Showing 60001 words to 63000 words out of 98809 words

Chapter 21 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ga yanda su ka yi da Saifullah ba balle wani ya zarge shi.
"Aure mijinta zai ƙara, yarinyar nan ta amince ta yi tawakalli na zan laminta ba a fake da taron suna a zuga ta" shine hujjar da ya bayar wanda sosai yaransa maza su ka yi na'am da hakan.


Har gida Baba Salihu ya je ya samu Amatullah ya mata nasiha sosai, ya nuna mata rayuwar ma gaba ɗayansa guda nawa ne, da suna ko babu suna abin da ya ke rabon ta ba zai wuce ta ba.


"Baabaa!!!" tace tana mai son fadi masa halin da ta shiga lokacin rainon cikin ta da halin da suke ciki a yanzu. Damuwar da ta hango a kwayar idanunsa ya sanya ta faɗin.


"Next week za mu koma makaranta, ina jin tsoro kar na kasa making result ɗina" kallon ta yayi a matsayinsa na ɗan jarida yana son ya fassara ma'anar abin da ta ce.


Saifullah da ke maƙe bakin ƙofa ma saukar da ajiyar zuciya yayi da ya ji abin da ta faɗi, kafin Baba Salihu ya kai ga cewa komi ya shiga falon haɗi da sallama. Sai da su ka gaisa da Baba Salihu sannan ya kalli Amatullah ya ce


"Baba yarinyar nan da ita ce auta ban san ya za ta yi ba, kin wani tasa Baba kina hawaye"


Dariya Baba Salihu yayi ya ce
"Wai tsoron boko take yi kuma sai kace kanta farau boko da goyo. Ni dai abin da zan ce miki shine ki sani gatanki ne bokon nan, kar ki ji tsoro ki dage ki fauwala ma Allah komi sannan ki yi addu'a. In an buɗe portal ki cire transaction ID zan sa a ƙarasa miki registration, Allah barshi sai ki koma in an fara lectures." yace zuciyar sa cike da tausayin ƴarsa.


Nan dai su ka cigaba da hira su ukun, kafin da ga bisani Baba Salihu ya tashi ya tafi ba don ya so ba.


***
Tun bayan da aka yi kwana bakwai, Saifullah ya sallami innarsa Amatullah ke yin komi, tun daga yi ma jariri wanka har zuwa yin nata wankan. Ga shi dinkin ta sam ko hanyar warkewa bai dauka ba, ko da ta yiwa Gwaggo korafi sai cewa ta yi tsabagen raki ne irin na Amatullah, dama Inna Jamila ta ce ba ta san shiga ruwan zafi to ina kuwa din ki zai warke? Lalle ta dage da shiga ruwan zafi.


Ana cikin haka wayarta ta lalace, gaba ɗaya sai ta koma kurma, ba ta jin kowa babu mai jin ta, ga zamansu ba laifi yau lafiya gobe akasin haka.


Kamar yadda baba Salihu yayi alkawari shi ya tsaya ta kammala registration sannan ya ɗauki dubu goma yace ta rike ko za ta bukaci wani abu.


Sai kwana uku da fara lectures ta koma makaranta, duk dai har lokacin ta kan ji dinkin da aka mata ya na sukar ta, idan ya tashi mata ciwo har kwakwalwar kan ta take ji, ga wani dan hamami hamami da ta kan ji ya na tashi duk sanda ta ɗan bude wajen.


Ranar da ta fara zuwa ranar lectures din Dr. Muhammad Zayyad ne ta shiga kusan a makare ga goyo kuma.
Kujerar da ke kusa da ita ta zauna inda wacce ke zaune ta matsa mata cikin fara'a.
Karatu yake musu cikin gwaninta da iya koyarwa a fannin clinical pharmacy. Sosai ta ke jin daɗin karatun, cikin rahamar Allah har ya gama awa biyunsa Emjay bai tashi ba.


