Showing 33001 words to 36000 words out of 98809 words

Chapter 12 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

da na ke ciki, Allah kar ka jarrabe ni da wannan masifar bayan ka sanya tazara mafi girma a tsakanina da wannan bawa na ka, ya Allah.....ya Allah...ya Allah..... ya Allah......"


Kuka ne ya ci karfin ta, ta kasa magana sai shasshekar.


****
Yanda Amatullah ke cikin halin ha'ulai, haka Saifullahi ke cikin halin damuwa, tun barowar shi Zaria babu abinda ya ke tunani face kyakkywar surar Amatullah, haka zalika ko ya rufe idanun sa da niyar runtsawa ita ɗin dai ya ke gani. Abin takaicin shi shine wai kamar shi Saifullahi duk surar da ya sha gani birjik a titin Allah a kasar turai ya rasa wanda zai gigita shi wai sai na bagidajiya, yar kauye kamar Amatullah!!


Zaune ya ke Airport ya na jiran isowar jirgin da zai tashi da su zuwa Lagos, dake an sami delay na wajan minti talatin kafin isowar jirgin. Idanun shi lumshe yayinda ya kifa fuskar sa cikin tafikan hannun sa, yayi kusan minti goma cikin wannan halin kafin daga bisani ya dago yana mai zaro wayar shi daga cikin aljihun wandan sa, kai tsaye wajan hotuna ya shiga in da ya lalubo hoton budurwarsa Aysha Ayuba Daneji, wacce aka fi sani da Ayush.


Ayush 'yar Kano ce, irin 'yan matan nan ne marasa kamun kai, da tarbiya, Amma idan wajan wayewa, ado, matse jiki da fidda tsaraici idan aka same ta sai dai a shafa fatiha. Kasancewar ta ɗiyar hamshakin mai kudi, primary school kaɗai ta yi a Nigeria, hatta secondary turai ta yi, saboda haka za a iya Kiran ta rainon turawa. Tare su ke masters da Saifullahi, duk duniya ta ce babu wanda yayi mata sai Saifullahi, shi kuwa dama faɗuwa ce ta zo ma sa daidai da zama, domin kuwa burin shi ne auran wayayyiyar mace.


A shekaru Ayush ta girmewa Amatullah, saɓanin Amatullah ita fara ce tas, duk da dai ta kan ƙara da na kanti. In aka dauke fari da wayewa babu abin da za ta nunawa Amatullah.


Idanun sa kan hotan Ayush, wanda take sanye cikin kananan kaya riga da wando, kan nan ba dankwali an zubo da gashi har kyeya. Ajiyar zuciya ya saki, a zahiri ya furta


"Me zan yi da wannan bagidajiyar when I've someone like you? Haba ga mace nan har mace zuciya ta za ta addabe ni da wata yar kauye mamalam!"


Jin ana sanarwar jirgin su zai fara boarding ya sanya shi tashi da sauri ya na mai tura wayar cikin aljihu.
[2/17, 9:31 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA GOMA SHA BIYAR


Allah ya kai su Dee Yola lafiya, kasancewar da daddare su ka isa, Nan family house din mamacin aka sauka, in da su ka tarar da yan uwa da abokan arziki suna tsimayin isowar na su. Tun a daren ranar Dee da ƴan uwan mamacin su ka fara shirye-shirye bikin birne gawar, wanda za a yi nan da kwana goma sha biyu zuwa sha uku. Kamar yanda kwanaki su ka yiwa Dee tsawo, haka su yi ma Amatullah, kwana bakwai da aka ba su hutun midsemester ɗin ya zame mu su kamar shekara bakwai, a ɓangaran Dee; rashin Amatullah da mijin Mahaifiyar ta shi ba karamin karamin girgiza shi ya yi ba, gashi shirye shiryen birne gawar kaɗai ya isa ya gajiyar da ɗan adam. A ce an rasa mutum amma sai an yi gagarumin biki ranar da za a rufe shi? Shi kam Dee wannan na ɗaya daga cikin al'adar kiristanci da sam bai ma sa ba.


