ya sha gyara, tambari alamun gidan sarauta liƙe a ƙofar gidan nasu.
Kallon makotan gidan su ka yi sai su ka ga sabbin gine-gine masu kalar zamani uku ne kuma duk ba a kammala ba.
"Marhabin sannunku da zuwa" Habiba matar Baba Mahmuda ta faɗi tana mai musu iso..
Turkewa su ka yi a ƙofar gida ba tare da alamun niyyar shiga ba, sai da ta sake faɗin
"Hajiya bismillahnku ai sasan su na da ga ciki ne" tace kamar zata musu sujjada saboda ladabi ganin kallo ɗaya ta musu ta gane sun tsumu da Naira.
"Anty wai har dankin a family house za ayi" hajiya haske da ta kasa hakuri ta ɗaga waya ta kira yayarta ce ta faɗi cikin tsananin ɓacin rai.
Hakuri ta ba ta daga can ɓangaren tana mai nanata ai ƴar su ce ta ja musu wannan kaskancin. Hakan ya sanya su ka shiga ciki ba tare da ba da umurnin a sauke komi ba na kayan.
"Don Allah muna son a mana iso wajen babba a gidan nan" faɗin Hajiya Jamila kanwar mahaifin Ayush.
Kallon ta Habiba ta yi sannan ta aika a faɗi ma Baban Sasa kafin su isa, cikin ikon Allah Baba zubairu da Baba Anas na nan a wajen sai su ka ce a faɗi masu su shigo.
Ƙatuwar dardumarsa mai cike da ƙamshi aka shimfiɗa musu, ko da su ka shigo sun iske ɗakin bai rasa komi na nagarta ba sai kuɗi amma su ka tsunga kamar masu kyamar ɗakin.
Sun gaida Baban Sasa babu yabo balle fallasa a nan ne Hajiya Jamila tace
"Sunana Hajiya Jamila, ina aure da aiki a birnin California, ni ƙanwar mahaifin Ayush ce, mun zo jere ne Baba amma Sam ba mu ga muhallin da za a sa kayan da mu ka zo da ita ba, balle har mu ce zamu ajiye ɗiyarmu a ciki" tace tana mai yatsina fuska, saura su ka amsa da Aikam dai.
Baba Anas har zai magantu sai Baban Sasa ya hana masa, kallonsu yake yana raya a ransa har za su nuna ma bazazzage jin kai, bazazzagen ma Bamalle. Murmushi yayi yace
"MaashaAllah! Allah ya ma rayuwa Allah, ai Muhalli nagarta da soyayya ke samar da ita ba kuɗi ko Nasaba ba.
Ga ɗakuna can da mijin Ayush zai iya affording, if she really love him, she will be ever happy to live in it" turancin da ya ƙarasa maganarsa da ita ya sanyaya masu guiwa, saboda turanci ne irin na sarauniyar Ingila, duk a tunaninsu bai taɓa zuwa aji ba dole jin California ya San ba ƙaramar yarinya za a kawo ahlinsa ba. Jiki a sanyaye Hajiya haske ta ce
"Baba ba mun raina bane, ganin kayan daidai wancan ginin da Saifullah ya nuna ne, garanta kaɗai ma ya isa ya ɗauke duka ɗakunan komi ashirin da huɗu ne" Tace cikin sanyin murya da fariya.
Dariya Baban Sasa yayi ya ce "Ana iya siyarwa a ba amarya ta ja jari, tunda dai kun ga irin gidan da ta shigo" bai sake faɗin komi ba su ma suka ɗan ƙara zama na yan mintuna su ka miƙe.
Daidai gwargwado Saif ya zuba kayan zamani sasan, ɗakuna biyu ne da kitchen da store da bayuka a kowane ɗaki.
Nan dai suka shirya kayan da suka iya shiga ciki, sosai waje yayi kyau amma sun ji takaici da kayansu da dama basu samu waje ba.
Motar ta da suka zo mata da ita su ka ajiye a wajen adana motoci duk da dai ba an tanadar da wajen don haka bane amma ahlin gidan anan su ke ajiyewa.
Ko da suka shiga sashin su Hajiya, sakin maganganu kawai su ka dinga yi, matan gida aka samu chapter badawa.
***
Bukukuwa sosai na gani na faɗa aka yi a ɓangaren su Ayush. Ango da Amarya sun yi kyau sosai, yan mujallu sun hallara sun ɗauki hotuna a duk wani event da aka yi.
Faɗin farin cikin da ma'auratan su ka shiga ba zai misaltu ba.
Ranar Lahadi da ƙarfe tara da rabi na safe aka ɗaura auren Saifullah da Aisha, ɗumbin masu kudin Nijeriya da kasashen da ake maƙotaka duk sun halarta. Bayan ɗaurin Aure aka ɗauko zuga zuwa gidan Amarya.
Tafiyar Awa uku ya kawo su gidan Jamoh tun daga ƙofar gidan mahaifin Ayush, nan ma yan uwanta da kawayenta su ka shiga yaɓa magana. Duk kokarin Ahlin gidan Jamoh bai birge su ba, suna miƙa ta suka nemi hanyar tafiya, faɗi suke
"Allah ya baki ladan zaman talauci, gida a ƙuntace, ina aka samu wajen zama a wajen nan balle ki miƙa ƙafa" haka suka dinga faɗi har su ka fuce su ka barta cikin ƙunci.
Kamar yanda su ka tsara da Saifu ana jibi biki cewa kwana bakwai na amarcin su a hotel za su yi Don ba za su iya da takuran gidan gandu ba.
Ana idar da isha'i