Bayan fitarsa ne su ka gaisa da wacce ke kusa da ita.
"Great pharmacist ce yau a ajinmu" tace cikin fara'a
"suna na Hannah Dawud ana ce min mimi, tun da nazo 100level nake son zama da ke, like sosai kike birge ni, ba ruwanki da gayu always in hijab kuma first class student" tace cikin tsantsan farin ciki.


"mimi kenan, to tell you nothing is permanent in life yau gani repeating 300lvl. Anyway it's nice meeting you" tace tana miƙa mata hannu.


Nan Amatullah ta faɗi mata courses din da za ta yi, mimi ta bata update akan su.
"in ba za ki damu ba, let's be friends please, na san circumstances su ka yi leading to carry over ɗinki, Kinga ni Christian ce daga Adamawa, amma family ɗinmu duk mix ne, I hope ba zaki damu ba" ta ce cikin fara'a, yayinda ta ji mummunar faduwan gaba jin ta ambaci ita christain ce, kuma daga Adamawa.


Dee Yusuf ne ya faɗo mata, yayinda ta ke kallonta tana mamakin kyanta da gayunta haɗe kuma da surutun Mimi, amma ace christain ce, wannan asara har ina.


Tun daga ranar gaba ɗaya harkan karatu tare su ke yi, su na ba juna assignment su na ma juna bayani. Mimi ta bata shawaran samun cikin masu shara da zata kula mata da Emjay( sunan da take kiran babyn ta kenan) sai dai in sun samu sarari ta je ta bashi nono.


Duk wanda ya san Mimi a gidansu da hostel ya san Maman Emjay ko a labari ko a fuska. Haka Amatullah bata kyashin kiranta da mummyn Emjay saboda kulawar da mimi ke bashi.


Abin da ta lura da shi shi ne shakuwar da ke tsakanin Mimi da cousin ɗin ta, wanda kullum ba ta da magana sai na shi, bini bini ta kira shi, ko kuma ta ce da Amatulah ta raka ta office din shi nan bayansu a faculty of medicine da yake ta ce da ita assistant lecturer ne, wannan session din ya fara koyarwa. Amma hakan nan Amatulah ta ji ba ta son raka ta, har Mimi ta gaji ta daina mata tayi, a cewar ta kila Oga ya hana ki zuwa office din lecturers, ciki har cousin din kawar ki, ita kuwa ta bi ta eh ba tare da ta taɓa tunanin jin sunan cousin din na Mami ba, ta kan tsoka ne ta da Mimi cousin.


Tsakanin ta da su Zulaikha kuwa sai dai idan ta shiga hostel ko sun haɗu wajen sallah dan kuwa yanzu sun zama seniors din ta.


****


Dinki ta ba karamin damun ta ya ke ba, Amma duk sanda ta tunkari Saifullahi da maganar sai ya ce tsabagen gudun kar ya koma mata ne, ta kwantar da hankalin ta shi kan shi ba ta bashi sha'awa yanzu, dan kuwa ba dan ba dan ba sai ya ce ya kan ji dan wari wari na fita daga jikin ta, in dai haka ake jego Allah wadar jego irin na ta.


Ranar haka ta sha kuka har ta yi mai isar ta, duk tsafta da kula irin na ta Saifullahi ya ce ta na ɗan wari wari, duk da dai ita kan ta ta san ba daidai ta ke ba.


Washagari ya kama satin da za tafi mid semester, Amatullah na zaune da Mimi suna bitar wani course dinsu na pharmacology da za su yi test ranar Juma'a da za a tafi midsemester.


"Maman Emjay me ke faruwa ne? Na ganki kwana biyu wata iri, yau idanun ki a kumbure" Mimi ta tambaya cike da damuwa.
"wallahi mummyn Emjay, ina fama da ciwo sosai a ƙasa na, tun bayan haihuwa da aka min dinki ban sake jin dadin gurin ba, har ruwa yake yi, I think I got infected, idan ya tashi min ciwo har tsakiyar kai na, yau har jiri na ke ji" tace cikin hawayen da kamar dama suna jiran izinin fitowa.