Amatullah kuwa a nata ɓangaran yanda matan gidan kan kira ta da Amarya duk da tana hango isgilanci a sautinsu yayin da su ke ambato mata wannan sunan ya hana ta sukuni, Ba wai isgilancin ke ƙona mata rai ba, jin da take hakan kamar danganta ta da saif ne ya fi komi ɓata mata rai.


Angon na ta kuwa tun da ya sa kafa ya tafi babu wanda ya sake jin ɗuriyar shi, hatta Baba Anas yayi kokarin samun shi a waya, amma abin ya gagara, shi kuma bai kira ya shaida mu su isar sa Russia ba.


Ranar Laraba da safe ta tashi da matsanancin tsanar gidan, tunanin wajen zuwa ta ke yi don ta samu sauyin iska.


"Zulaikha"


Kawai taji ɓarin zuciyarta ta ambato mata hakan ya sanya ta sakin murmushi.


Kamar yadda ya ke al'ada garesu gaida iyayensu bayan sun idar da azkar hakan ta tashi ta yi, haka kuma kamar yadda mahaifiyarta ta umurce ta duk ta shiga ɗakin Hajiya ta kan ɗan ɓata lokaci, don ko jiya sai da ta kama mata ninkin kaya sannan ta fito.


Cikin sa'a ta samu Baba Anas zaune yana sauraron sashin hausa na radiyon BBC, gaishe su tayi a ladabce sannan ta yi shiru tana ƙara sunkuyar da kai.


"Ƴar Baba Anas da magana a bakin nan"


Baba Anas ya ce cikin sakin murmushi. Ƙara sunkuyar da kai ta yi. Harara Hajiya ke watsa mata tana zagin ta a zuciya, ita da Amatullah za ta hakura da shigowa ɗakin ta da ya fiye mata komai.


"Ehmm! Amatullah Ina saurarenki" ya ce yana mai rage sautin radiyon sa don ya ji me take tafe da shi.


"Baba don Allah izininka nake nema, ina son in duba ƙawata Zulaikha" tace gaban ta na faɗuwa, tsoro bai sake cika ta ba sai da ta ɗan ɗaga kai ta kallo sashin Hajiya ta ga harar da ta watso mata, ta ke ta shiga da na sanin tambaya tun farko. Gani ta yi shine mahaifin mijinta a tunanin ta zai iya bata izini makwafin mijin nata.


"Allah ya dawo da ke lafiya, kar dai ki kai almuru a waje" yace yana murmushi.


"Na gode Allah ya kara girma da lafiya" ta ce cikin farin ciki.


"Aameen Ƴar Baba" yace Shima cikin farin ciki.


Da haka ta tafi ɗakin mahaifiyarta cikin farin ciki, jinta take zaman ta a gidan Jamoh kamar wacce ke zaune a gidan maza.


Da wannan farin cikin ta iske mahaifiyarta ta faɗi mata yanda su ka yi da Baba Anas, tana kallon yadda murmushin fuskar mahaifiyarta ya ke dusashewa a hankali.


"Yanzu ke sai ki ɗauki jiki ki fita tsigau tsigau se kace wacce ba ta da mafaɗa, ko da can kan ki yi aure haka kike fita kamar baƙar Leda balle yanzu da aure ke kanki? Mijinki kawai zai baki izini in bari ki fita, sakarai mara kishin kai" Gwaggo ta faɗi tana tashi daga wajen.


'Oh ni mai na yi na laifi yanzu da Gwaggo ta ke kausasa halshe akai na. Allah na tuba ka yafe ni ba zan sake ba' ta ce cikin ranta tana mai tausayin kanta.


Wayarta ta ɗauko ta kunna cike da addu'ar ganin saƙo daga Dee, maimakon nashi sai na mahaifinta ta gani wanda ya wuce Abuja a safiyar Litini, nasiha ce da addu'a haɗe da fatan alkhairi gareta. Tayi murna sosai, kaunar mahaifinta na ƙara cika ta, gani take wacce ta rasa uban da zai bata kariya da tallafi a duk halin da za ta shiga lallai ta yi rashin majingini babba.


Ba ta fita daga akwatin tura saƙo ba ta lalubo lambar zulaikha ta aika mata da sako, daga nan ɗauko littafin 'the end of the world' na Dr. Muhammad Abdulrahman Al-arifi ta fara dubawa cikin natsuwa, tsoron Allah na ƙara ratsa ta. Ba ita ta tashi ba sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya na rana in da ta tashi ta je taya mahaifiyar ta ɗaura sanwar abincin rana.


***


Zulaikha ba ta ga saƙon ba sai kusan ƙarfe goma sha biyu, "An ɗaura aure na da yaya Saifullah ranar Asabar bayan sallar asuba" ta karanta ta ƙara karantawa tana mai ƙaryatawa.


Numbar Amatullah ta latsa kira ya ci ringing har ya tsinke ba tare da an ɗaga ba. Haka ta dinga kira ganin ba a ɗaga bane yasa ta kira maman Jaafar.


"Zully ke ce yau da kira" tace tana ɗagawa. Su kan yi ma zulaikha tsiyar ba ta kiran waya walau ta turo sms ko kuma ta ishe mutum da flashing.


"Yoh maman Jaafar ai dole na kira yanzu, kinji an ɗaura auren Amatullah wai" tace cikin mamaki da rashin yarda.

"Aure kuma, sai kace ƴar takarda" maman jaafar tace cikin ƙin yarda.


"Yanzu na ga text ɗinta, na kira kuma bata ɗaga ba, amma Daman akwai alkawarin aurenta da Yaya Saifullah ɗin" Zulaikha ta faɗi tana son ta haska ma maman Jaafar yiwuwan auren.


"Allah sarki Dee Yusuf kuma kin san ranar Juma'a na kwatanta masa gidansu, yanzu shike nan ba rabon sa bane" maman jaafar tace cikin tausayawa don ba za ta mance tsantsan son Amatullah da ta hango a idanunsa ba ranar..


"Haba! Ai in har Dee ya isa gidan su Amatullah toh tsaf Baban Sasa zai sa a ɗaura auren nan. Ai jin auren nan yake kamar in ba ayi ba ya rasa wani sashi na jin dadin duniyar sa ne" Nan zulaikha dai ta ba maman jaafar labarin da ta sani a takaice.


Tayi mamaki kwarai musamman da ta ji Dee Yusuf ba musulmi bane. Da ga baya su ka yi sallama akan sai sun ji daga Amatullah.


****
Ana sauran kwana biyu bikin birne mijin mahaifiyar Dee aka koma makaranta. Da sassafe Amatullah ta hada nata ya na ta cike da farin cikin za ta bar gidan ta huta da habaice habaice. Kafin ta ta tafi sai da Gwaggo ta zaunar da ita ta mata fada sosai, irin wannan fadan mai shiga jiki.


Har sun yi sallama ta dau jakar ta Gwaggo ta dakatar da ita ta na mai fad'in
"Amatullah?"


"Na'am Gwaggo"


Amatullah ta amsa jiki a sanyaye.


"Na yarda da ke tun kafin nauyin aure ya hau kan ki, bare yanzu, dan Allah ki tsare mutuncin ki, dan Allah Amatullah, kin dai san ke matar aure ce, wannan yaran da na ji ana magana akan shi......"


"Gwaggo....."


Amatullah ta katse ta yayinda idunun ta ke fidda kwalla. Kana ta kara fadin
"Gwaggo kin ce kin yarda da ni....."


Tashi tsaye ta yi ta zo gaban Amatullah, ga mamakin Amatullah sai ga Gwaggo ta ruko hannayen ta biyu, cikin sassanyar murya ta furta


" Na yarda da ke ɗiyata, Amma zuciya ba ta da kashi, ba na so in ji ance ko sannu ta haɗa ki da wannan yaron, dan Allah Amatullah ki rufa mana asiri, kar ki ga kamar ban damu da lamarin ki ba, kawai ina kawaici ne"


Kai Amatullah sannan ta ce


"Na mi ki alkawarin cigaba kare mutunci na da hakkin addinina kamar yanda na saba Gwaggo"


Cikin jin dadi Gwaggo ta rakota har kofar falo, sannan ta umarce ta da ta je ta yiwa Hajiyar Saifullahi sallama.