"kin kula yana wari kuwa, tun last week na ji, amma ina ta neman hanyar faɗa miki, me Dadyn Emjay yace" mimi ta faɗi cikin kulawa.


"Mimi me zai ce, aurensa saura wata biyu, gaba ɗaya hankalinsa na wajen ne, labari na mai tsawo ne wata rana zan baki" tace tana murmushin takaici.


"tashi mu tafi asibiti, ki na ɗiya mace be kamata ki yi wasa da abu irin haka ba, darajar ki ne fa, yanzu haka za ki zauna har a kawo mi ki kishiya jikin ki da wannan ciwo haka? Ai ya zama ciwo Maman Emjay, tashi mu tafi gaskiya......"


Duk da Amatulah ta ɗan girme mata, yau sai Mimi ta zama kamar ita ce Yaya gurin ta. Amatullah na mai raunana idanu ta ce
"Ki na gani za su karɓe mu? Har biyu fa Mimi?"


"Kar ki da mu, ai nan shika za mu ce, akwai wata Anty na da ke aiki wajan, na san za ta iya taimaka mana"


Cikin jin dadin yanda Mimi ta damu ya sanya Amatullah jin dadi, ga ta dai ahlil kitab amma sai zuciya mai kyau kamar 'Dee Yusuf...'


Karo na hudu da ya kara faɗowa cikin ran ta kenan, ta na mai kokarin cire shi daga cikin zuciyar ta, tare da kwabar zuciyar na ta ta tashi, su ka ɗauki hanyar fita daga ajin ta na mai yiwa Mimi godiya.
Wata coursemeta din su ce su ka samu ta rage mu su hanya. Kamar yanda Mimi ta faɗa Anty din ta ce ta taimaka su ka ga wata Gynecologist.


Ko da Amatulah ta bude mata ga halin da ta ke ciki kuka ne kawai ba ta yi ba in da ta rufe Amatullah da faɗa sosai. Ya ta na ƴa mace za ta bari ta lalace haka? Shin ina iyayan ta su ke?


Kuka Amatullah ta saka mata dan kuwa dai rasa da mai za ta ji ta yi, ciwon da ta ke ji ko kuwa masifar gynecologist da ake kira Dr Hajara. Sai ta karaci masifar ta har ita kan ta Antyn Mimi da ba ta ji daɗin halin da Amatulah ke ciki ba ta saka baki, dan kuwa Dr Hajara cewa ta yi ba za ta iya taba Amatullah ba.


Dr Hajara na mai kallan dinkin Amatullah da har kore kore yayi tsabagen rashin kula ta ja tsaki a karo na uku kafin ta ce


"I'm doing everything a fresh, kankare shi zan yi na sake buda ta, a sake mata wani dinkin, wajan is infected, Allah ya sa bai zama sepsis ba, fatana dai shi ne ace iya ka dinkin infection din ya tsaya!"


Ta na gama faɗin haka ta tashi ta fice daga office din. Antyn Mimi na mai taɓa hannun Amatullah cikin bata karfin gwiwa dan kuwa gaba daya hankalin ta tashe ya ke. Mimi wacce ke rike da babyn Amatullah Antyn ta kira, in da ta ke shaida mata halin da ake. Mimi na mai duban Amatullah wacce idanun ta ya cika da hawaye ta ce


"You will be fine Amatullah, don't worry, ga waya ta ki kira Dadyn Emjay ki fada ma sa halin da ake ciki"


Hannun ta na rawa ta karbi wayar a hannun Mimi, ta kira number Saifullahi har sau wajan biyar amma bai ɗaga ba. Murya sanyaye ta ce


"Mimi ya ki dagawa...."


"Toh ko Momcy za ki kira?"