Ta ci sa'a ba ta sami Hajiya ba, Baba Anas ma gun Baban Sasa ta same shi tare da su Baba Zubairu. Nan duka su ka mata nasiha tare da sa albarka, Baba Anas ne ya bata kudi a cewar shi yanzu dole ya na wakiltar Saifullahi, gashi babu yawa. zuciyar ta cike da farin cikin addu'oi da ta sha daga gare su ta wuce makaranta.


Tun da ta sa kafar ta cikin makarantar gaban ta ke faduwa ba dan komai ba dan Dee Yusuf da ta ke fargaban gani, da ta hangi namiji ya doso ta sai ta yi saurin kau da kai, kai har gani ta ke kamar ma gizo ya ke mata.


Kirjin ta na dukan uku uku yayinda ta ke karanta 'Lailaha illaanta subhanaka inni kuntu minil zalumin'. Ba ita samu kwanciyar hankali ba sai da ta ganta cikin hostel. Kaf ɗakin ita ta riga kowa kowa dawowa. Mayafi da jaka ta aje ta shiga gyaran daki..
[2/20, 8:39 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA GOMA SHA SHIDA


Tun tana tsumayen Zulaikha har ta tabbatar da ba za ta dawo a ranar ba, hakan ya sanya ta zama sukuku kamar raguwar ciwo, duk yanda ta so kar ta zurfafa tunani ta gaza hakan ya sa ta ɗauki littafin da ta fi so watau Don't be Sad ta fara bibiyar hikimomi na samun nagartaccen kwanciyar hankali,da haka bacci ɓarawo ya sace ta.


Washegari Monday basu da aji sai ƙarfe tara na safe, hakan ya sanya ta ɗaukan lokacin ta wajen shiryawa. Takwas da rabi daidai ta fita daga hostel. Sauri take don ba ta fatan ganin Dee. Ta kai daidai biological science da za ta bi ta je chemistry department in da za su yi ajin ta jiyo sallama.


Ƙara sauri ta yi don ba ta da niyyar tsayawa duk da sautin muryar kamar wanda ta sani.


"Anty Amatullah an tashi lafiya" ya faɗi hakan ya sanya mata juyawa, tana ganin fuskarsa ta juya cikin sauri ta cigaba da tafiya. Ba za ta ce ga yadda aka yi yazo gabanta ba.


"Don Allah kiyi hakuri, wallahi na yi tunanin ya faɗa miki ne shi ya sa na kaiki don Allah ki gafarce ni" yace cikin sanyin murya.


"Babu laifin da ka yi min Yaya Hamza, ban tsaya bane saboda guje ma keta haddin aure. Babu sauran Alaƙa tsakanina da Dee. Ina masa fatan Alkhairi" tace tana mai jan jikinta ganin Taran na gabatowa.


"ban gane haddin Aure ba, ai ba a sanin maci tuwa" yace yana dariya.


"wannan miyar ta daɗe da ƙarewa. Yau kwana goma kenan da ɗaura min aure, David bai faɗa maka ba?" tace tana ƙirƙiro farin ciki.


"Kinga yau kwana goma kenan da mutuwar mahaifin Dee Yusuf. Kice double rashi yayi" ya faɗa cike da Alhini tare da tausayin amininsa.


"Allahu Akbar, Allah ya jikan musulmai, su kuma Allah ya basu hakurin rashi. Bari in je kar in latti" tace tana barin sa tsaye.
Mamaki ya cika shi ainun, duk ya cika da tsarguwa akan tashin hankalin da ya gani a idon Dee.


Amatullah kuwa tana gama magana da shi ta juya ta isa aji cikin sauri, ta shiga ko hutawa ba ta yi ba malamin ya shigo, karatun rabi da rabi ta fahimta saboda tsilla-tsilla da zuciyarta ke mata akan halin da Dee Yusuf ke ciki da istigfari da take yi.


Sai da azahar ta samu ganin su zulaikha wainda su ka zo latti.


"Amarya!" su ka haɗe bakin faɗi. Dariya ta bi su da shi wanda ko laɓɓanta bai wuce ba.


Nan su ka zauna suna mata tambayoyi kamar wacce ke gaban kuliya. Wasu ta amsa musu wasu ta sa musu dariya kawai.