Cewar Mimi cike da damuwa. Amatullah na mai girgiza kai te ce


"Ah ah, kar na ɗagawa Gwaggo hankali, dama shi din dai zan iya faɗa ma, amma tunda bai daga ba, a yi min kawai na huta da wannan masifar"


Da wannan Mimi ta shaidawa Antyn na ta, da izinin Amatullah tare da ƙwarin gwiwar Mimi da Antyn ta, wajan karfe uku aka shigar da Amatulah daki na musamman da aka ware domin aiki da ya shafi mata.


Allurar kashe wajan da kuma girman dakin bai hana Mimi jiyo ihun salatin Amatullah ba, tun ta na iya jurewa har ta kasa, tashi ta yi tana da jijjiga Emjay da ya ɗan fara koke koken yunwa, su ka fice can waje. Sai wajan biyar da rabi aka gama Antyn Mimi ce ta kira ta in da ta ke shaida mata an ci sa'a infection din be shiga cikin tsokar ta ba. Cike da fargaba Mimi ta tambaya ko za ta iya ganin Amatullah.


"Sosai ma kuwa, Nan da one hour ma da ta ji dan dama dama za ta iya tafiya, Amma gaskiya ki jawa kawar ki kunne ta bi duk dokokin da Dr Hajara ta ba ta in dai ta na so ta sami sauki"


Da wannan Mimi ta sami ganin Amatullah da har lokacin ba ta dawo cikin hayyacin ta ba. Mimi ce ta kara kiran number Saifullahi amma har lokacin bai dauka ba, sai kawai ta tura ma sa sako kamar haka


"Hello Dady Emjay, his mom, your wife Amatullah is very sick and in the hospital, kindly call me back it's urgent"


Ta tura ma sa, har tsahon minti 30 shiru, dan haka kawai sai ta kira cousin din ta, ta roke shi alfarmar ya zo ya same ta hospital. Da ya ke ya ji batun asibiti sai yayi tunanin Mimi ce ba lafiya, dan haka ba tare da bata lokaci ba ya garzaya asibitin.


Mimi ce ta taro shi daga in da yayi parking, dauke da Emjay wanda ya sha kuka ya gaji har bacci ya sace shi kwance bisa kafadar ta, suna tafe ta ke shaida masa halin da Amatulah ke ciki, ta kare da


"Har yanzu dai mijin na ta bai kira ko ya min reply ba, shi ya sa ma na kira ka ko za ka taimaka ka bani 15k dan biya kudin asibitin, sai mu kai ta gida I take God beg you..."


Bakin kofar ɗakin da Amatulah ke kwance su ka tsaya, ya na mai kallan ta ya ce
"Mimi rigima, like how can you get your self involved in something like this? Mijin ta ba ya daga waya ba sai ta hakura ta je gida ta faɗa ma sa..."


"Believe me, it was an emergency, please ka taimaka....."
Ta fada ta na mai marairace masa


Cikin dariya ya lakace hanci ta tare da fadin
"As usual dole na yi yanda ki ke so Mimi, you always have that power over me, wanna shi ne babyn na ta ke nan"


Ya na maganar ne yayinda ya ke kai duban sa ga fuskar yaran a karo na farko, wani iri mummanar faduwar gaba yaji yayinda yayi ido hudu da Emjay.
"Eh Emjay kenan, yayi kuka ya gaji ya fara bacci"


Hannu ya sa ya shafi fuskar Emjay, yayinda kamanin ta ke dawowa zuciyar sa
"Ya sunan ta ne? Maman Emjay?"


Zuciya daya Mimi ta ce
"Sunan ta......."


"David dantawaye idanun ka kenan?"
Antyn Mimi ce ta katseta, yayinda Dee Yusuf ya ja ajiyar zuciya ya na mai duban Antyn ta su ya ke murmushi, ya ba ta amsa da


"Ni na isa Anty, ai tuwo tuwo ne ba a sake ma sa suna Mama na"


"Ka dai yi bayani, yaushe rabon da na saka ka a ido na? Ko ka dena iyayen da mu ne?"


"Kai na bisa wuya na Anty, ai ban isa ba, aikin ne sai a hankali"


Nan ya gaishe ta cike da girmamawa, kafin ta shedawa Mimi kawar ta fa ta dan sami dama dama, za su iya tafiya gida.