"Kinga Amatullah ki kwantar da hankalinki, zan kawo miki littafan hausa ki karanta saboda ki san yanda za ki tafiyar da Megida Saifullah. Duk taƙamarsa da ya ɗanɗana zumarki dole ya so ki, dole yai marmari ki" maman Jaafar tace tana mai dulmiyar da Amatullah cikin duhu don ita ba ta san wani abu zuma ba, ita Sam ba ta damuwa da sanin abubuwan da su ka shafi wannan, ita dai a barta da karanta littafan addini sun fi komi sa ta nishaɗi. Haka dai Maman Jafar ta shiga yi mata bayani akan yanda za ta sace zuciyar angon na ta, ita kuwa Amatullah jin ta take kawai, gani ta ke soyayya tsakanin ta da Saifullahi abu ne mara yiyuwa. Sai dai biyayyar aure.


***


Ranar talata ya kama ranar bikin birne mamacin ƴan uwa da abokan arziki sun yi dandazo a Coci, duka sanye cikin bakaken kaya mazan su da matan su.


Gawar mamaci aje gaban jama'a cikin akwatin da aka kayata da furanni. An bude taron ne da yiwa mamaci addu'a bisa ga al'adar kiristanci na raye-raye, bayan an gama minister ya ba da taikaiceccen jawabi akan rayuwa da mutuwa, haka kuma aka bawa ɗan uwan sa mafi kusa da shi damar jawabi akan halayyar mamaci da abinda ya bari na iyali.
Tun da aka fara Dee bai bar gefen mahaifiyar shi ba, wacce in ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanun ta. Minister ne ya bada taikaiceccen lokaci ga jama'a domin mika ta'aziyan su ga iyalan mamacin, kafin aka dauki gawar zuwa makabarta su na mai cashewa yayinda kiɗa da waƙa ke tashi, da ya ke babu laifi mamacin mai jama'a ne, na kasa da na mota haka aka dunguma zuwa makabarta.


Hankalin mahaifiyar Dee bai tashi ba sai da ta ga an ɗauki akwati an sa cikin rami, nan ta ƙwalla ihu ta na mai kiran sunan mamaci yayinda da ta ke kokarin shiga ramin, da kyar Dee tare da taimakon kannen mahaifiyar ta shi su ka fitar da ita daga makabartar.


Babu laifi an cashe, an kuma ci an koshi domin kuwa gangarumin biki aka yi a ranar, idan aka ɗauke Dee da mahaifiyar sa, da kannan sa biyu babu wanda bai cashe ba. Ranar haka aka kwana ana raye raye da ciye ciye family house ɗin gidan mamacin.


***


Bayan kwana uku Dee zaune a falo, hannun sa biyu bisa kuncin sa ya rasa abin da ke masa daɗi a duniya, idan akwai tunanin da baya so ya bi bayan na komawar shi makaranta ba, ba dan komai ba sai dan Amatullah, Sam ba ya fatan sake saka ta a Ido alhalin ta na matar wani, tsananin kishi da bakin cikin auren ta ya fi komai damun shi a halin yanzu.


Babban falo ne mai dauke da manya manyan kujeru, da ya ke family din mamacin babu laifi suna da arziki. Bai ji shigowar ta ba, kamshin turarenta ne ya bakunci hancin shi. Dab da shi ta zauna kugunta na gogan na shi yayin da ta ɗaura hannu bisa kafaɗar shi ta na mai fadin


"Dee is owk na, ka fa tuna sanda Dady ya mutu kai ne kan gaba wajan kula da ni, you told me Dady will not be happy if I keep crying.......Dee"


"I'm not crying Mimi"


Cewar Dee yayinda ya dago ya na duban cousin ɗin ta shi da ya kira Mimi. Mimi diyar Yayan mamacin ce, ma'ana uncle din Dee da ya mutu watanni uku da su ka wuce. Yar matashiyar buduwar ce mai kimanin shekara goma sha bakwai a duniya, irin wannan siraran da ake danganta su da model, mashaAllah idan kyau ne ko cikin larabawa ta shiga ba a mata kushe ba, Mimi kamar dawisu ga kyau ga ado. Kusan yanayin farin ta daya da Dee,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login