Dee Yusuf da tun ganin Emjay gaban sa ke faduwa tuni yayi gaba, ya ce da Mimi su same shi a mota bayan ya ciri kudin da Mimi ta tambaye shi, naira duba goma shabiyar ya bata.


Sai da ta yi biya komai sannan ta koma gun Amatulah wacce ta tabbatar mata ta na cikin hayyacin ta, za ta iya gane hanyar gida sannan ta sheda mata cousin din ta na mota ya na jiran su.


Hannun Mimi ɗauke da magunguna Amatullah, Daf da magarib, Amatullah na godiya babu adadi, ta na tafiya kamar mai koyan tatata har su ka isa motar Dee Yusuf. Ya na daga zaune bai damu da ya fito daga motar ba su ka yi sallama da Antyn su, bayan mota Mimi ta budewa Amatullah ya zauna sannan ta zaga dauke da Emjay ta zauna gaban mota. Sai da ta zauna ta ce


"Maman Emjay yau dai ga cousin dina da ki ke min tsaya akan shi, Dee meet Maman Emjay"


Duk radadin da ta ke ji bai hana gaban ta faduwa ba jin Mimi ta furta 'Dee' shi kuwa zuciyar shi daya ya juyo ya na fadin
"Sannu Maman Emjey......."


Nan ya tsaya cak yayinda yayi ido biyu da fuskar da ya kasa mancewa a rayuwar sa


"Amatullah"


Ya tsinci bakin sa na furta sunan ta cikin numfashi, Amatullah kuwa gaba ɗaya rudewa ta yi, ba ta taɓa zaton za ta karasa shi a Ido ba, haka kuma ba ta so a ce cikin halin nan da ta ke za ta gan shi ba, ba ta yi shirin sake ganin shi ba.
Shirun da ta ga sun yi suna duban junan su ya sanya Mimi faɗin


"I'm missing something here? Dee dama ka san ta ne?"


Dee na mai jinjina kai, ya juyo ya tada motar, ya ce
"Na san ta sanda ina under graduate, Amatullah......"


Ya fadi sunan ta yayinda ya tada motar su ka fara tafiya, cikin ran sa ya na jin ciwon da ke kasan zuciyar sa da Mimi ta fama masa. Mimi kuwa gyada kai ta ce
"Oh yes guru dole ya san guru duk da dai akwai tazara a tsakanin ku, idan na yi lissafi daidai su na hundred level ka yi graduating ko?"


Kai kawai ya gyada mata, daga nan bai sake furta komai ba domin kuwa gaba ɗaya rasa abin da ke ma sa daɗi, ashe Amatullah ce Maman Emjay din Mimi? Ashe duk wannan azabar da Mimi ta ba shi labarin Maman Emjay ta sha wajan dinki ashe Amatullah ce? To ina mijin ta? Wani irin soko Amatullah ke aure?
Zance da ya ke yi cikin ransa kenan har su ka isa bakin gate din asibitin.




Amatullah kuwa mutuwar zaune ta yi, sai da Mimi ta tambaye ta sau uku sannan ta fahimci da ita Mimi ta ke magana, ta faɗa ma su sunan unguwar da su ke zaune. Cike da tausayawa Mimi ta ce
"Maman Emjay please ki rage damuwa, Allah zai ba ki lafiya kin ji?"


Kai Amatullah ta jinjina mata ba tare da ta iya furta komai ba, Allah Allah ta ke su isa gida ta fita daga motar Dee, ba dan halin da ta ke ciki ba da tuni ta sauka ta gwammaci ko machine ne ta hau, fatan ta Allah ya sa har su ajiye ta kar su hadu da Saifullahi, duk da dai ba ta da tabbacin ya san Dee, ko ya san shi ba lalle ya gane shi ba.


Ganin yanayin Dee ya canza sam Mimi ba ta kawo komai cikin ran ta ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login